[Advertisements⬇️]

BAKIN DARE CHAPTER 18 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BAKIN DARE


CHAPTER 18

Alhaji Bala kuwa tuni akajingine case dinsa a gefe guda sabida shi da matacce babu maraba Dan kamar ma ba mutum ba in banda wari da rokon mutuwa babu abinda yake yi dan Na Maliya bai fasa zuwa ya watsa mishi ruwan kaikai ba duk da yanzu babu fata a jikinsa sabida cizgeshi da yake yi da kansa 
Akram kuwa bashida wani Matsala arayuwarsa sai na rashin shawo kan Samha dan zuwansa gidan uku bata yarda ta fita last zuwansu ne ma sukayi kicibus da ita ta dawo daga Islamiyya a lokacin da yayi tozali da ita ji yayi kamar kara kwarara mishi wutan Santa ake Ashe kallon tsoro yayi mata daddare Samha ba karamar kyakyawa bace 
Samha kuwa jikinta ne ya dau rawa gabanta na Balain fad’uwa ita kadai tasan abinda ya ringa mata yawo a kowane sassa na jikinta a lokacin da ta hada ido dashi amma dan karfin hali irin nata da taurin zuciya daure fuska tayi ta ratsa ta gefensu ta wuce duk da kiranta da yake yi da husky voice dinsa dake kara narkar mata da zuciya a lokacin Alhaji Nazifi baya nan haka su Akram suka zauna zauna a mpta suna jiran dawowarsa dan Akram kasa tafiya yayi dan gani yake idan bai Shawo kan Samha ta aminta dashi ba komai zai iya faruwa dashi dan duk fitar numfashinsa kaunar Samha linkuwa yake aransa fuskatar kawai yake gani a idonsa da sexy eyes dinta dake sa shi kasala 
Samha kuwa aguje ta karasa dakinta sabida bugun da zuciyarta keyi a kasa ta zube tana maida numfashi tare da dafe saitin zuciyarta sabida harbawa dayake dan Kaunar Akram 
ayau data gan shi wani San sa ne yakara bin ko ina najikinta babu abinda ke amsa kuwaa 
a kunnenta sama da muryarsa mai dadin gaske sigar ma daya kira sunanta ya bambamta 
da yanda ake kiranta babu Wanda ya kai shi iya kiran sunanta 
Lumshe idonta tayi ta najin muryarsa a kunnenta still tana dafe da kirjinta a hankali ta mike taje bakin window ta daga labule dan ta kara kallon sa 
Kirjinta ne ya hau bugawa da Sauri a lokacin data hango shi a saman motar shi a zaune ya dafe kwantacen suman Kansa daya sha gyara bakin agogon dake sak’ale a hannunsa sai kyalli yake shigarwhite and black yayi na kananan kaya fadar kyaun da yayi ma b’ata 
bakine
Samha ko kifta idonta batayi sabida kallonsa da take wani irin Kaunarsa na ratsa ilharin jikinta 
Motsin da taji a bakin kofa ne yasa tayi sauri ta saki labulen tare da nufar kan gadonta dan bata so ‘ya’yyenta su gane halin da take ciki sabida hardasu ake rarrashinta akan ta saurari Akram 
Alhaji Nazifl sai da Magriba ya iso gida bai shiga da motarsa ciki ba ya sauko sabida hango su Akram da yayi haka kawai yake tausayin Akram dan yasan yana balain San Samha sai dai har yanzu Samha taki ta karbeshi a matsayin mai sonta duk da ban baki da Nasihar da yake mata 
Su Akram kuwa suna hango shi suka tareshi tare da zubewa agabansa suna kwasar gaisuwa bayan gaishe gaishe da tambaye tambaye Alhaji Nazifi yace musu su shiga suyi 
Alwala suyi sallah tunda Magriba tayi inyaso idan sun idar sayi magana 
Shiru su Akram sukayi suna Sauraren Alhaji Nazifi dake cewa Akram ya hakura da Samha ya zabi a cikin Suhaima da Saheeba tunda Samha taki ta aminta dashi yasan Suhaima da Saheeba bazasu bashi Matsala ba sun dan fi Samha saukin Kai duk da itama Samhar ba fin karfinsa tayi ba zai iya tilasta mata amma baya so ya tilasta mata din dan yiwa yaro Aure dole baya cikin tsarinsa baya kuma so ya takura mata dan yarinya ce sosai kuma shi har ga Allah yana so ya hada zuria dashi sabida nagartattun halayenshi dafatan zai amshi tayinsa ya zabi Suhaima ko Saheeba tunda duk daya suke da Samha 
