[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE 
CHAPTER7
A hankali take tafiya, tana tinani iri daban daban, ahaka har tahauro saman 
bene, inda tashigo wani ma’keken waje mai suna (CEO Villa). 
Kai tseye tawuce wajen secretary office dake dap hannun da’marta, awurin tahad’u da taron jama’a kowa da takardu ahannu, daga turawa, larabawa harmada ba’kaken. 
Layi sukabi, in an orderly manner aka karbi credentials d’insu dika Sannan suka koma wuraren da aka tanada musu suka zauna, Ana ‘kiran sunayensu d’aya bayan d’aya suna shiga interview a ofishin CEO, har seda aka akai 
sunan mutumiyar ‘Ma’inah. 
Ma’ina Sambo Maidugu. Seketerin yadanna kararrawa ma‘ana lokacin interview’n ta yayi. Kai tseye aka bud’e mata kofa tamike jikinta yana d’aukan zafi tashige tana rabe rabe. Rasa abun fad’a tayi muryanta na karkarwa tace; S.. San.. Sannu, ina wuni. 
Se yanzu Zaid yajuya da kujerarsa na taya inda ya daga ido ya kalleta ‘You again? Yafad’a cikin tsananin mamaki. 
Kanta na kasa ta gyad’a kai ” I’m sorry Zaid kayi hakuri wallahi nafi kowa bukatan wannan aikin I’m sorry kawai ka kaddara bamu taba had’uwa ba na’tabbata idan… 
Excuse me…. Zaid yadakatar da ita; kin cika hayaniya and I hate talkatives saboda haka I don’t think zamuyi aiki tare dake just get out. 
Kuka Ma‘inah tasaka, cikin tsananin damuwa tasauka kan guiwowinta tana rokansa “I’m Sorry please ka taimakamin, ko wace irin aiki kabani nayarda zan kareba hannu bibbiyu kayi hakuri ban…. 
“Excuse me, ya isa haka  Yana fadan wannan yad’auki littatafanta yaduba kai tseye yasa hannu inda yamikomata wata takarda yanacewa; Welcome to Zaid Muhammad Zabir Builders Company daga yau kece Masinja’ta bcoz i don’t think you will fits in any other position bayan wannan Sabida haka nabaki zabi “TAKE IT OR LIVE IT”. 
Ma‘sinja? Ma’inah tasa’ke tambayarsa cikin rudani ” I’m a masters graduate kasa’ke duba credentials dina da kyau kila ko baka duba da kyau ba, please go through them again. By the way na manta banyi introducing Kai naba, 
sunana Ma’inah Sambo Maidugu…. Idon’t care; Zaid ya katseta cikin sananin bacin rai, lnda ya watsa mata takardun nata dika a ‘kasa yanacewa; Ki kwashe tarkacenki kiyi waje after the count of 5, And I mean it, kai tseye kiyi gida ba’nason insake ganinki anan cikin Company Sunkuyawa tayi tana hawaye masu tsananin zafi yayinda ta kwaso littatafanta d’aya bayan d’aya tafice cikin tsananin kuka da damuwa. Wajen receptionist tayi, Kai tseye tami’ka mata godiya mai zurfi Sannan tace tayi ‘kokari idon CEO yafito shima taba’sa hakuri ko ta’ji sanyi aranta. Daganan tayi hanyan waje, Inda Tashige motarta tana tuki cikin hawaye, tunani, damuwa da tsananin da’nasanin kuskuren marinsa datayi jiya.
Tuki take ahankali har takai gida, Gabantane ke fad’uwa yayinda take karasowa cikin gida, daker tasamu tashige ciki, ahaka tawuce d’akinta inda anan tazube kan gado, Sanin babu kowa agida awannan lokacin yasa ta’kara zagewa tana kuka iya sanranta, tinanin hanyarda zatabi taka’re kanta wajen Daddy take amma da dukkan alamu babu alaman wata mafita haka zata cigaba da boye sirrinta hartse lokacin bayyanarsa ta’yi. 
