[Advertisements⬇️]

BAKIN DARE CHAPTER 20 THEND - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BAKIN DARE CHAPTER 20 THEND
Shirye shirye ake tayi kowane b’angare babu kama hannun yaro inda kan amaren ya d’au zafi ga exams da suke yi ga gyaran jiki da ake musu kullum basu da lokacin Kansu k0 kad’an Dan ana musu gyaran jiki suna karatun exams basa ma iya wani wayan kirki da angwayen nasu sai dai messages dama tuni suka daina zuwa zance 
Alhaji Nazifi kuwa gyara yayi 
wa gidansa sosai Dan sai daya canza komai na gidan ya koma sabo hatta bangaren Hajiya Nafeesa sai da aka saka sababin furniture’s dangi kuwa sai murna suke suna yayi gyaran gida adaidai kamar yasan shima angwancewar zaiyi. 
Ba karamin kudi ya kashewa su Suhaima ba komai iri daya 
yayi musu sai dai bambamcin kala dan k’aramin lefe ya k’ara musu bayan uban lefunan da aka kawowa kowace a cikinsu abinda ake cewa gata kam sun same shi Dan wasu kayan ma sai su shekara biyu basu yi amfani dashi ba 
Akwana a tashi babu wuya duk abinda aka sawa rana sai yazo an shiga satin biki an fara shagulgula duk daSu Suhaima sun ce basa San wani party waleema kawai zasuyi a ranar da akayi d’aurin Aure amma sai da Angwayen suka tilasta musu zuwa dinner da suka had’a gabadaya a wani katon hall Amare sun sha kyau sai walwali suke Akram ya k’asa d’auke idonsa daga kan Samha sai kallonta yake yi Dan tunda yake da ita idan ka d’auke wet lips k0 
kwalli bai tab’a ganinta dashi ba sai gashi ta sha Heavy make up ta canza mishi kamar ba ita ba Samha kuwa kamar ta nutse Dan kunyar irin kallon da Akram ke binta dashi dan ba normal kallo bane daya saba yi mata ba
Ahaka taro ya watse cike da farinciki da annashuwa 
Samha a ranar Sam bata ganewa Akram dan sababbin abubuwa 
ya bullo mata dashi da suka je sauke su a gida kamar ba Akram mai kunyar nan ba rikice mata yayi yana matse hannayenta ita kuwa jikinta ya hau rawa wani irin tsoronshi ya rufeta data 
ga yanda idonsa ya kada yayi jajur dak’yar ta fusge hannunta ta fito daga motar aguje har suna bangaje juna da Saheebar da itama ta Fito jikinta na rawa 
dan kamar hadin baki Yazeed shima birkice mata yayi yana Neman maida ta cikinsa sabida rungumar da yayi mata 
Jiki a sanyaye suka k’arasa part dinsu kowace da tunanin da take a zuciyarta take tsoron angwayen nasu ya rufesu 
Su Saiam kuwa sai tambayarsu suke abinda yafaru suka gansu haka babu wacce ta iya magana acikinsu suka fara kok’arin rage kayan jikinsu 
Suhaima ce karshen shigowa itama kana ganinta kasan a firgice take a k’asa ta zube tana sauke numfashi dan dakyar ta iya kwatar kanta a hannun khaleed dan shi har dasu kiss ya mata 
Su Saiam mai zasuyi idan ba 
dariya ba dan ko basu fad’a musu ba sun gano su 
Suhaima ce tayi k’arfm halin magana tana “Aunty wai dan Allah wane irin turare kika 
fesa mana haka gaskiya kar ki kara fesa mana bama so fyad’e Khaleed ya kusa yimin a mota yana tambayata wane irin turare na fesa mai d’aga hankali” 
Babu abinda su Saiam keyi sai dariya Safna kuwa tace ” kinsan nawa muka kashe kuwa wajen had’a muku turaren nan ai sai ma gobe wlh wanka zamuyi muku dashi” 
Samha da Saheeba kuwa tunda kowacensu ta zauna suke ta sake sake aranau suna ta ganin kiran angwayen nasu suka k’asa d’agawa 
Suhaima ce kawai bakinta bai mutu ba sukayi ta magana dasu Saiam dan su basa jin wani nauyin juna tamkar kawaye haka suke Safna ganin bakinsu Saheeba ya mutu basa magana yasa ta koma tana tsokanarsu dan tun yanzu su bari ma sai gobe Saiam ta karashe da ‘kallon idon Auta gobe a karshen gado tana dan Allah Akram kayi hakuri” 
Samha kuka ta fashe dashi tana ta fasa Auren su Suhaima kuwa sukayi ta mata dariya 
Washegari karfe 11 dubanin mutane suka shaida daurin Auren Suhaima da Khalid Saheeba da Yazeed Samha da Akram a karshe yayan Alhaji Nazifi ya matsa kusa da liman 
ya mik’a mishi bandir din dubu hamsin yace a d’aurawa Alhaji Nazifl Aure da ‘yar uwarsa Nazifa 
Alhaji Nazifi k’asa kwakwaran motsi yayi sabida mamaki har sai da aka d’aura Auren shi da Nazifa surukan nasu sai murna suke dan dama suna tunanin yanda zai yi rayuwa shi kad’ai idan yayansa suka tafi gidajen mazajensu 
Ciki kuwa amadadin farinciki kuka amaren suka fara yi da suka tuna Hajiya Nafeesa kafin kace me kowace ta fara k’walla tana ina ma Hajiya Nafeesa tana rayye taga Auren ‘ya’yanta gabadaya tuni mutuwarta ya dawo musu sabo fill aka hau koke koke duk yanda anwagwayen suka so 
suyi hotuna da amaren nasu sai hakura sukayi 
Alhaji Nazigi kuwa ana gama daurin Aure ya nufi bangaren Hajiya Nafeesa ya tafi can kuryar d’akinta ya kwanta akan gadonta ya d’auko hotonsu dake taya shi kwana ya kife kansa akai yafara kuka yana mata addu‘oin samun rahamar ubangiji dan bai tab’a tunanin zai auri wata ba bayan mutuwarta shi da yake tunanin bazai iya rayuwar Aure da wata ba sai gashi an daura mishi Aure da Nazifa 
