[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 8 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE 
CHAPTER 8
‘Karfe bakwai da rabi ta_dare Ma’isha tafito gidan Zaid tareda securities d’insa, lnda suka rufe dukkan kofofin gidan Ka’na sukayi mata gargad’i cewa kada tasa’ke zuwa wajen kuma koda wa’sa basason su’kara ganinta a hanyan gidan bare har tayi tunanin shigowa ciki, 
Sabida oga yayi musu federal warning akanta. 
Uffan… bata tankamusu ba, haka tacigaba da tafiya a gefen titi tana watsa cingam tamkar  daga shigarta har izuwa k’anta, babu dankwali, gashinta ne ke zube Baki wuluk 
har izuwa tsakiyar ba’ya. 
Ma’inah kadei ce a gida tinda safe take shiga da fita babu kowa, ta rasa inda momy tashige yau, ko irin dawowar datake cin abincin ra’na batayiba, gashi yenzu har karfe takwas da rabi tayi babu alamarta ko Daddy. 
Wayarta dake cha’ji taciro kai tseye takai layin Momy Inda a bugu d’aya ta amsa; Ma’inah kizo gidan Ishah kisamemu nida Daddinki muna chan…. Daga nan takatse wayar, Muryarta ta nuna cikin damuwa take sosai
 yayinda take magana. Hakan yasa Ma’inah bata bata lokaciba, Dasauri tashirya, lnda Driver Bashar yaja’ta zuwa Ma’isha Sambo Maidugu resident. Suna isowa tasauko, aguje ta’karaso cikin parlour, anan tahango momy a dakin Ma’isha tana rusa kuka tamkar rasuwa akayimusu. Kai tseye Ma’inah ta‘karaso inda take,jiki a sanyaye tace; Momy me yafaru kike kuka? 
Janyota momy tayi, cikin tsananin damuwa ta rungume ta, tanacewa; Yar uwarki tayi hatsarin mota yanzu akabugowa Daddyn ku akafada Masa. 
Cikin Sananin kuka tarike hannayen Ma’inah duka biyu tanacewa; I really don’t want to lose her, you two are the only thing i have, Ma’inah dan Allah kifadamin cewa Ma’isha zata dawo gareni, wallahi bazan iya rayuwa batareda ita ba, she is my daughter I love so much…. 
Share mata hawaye Ma’inah tayi, yayinda take kokarin ri’ke nata hawayen dasuke ko’kuwar 
gangarowa cikin kwayar idanuwarta; Daddy fa? A ina yake? lya tambayarda tayi kenan. “Ban saniba, yana amsa wayar da akayimasa yatafi batareda yafad’amin inda yake zuwaba;. Momy ta amsa cikin nunfashi d’aya. Yayinda tamike Kai tseye tasa hijabi ta fice, Inda Ma’inah tabiyota a baya tana tambayarta Inda take kokarin zuwa. Uffan bata fada ba, Motar ta tashige fuuuu…. Tafara tuki full speed tamkar barin garin zatayi. ‘ Ma’inah ma motar nata tashige, Inda Bashar yake biyeda Motar Momy hartseda suka kai City Hospital. 
Fitowa sikayi alokaci d’aya. Momy na gaba Ma’inah na bi a baya, ahaka har suka kai d’akinda Ma’isha take. Kai tseye suka shigo Inda suka tarar da Daddy tseye akofar d’akin yana zuba addu’oi da salati. Meye ya tsameta? Momy ta tsaya lnda take tana tambayarsa cikin mutuwar jiki. Ahankali ya 
janyota Inda yake yayinda ya rike hannayenta duka biyu yanacewa; ki gafartamin Safeenah inaga rashin kulawar dakike fada cewa bana baiwa Ma’isha ya tabbata domin likitoci sun tabbatarmin cewa Rashin Kulawa ce da Stress yakaita gayin hatsari, Amma abun tashin hankalin kuwa shine Farfad’owarta dasunan wani mutum wai shi ZAID ta ta’shi, na rasa 
waye wannan mutumin Zaid. 
Zaid: Ma’inah tayi saurin katse shi cewa; Zaid dei wanda nasani dawuya Ma’isha tasansa domin Babban attajirine Kuma Ogan mu a office, na tabbata bashi bane. domin wanchan 
Zaid da alama baya kula mutane bare Mata. 
