[Advertisements⬇️]

BAKIN DARE CHAPTER 16 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BAKIN DARECHAPTER 16

Saheeba ce tayi karfin halin daga wayarta dan dukansu sun kasa daga wayar TV kawai suka kurawa ido ko kifta idonsu basa yi 
Cikin rawar Murya Saiam ta hau cewa su kunna TV su ga Tsinanne nan da ya kashe musu mommynsu dubunsa ta cika Allah ya tona mishi asiri 
Saheeba tace mata yanzu haka shi suke kallo bata Kara tsayawa taji mai Zata ce ba ta kashe wayar 
Alhaji Nazifi kuwa ba ganin Alhaji Bala dan fashine ya girgiza shi ba ganin Alhaji Bala mai taimakon talakawa da suke hirar shi shekaran jiya akan irin ayyukan alherin da yake yiwa Mara sa shi har suna cewa da za’a samu irin shi guda Ashirin da talakawa sun daina kokawa har addu’oi suka runga mishi sai gashi wai Ashe shine wannan gagarumin dan fashin Daya addabi manyan masu kud’i 
Samha kuwa tana nan a tsaye kamar an dasata waje daya Akram kawai ta zubawa ido dake kwarara bayani wani irin strange feelings da bata taba ji ba taji yana zagaye kowane sassa na jikinta 
Suhaima ce tayi karfin halin magana tace “Allah mai iko yanzu wanan Alhaji Balan mai taimakon talakawa dama shine tsinanne Dan fashin nan dayazo ya kashe mommy” 
Saheeba da sauri tace “ni bashi yake bani mamaki ba yanzu dama wannan Dan iskan 
mutumin ba Dan fashi bane ya tsaya aka kashe Mommy agaban idonsa bai iya tabuka 
komai ba duk da sunan bincike ake tafiya dashi Fashi ayi kissa agaban idonsa ayiwa mata fyade duk yana tsaye yana da ikon da zai hana shi aiwatar da mugun nufinsa akan yaran mutane yana da ikon da zai hana shi ya Harbe mana Mommynmu amma ya tsaya aka 
kashe Mommy a gaban idonsa na tsane shi wlh bai burgeni ba bai tashi sawa a kama shi ba 
sai da aka kashe Mommy” Ta karasa maganar sirarran hawaye na bin kuncinta 
Nanauyan ajiyan zuciya Alhaji Nazifl ya sauke ya juya ya kalli Suhaima yace “karki’ tsane shi Suhaima akan aikinsa yake ba kowane zai iya daukan risk din da ya dauka ba mutane da yawa sun sha rasa rayyukansu agarin binciken mai laifi irin na Alhaji Bala masu fuska biyu ni kuma ji nayi ina kaunarsa araina ba dan shi ba mutane ba zasu taba sanin waye Alhaji Bala ba haka zai ta tafka zalunci a doron kasa ba tare da ansan shi bane ki daina alakanta mutuwar Mahaifiyarku dashi domin k0 daya hana k0 bai hana ba lokacinta ya Riga da yayi gaskiya Akram S Adam yayi namijin kokari sosai sai dai ayi mishi addu’ar gamawa da duniya lafiya Kiran makocinsu daya shigo wayarsa ne ya katse mishi maganarda yake yi yana d’agawa shima yace ya kunna TV yaga ikon Allah murmushi kawai yayi yace yagani 
Aranar duk Inda ka zagaya hirar Alhaji Bala kawai ake yi duk wani social net labarin Kawai zaka ji anayi na irin namijin kokarin da Akram yayi har asirin Alhaji Bala ya tonu 