Kuka ya sha sosai har sai da yaji kansa na Neman darewa gida biyu dak’yar ya iya mik’ewa ya wanke fuskarsa yafito sabida kiran da ake ta damunshi dashi a waya. 
Ciki kuwa Sai a lokacin su Saiam suka ji labarin Auren Alhaji Nazifi da Nazifa 
Sunyi farinciki sosai da daurin Auren dan suna ta tunanin yanda Mahaifinsu zai yi rayuwa shi kad’ai idan sun tare. 
Ahaka aka cigaba da shagulgula k’arfe biyu aka fara Walimar da Yayan Hajiya Nafeesa ya had’a musu a harabar gidansa 
Nasiha da wa’azi akayi musu sosai mai ratsa jiki sai zubar da hawaye sukeyi 
K’arfe hud’u da rabi dangin khaleed suka iso dan tafiya da amaryarsu dan Bauchi za’a kai Suhaima 
Alhaji Nazifi kuwa dama guduwa 
yayi daga gidan yace yayansa ya 
wakilce shi wajen yi musu addu’a 
dan Sam bazai iya jure ganin kukansu ba dan sai arasa mai 
rarrashin wani 
Rungume juna sukayi sosai suna kuka kamar zasu shide dak’yar aka bambare su daga jikin juna 
Ahaka aka tafi kai Suhaima gidanta sai kuka take 
Karfe shidda dai-dai aka zo tafiya dasu Saheeba dan gidansu d’aya da Samha Katanga ne kawai ya raba su hakan kuwa ba karamin dadi yayi musu ba dan at least idan suna ganin juna zasu ringa rage kadaici 
Suna rungume da juna har aka kaisu gidajensu sai kuka suke kamar zasu shidde kan Samha 
kuwa kamar ya rabe biyu sabida kuka 
Ana fita dasu Samha aka shigo da 
amarya Nazifa b’angaren Hajiya Nafeesa aka kaita itama sai fargabar irin tarbar da angonta Alhaji Nazifi zai mata take dan tana da masaniyar bai San da Auren ba sai yau 
Sai karfe goma sha d’aya su Akram suka shiga gidajensu Akram kamar ya zuba ruwa a k’asa ya sha dan cikar burinsa 
A can karshen gado ya hango Samha nata kuka ta rike kanta 
Nufarta yayi da sauri tare da watsar da kayan dake hannunsa birkitota yayi gabadaya jikinsa hankalinsa a tashe ya fara tambayarta abinda ya sameta 
Samha kuwa luf tayi a kirjinsa tana nuna mishi kanta 
Hannu ya kai ya taba kanta aikuwa yaji da zafi rau da sauri ya duro daga kan gadon ya had’a mata ruwa mai dan dumi dan tayi wanka 
Ganin tana ta wani nonokewa da dukan alamu a tsorace take yasa ya roketa data kwantar da hankalinta babu abinda zai mata ta dai bashi hadin ya bata abinci tasha magani stress ne ya mata yawa 
Da haka hankalinta ya kwanta ta shiga bandakin tayi wanka tana fitowa ya tura mata gashashen kazar da ya shigo dashi gabanta ya roketa taci ta sha magani dak’yar taci cinya biyu tace ta koshi ta dai sha yoghurt d’in sosai 
Paracetamol biyu ya bata ta sha daga nan ya umarceta data 
kwanta tayi bacci 
Kan gadonta ta hau k0 minti biyar batayi ba bacci yayi awon gaba da ita dan tana da tabbacin babu abinda Akram zai mata 
Akram kuwa shima kintsawa yayi yayi nafilolinsa ya kwanta abayanta yana karewa surarta kallo sai hadiyar yawu yake yi 
Su Suhaima da Saheeba kuwa angwayensu basu d’aga musu kafa ba aranar suka baje amarensu 
Alhaji Naziii kuwa Palo ya dawo ya kwanta dan Sam baya jin zai iya kwanciya da wata macen idan ba Hajiya Nafeesa ba Nazifa kuwa ganin bai kulata ba yasa itama tayi kwanciyarta da kudurin sai ta karkato da hankalinsa gareta. 
Akram time to time ya ringa taba jikin Samha yaji kanta ya rage zafi ahankali shima bacci yayi awon gaba dashi yana rungume da Samha kiran sallar asuba ne ya tashe shi daga daddadan baccin da yake ahankali ya matsa kusa da Samha ya fara hura mata iska a kunne da zumar ya tasheta amma me kamshin turarenta Ne ya fara rikita shi daga hura kunne yafara kai mata kiss k0 ta ina
Samha jiki na rawa ta bud’e idonta ta fara kokarin tureshi daga jikinta amma ina hankalin Akram ba a jikinsa yake ba romancing d’inta kawai yake yana rabata da kayan jikinta kai kana ganin yanda ya rikice kasan jjc ne his new to the club 
Samha kuwa tuni ta b’are baki ta fara kuka tana hadashi da Allah da annabi nikuwa nace sorry dear Akram yayi nisa 
Sai da ya maida Samha cikakiyar ‘ya mace ya dawo hankalinsa daga nan kuma fa ya fara bada hakuri yana rarrashi 
Samha kuwa sai kuka take tana ta tsaneshi ita gidansu zata koma 
Dakyar Akram ya shawo kanta ya gyara barnar da yayi 
Akram k0 kofar gida bai leka ba yana ta aikin rarrashi Samha kuwa sai Langabewa take 
Daddare kuwa tana idar da Sallar 
isha ta kulle kofar dakinta babu yanda Akram bai yi da itaba akan ta bude kofar taki akan dole ya hakura ya tafi dakinsa ya kwanta yana ta juye juye 
A Daren ranar Alhaji Bala ya amsa kiran Mahalicci bayan uban wahalar daya sha haka aka tattara kasusuwansa aka binne shi 
Tuni labarin rasuwarsa ya zagaye k0 ina daidaiku mutane ne kawai ke mishi addu’ar Samun rahamar Allah 
Mahaifiyarsa tayi kuka tayi nadama da bata binciki irin sana‘ar da Alhaji Bala yaringa yi ba gashi duk kudin daya Tara da dukiyoyin da ya ajiye 
bai amfanesu da komai ba bai hana Alhaji Bala mutuwa ba bai hanata buya ta kasa fitowa Cikin bainar jama‘a ba