Suna kan tattaunawan, Likita yafito inda yashedamusu cewa aiki dei yayi kyau kuma da yardan Allah babu wata matsala anjuma kadan za’azo a sallamesu sukoma gida. Sedei 
akwai bukatar abata cikekken kulawa sabida bai kamata ta ringasa damuwa a ranta ba. 
Nan ne suka ‘karaso ciki, Ma’inah ta tsaya a dedei kofa tana lekowa, Daddy da Momy kuwa Kai tsaye suka nufo gadonta, Tana doura idanunta akansu tamike dasauri tana hawaye yayinda ta rungumesu dikkansu biyu tanacewa; Momcy meyasa kuka barni nikad’ei nafito har nagamu da hatsari. Believe me or not I’m your only daughter meyasa kuke zabin Ma’inah kubarni, Daddy I don’t understand. why I’m I always your second class daughter, 
wace laifi na aikata kuke sa’kamin da wannan hukuncin? Tafada cikin nunfashi d’aya. 
Girgiza kansa yayi yayinda yakecewa; Ma’isha zuwa yanzu ya’kamata mudena wannan maganar domin munrigada mun yi’ta a baya kuma kusan ko yaushe ita mukeyi, Ki yarda ko kar kiyarda Ma’inah Y’ar uwarki ce Kuma ni nan dakike gani Mahaifinta ne, ga kuma mahaifiyarta anan Safeenah, Sabida haka yakamata wannan zancen taka’re daga yau 
banson ki’kara sa wannan tunanin a ….. 
Haba Alhaji meye haka? Kulawar kenan? Momy takatse shi; Haba dan Allah, kawai lnaga yakamata ku koma gida tareda Yarka, kabarni tareda Maisha anan zamu dawo idon an sallameta anjuma… 
Fine, if you insist; lya abinda Daddy yafad’a kenan, ba’tareda wata jayayyaba haka yashafa ‘Kan diyar tashi Ma’isha Sannan yayi waje, inda ya rike hannun Yarsa Ma’inah. 
A hankali suke tafiya har tseda suka iso wurin ijiye Motoci ma’ana “Car Park” Dakansa yabud’e mata mota tashige Sannan yashige shima abaya suka zauna tsit!!! yayinda Driver yakejansu cikin kwanciyar hankali. 
Motar shiru take her tseda suka ‘karaso gida domin ako yaushe Daddy yakan shiga cikin tsananin bakin ciki, tareda bacin rai idan Ma’isha tana nuna wannan bakin halin nata ta’kin yar uwarta wacce suka fito ciki d’aya kuma alokaci daya, Addu’ar sa ako yaushe shine Allah 
yashiryeta yakuma dedeita kanta da Yar uwarta Ma’inah. 
Ma’inah tana ambatan sunansa tin dazu Amma alamu sun nuna cikin damuwa yake sosai domin baima san tanayiba, Fitowa yayi jugum! yana tafiya abun tausayi. Dasauri tarike hannayensa; Daddy meye kake tinani haka? Girgiza kansa yayi tareda murmushin ‘karfin hali yanacewa; Babu komai Y’ata yisauri kizubomin ruwan Lipton kikawomin d’aki kinji’. 
Toh.. Ta amsa cikin ladabi da biyayya, suna shigowa Daddy yayi d’akinsa, lta Ma’inah kuwa tawuce kitchen, anan tahada masa ruwan Lipton d’in kamar yedda ya bu’kata Sannan 
takaimasa ‘Daki. Daddy gashi nan ruwan Lipton ce wacce kafiso, its your favorite tashi kasha”. Babu musu yamike, hannun da’ma yasa yakarbi ruwan dake hannun Yarsa lnda yafara kurba ahankali,ahankali…. 
Tsayawa tayi agabansa tana kad’a kai Sannan tarike kwankwaso tana dariya; Daddy ka tina, this is the most simplest way to make you smile and laugh. 
Tsayawa agabansa tayi tanata yaranta da shirme wanda ahakan takesa Abban nata Farinciki da dariya tin tana Y’ar shekara goma. 