Manyan masu kudi da ‘yan siyasa zirya kawai suka ringa yi suna zuwa ganin Akram tare jinjina mishi aranar Akram Sam bai samu zama ba kansa harwani ciwo yake 
Alhaji Bala kuwa hannunsa da kafa sanye yake da ankwa banda ‘yan sanda biyu dake gadinsa Dan ba waje daya aka sa shi dasu killer ba for the first time da yaji wani irin kunya da nadama ya lullubeshi wai shi da jama’an gari suka sani amatsayin mai taimakon talakawa sai gashi asirinsa ya tonu cikin kankanin lokaci Lallai Akram ya gama dashi yanzu Ashe dan yagano shi waye da irin sana’ar da yake yi yasa ya bishi har port Harcourt yaringa siyar da alewa ya San yanzu ‘Yan garinsu sun ji labari har da Mahaifiyarsa da wane ido zai kallesu da wane ido zai kallijama’an gari inama mutuwa ta dauke shi yanzu ina ma kasa 
ta tsage ya shige ciki 
Ahaka ya ringa zancen zuci hawaye na kwarara a idonsa 
Samha kuwa wunin ranar sukuku tayi shi ta kuma rasa mai yake damunta babu Wanda ya kai ta farincikin tonuwar asirin Alhaji Bala Dan kullum addu’arsu kenan to amma me wani Abu mai nauyi takeji game da Akram duk Fitar lafazinsa na jawabai da yake yi akan Alhaji Bala da hanyoyin da yabi haryayi nassarar kama Alhaji Bala sai taji gabanta ya fadi ta kuma rasa dalili haka kawai takeji aranta tsabar kiyayyan da take musu ne ya janyo haka amma me ta kasa dauke idonta daga kansa a hotunan sa da ake ta watsawa a shafukan facebook dasu watsapp 
A cikin kankanin lokaci aka mika Alhaji Bala kotu Dan a yanke mishi hukuncin sabida duk 
shaidun da ake bukata akwai su 
Motocin ‘yan sanda sunfl ashirin da suka yi layi kawai dan rakiyar Alhaji Bala zuwa kotu 
Alhaji Bala kuwa kamar ya shide yayi kukan yayi nadamar har ya saba da ganin Na Maliya na zuwa yi mishi dariyar keta banda Hajiya Nafeesa da Mai gida dake yawan zuwan mishi dadaddare aikuwa yayi ta ihu kenan har gari ya waye nan da nan ya zama siririn karfi da yaji banda kasumbar daya ajiye 
Ana fitowa dashi ‘yan jarida sukayi dafifi suna sheka mishi tambayoyi hasken flash kake gani kota ina 
Babu ma hanyar da za,a wuce 
Alhaji Bala kuwa sunkuyar da kansa yayi kasa hawaye kamar an bude famfo jama’ar gari kuwa duk sun hau hau saman kwanun gidajen mutane Dan su hango Alhaji Bala mai fuska biyu 
‘Yan sanda turejama’a kawai suke Dan su samu hanyar wucewa Wani Dan jarida ne ya roki Alfarmar abasu minti goma kawai suyiwa Alhaji Bala tambayoyi Dakyar aka amince suyi mishi tambayoyin inda Alhaji Bala yaji kamar ya nutse dan kunya 
Wata ‘yarjarida ce ta farajefo mishi tambaya “Alhaji Bala mai zaka iya cewa game da tuhumar da ake maka na fashi da makami kai da jama’an gari suka san mutumin kirki ne mai taimakon talakawa”? 
Tana rufe baki wani ya jefo masa nashi tambayar ” Alhaji Bala tsawon wane lokaci ka dauka kana wanan mumunar aiki shin dama can ta silar fashi kayi kudi kake taimakon mutane ko kuwa dama kana da kudin daga baya ka koma kana farautar dukiyoyin jama‘a? 