Ta bangaren Ma’isha kuwa tinda safe tafita tareda momy sayayya a wata babban boutique dake kusa da gidanta. Momy ta sayo mata kaya masu kyau da tsada, sun sayo jakan office dama sauran abubuwan bu’kata duk nazuwa aiki, daga nan ne suka dawo gida, Inda momy tashirya dawuri tatafi wajen aikinta. Ma’isha kuwa ta sha’fa tsahon lokaci tana kwalliya agaban madubi, bayan ta kammala tsap! tashirya cikin wata damemmen ‘bakar wando wacce turawa suke ‘kira pencil trouser, da wata Farin Riga mai doguwar hannu. Da bakin 
Gele tayi dauri akanta, daga nan tadau keyn motarta tafice tana rangwada. 
Tsabar iyayi, dukda latti datayi Saida tanemi Malam lro driver yazo daga gidansa yaja’ta a motarta yakaita office, ‘Karfe Sha biyu da minti arba’in suka ‘karaso inda ko ajinta tafito tana watsa cingam daya dade abakinta, don gudun rana yasa tad’au wasu ba’kaken madubi tasa‘kasu a idanuwarta. 
Taba‘rau wacce akeyiwa la’kabi da “No respect”. 
Tanasa ‘kafa a kofan reception wayarta tafara ‘kara, dasauri tad’aga, ganin 
abokiyarta Saratu ce ke kira “Sarah ya akayi kwana biyu”. 
Muryar Saratu ya nuna a bige take sosai yayinda take gayyatar Ma’isha Partin wani abokinsu Reza Micheal a Gala house dake cikin gidansa. 
Ai kuwa tamkar hakan takejira, domin bata bata lokaci wajen amsa gayyatar da akayimata ba. Muryarta cike da zumudi ta amsa mata cewa ga’tanan tafe yanzu kuwa, ko 
Bata lokaci bazatayi kuskuren yi’ ba domin Reza Micheal ba ya hada ‘karamin 
cha’su, inyaso koda yamma ta’ dawo wajen aikin. 
Daganan ta‘karbi ki wajen Malam Iro, Inda taja motarta zuwa area 7. Unguwa ce tama’su kud’i da dala anan gidan Reza Micheal take. Dashike wajen babu nisa da confanin ta’su, tukin mintuna arba’in kachal ya kaita, Kai tseye ta’karaso ciki. 
Yawancin Mutanen wajen a bige suke harma da mai gayya Mai aikin dakansa Reza Micheal a bige yake sosai, wasunsu suna ta’ka rawa wasu suna dabdala 
da ‘kayan abinci dakejere asaman teburin zaman kowa.
Wow!!! The most beautiful princess in the world is finally here hurrayy!!! Reza yata’so daker ya’karaso wajen Ma’isha da kwalbar shayensa a hannu yanacewa; Please everyone ku tafawa aminiyata kuma ‘kawa’ta Ma’isha Sambo Maidugu. Ganin yanayin dayake, a bige yake sosai yasa Ma’isha tanaja’ da baya, baya domin wa’rinsa ya addabeta; Thank you na‘gode sosai amma inagani ba dad’ewa anan zanyiba sabida na’ga kowa a bige yake ni ko yau inada wani uzuri mai anfani banson Insha wata ruwan kwalba. 
Fad’owa akanta Reza yayi; Come on Ma’isha chill out, kimore rayuwarki, manta dawani banzan abu waishi uzuri just enjoy yourself.” Turesa tayi iya ‘karfinta, tamike kai tseye tayi hanyan waje, bata ‘karasa 
kofan wajenba yayinda Saratu ta iso wajen itama da kwalbar a hannunta 
tanacewa; Beb lnaaa zaaki kuma? bayan na gayyatoki nan kizo muci duniyarmu da tsinke. 
Girgiza kanta tayi tanacewa;Wajen aiki zani and please understand me, wallahi I really need this job banson inje wajen a bige, Kuma ina gida tareda momcy itama banson taganni a bige. 