Daddy yakwanta, yana ganin abubuwan datakeyi har tseda bacci yad’aukeshi Sannan ta rufe masa jiki da bargo tafito tana hawaye. Fitowarta tayi Kicibus da Momy tareda Y’ar 
lelenta. Dasauri tasa hannu tashare hawayenta yayinda tafara murmushin ‘karfin hali tanamusu maraba; Sannunku, yajikin naki. Uffan…Babu wacce ta tankamata daga Uwar har Yar, tamkar banza dabba suka sha’reta lnda suka hauro sama zuwa d’akin Momy. 
lta kanta bata ‘kara furta k0 da kuwa kalma d’aya ce’ba juyowa tayi kurun! tashige d’aki takwanta. Daga nan ta dafa fillo tarike se kuka take tana Jimamin yanayin rayuwarta ita kwata kwata aganinta babu mai santa a duk fad’in duniya fa’ce Iyayenta na Maiduguri, Sekuma Daddy da Miemah, shiyasama wataran take Addu’ar Allah ya d’auki Ranta ko ta huta dagannin wannan bakin ciki ta rashin kulawar mahaifiya. 
Wannan tunanin take har zuwa lokacinda barci ya d’auketa daga nan bata sa’ke sanin inda takeba har izuwa wayewar gari nan ne ta d’oura alwala tareda sauke farillan Sallar asuba. Tana idarwa takoma kan gado daman kwata kwata yau bataji fitowa ko inaba domin Ma’isha ta kwana a gidan nasu, futowarta zai iya janyo matsala babba. Ta dade tana barci cikin kwanciyar hankali tareda mafarke mafarke masu dad’i da bada nishadi. Zaid tagani cikin mafarkin nata yana kuka abun tausayi Sedei kuwa idan tayi ‘kokarin tambayarsa bacewa yake yana ‘kokarin furta mata wata ‘kalma amma babu abinda takeji. Wannan mafarkin take yayinda kunnuwarta sikafara kad’awa dawata Sauti mai tsananin 
‘kara tamkar a mafarki. A firgice ta tashi tanacewa; Zaid babu abinda zai tsameka dayardan Allah kuma matuqar
inada rai babu wanda ya Isa yaga bayanka. Se yanzu tadawo cikin hayacinta lnda tafara goge idanuwarta tana mamakin wannan mugun mafarkin datayi, kwatsom ‘karar tasa’ke buge kunnuwarta, Sanda idanuwarta suka bude kororo sannan tagane lnda sautin ke fitowa. Bibbige ‘kofar d’akinta akeyi tun dazu. Dasauri tamike Inda tabud’e kofar ahankali tana lekowa, Ai kuwa kamar ta sani ‘Dan halak, Daddy ne tseye yana murmushi yayinda yakecewa ” Oya Sleeping beauty yimaza kiyi breakfast sannan kishirya, Yau dakaina zan ‘kaiki Wajen aiki because today is your first day in office ya’kamata muje tare koda kuwa akwai… 
Ah, Ah Daddy”; Ma’inah tayi saurin katse shi; Daddy ba’nason kaje wajen aiki na, I will definitely handle it, zanje ni kadei kada kadamu;. Daganan taja kofar d’akin tana kokarin rufewa “anyway thanks nagode sosai. 
Rike kofar Daddy yayi, ya kura mata ido taredacewa; Na’fi kowa sanin Y’ata kuma idan akwai abunda take boyemin zan ga’ne, Ma’inah meyasa bakya san muje office d’inku kodei akwai wata matsala ce. 
Muryarta na ‘karkarwa ta amsa “Aaah.. Aaah babu komai nayarda bari nashirya dasauri 
mutafi to…. 
Gyad’a Kai Daddy yayi Sannan yarufe mata kofan d’aki yakoma falonsa. Yana zaune Ma‘isha tashigo aguje ta sameshi “Daddy I gotta go bye bye zan tafl” Tana fad’an wannan tajuye aguje tamkar guguwa, Sanda ya tse da ita “Ina Kuma zaki ahaka? har kin samu lafiyar fitowa yanzu Ma’isha? Daddy wajen aiki za’ni kuma yau ce ranata ‘a farko achan kaga ya‘kamata nayi musu sammaci” Tafad’a tana had’iye miyau tareda murmushi tamkar kujerar Makkah akayi mata Albishir. 
