[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 4 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE
CHAPTER 4
Bankado kofa yayi yashige kamar daga sama yafado, da kaga fuskarsa zakasan akwai alaman damuwa da bacin rai. Muryarsa na karkaruwa ayayinda yafara ambatan sunan Matarsa “Safeenah, Safeenah ina kike neh, Safeenah”… 
Shigowarsa keda wuya, yayi Kicibus da Safeenah, yayinda take ko’karin bude masa kofan dakin; “Baban Ma’isha Lafiya kashigomin daki haka ko sallama babu? Ta fada a tsorace. 
Tabe baki Alhaji Sambo yayi ya fuskanci gabas yanacewa “Ya Allah wani irin laifi na’aikata kake sakamin da wannan hukuncin, Ya Allah kagafartamin duk laifukan dana aikata maka”. Zuciyarsa ce ke tafasa, idanuwarsa suna kwalla wanda kan nuna tsananin radanin dayake damunsa a zuciya. Tsayawa Safeenah tayi Jugumm tana binsa da kallo da idanuwan tausayi tace: Mijina yau kuma dame kazo da ita? Ko dai matsalar tsakaninka da Yaya Saminu ne? Tafada cikin sanyin murya. “Safeenah, matsalar Yar muce Ma’isha, munyi kuskuren tarbiyantar da ita tun afarko gashi yanzu muna samun sakamako Imagine Yar da muka Haifa ta gagaremu tafi’karfin mu kuma bata Jin maganar mu. Safeenah wannan wani irin rayuwa neh? Yafada cikin sanyin murya da fuskan tausayi. Matsowa Safeenah tayi har kusa dashi ta rike hannayensa tanacewa; Ma’isha bata gagaremuba kuma ko kadan bamuyi kuskure wajen bata tarbiya ba, ka tuna Ma‘isha jinin mune kuma mun haifeta da Iarura yakamata mu ringa binta a hankali har zuwa lokacinda zata mallaki hankalin kanta domin ita yarinyace yakamata ka fahimceta. Mikewa yayi wuf, yahada da ajiyar zuciya yanacewa: Saukowata daga jirgi Gidan Ma’isha nawuce inda na tsameta tareda wani shashashan yaro wai shi saurayinta, suna zaune su kadai suna soyyayya nayi kokarin janyota mudawo gida amma Ma’isha ta nunamin fin ‘karfi,jefoni tayi awaje tayi cikin gida… Awannan lokacin Safeenah ta ‘kasa rike hawayenta, kai tsaye tabarsu suna zuba iya san ransu…. 
Ata bangaren Ma’isha kuwa a kwance take kan gado tana rusa kuka tareda da’nasanin abubuwanda ta aikatawa Mahaifinta, Sedai babu yadda zatayi hakan shine kawai zai iya taimaka mata gamida zancen komawa Gidan Daddy, duk dacewa tana kewar Momcy sosai an Kwan biyu Momy Bata ziyarcetaba, Kuma harga Allah tanason ta ziyarcesu Amma babu Hali. Wannan dalilin yasa take dada tsanan Ma’inah Wanda ta tsanadiyarta ne ta rabu da dukkan Farin ciki a rayuwarta, ta rabu da Daddy dakuma Momcy. Da wannan tunanin na bacin Rai da bakin ciki Ta mike Kai tseye tawuce bathroom anan ta wasa ruwa ajikinta tafice zuciyarta na tafasa ta zauna gaban Mirrow. 
Fuskar dake fuskantar ta cikin Madubin yasa tasa kafa tarusa ta Pakzzzz… madubin ta watse tsakar daki. Inda ta zube ‘kasa tana rusar kuka mai kona zuci “Ma’inah meyasa kike biye da rayuwata? Meyasa kika shiga rayuwata, Why? Na tsaneki Ma’inah why do you have to take everything from me why Ma’inah? Har madubi idan na duba fuskarki nake gani, Ma’inah 
you are my worsed enemy I hate u Bata taso inda takeba, tasa hannu ta lalubo wayarta dake saman drawer, inda takai layin Hamza Scissors. (abokinta) A bugu daya ya daga wayar “Maisshhhhh Ya akayi toh? Saida taja doguwar nunfashi Sannan tace; Scissors kahada yan gidanka da kungiyar su Suratu kuzo gidana na shirya mana party. Party Kuma Hajjaju? yau Kuma me yafaru? Na san abokiyar tawa bata shirya mana chasu se in ranta ya baci Ma’ishhh waya tabomin ke neh?” Scissors yayi responding cikin muryar Kulawa. Kuka Ma’isha tasaka tareda cewa; Scissors it‘s Ma’inah she is trying to distroy my life Don Allah kuzo I really want to drink shiyasa nashirya mana chasun zamu shakata sosai. “Calm down Friend I will always be there for you karki damu zamu kawo  🍾 iya son ranki”…. Da wannan magana Scissors ya katse wayarsa, Ma’isha kuwa se yanzu jikinta yayi karfi inda ta taso tashirya cikin wata Yar guntun Riga mai fllawowi Sannan ta rangada kwalliya kamar yadda tasaba. 