Maijiddah ce ta‘karaso wajen, tana tafiya kamar hawainiya, alokacin ji take tamkarwata duniya tashige yayinda ta rike hannun Ma’isha takaita wajen teburin kungiyar yan iskan wanda anan ne special guest of honor take, a wajen suka tilastamata dole ta shanye Kofi guda dukda ba’asan rantaba, haka tasha kwalbaye Biyar (5) alokaci d’aya, wanda tunda ta ta’so aduniya bata taba shan kimanin kwalbaye biyu ba, bare Uku harma zuwa Biyar. 
Jinta take asama ta bakwai tana firewa tana yawo achan, dankwalin dake kanta ta wurgar Sannan tamike ‘kanta na bala’in ciwo yayinda tad’auki Jakarta tayi waje. 
Da kafa tapaso daga gidan Reza Micheal har izuwa ZMZ Company. Tamkar mahaukaciya take tafiya akan titin wucewar motoci tana kuka tana 
neman taimako gaduk mai wucewa. Wata mota tagani baki wuluk, wacce idanuwarta sukaganta tamkar jirgin ‘kasa, razzz zuciyarta ta tsinke ayayinda jiri yadebeta tafadi, daga nan bata sake sanin inda takeba. Ba alaman motsi tattare da ita, haka yasa hannu yad’auketa chak!!! Yakaita Cikin motarsa. Inda Cikin damuwa dreba yake tambayarsa ko ya’san yarinyan, Ganin irin mamakin dake bayyane a fiskan Ogan nasa. Girgiza kai Zaid yayi yayinda yakecewa; Just mine your business. 
Asibiti zamu kaita ko gida? Dreba yasa’ke tambayarsa Cikin nunfashi daya. Gida; Zaid yafad’a alokacinda yake fifita Ma‘lsha yana share dattin aman dakejikinta; I can‘t believe this daman haka kike Yar shaye shaye ce ashe, 
Ma’inah you really disappoint me. Na’am dani kake? Dreba yajuyo yana tambayarsa cikin rud’ani. 
Rasa abun fada Zaid yayi; ba’nason hayaniya. lya abinda yafad’a kenan. 
Daganan shiru motar take har suka kai ma‘keken gidan Zaid. Suna Isa yabude motar dakansa yasa hannu ya dauketa sama yakaita d’akin baki dake cikin gidan nasa, kan gado yakwantar da ita shiko ya tsaya yanamata kallon mamaki ‘I can’t believe this“. lya abunda yake fad’a kenan tunda yadaukota har izuwa yanzu.
Bakin ciki yakeji har cikin zuciyarsa ganin Ma’inah a irin wannan yanayi ya matu’kar batamasa rai wanda shi kansa 
baisan dalilin hakanba. 
Kyau’n dan maciciji kenen yafad’a Yana murmushin karfin hali, daganan 
ya’kira layin likitansa. Cikin mintuna ‘kalilan likita ya ‘karaso. Drip yafara sakamata sannan yayi mata allura. “Doctorl hope she is going to be fine?” Zaid yatambayeshi cikin Kulawa. 
Insha Allah nanda awa biyu zata iya tashi amma gaskiya yakamata a ringa sa mata ido sabida kada tasa’ke shan wannan kwayar domin tanada ‘karfi sosai zata iya bata kwakwalwarta baki d’aya: Likitan yana fada wannan yabasa magunguna sannan yayi masa sallama yatafl. 
Tare suka fito da Zaid sabida baiga wata dalilin dazaisa ya tsaya waje d’aya da Y’ar shaye shaye irin Ma’inah ba. 
Ya rako Doctor kofar parlour, shiko yayi wajen swimming pool lnda awajen yasa“ ba sauke bacin ransa ako da yaushe. ‘Kayansa yaciro dika, dagashi se wata dan ‘karamar wando haka yashige ruwa yanata kaiwa da kawowa. 
Momcy, Daddy ni kadei ce yarka, Momsy dan Allah kifadawa Daddy gaskiya nikad’ei kika haifa;. 
