[Advertisements⬇️]

BAKIN DARE CHAPTER 17 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BAKIN DARE
CHAPTER 17

Tuni mutane suka kaure da sallati sakamakon rawan alantar da Alhaji Bala ya ringa zubawa shi kadai yana ihu babu abinda kakeji sai sautun bulalai yana suyi hakuri zai fadi gaskiya tuni ya fito daga inda masu laifi ke tsayawa ya nufi tsakiyar kotun ya ringa tsalla ihu yana shoshe shoshe 
‘Yan jarida kuwa tuni sukaja da baya suna daukarsa hotuna da video 
Wasu ‘yan sanda biyune sukayi k’arfin halin zuwa kusa dashi aikuwa sukaji saukan bulalai a gadon bayansu aguje suka barwajen 
Mutanen kotun kuwa hankalinsu a tashe suka zubawa Alhaji Bala ido dake Neman fita daga hayyacinsa sabida tsabar azaba 
Alhaji Bala kuwa wani wawan ajiyar zuciya ya sauke a lokacin da suka b’ace take Na Maliya ya bayyana saman kansa yana kyakyata dariya sai yawo yake a saman ruwa babu Wanda ke ganinsa sai Alhaji Bala 
Sai da na Maliya yayi dariya mai isarsa yace “Bala kadan kagani sai na kara taso wayanda suka fi wanan yawa wlh sai ka roki mutuwa ta dauke tsabar masifa da azabar da kake ciki” 
Alhaji Bala kuka ya fashe dashi yana “Na maliya ka rufamin asiri na tuba wlh iya masifar da nake ciki ma ya isheni” 
Dariya Na Maliya ya kara kyakyalewa dashi ya bace 
Duk mutanen dake cikin kotun zubawa Alhaji Bala ido kawai sukayi suna mamakin surutun da yake yi shi kadai 
Alhaji Bala bin jikinsa dake masifar rad’adi dan azaba ya ringa yi da kallo dan ji yake kamar an hura mishi wuta nan da nan wasu kuraje masu masifar kaikayi suka feso mishi 
wani razanan ihu ya saki ya fara Sosa ko ina kamar sabon mahaukaci 
Tuni mutanen dake kotun suka kaure da hayaniya suna Alhaji Bala ya haukace tun ba a je ko ina ba 
Duk abinda akeyi Akram na daga gefe ya zubawa saurautar Allah ido dan ya dan girgiza da lamarin Alhaji Bala tunda gashi dai sautukan bulalai kawai suka ringa ji basu ga kowa ba 
Dakyar aka samu mutanen kotun sukayi shiru sabida Alkali dake San magana 
Alkali sai da ya gyara zaman glass d’in fuskarsa ya kara karewa Alhaji Bala dake Sosa jikinsa a haukace kallo yayi gyaran murya yana tunda Wanda ake case dashi ba’aji ta bakinsa ba sabida halin da yake ciki za’a dage kara zuwa sati biyu masu zuwa aranar kuma za’a yanke mishi hukuncin daya dace da laifin da ya aikata su kuma su killer tunda sun amsa laifmsu batare da sun wahalar da sharia ba zasuyi life imprisonment with hard labour daga haka Alkali ya buga guduma tare da mik’ewa 
‘Yan sanda hudu ne suka rike Alhaji Bala sakamakon flflzgewar da yake yana ihu dan tsabar Susa da yakeyi harjini jikinsa ke yi 
Ahaka suka jashi sukayi mota dashi yana zunduma ihu 
Ahankali mutanen kotun suka fara fitowa data kotun suna  Al ajabln abunda ke iaruwa 
Hajiya Lubna kuwa ko ajikinta Dan Sam Alhaji Bala bai bata tausayi ba tunda lokacin daya ke tapka rashin Imaninsa shima babu digon tausayin wayanda yake zalunta aransa 
Hajiya Saude Mahaifiyar Alhaji Bala kuwa kuka ta ringa rizga hannunta aka dan ita kad’ai tasan irin masifar da take ciki bata jin zata iya komawa kauyensu dan tunda ‘yan garinsu sukaji labarin Bala dan fashine sukayi zuga suka tafi gidajen kannensa suka ringa jifansu suna asirin yayansu ya tonu Ashe d’an fashi da makamine 
lta kuwa sai a makota ta buya Dan petur suka zazzagawa gidanta suka cinna mishi wuta suna munafika ce itama