Cikin mintuna kalilan tasa aka shirya mata gidan gwanin sha’awa, Aka saki kida tamkar gidan gala…
Ta bangaren Ma’inah kuwa tajima sosai a parlourn Daddy tana jiran shigowarsa. Tunda yadawo take zaman jiransa bai fitoba. Aiko tana mikewa daniyar tafiya ta hango Abban nata yana shigowa, batayi dayan biyu ba kai tsaye ta rungumosa domin ta dade bata hadu dashiba tun komawarsa America yanzu watansu hudu kenan basu hadu ba sau yau. 
“Daddy sannu dazuwa, Kuma ya banganka da Ma’isha ba? Bayan jiya kayimin alkawari cewa Zakuzo tare kayimana wani albishir wanda zamuyi Farin cikin jinta matuka” Ma’inah tafada cikin nunfashi daya. Kada kai Daddy yayi yanacewa “Yes my dear har yanzu dai albishirin tana nan Sedai wa kekadai ce because I don’t think your sister will be happy with it. ‘Karasa kalmaryayi kan kujera inda ya dauki lemu Yana Sha Yana shafa fuskan Ma’inah. “Come on daddy it’s okay babu komai Kuma karka bata Rai domin na tabbata Ma’isha zataji dadin Albishirin nan maybe not now, kadai ‘kara hakuri zata dawo garemu Insha Allah” Ma’inah tafada tana murmushin nan nata Mai bayyana dimples din fuskarta. Gyara muryarsa yayi, ya gyara zama Sannan yafara magana ‘Ma‘inah Dear kin kammala Makarantarki dasa kamako masu kyau, kuma awannan karancin shekarun wanda yanzu za’a iya kiranki ‘young graduate, I’m really proud of you Yata. Da wannan nakeson na miki wata muhimmiyar Albishir wanda na san zakiji dadin hakan sosai domin ako yaushe Mominki kan ‘kirani tana fadamin cewa kina matukar bukatan aiki, kin gaji da zaman kadaici a gida. 
Haka ne Daddy, nakan gaji da zama Ni kadai cikin gida Sabida babu sa’ata; Ma’inah ta katseshi cikin sanyin murya. 
Ki kwantar da hankalinki Yata Insha Allah kin samu aiki Kuma a wata babban confani Wanda take da branches a kusan duk fadin duniya. Babban Branch dake nan Abuja tafi duk wani confani dake nan ‘kasa Nigeria Kai harma Afrika gaba daya. Appointment letter na samo miki ke da yar uwarki Ma’isha, Amma na’san ita Ma’isha zayyi wahala tahada wurin aiki tareda ke, zanyi kokarin samo mata wani inda hali. Ke koh kiyi kokari gobe da sassafe kije interview i know you can do it, although sunada rules sosai Kuma basa tolerating lazy people damasu hazaqa suke aiki,Amma na tabbata zaki samu kiwuce domin kinada kwazo dakuma hazaqan baki d’aya. Kukan farin_ciki Ma’inah tasaka, ganin Mahaifin nata ya yarda da ita sosai Yana kuma da tabbacin cewa zata wuce Interview tasamo aiki achan. “Thank you Daddy, nikuma da yardan Allah bazan watsa maka ‘kasa a ido ba. Alkawarinda zan maka kuwa shine ka kwantar da hankalinka aiki dai lnsha Allah ka kaddara na samu domin zanyi iya ba ‘kin ‘kokarina wajen samun wannan aikin domin na tabbata dawata muhimmiyar niyya karike wannan appointment letter daga chan ‘kasar Amurka zuwa nan Nigeria da yardan Allah niyarka bazata fadi abanza ba. Da wannan magana ta mike, babu inda ta tsaya se da’kin Momy inda ta sameta zaune a gaban computer tana danne danne. Da sallama tashige dakin kamar yadda tasaba “Assalamu aleikum Momy surprise”. Tafad’a yayinda take ‘kokarin boye appointment letter’n da Daddy yabata. “What is it my dear? Momy ta amsa hankalinta duk akan computer da take dannawa. 