Mikewa Daddy yayi yanacewa; Wajen aikin ne dawannan kwaliyar haka dakuma wannan murmushin tamkar Amarya, Maishatu, Jirani awaje bari nad’auko kin motana zanyi 
dropping inki, kinji, kodei… 
Ba se kayi hakanba; Momy takatse shi; Da kaina zanyi dropping inta ba’se ka wahalar 
dakanka ba. Daga nan tarike hannun Ma’isha suna kokarin wucewa, Ya yadakatar dasu; Ma’inah fa wace 
Uwar kikabari agidan wacce zata kaita wajen aikin tunda kince kada nawahalar da kaina. 
“Kayi kokari ka kaita, Sabida saida nayiwa Ma’isha alkawari cewa idan ta’zo nan gidan, bazan kula Ma’inah ba sannan tayarda muka dawo nan tare, Amma karka damu zata koma 
bayan tasamu cikekken lafiya daganan zanfara kaita (Ma’inah) wajen aiki dakaina because she is also my responsibility. Tana fad’an wannan tarike hannun Yarta sukayi waje. Girgiza kansa yayi alamun ya tausaya mata “Allah yashiryeki” iya abunda bakinsa ya iya furtawa kenan. 
Ma’inah ta shirya tsap!!! cikin doguwar Riga kalar Baki da Fari wanda sukayi dedei da 
kekkyawar Farar fatarjikinta… 
Tana fitowa Daddy yamike “My daughter look so adorable”. Thank you Daddy; Ta amsa cikin murmushi. Daddy yazaro key’n motarsa suka wuce tareda Ma‘inah. 
Ta Bangaren momy kuwa; ta sauke Ma’isha wajen aiki ‘karfe bakwai da rabi dedei sannan taja motar zuwa ofishin aikinta. 
Da kafar da’ma tashige confanin, tana rangwada yayinda tawuce kai tseye wajen receptionist “Excuse me Madam ta ina ne offishin CEO yake? “You are welcome to Zaid Muhammad Zabir Company, Sama Zaki haura sannan ne 
zakishiga CEO Villa anan ofishinsa take. Receptionist ta amsa cikin murmushi. 
Maisha bata sa’ke cewa komaiba. Kamaryadda tafad’a, Sama tahauro zuwa CEO Villa anan ta ijiye Jakarta awaje sannan ta’karaso ciki tana duba wajen Sama da ‘Kasa tana mamakin irin Dukiyar da aka kashe aginin confanin. 
Wani d’an Sanda Mai Bakin ‘kaya ne yataro ta tun kam tashige yanacewa; Madam ba’a 
yawaita kallace anan wajen Sabida tsoro domin CEO yashigo yanachan cikin ofishinsa. 
“Dallah Malam bar nan” Tafad’a ahankali Wanda ba ballene yaji abinda takecewa ba. Daganan ta ‘kama ‘kanta tashige a nitse. 
ofishin seketeri tanufa kai tseye tami’ka masa hannu tareda cewa “Sunana Ma’isha Sambo Maidugu nazo wajen CEO da appointment letter ahunnu na”. 
Bayan sun gaisa neh yakarbi pepan dake hannunta ya’karanta sannan ya’kira Zaid tawaya 
ya sheda masa zuwanta’. Babu mutsu ya amsa masa cewa ta‘karaso ciki. Nan ta’ke suka budemata kofa “Madam muna miki maraba da zuwan Babban Confanin Zaid Muhammad Zabir Builders Nigeria; Muryar tafito from no where da harshen turance. 
Ma’isha ta’kara shiga yanayin birgewa yayinda tasa ‘kafar dama tashige tareda sallamar musulunci “Assalamu Aleikum Wa Rahmatul Lahi Wa Barakatuhu. Tamkar Ustaziya tashige tana gyara gelen dake daure a’kanta. 
“Wa’aleikumu Salam” Zaid ya amsa batareda yad’auke idonsa daga wayar dayake 
dannawa ba. “Have a seat”. Yafada Yana dannana wayarsa. 