tasan irin sana’arda Alhaji Bala yake yi ita take daure mishi gindi 
Magana take so tayiwa hajiya Lubna akan ko zata taimaka ta tafi da ita gidansu Dan bata da wurin zuwa Dan ko kannen Alhaji Bala sun bar garin sabida tsabar tashin hankali amma ga mamakinta wani mugun harara Hajiya Lubna ta watsa mata tare da Jan tsaki tayi shigewarta mota Baki a sake Hajiya 
Saude ta bita da kallo har sai data daina hangota 
Akram kuwa sai da ‘yan jarida su ka kara tsayar dashi suna jera mishi tambayoyi dakyar ya yakice ya gudu ya barsu dan ya gaji da wanan tambayoyin da suke mishi dan Sam shi ba gwanin magana bane yanzu nan zaiji kansa na ciwo 
Alhaji Bala kuwa tukuru ya zama k’aramin Mahaukaci yana surutai tare da soshe soshe cikin kankanin lokaci hallitarjikinsa ya fara sauyawa yana komawa wani irin hallita cisge gashin kansa kawai yake yana buge buge a jikinsa sai jini yake yana fadar abubuwan da ya aikata Lokaci lokaci Na Maliya ke bayyana ya ringa sheka mishi dariya yana zuba mishi wani ruwa dake sa ya kara haukacewa wajen Sosa jikinsa 
Bayan sati daya da zaman da akayi a kotu aka karawa Akram 5 Adam mukami ya zama 
babba banda uban kyaututukan da manyan masu kudi suka ringa bashi gida ne mota kudi banda uban kyautar da Governor ya mishi har da su hutun wata uku Dan ya zagaya kasashen ketare yaje ya huta Akram kuwa godiya kawai yake yiwa Allah akan d’aukakar da ya mishi dan yasan duk abinda ya samu yin Allah ne ba nashi ba
Duk inda ka zagaya gidajen television gidan jaridu duk wata media hirar Akram s Adam kawai ake yi na irin namijin kokarin da yayi na chapke Gagarumun dan fashi Alhaji Bala 
‘Yan mata kuwa tuni suka haukace burin kowace ace tazama buduruwar Akram s Adam ga kyau ga kudi 
Samha kuwa bakon al amarin data tsinci kanta a ciki ne ya sata fara rama dan idan dare yayi Sam bata iya bacci Haka kawai take tunani na babu gaira babu dalili babu dama ta hau wani net sai taci karo da hoton Akram da labarinsa ita dai tasan babu Wanda ta tsana sama 
da shi amma ga mamakinta bata iya bacci sai ta budo hotonsa ta kalla bacci kuwa idan ya dauketa sai tayi mafarkinsa ta kuma rasa Wanda zata samu ta gayawa halin da take ciki 
Alhaji Bala kuwa lamarinsa yayi tsamari duk dare sai ‘yan sanda sunji saukar bulalai amma sun rasa wayanda ke dukan Alhaji bala 
Haka zai kwana yana ihu yana sosa jiki fatar jikinsa duk ta kwaye har wani wari yake yi sabida bayan ya sha bulala Sai Na Maliya ya watsa mishi ruwan da zai ringa cisgo fatar jikinsa 
Rokon ‘yan sanda kawai yake akan su harbeshi da wanan azaba da yake ciki 
Akram kuwa tunda aka bashi Hutu yafara shirye shiryen zuwa gidansu Samha duk da yasan by now ta riga da tasan ko shi waye amma still wani fargaba da rashin kwarin gwiwa yakeji dan yasan sun Riga da sun tsane shi tunda yana tsaye aka kashe mahaiflyarsu bai ma San ta ina zai fara tunkurar gidansu ba harya kai shi da sanar da su abinda ke tafe dashi nasan Auren Samha ba dan ranaku daidayane bai yin mafarki da ita tunda yake bai tabajin San wata ‘ya mace kamar yanda yake San Samha ba 
Ahaka Akram ya ringa sakawa rana rashin kwarin gwiwa da fargaba na hana shi zuwa sai da ya samu sati d’aya ahaka kafin ya iya d’aurewa yaje tare da Amininsa Yazeed da yaringa karfafa 
mishi gwiwa ….. 