Matsowa tayi a hankali tanacewa : Surprise” Sannan taciro appointment letter’n ta ajiye a gaban Momy. 
Se yanzu hankalinta yadawo kan Ma’inah inda tabud’e appointment letter’n ta ‘karanta “Congratulation my dear, nayi matukar Farin ciki”. Iya abunda Momy tafad’a kenan Sannan ta maida mata da takardan. 
Jiki a sanyaye tasa hannu takarba, daman ta saba dahalin mahaifiyar nata, aganinta Momy ta’fisan Ma‘isha akanta, domin takan chanza idon tana tareda Ma’isha kuma takanyi Farin ciki matuka idon Ma’isha tasamo cigaba. Wannan tunanin takeyi ba! takai dakinta ba, ta tsaya gaban wata babban inlajiiment ta hotonta da Miemah. Tace Teddy I miss u so much, Se yaushe zakizo Abuja wajen Teddinki I really miss you Twiny… 
Bata matsa inda takeba, wayarta tafara ‘kara “Yar Halak Miemah ce” Dasauri tadaga “Teddy ya kwana biyu. 
“Banza shine koh ki ‘kirana bayan kinsan Miematun tayi kewarki sosai sosai how fa toh ya gida?” Miemah ta amsa cikin sanyin murya. 
Lumshe ido Ma’inah tayi tareda cewa; Ke Banza Albishir, na kusan zama Millionaire Daddy yasamomin Aiki a Confanin KSM Builders. Ihu Miemah tasaka “Wayyo Allah Teddy da gaske kike you mean KSM Builders dai wanda nasani?’ 
Uhum; Ma’inah ta tabe baki, “Teddy mantawa kikayi ne CEO Confanin Kashim Sa’ad Mahmud Ogan Daddy neh a Contract da aka bashi last year Sailub Investment. “Ai niko na’san Kashim Sa‘ad Mahmud ba wannan dattijon damuka taba haduwa a sailub ba, wannan wanda Kawu Sambo yake ‘kira Master KSM”.. “Shi ne dai wallahi… Kin ga’ma tunda har ya sanni kuma ya san mahaifina bazai bata lokaci wajen bani aiki a Confanin saba. Ke dai bari se anjima zamuyi magana. kuma kifadawa Umma cewa zan kirata anjima kadan ita da Abba susamin albarka a sabon aikin danake Shirin samu. 
Dawannan takatse wayar. Inda tabud’e akwatin takardunta na makaranata tana hadasu d’aya bayan d’aya cikin jakar Office. 
Kida ne ke tashi tun awaje zakafarajin bugu da Sauti mai haukata kwakwalwa. A cikin gidan kuwa ko ina mutane kake gani maza da mata daga masu taka rawa, masu Shan ruwan kwalba dama sauran baki Wanda suke barci rigingine tamkar matattu. Chasu iya chasu suke ta kwasa cikin gidan Ma’isha. “Every one Cheers, enjoy the party” Ma’isha tafada tana d’aga musu kwalbar dake hannunta “Don’t decieve your selfs, A gidan Yar Sambo Maidugu kuke, feel free kowa yaci, 
yasha ya more rayuwar daniya because it is a free world. 
Hurray!!! Ma’isha muna yi dake wallahi, idon babu irinku a ‘kasar nan I don’t think irinmu zasu rayu a duniya’ Enjoy the party. Wani matashin Saurayi yafada shima datasa kwalbar a hannu. 
MA’ISHA_POV 
Enjoy the party everyone; Se yanzu na sauko daga stage wajen rawa. Saukowata nawuce wajen ‘kawata Mai_jiddah Yar minister’n kudi ta Abuja, itace wacce nafi ji da ita aduk cikin ‘kawaye na domin kekkyawa ce tanada aji kuma Yar babban gida ce. Anan na tsaya muna fira jifa jifa, Inda ‘karar wayata ta katsemu, Sunan momcy nagani a fuskan wayan, ban tsaya wata tunaniba, nan da nan nadaga “Momcy na ina wuni”… “Kizo gida ki tsameni yanzun nan inason muyi magana” Abunda momy tafada kenan sannan takatse wayarta. 