Kallonsa Ma’isha keyi tun shigewarta ta ‘kasa d’auke idanuwarta akansa, ayayinda zuciyarta take sa’kamata wasu irin mafarke mafarke masu d’adi irin wacce turawa suke ‘kira “Day dreaming”. 
You again? Ma’inah meye kuma kikeyi anan? Ya katse tunanin nata dawannan tambayar. “Zaid Ashe ka’san Yar uwata Ma’inah? What a Coincidence a ina kasanta? Ni Sunana Maisha Sambo Maidugu, Twin Sister’n Ma’inah Sambo Maidugu …….. Daga wannan tambayar dayayi tafara zuba tamkar lalatacciyar fanfo Sanda surutan suka ishe’sa sannan yadakatar da ita “Excuse me ba’nason hayaniya just go straight to the point 
meye yakawoki nan? 
Gyara murya tayi sannan ta gyara zama “Sunana Maisha Sambo Maidugu na’taso a US ma’ana United States of America achan nayi ‘karatu har zuwa secondary School sannan nadawo nan nacigaba Inda na tsaya a Master’s Level. 
Tana gama bayanan ta mikomasa littatafan nata tanacewa; Go through them na tabbata zaka gamasu Sabida ni k0 agida daban nake ba’na wannan banzan halin ta Ma’inah takeyi ba’na Shaye shaye ….. Bai tankamata ba her tseda yagama duba littatafan nata sannan yayi murmushi “Welcome to ZMZ Builders, Mu had’u a conference room ‘karfe Goma (10;00AM) Inda zan mallakawa kowa kujerarsa. No African Time. Da wannan ya tsallameta sannan ya’kara danna ‘kararrawar. 
§§§§§§§§§ 
Karfe Goma da minti Goma Ma’inah ta’karaso wajen aiki tareda Mahaifinta. “Toh Daddy na’gode se anjuma”. Tabud’e mota tafito, Ai kuwa tana rufe kofarta Daddy yabud’e nasa 
yafito shima yanacewa: Tare zamuje ai, ko dei bakyason naga ofishin ta’ki ne? 
Rasa abun fad’a tayi. Cikin tsananin damuwa ta hadiye miyau dake bakinta sannan ta 
girgiza kai muryarta na mugun ‘karkarwa tace “Ba komai Daddy zaka iya shigowa”. 
Suna shiga receptionist tayi saurin aikata dakin Meeting dasukeyi a sama. Babu mutsu suka hauro tareda Daddy lnda yasamu waje yazauna adedei kofan dakin ta’ron. Ma’ina kuwa kai tsaye tayi ciki. 
‘Kafafunta suna rawa yayinda take tafiya, tana kallon ‘kasa har takai wajen zama lnda ahankali tazauna sannan tafara saura ransu. 
Ya ‘taro dikkan jama’a masu aiki a confaninsa zuwa babban d’akin taronsu, conference room anan suka tsaba yin meeting musamman idan wani gagaruman project mai wahala 
tana gabansu. 
Awannan ‘karon kuwa ta’rosu yayi musamman domin ya gaba’tar da sabbin yan aikinda 
ya debo cikin ma’kon nan dashike, ya debo yan aiki da dama. 
D’aya bayan d’aya yake ‘kiran sunayensu yanashedawa kowa masayinsu dakuma dalilin 
dayasa ya daurasu awannan kujera. 
Ma’inah tana zauneh a chan baya tana ganinsu, yayinda ya’kira yawancin dikkan mutanen wajen Amma bataji sunantaba daga nan tacire hope na’samun aiki a gurin. Tana Cikin wannan tinanin, taji sunan Ma’isha Sambo Maidugu dasauri tamaida hankalinta akansu. Inda Zaid yakecewa; Daga yau itace Manajan ma’su kulada har’kokin interior decorations na nan Abuja, Na’bata wannan kujeran ne Sabida haza’kar data nuna alokacin interview dakuma takardunta na makaranta, tanada first class a fanin tattalin ‘kasuwanci ma’ana 
Business Management ….. 
Daganan kowa yasa tapi, Yayinda Ma‘isha tafito, ba’ki ta’kusan taba kunnuwarta tana wani blushing tana Jin d’adi. 