Tunda ya fara magana Akram ya jike da Gumi yaji kamar guduma yake kwada mishi dan San da yake yiwa Samha bayajin zai iya hakura da ita sai dai idan Aure aka daura mata da wani batun su Suhiama kuwa bai ma San kamaninsu ba ballantana har daya daga cikinsu ta kwanta mishi aransa gashi yanajin nauyin Alhaji Nazifi baya jin zai iya duba tsabar idonsa ya watsa mishi kasa a ido 
Yazeed shima tuni hankalinsa ya tashi daya ji abinda Alhaji Nazifi yace dan ya kamu da San Saheeba yana tsoron Akram yace Saheeba yakeso 
Alhaji Nazifi kuwa kamar yasan tunanin da Akram yake yace mishi kar ya damu yaje yayi tunani bazai mishi dole ba idan dai babu wacce ta mishi a cikinsu kar yaji nauyinsa ya fada mishi 
Wani dan ajiyar zuciya Akram ya saki dayaji abinda yace dan hanya kawai yake nema da zai zille yake
Godiya ya hau yiwa Alhaji Nazifi 
Alhaji Nazifi yayi murmushi yace ba komai su tsaya suci abinci sai su tafi A tare suka mike suna ce mishi sun koshi sun gode 
Babu yanda Alhaji bai yi dasu ba akan su tsaya a kawo musu abinci dan so yake yayi amfani da wanan damar yasa su Suhaima su kawo musu abinci daga nan yaga wacce ta kwanta mishi amma fir suka ki ahaka suka mishi Sallama suka tafl suna mishi godiya. 
Suna fita waje Yazeed ya cakumi wuyan rigar Akram yana kar ya sake ya zabi Saheeba dan ita yake so 
Akram doke hannunsa yayi ya buga tsaki tare da shigewa cikin mota dan shi yama manta kamanin Saheeba ai bayajin ko sarauniyar Indiya za’a mishi tallarta zai so ta kamar yanda yake San Samha 
Yazeed ne ya ringa surutansa shi kadai yana ya hakura kawai da Samha tunda bata San shi 
ya zabi daya yar uwarta ta kawai tunda yaga alamar dukansu kyawawa ne Akram shi dai bai ce uffan ba har suka isa gida yana tunanin hanyar da zai bi ya shawo kan Samha taso shi gashi bashida lambar wayarta ballantana ya ringa communicating da ita koya samu ta 
saurare shi 
Aranar Akram kwana yayi yana addu’ar Allah ya mallaka mishi Samha amatsayin matar Aurensa indai Alheri ce agare shi idan kuma ba Alheri bace a gare shi Allah ya cire mishi Santa a zuciyarsa 
Bangarensu Samha kuwa bayan sallar ishai Suhaima ta zubo musu abinci a faranti suna ci 
harda Alhaji Nazifi dan tunda Hajiya Nafeesa ta rasu ya maye gurbinta suke cin abinci tare 
Alhaji Nazifi kallon Samha yayi dake tajuya cokali tana cakalar abincin haka ta koma shiru shiru tunda Akram yace yana Santa tunani yayi watakila sabida Kin da takewa Akram ta koma haka 
Murmushi yayi yace “Baby meyesa bakya cin abincin? Samha dagowa tayi tana murmushin yake tace ” Babu komai daddy” 
Girgiza kai Alhaji Nazifi yayi still da murmushi a fuskarsa yace “Baby kenan ai nasan meye yake damunki tunda yaron nan yace yana sanki kika bi kika takura kanki kina tunanin zan tilasta miki ki so shi to ki kwantar da hankalinki bazan miki dole ba yau yaron yazo ya sameni nace ya hakura dake zan bashi Suhaima ko Saheeba dan nasan su bazasu ki shi ba” 
Alhaji Nazifi da zai lura da ya hango tsantsar tashin hankalin dake kwance a saman fuskar Samha da ya jiyo irin bugun da tsallen da zuciyarta yake yi kamarya fado kasa 
Alhaji Nazifi kuwa bai lura da halin da take ciki ba ya maida kallonsa kan su Suhaima dake cin abincin su hankalinsu kwance da alama basu damu ma da maganar da Alhaji Nazifi ya fada ba hasali ma kowace a cikinsu fata take ace Akram ita ya zaba dan duk wace ta amsa sunanta mace mai aji da kyau bata da burin da ya wuce ace Akram ya zamo mallakinta 
Alhaji Nazifi cewa yayi “Suhaima Saheeba nagayawa Akram ya zabi daya a cikinku tunda ‘yar uwarku bata San shi kunga kuma babu yanda za’ayi na tilasta mata dafatan duk wacce ya zaba a cikinku bazata watsa min kasa a ido ba” 