*3months later* 

Idan kaga su Samha baza ka gane su ba sabida tsabar kwanciyar hankalin da suka samu a gidajen mazajensu  basu da wani burin da ya wuce su faranta musu dan suna balain sansu 

Quote 

*get married to the person who loves u and is ready to spend the rest of his life with you than for you to marry the person who you love the person u loved would take advantage of that love u have 
for him and misbehave cos u are going to tolerate him bcos of d love u have for him but wen you get married to the person dat loves you so much dear u would be treated like a queen cos there is no any woman on earth that can compare herself with you and steal your man from you be wise in choosing your life partner don’t go for what your hrt loves so much* 
Akram kamar ya had’iye Samha sabida so da kauna 
Samha kullum tana tare da Saheeba suna hirar yanda zasu ringa farantawa mazajensu kowace na d’auke da juna biyu 
Haka ma Suhaima tana jin dadin zaman gidan Aurenta abinda ya rage mata jin dadi shine nisan da 
tayi da ‘yan uwanta amma duk da haka kullum tana makale da waya a kunnenta suna waya dasu 
Saiam da Safna kuwa duk sun haihu sun sanyawa ‘yayansu Sunan Hajiya Nafeesa dan dukansu mata suka Haifa ‘yar Saiam ana ce mata momy yar Safna ana ce mata Ammi 
Bangaren Alhaji Nazifi kuwa tun yana dauke kansa yana nisanta kansa da Nazifa har sai da yazo ya fara kulata sabida yanda ta jajirce wajen faranta mishi rai duk wani Abu data San zai faranta mishi rai yinshi kawai take tuni shima ya koma d’an yaro yafara soyewa dan Nazifa dama yarinya ce tunda mijinta ya mutu bata k’ara Aure ba duk wata yakan leka gidajen ‘ya’yansa yaga lafiyarsu 
Hajiya Lubna kuwa tuni ta samu dan garinsu ta Aura duk da 
yana da mata ita taje ata biyu hankalinta a kwance yake dan tasan irin sana’ar da yake yi idan ta tuna Naila takan yi kuka ta bita da addu‘a 

*Alhamdulillahi rabbil alamin anan na kawo karshen Bakin Dare kura kuran danayi a ciki Allah ya yafemin ina kaunarku 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]