Ita kanta Ma’inah dariyan takeyi. Tana taya yayarta farinciki dajin dad’in wannan babban kujeran da aka nada ta kuma ta tabbata Ma’isha zata rike amana Kuma tayi aiki tsakani da Allah. Ma’lnah Sambo Maldugu. Sunan tace ke binta Ma‘isha. Cikin tsananin Farin ciki da mamaki tamike, dasauri ta hauro sama, tana ‘kokarin ‘karasowa wajen ta’ron mutanen yayinda Zaid ya dakatar da ita “Anan Zaki tsaya Sabida masayinsu daban take data ‘ki. 
Yana fad’an wannan yajuya ta Gangaren mutanen yanacewa; Ma’inah Sambo Maidugu itace sabuwar Ma’sinjata, duk dacewa ta’yi karatu kuma tanada tsakamako mai kyau na bata wannan masayin ne Sabida yanayin rayuwarta; she is a drunkard, Yar Shaye shaye ce, ta gagare Iyayenta kuma tana ‘kokarin shiga duniyar ‘karuwanci. Aganina wannan masayin 
dana bata itace zata zamto tsandiyar shiriyarta dakuma… 
Bai ‘karasa kalmar dayake kokarin furtawaba, yayinda Ma’inah tafito aguje tabar wajen tana hawaye masu tsananin zafi. 
Daddy yana hanganta yamike dasauri ya’karaso Inda take “Lafiya Ma’inah meye ya tsameki kike kuka Kodei akwai matsala ce? Ya tambayeta cikin tashin hankali. Murmushin’karfin hali tayimasa sannan tayi ajiyar zuciya tashare hawayen dasuke zuba a idanuwarta duk da ‘konuwar da zuciyarta keyi tayi ‘karfin hali ta’kara masa ‘karya cewa ‘Dorata CEO yayi a wata babbar kujerar da bata taba tunanin zai daurata akai ba, shiyasa take kukan farin ciki. 
“Alhamdulillah” Yashafa hannayensa afiska yana godewa Allah wannan ai abun farin ciki ne matuka yakama mu shirya miki gagarumar Parti dakuma Walimar samun nasara, a gida idan kin dawo. 
Wani lawya ne yafito daga d’akin taron yakawo wa Mainah wasu takardun sheda wanda zai tabbatarwa kowa cewa ta karbi aikin da akabata domin tasa hannu. Nuna mata inda zatasa hannun yayi batareda ya’kara wata magana ba. Takardan sheda ce Yata kisa hannu this is your only opportunity; Daddy yafad’a cikin tsananin farin ciki. 
Murmushin karfin hali tasakeyi, ayayinda wasu Zazzafan Hawaye suke zuba a idanuwarta, Dakyar tasa hannu, tayi signing a duk pepopin shedun. Daga nan mutumin yakoma ciki. Suka cigaba da ta’ron dasuke. Ma’inah kuwa tsayawa agun tayi tana hawaye, wanda ta’kasa rikesu tun dazu take kokarin hanasu zubowa… 
IYA ABUNDA YA SAWWAKAAYAU KENAN ‘ .  
XCHAPTER NINE SPOILER×
 Daddy meye mukeyi anan? Kuma meyasa aka tattaro dikkan kayyakina aka dawo dasu nan gidan? Ma’inah ta tambayesa ne atsorace yayinda ta’kara damke hannunsa tanacewa; Daddy ba’nasan zama anan gidan nikad’ei zan koma gida mucigaba da zama Ni da Kai da Mommy. 
Budan Bakinsa cewa yayi ” Daga yau Ma’inah kin dawo nan gidan dazama domin na 
tabbata zakiji dadin rayuwarki anan fiyeda chan gidana. 
Uncle itace Yar taka? Zaid yashige kai tseye tareda wata yar yarinya mai kimanin shekara biyu zuwa Uku. 
Innalillahi wa inna ileihi rajiun’… Wuf!!! Ma’inah tamike cikin tsananin mamaki da rudani ta hadiye miyau, nunfashinta na kokarin tsinkewa yayinda take tambayan Mahaifinta “Daddy a ina kasan shi? Zaid Muhammad Zabir shi ne Ogan mu a office. He is a ghost. …” 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]