Alhaji Bala kansa ya kara sunkuyarwa Dan bai San mai zai ce musu ba sai da wani ya kara jefo mishi nashi tambayar yayi karfin hali ya dago aikuwa tuni aka hau kashe mishi ido da flash ‘yanjarida kuwa kamarzasu shige jikinsa sabida kawai suji ta bakinsa kowa mika recorder dinsa yake saitin bakinsa Dan yaji mai zaice Sosai 
Alhaji Bala cewa yayi “bansan mai zance ba ayanzu banida bakin magana a yanzu ni banma San yanda zan muku bayani ba kuma yanda kuke mamakin tuhumar da ake min nima haka nake mamakin tuhumar da ake min” 
Haka kawai Yaji kalaman na fita a bakinsa Dan gani yake idan yayi saurin mika wuya mutane sai sunfi yarda da shi Dan fashi ne amma idan ya ringa musanta zargin da ake mishi ahaka zaiyi ta wahalar da shariar 
Mamakine ya rufe Akram da yaji mai yace 
Alhaji Bala na kokarin magana ya ji an jefo mishi dutse a goshi kafin kace maijama’an gari sun hau cewa “karya kake azzalumi asirinka ya tonu dutse akejefa mishi ko ta ina 
‘Yan sanda kuwa tuni suka hau sakin harbi sama dan su tsawatar musu da haka suka samu suka dan watse suka koma daga nesa suna jefo duwatsu 
‘Yan jarida kuwa tuni suka yi nasu wajen dan wasu a cikinsu sun samu nasu rabon dutsen 
Ahaka aka tisa keyar Alhaji Bala da goshinsa Ke tsiyayardajini da gefen kansa suka dau hanyar high court 
Cikarda kotun yayi bata bakine dan har waje mutane ne burin kowa yaga Alhaji Bala mai fuska biyu manyan masu kudi ma da suka san shi sun samu zuwa ciki har da Alhaji Nazifi da Ghali 
‘Yan sanda sai da sukayi dagaske suka shige da Alhaji Bala ciki ‘yan jarida kuwa suma sun cika kotun burin kowa ace shi yafi daukan rahoto Alhaji Bala kuwa addu‘a kawai ya ringa yi mutuwa ta daukeshi dan abinda ake cewa kunya kam jinshi kawai yake a hankali ya dago da kansa aikuwa suka hada ido da Mahaifiyarsa idonta yayi jajir sabida kukan da ta sha yana kokarin dau ke idonsa suka hada ido da Hajiya lubna idonta kamar ya fado sabida harararsa da take yi da gani itama zuwa tayi ta tona mishi asiri 
Wajen da masu laifi suke tsayawa ya tsaya ya sunkuyar da kansa a lokacin da aka ringa shigowa dasu lion Akram ne karshe daya shigo yana sanye da Uniform dinsa yai balain yi mishi kyau waje ya samu ya zauna ba tare da bata lokaci ba Alkali ya fara gabatar da laifin da ake tuhumar Alhaji Bala dashi 
Duk hadin kan da ake so su Lion su bayar sun bayar dan sun fadi irin aika aikan da suka ringa yi Black ne ma yaso yayi karya yaji an kwashe shi da wani mugun mari daya sa sai da ya jingina da bango murya kawai yaji ana ka fadi iya gaskiyarka kona canja ma kamani
Da Sauri Black ya fara basu labarin duk abinda ya sani kamar an kunna radio ko ajiyar zuciya baya saukewa sai da suka gama amsa duk tambayoyin da aka musu aka koma kan Alhaji Bala daya sunkuyar da kai idonsa a runtse 
Full name dinsa Alkali ya kira Alhaji Bala ya dago ahankali yana kallonsa 
Alkali tambayarsa yayi akan ya basu labarin yanda akayi ya tsinci kansa a cikin wannan mugun sana’a mai kuma zai iya cewa game da tuhumar da ake mishi 
Alhaji Bala sai daya d’auki tsawon minti goma yana tunanin mai zaice dan fa Sam ba zai iya mika wuya Cikin sauki ba 
Kau da kansa yayi yace duk abinda ake tuhumarsa da shi karyane sharri aka mishi Yana rufe baki yaga fatalwowin wayanda ya kashe sun fara bullowa tajikin bango dukansu 
da dogayen bulala a hannunsu 
A razane yaja da baya ya wage baki zai yi ihu aikuwa yafara jin lafta ko ta ina ………….

Hmm kowa ya tuba dan wuya 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]