Murmushi kawai sukayi suka sunkuyar da kai alamar dukansu sun amince Alhaji Nazifi kuwa murmushinjin dadi yayi dan yasan mai murmushinsu ke nufi
Samha kuwa wani irin jiri ta ringaji yana Neman kayar da ita sabida tashin hankali murmushin data hango kwance a saman fuskar su Suhaima ba karamin daga mata hankali yayi ba
Babu Wanda ya lura da halin da take ciki har suka kamalla cin abincinsu suka mike dan dama idan suna cin abinci itace take tashi a karshe 
A daddafe ta mike ta kai farantin kitchen ta wuce daki tana zuwa ta zube a kasa wani zazzafan zazzabi ya rufeta atakaice aranar da mugun zazzabi ta kwana da mafarkan Akram 
Suhaima da Saheeba ganin Asuba tayi bata tashi dan tayi sallahr asuba ba yasa suka nufi 
kan gadonta dan su tasheta 
Sallati sukayi gabad’aya da suka ga halin da take ciki a rude suka dagata suna tabajikinta dake tururin zafi
atakaice sai da Samha tayi kwana uku a asibiti kafin a sallameta tabi ta rame sabida tunanin Akram haka kawai takejin haushinsu Suhaima 
Alhaji Nazifl kuwa sai lallab’ata yake yi shi dasu Suhaima abunka da yar Auta 
Bayan kwana biyu da aka sallamota daddare wajen karfe biyu tana kwance tana tunanin Akram saijuyi take sirarran hawayen nadama na bin kuncinta sai yanzu take data sani kin amincewa Akram sai yanzu take data sani bata dorawa kanta girman kai taki karbar soyayyar Akram ba yanzu gashi Akram ya hakura da ita zai zabi daya daga cikin ‘ya’yyenta ya Aura Juyawa tayi ta kalli su Suhaima dake baccinsu peacefully duk abinda take yi Saheeba na kallonta dan juyawa tayi da zumar gyara kwanciyarta ta hango samha na Jan majina tana sharar kwalla mamaki ne ya rufeta tayi kamar bacci take yi 
Samha kuwa durowa tayi daga kan gadon ta nufi Palo dan ta sha kukanta ta gode ma Allah Tana ficewa Saheeba tayi sadaf sadaf tabi bayanta 
A 3 seater Samha ta kwanta ta bude wayarta ta shiga gallery ta budo hotunan Akram tana kallo tana shafa kan wayarta hawaye sai zubowa suke a idonta 
Saheeba dake jikin labule ta dan bude dan ta ringa hango abinda Samha keyi mamakine ya kara rufeta data hango tana kuka tana shafa hotunan Akram 
Samha kuwa magana ta fara yi ahankali Saheeba ta kasa kunnenta dan ta jiyo ta 
“Ina Sanka Akram ina Kaunarka Girman kai da taurin zuciya zai sa na rasa ka bansan yanda zanyi rayuwa babu kai ba ina kunyar na koma wajen Daddy ince inasanka yanzu ya zanyi Akram”? 
Kuka take sosai har da shesheka 
Saheeba kuwa ahankali tayi baya ta koma dakinsu jikinta a sanyaye bata tsaya bata lokaci ba ta tashi Suhaima ta rike hannyenta sukayi wajen palon suka kuma labewa 
Samha kuwa surutanta take ita kadai tana shafa screen din wayarta sai da suka ji duk abinda take cewa a karshe ta rungume wayarta a kirjinta tana sauke ajiyar zuciya 
Suhaima tsaki tayi lokacin da suka koma ciki tacewa Saheeba “Kece fa baki sani ba wlh na dade da sanin tana San sa tsabar munafirce da taurin zuciya yasa ta Dage bata San shi aikuwa sai na wanata na wajigata zan gayawa Daddy gaskiyar tana San shi ni gobe ma hirarsa zan tayin zancen ina sansa sai zuciyarta ta kusa bindiga zan kyalleta“ 
Murmushi Saheeba tayi tace “kai Aunty Suhaima Auta ce fa” 
Tsaki Suhaima ta karayi tace “Autar fa dalla jekiyi kwanciyarki Ashe shiyasa ta ringa ma rashin lafiya takaicina ma Daddy yaringa lallabata akan taso Akram Ashe ta dade tana sansa” 
Takun da suka jiyo ne ya sa suka hau gadonsu da sauri suka rufe ido kamar masu bacci 
Samha kuwa sai data leleka fuskarsu taga bacci suke ta hau kan gadonta ta kwanta tana 
sauke ajiyar zuciya sabida kukan da tayi …….. 

Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]