Karfe hud’u na yamma suka isa gidansu Samha gaban Akram sai faduwa yake dan bai San wane irin tarb’a Alhaji Nazifi zai masa ba ballantana uwar gayyar Samha Yazeed ne ya ringa karfafa mishi gwiwa 
Har suka aika mai gadi yayi musu sallama da Alhaji Nazifi gaban Akram bai daina faduwa ba 
Mai gadin tare suka fito da Alhaji Nazifi Dan yaga Wanda yake Sallama dashi 
Ganin Akram ne yasa mamaki ya rufe Alhaji Nazifi sakin murmushi yayi a lokacin da suka zube a kasa suna gaishe shi Akram kuwa sai sunkuyar da kansa yake 
Palon Saukar baki Alhaji Nazifi ya kai su yana ta tunanin mai ya kawo su wajensa 
Kara gaishe shi sukayi Alhaji Nazifi ya amsa tare da kara jinjina mishi irin kokarin da yayi wajen kama Alhaji Bala ya kara da mishi addu’oin nassara a rayuwarsa 
Akram shi dai kansa a sunkuye yake yana Dan samun relief na faduwarda gabansa yake yi dan yaga alamar Alhaji Nazifi bazai bashi matsala ba 
Alhaji Nazifi wayarsa ya Ciro daga Aljihunsa ya kira Saheeba a waya akan ta kawowa baki ruwa da lemo yana katse wayarya maida hankalinsa kan su Akram Dan yaji abinda ke tafe dasu 
Ganin sun kasa magana sai zungurar juna suke yasa Alhaji Nazifi yayi murmushi yana Allah 
yasa shima ba laifi yayi ba suka zo bincikarsa Murmushi sukayi gabadaya Yazeed yace ba Laifl yayi ba sun dai zo nema ne a gurin shi 
Adai-dai lokacin Saheeba ta shigo da faranti a hannunta sanye take da doguwar Riga ta yane kanta da farin mayafi 
Sallamarda tayi ne yasa suka dago gabadaya suna amsawa 
 Saheeba a Razane taja da baya tana sallati a lokacin da suka had’a ido da Akram 
Tuni ta saki farantin hannunta jikinta na rawa Dan take ta tuna bakin daren da suka zo gidansu 
ta fara yi tana nuna Akram da Hannu 
Alhaji Nazifl kuwa yayi Sauri ya mike ya rukota yana “Saheeba mai haka Akram din ne bakisani ba” 
Akram kuwa shima jikinsa ne ya dau rawa hankalinsa a tashe dayaga yanda Saheeba ta razana da ganinsa 
Yazeed kuwa tunda tayi sallama ya kafeta da ido baya ko kiftawa
Dakyar Saheeba tace cikin in,ina tana nuna Akram “Daddy yana tsaye fa aka kashe 
Da Sauri Alhaji Nazifi ya katse ta yana “Sau nawa kukeso na ringa fada muku kwanan mahaifiyarku ya Riga da ya kare ko ya hana shi k0 bai hana shi ba sai ta amsa kiran mahallici and i told u guys this young guy is doing his job bansan wane irin kunne ne daku ba maza ki koma ki dauko musu ruwan sha kafin na saba miki” 
Da Sauri Saheeba tayi waje a tsorace Dan wani irin tsoron Akram takeji 
Tana ficewa Alhaji Nazifi yace “am so sorry for what happen kasan yarinta ke damunsu tun ranarda asirin Alhaji Bala ya tonu suke ta surutai sun kasa ganewa akan aikinka kake aikinku ya gaji haka in banda yarinta idan Ajali ya kira ai sai kaje” 
Akram jiki a sanyaye ya dago yace “Alhaji nasan hakan zai faru Dole yaranka su tsane ni zakayi mamakin abubuwan danayi undergoing kafin nasamu nassarar capke Alhaji Bala wlh I left my family l live a miserable life just to reveal his secret pls tell your children to forgive me wlh ba laifina bane sai kayi pretending you are one of them zaka iya gano irin su Alhaji Bala” 
Alhaji Nazifi murmushi yayi yace “haba Akram karka wani damu aikin Alheri kayi Dan ba dan kai din ba babu Wanda zai San true colour d’in Alhaji Bala da yana nan yana tapka barna a doron kasa karka wani damu yarana basu tsaneka ba kawai wannan bakin Daren da suka rasa Mahaifiyarsu ne bazasu iya mantawa ba” 
Yazeed godiya ya fara yiwa Alhaji Nazifi shi kuwa Akram gabadaya jikinsa ya kara sanyi ya rasa mai ke mishi dadi dan yasan watak’ila haka Samha ta tsane shi idan taganshi zata tsorata kamar yanda Saheeba ta tsorata 
