[Advertisements⬇️]

GIMBIYA SA'ADIYA CHAPTER 22 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GIMBIYA SA’ADIYA 

CHAPTER 22
Hannunshi na haggu yasa ya cabe kurmar tata, idanuwa yake Iumshewa, yana sakin wasu kananan maganganu dashi kadaiya barma kansa sanin abin da yake fadi. 
Wata katuwar kwalba mai murfiya bude, a take sai kurwar ta canza akala ta nufi cikin kwalbar. Bayan ta shige ciki ya cigaba da surkullenshi baji ba gani. Ya dunkule hannunshi ya furzar da iska daidai cikin kwalbar, hayaki ya mamaye bakinta. Da akaifar hannunshiya hada wani murfi wanda shi kanshi wani tashin hankalin ne. Ya saka ya danne bakin kwalbar 
kafin ya saki dariya da karfi, suka bace bat daga wurin. 
A kasan dakin suka bulla, daga inda yakebullowa a duk sadda su Kursiyya suka zo wurinshi. Wani tafkeken teku ne kasan mai cike da abubuwan firgici da tashin hankali. Kalarruwan tamkarjini, sannan ga wasu kanana kifaye na bultsowa daga ciki bakinsu a bade. Harba kwalbaryayi da karfi ta fada cikin tekun, sannan ya zauna yana mai ci gaba da 
mugayen tsafe«tsafenshi. 
Sai da Zabbau ta bude kofar a hankali ta leka ta ga babu kowa a hanyar sannan ta fice hannunta rike da kaskon turaren wutar da kamshinsa ke tashi sosai saboda zubawar da Kursiyya tayi a ciki. Bayan tayi nisa da dakin Kursiyya ta dora hannu aka ta fasa ihu wanda duk sai daya karade gidan, kowa ya tsorata da ihun. 
Dukkanin al’ummar gidan hankulansu suka karkata da ihun Kursiyya, kowa na son sanin ta 
inda take yo wannan madaukakin kuwwa mai tsananin firgici da tashin hankali. 
Ajiyar zuciya Salbiyya ta saki. Tuni ta ayyana a ranta ihun makirci ne Kursiyya keyi’, saboda duk wani wanda zai bada labarin Kursiyya to ya biyo bayanta. Ta san duk wani salon munafurci da makircinta, daji akwai wani boyayyen al’amarin. 
“Salbiyya dole inje inga meyake wakana a cikin gidan nan. Da alama akwai wani mummunan tashin hankali cewar msi martaba.” 
Batayi yinkurin dakatar da shi ba sai ma bin bayanshi da tayi tana gyada kai. Dafyar aka gano cewa daga cikin dakin Sa’adiyya ne Kursiyya ta fasa wannan kuwwar. Mutane na ganin mai martaba duk sai suka hau darewa. Ya iso cikin dakin a firgice yana tambayar lafiya? 
Kai kawai take gyadawa ba tare da tace wani abu ba. Ya sake tambayarta a karo na uku 
“Ranka ya dade tun shigowata dakin nan nakema Halimatu magana amma naji shiru. A karshe na tattaba ta sai naji jikinta a sake. Yallabai da alama Halimatu najinjiki sosai, ya 
kamata a kai ta asibiti da hanzari.” Jikinshi na rawa ya zauna a bakin gadon Sa’adiyya. Ya hau bubbuga ta a hankaIi yana furta, “Gimbiya Sa’adiyya, ‘yata ki tashi don Allah. Tashi maza mu tafi? asibiti. ” 
Duk a rude yake yin wannan maganar, yama kasa Iura da idonta da ya kafe, da kuma nauyin da tayi sosai. 
Waziri dake tsaye ne ya lura sosai da idanuwanta. Ya gyada kansa ya ce, “Yallabai anya yarinyar nan tana raye kuwa?” Wata irin wawuyar cakuma sarki yakai mishi, ya shake mar wuya sosaiyana fadin 
“Ina tayi ciwon da harza ta rasu? Ban aurar da ita ba bare ta tafi. Ban shirya rabuwa da ‘yata ba. Ina so ta samu gata sosai a gidan mijinta. Ina so ta zama ’yarlele, ta samu duk 
wani gata data rasa a cikin gidan nan. Me yasa zaka ce Gimbiya Sa’adiyya ta mutu?” 
Ya saki wazirin yanajin yadda idanuwansa suka cika tafda hawaye. Inda ace shi din ba 
jarumi bane yadda yayi wannan zaucewar da tuni hawaye ya gama wanke masa fuska. 
 Suna cikin haka wani bafaje ya iso ya rusuna, cikin hakiya ce, 
“Ranka ya dade munyi baki. Yerima Abu Sufyan dan sarkin Kubaisu ne yazo. Ana ta buga 
karaurawa kuma munji shiru. Zuwan ba zata ne da alama. ” “Ka shigo da shi man. Yazo mu kai Halimatu asibiti tare da shi.” Kai Salbiyya ta gyada bayan ta rike hannun Sa’adiyya ta saki. ”Yallabai sai dai fa kayi hakuri, amma da alama ta tabbata yarinyar nan bata raye.” 