Wannan ne kaya kala ta bakwai wanda tun dazu nake aikin gwadawa domin insamo ‘kayanda zasufi dacewa aranata ta farko a office Kuma wallahi duka basumin ba indai ara’ayi na ne, domin so nake infito daban ga sauran ma’aikatan domin hakan ne zaisa Master KSM yayi saurin bani aiki kuma a babban kujera Wanda Daddy zayyi alfahari matuka. 
Hayaniyar danaji a palour yasa nafito batareda naciro kayan dake jikinaba “Ma‘isha sannu da zuwa, amma lafiya kike sauri haka” Na tambayeta Kai tsaye ganin irin gudun datake tana haurowa upstairs. Shareni tayi kamar yadda tasaba, Inda ko juyawa batayiba, tawuce bedroom din Momy. Binta a baya nayi a hankali na labe a kofar Dakin Momy ina sauraronta. 
Momcy sauri nakeyi nabar mutane a gidana ko meyasa kike nemana? Mikewa Momy tayi taredacewa; Ga wannan appointment letter ce Daddy’nki yakawo miki daga America. Tafad’a yayinda take mikomata takardan a hannu. “KSM Builders Company, wow!!! Momcy thank you so much. Kuma zan Kira daddy inmasa godiya da yardan Allah gobe da sassafe zanje Interview awajensu thank you so much” Tamkar korota akeyi tana fadan haka tajuye tayi tafiyarta…. 
Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun; lya abunda Ma’inah ta iya fada kenan domin dazaran Ma’isha ta samo aiki a confanin KSM duk wannan Shirin da takeyi a banza take. 
IYA ABUNDA YA SAWWAKA AYAU KENAN…. 
xCHAPTER 5 (Five)SPOILER x 
Mutane ne kota ina akan hanyan, Motoci iri daban daban, duk sun rufe hanya babu wurin wucewan mutum Barre ta mota. Mamakin hakan yasa ma’inah fitowa daga motarta, daman saura mintuna ‘kalilan tayi latti zuwa wajen aiki “Such a crowd meyake faruwa anan neh?”. Ta tambayi wani Security dake tsaye cikin rundunar mutanen. 
Hajiya yau hanyan nan bazata biyuba domin Oga yasa anrufe duk hanyoyin shigewa, Sabida akwai wani dan aikin damukeyi anan. ‘Dan Sandan ya amsa mata kai tsaye. “Wace irin aiki? Ma’inah takatseshi cikin bacin rai “Shi Ogan naku bashida hankali neh? Ko don shi kadai akayi hanyan? muma nan aikin zamu se yaya maza kubudemin hanya in wuce saboda banida lokaci ba nason in makara. 
Wani Matashin Saurayi dake tsaye a gefensu neh ya soma bakinsa cikin maganar “Hajiya ki iya bakinki, gwara ma kijuya kiyi gida domin idan Mutanen Master Zaid Muhammad Zabir sukaji wannan maganar dakikeyi bazayyi dadi ba, domin Zaid ba mutunci ne dashiba. “Zaid Muhammad Zabir” Shi waye? Ma’inah ta nanata Sunan a hankali. 
MA’ISHA 
Da sassafe karfe biyar da rabi dadai Ma’isha ta iso wajen aiki. nan Sake baki tayi tana kallon ginin Confanin wanda k0 achan America se wane da wance suke Gina irinta. Tamkar bakauyiya tashige tanata kallace kallace Inda wani Security ya tse da ita “Madam from where?” 
Se yauzu hankalinta yadawo, lnda ta chanza tafiya tana rangwada “Excuse me security ina ne ofishin Oga Kashim Sa’ad Mahmud?” “Madam kina nufin bakida labari cewa Oga Kashim Sa’ad Mahmud ya tsayar da wannan Confanin?”… Ma’aikacin ya tambayeta cikin mamaki. 
Tseyarwa kuma? kaman ya? Ma’isha ta tabe Baki tana tambayarsa cikin rudani. 
Kai tseye Ma’aikacin ya amsa mata cewa; Kashim Sa’ad Mahmud ya tsayarwa Zaid Muhammad Zabir wannan Confanin wanda yanzu takoma ZMZ Builders. “Zaid Muhammad Zabir” Ma’isha ta nanata sunan a hankali…. 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]