Yazeed fad’awa Alhaji Nazifi yayi na abinda ke tafe dasu na Akram yaga daya daga cikin ‘ya’yansa yana so kuma ba wasa ya kawo shi ba Aurenta yake so yayi 
Akram d’agowa yayi ya kalli Alhaji Nazifl dan yaga yanda ya karbi zancen aikuwa ya hango tsantsar farinciki a fuskar Alhaji Nazifi dan murmushi kawai yake yi hakan ne yasa yaji sanyi aransa dan yasan koda Samha zata bashi matsala Alhaji Nazifi zai iya shawo kanta 
Alhaji Nazifi duk da yaji dadin maganar da suka zo dashi dan babu Wanda zai ki bawa Akram ‘yarsa ya Aura sai da yadan jinjina lamarin aransa duk da baisan wa yake so a cikinsu ba yasan sai an kai ruwa rana koma wacece a cikinsu zata amince ta Aure shi sabida kiyayyar da suke mishi 
Alhaji Nazifi ce musu yayi babu Matsala indai ta bangarensa ne addu’a zai raka su dashi Allah ya musu zabin da yafl Alheri amma Abu daya ne zai sa bazai bashi Auren ‘yarsa ba idan dai ta nuna bata sansa dan gaskiya babu wacce zai yiwa Auren dole a cikinsu 
ballantana ya tursasa wacce yake so duk da bai San wa yake so a Cikin yaran nasa ba Sai a lokacin Alhaji Nazifi ya tambayeshi wa yake so a cikin ‘ya’yansa 
Akram da jikinsa ya gama mutuwa gabad’aya da maganar Alhaji Nazifi dak’yar ya bude baki yace karamar cikinsu yake so” 
Ajiyar zuciya Alhaji Nazifi ya sauke yace babu damuwa bari ya fita ya turo musu ita Allah yasa su dai-daita 
Godiya suka hada baki suna mishi har ya fice daga palon 
Yana fita Yazeed ya daki kafad’arsa yana mikewa tare da tsallen murna yana “Abokina wlh na samu irin matar danake so na Aura gaskiya ‘yar nan tasa itama ta hadu
Akram tsaki yayi ya buga tagumi yana kallon bakin kofa fargaba duk tabi ta cika shi 
Yazeed kuwa sai santin kyaun Saheeba yake yana shima ana kwana biyu zai zo ya samu Alhaji Nazifi akan yana Santa 
Alhaji Nazifi kuwa a lokacin da ya isa bangarensu a Palo ya tarar dasu a zaune sunyi jungum jungum kamar wayanda akayi wa rasuwa 
Yana shiga palon Suhaima tayi Sauri ta tare shi tana tambayarshi dagaske Akram ne yazo gidansu? 
Suhaima kuwa tana rakube a gefe kirjinta kamar ya fado k’asa tunda Saheeba ta gaya musu Akram yazo tajijikinta na rawa tama rasa wane irin tunani zatayi 
Alhaji Nazifi kuwa waje ya samu ya zauna ya kirasu daya bayan d’aya suna Amsawa 
A hankali ya fara musu Nasiha mai ratsa jiki yana nuna musu su ajiye kiyayyar da suke yiwa Akram bashi da laifl a mutuwar Hajiya Nafeesa akan aikinsa yake koda ma basu zo ba a ranar kwanan Hajiya Nafeesa yariga da ya kare nasiha ya musu sosai sai da ya tabbatar da jikinsu yayi sanyi ya maida kallonsa kan Samha da ta hada gumi babu gaira babu dalili yace mata sabida ita Akram yazo wajensa yana Santa da Aure 
Wani irin mikewa Samha tayi hankali a tashe ta nuna kanta tana ” Daddy ni yake so da Aure kuma ka amince wlh ni bana sansa na tsane shi bana so na budi ido na ganshi bazan iya Aurensa ba”
Tana gama fadar haka tayi d’akinsu da gudu Tana kuka 
Alhaji Nazifi bayanta yabi da kallo har ta shige dan yasan dama za’a Rina bazata yi accepting Akram cikin Sauki ba 
Mikewa yayi ya koma palon b’aki ya bawa Akram hakuri akan su dawo wani lokacin insha Allahu zai yi kok’arin ya shawo kan Samha idan kuma ta dage bata San shi sai dai yayi hakuri dan bazai iya tilasta mata ba 
Akram ji yayi kamar guduma Alhaji Nazifi ke kwad’a mishi aka sabida yanda yaji nauyin maganar take hankalinsa ya tashi dan agaskiya bazai iya hakura da Samha ba yanda yake Jin mugun Santa a zuciyarsa 
Alhaji Nazifi kuwa ganin yanda Hankalin Akram ya tashi yasa yafara kwantar masa da hankali yana karya damu zaiyi kok’ari ya shawo kanta 
Ahaka suka mishi sallama suna mishi godiya Akram kuwa kamarya kife sabida tashin hankali …….

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]