Da wannan maganar Ma‘isha ta tashi a firgice tana kokarin mikewa taga hannunta a daure da drip, kai tseye ta balle igiyar, Inda tamike tana kokarin gane lnda take. D’akin tagani sama da kasa ‘kayan zamani ce acikinta 
wanda ita kanta Bata taba ganin d’aki makamancin irinsaba “Kodei gidan yankan kai aka kawo ni?” 
Ahankali tafito tana leke leke ko zataga wani wanda zai taimakamata 
Saukowa tayi tana leke, leke. Tana ijiye hannunta asaman wata teburi tahango wata takarda inda kai tseye babu tsoro tabude “Business Magazine” Hoton Zaid tagani a bayan takardan aka rubuta sunansa “Zaid Muhammad Zabir” ZMZ Builders CEO. 
Sake Baki Ma’isha tayi, harma da ido tana gannin wannan Magazine d’in tamkar a mafarki “Wannan shine Zaid Muhammad Zabir?” Tasa’ke tambayar kanta tamkar ba’kauyiya “Wowl! Sexy eyes i really like him“ Gaskiya wannan ake ‘kira “Love at first Sight”, Momcy Finally na samo miki suruki, wallahi tinda nake ban tabajin son wani mahaluki a duniya irin wannan mutumin ba. Zaid Muhammad Zabir welcome to my life. a 
Haka Ma’isha tazauna kusan minti talatin tana maganganu akan Zaid, har 
tseda wata mata tazo wajen ta tsameta “Sannu baiwar Allah”. 
Hi“ Ma’isha ta amsa mata, idanuwarta dama hankalinta duk kan wannan takardan dake hannunta. Suke
Mun shirya miki abinci a sama kibiyoni”, Matarta tafada in a polite way. Ma’isha kuwa tamike Kai tseye tana binta abaya batareda ta ijiye wannan Magazine d’in ba. 
Suna isowa matar taja mata kujera, tazauna, anan ta boye littafin dake hannunta cikin Riga, tafara ci cikin tsananin Farin ciki da annashuwa. 
Lekowa take ta Window’n wajen tanacewa; Disney world gaskiya wurin nan 
yayi ba laifi, Zaid you are my dream guy. “Assalamu Aleikum baiwar Allah, idon kin kammala cin abinci ga magungunanki Oga yace abaki Kisha Sannan ki koma gida yace ba’yasan yadawo nan ya sameki. Tana fadan wannan ta ijiye magungunan a teburin Ma’isha. Ina ogan yake? Ma’isha ta tambayeta Kai tseye. Yanachan bangaren swimming pool dinsa nacikin gida” Matar ta amsa mata sannan tayi tafiyarta. 
“A bige yad’aukoni kuma akan titi sabida haka ko kadan idanuwarsa ba’zasu taba ganina da daraja ba, zuciyarsa zata saka masa cewa, ni Yar iska ce kuma ba’nida tarbiya. Amma wa’sa da hankalinsa zanyi ta hanyan bayyana masa kaina amasayin Ma’inah Sambo Maidugu, kaga daga nan gobe mu‘a hadu a office amasayina na Ma’isha Sambo Maidugu.” 
Wannan ta‘kun Ma’isha ta shirya azuciyarta, Haka tabar abinci tafito tana aikin neman wajen swimming pool domin tayi wa’sa da hankalin Zaid tayi tafiyarta. 
swimming sunkai shida taje amma Zaid baya wurin daganan ne tayi giving_up lnda tajuya tana ‘komawa kenan tahango wata swimming pool achan wani bangare. Aguje ta’karaso wajen kuma awannan karon tayi sa’a awajen yake. Shiko yana ganinta ya ‘kara nitsewa cikin ruwa yanacewa; Me kikeyi anan? kibarmin gida ba’nason in’kara ganinki. 