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun yake ambata a bayyane. Ba yaso hasashen nasu ya tabbata. Bai san halin da zai shiga ba idan batun ya tabbata. Jiyake tamkar ajijjigashi ya tashi daga mummunar mafarkin da yakeyi. 
Yerima Abu sufyan na shigowa mai martaba ya cakume shi da sauri, yana ganin haka ya tabbatar ba Iafiya ba. 
Abu Sufyanu kaji wani zancen banza da suke fadi wai ‘yata bata raye. Ga yarinya ina gani 
har motsi tana yi. Duba fa ka gani da ranta. Wallahi tana numfashi.” 
Tsananin saka ma ranshi da yayi Sa’adiyya bata rasu bane ya sa yake ganin kamar tana 
motsi. Hargani yake tana mishi murmushi ma. Amma a haka sai ace mishi wai ta rasu? 
Gaban Yerima Abu sufyan yayi mugun bugawa a lokacin daya hada do da Gimbiya Sa’adiyya tayi irin kwanciyar gawa. Yanayin jikinta komaiya saki ko da bai taba taba. Ido ya bude bayan ya dafe kirjinsa da hannunshi na dama. Yaje daidai bakin gadon nata yayi kneel down yana maijinjina hannuwanta duka biyun, Ya Salaam! Mutuwa ya zakiyi mini haka? Me yasa zaki gaggauta zuwa ki daukar mini Sa’adiyya a lokacin da nake da burin kyautata mata? Innahllahi wa inna ilaihi rajiun.’ Allah ga baiwarka nan daka dauki ranta, Allah ka gafarta mata, Allah ka karbi bakuncinta. Allah 
yasa can ta fiye mata nan…” 
Ya dafe keyarshi, duk yadda ya so karyayi kuka kasawa yayi. Zafafan hawaye yaji suna 
sintiri a bisa fuskarshi. Yajuya ya kalli mai martaba daya zama tamkar mutum mutumi. 
Abba mun rasa ta. Duba sosai ka gani bata numfashi. Gabban jikinta duk sun tsaya. Shikenan Halimatu ta tafi?’ ta barmu. Ta tafi gidanta na gaskiya.” 
Kuka sosai yakeyi a daidai wannan Iokacin. Mai martaba ya rike masa hannu, yayi jarumta sosai da bai taya shi kukan ba. 
” Kawaiyake furtawa. 
“Halinki na gariya biki Halimatussadiyya. Hakika ke ‘yace ta gari, wacce samun kamarta ke wahala. Kin hadiyiguba tun yarintarki har kika girma. Ina fatan Allah yasa karshen abun ke nan. Allah ya kyautata miki a can yasa aljannah ce makomarki. Allah ya fadada 
makwancinki Sa’adiyya…” Ya rinka gyada kai idanuwanshi sun yijajur, yana ganin komai tamkar a mafarki. Cikin kuka Yerima Abu sufyan yace, 
“Tunjiya jikina ke bani akwai wani mummunan abu da zai faru da Sa’adiyya, tun daga alamomin data fara bani har izuwa munanan mafarkan da nayi wanda suka hana ni barcin kirki. Allah ya sani zuciyata taci burin aurenki. Wallahi ina sonki da dukkanin zuciyata. Na so na aure ki domin kema kiji dadi kamar yadda kowacce mace ke fatan 
samu. Ashe Allah bai nufi hakan ba. Ashe Allah baikaddara cewa zamu rayu tare ba. Ashe duka soyayyar tamu ba mai tsawo bace. Allah ya gafarta miki Halima. Allah ya kyautata makwancinki. ” 
Haka wurin ya yamutse, masu kuka nayi masujimami nayi. A lokacin ne duk wani asiri da akajima da ginawa na tsakaninta da mutane ya karye. Kafmutanen masarautar suka hau tariyo kyawa wan halayen Halimatu. Tausayinta kowa keji. Tausayin halin data taso cikinshi tun tana yarinya. Suna jin cewa basu kyauta ba na kinta da suka yi. Sunajin ina ma a 
ce ta dawo da rayuwarta su sota? Cikin rashin kuzari mai martaba ya ce,”Lokaci na tafiya, ya kamata a fara haramar jana’iza. A sanar cewa karfe goma na safe za a 
kai ta makwancinta. ” 
Yana gama fadin haka yayi saurin mikewa ya bar dakin, saboda kukan da yazo masa a Iokaci guda daya kasa dakatarwa. 
Yerima Abu sufyan kuwa duk aka watse aka barshi gaban gawar Sa’adiyya sai rizgar kuka yake, yana yi yana mata addua. 
Karfe tara da rabi masarautar ta cika da mutane makil, Sarkin Kubaisu ma yazo da iyalinshi da wasu da dama daga cikin sarakuna. Ban da mutane talakawa da attajirai da sukazo. Sosai janaizar Sa’adiyya ta samu mutane. Karfe goma aka gama aka nufi kai ta tabbataccen gidanta. 

Gaskia KURSIYYA bata da tausayi banga laifin azabar da aka fara gasa mata a baya ba 
Muje dai zuwa

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]