Chanza murya tayi, nan ta’ke tafara magana da muryan Ma’inah; I’m sorry CEO na gode da taimakon da kayimin, Amma inaga da bakayi hakan bama da yafiye maka alkhairi. Ni Ma’inah na rigada na saba da halin shaye shaye, iyayena ma na gagaresu, Twin sister na Ma’isha itace mai hankali ako yaushe takanmin wa’azi amma ba‘naji domin na’rigada na gagaresu, a takaice dei 
I’m a prostitute (‘Karuwa)… 
Ya Isa haka ,Zaid ya daga mata hannu cikin bacin rai. Nan ne yamanta jikinsa babu ‘kaya, yafito daga cikin ruwa ya tseya ahaka ya fuskanceta yanacewa: Ma’inah you better change your attitude for good Sam bata kamance kiba. 
Take jikin Ma’isha tayi sanyi, ganin irin kekkyawan suran da Allah yaba’sa. Hawaye tafara zubarya tanacewa; Zaid kayi hakuri na rantse maka da sunan Allah zan dena wannan shaye shayen adalilin ka, Zaid kai ne zaka zamto tsandiyar shiriya’ta, I will definitely change my attitude for you Zaid. Dasauri, yakatseta “You mean nothing to me, so you better change for your own good sabida rayuwarki ne kin chanza dabaki chanza dika bazata dami Zaid Muhammad Zabir ba. Yana fad’an wannan bai tseya ta’kara furta wata kalma ba, securities yanema 
Kai tseye aka kwaso Ma’isha aka kaita waje. 
IYA ABUNDA YA SAWWAKA AYAU KENAN
CHAPTER 8 SPOILER
Ya ‘taro dikkan jama’a masu aiki a confaninsa zuwa babban d’akin ta’ronsu, conference room anan suka saba yin meeting musamman idan wani 
gagaruman project mai wahala tana gabansu. Awannan ‘karon kuwa ta’rosu yayi musamman domin ya gabatar da sabbin 
y’an aikinda ya debo cikin ma’kon nan dashike, ya debo yan aiki da dama. 
D’aya bayan d’aya yake ‘kiran sunayensu yanashedawa kowa masayinsu dakuma dalilin dayasa ya daurasu awannan kujera. Ma’inah tana zauneh a chan baya tana ganinsu, yayinda ya’kira yawancin 
dikkan mutanen wajen Amma bataji sunantaba daga nan tacire hope na’samun aiki a gurin. 
Tana cikin wannan tinanin, taji sunan Ma’isha Sambo Maidugu dasauri tamaida hankalinta akansu. lnda Zaid yakecewa; Daga yau itace Manajan masu kulada har’kokin interior decorations na nan Abuja, Na’bata wannan kujeran ne Sabida haza’kar data nuna alokacin interview dakuma takardunta na makaranta, tanada first class a fanin tattalin ‘kasuwanci ma’ana Business Management ….. 
Daganan kowa yasa tapi, Yayinda Ma’isha tafito, baki ta’kusan taba kunnuwarta tana wani blushing tana Jin dadi. 
lta kanta Ma’inah dariyan takeyi. Tana taya yayarta farinciki dajin dadin wannan babban kujeran da aka nad’a 
ta, kuma ta tabbata Ma’isha zata rike amana Kuma tayi aiki tsakani da Allah. 
Ma’inah Sambo Maidugu. Sunan tace ke bin ta Ma’isha. 
Cikin tsananin Farin ciki da mamaki tamike, dasauri ta hauro sama, tana ‘kokarin ‘karasowa wajen ta’ron mutanen yayinda Zaid ya dakatar da ita “Anan Zaki tsaya Sabida matsayinsu daban take da taki. 
Yana fadan wannan yajuya ta bangaren mutanen yanacewa; Ma’inah Sambo Maidugu itace sabuwar Ma’sinjata, duk dacewa ta’yi karatu kuma tanada tsakamako mai kyau na bata wannan masayin ne Sabida yanayin rayuwarta; she is a drunkard, Yar Shaye shaye ce, ta gagare lyayenta kuma tana ‘kokarin shiga duniyar ‘karuwanci. Aganina wannan masayin dana bata itace zata 
zamto sanadiyar shiriyarta dakuma…. Bai ‘karasa kalmar dayake kokarin furtawaba, yayinda Ma’inah ta fito aguje tabar wajen tana hawaye masu tsananin zafi. 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]