[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 3 - Bankinhausanovels
Tue. May 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE 
CHAPTER 3
Alhaji Sambo da Safeenah kwana sukayi ido hudu babu wanda yayi gengedi cikin su bare barci. Tunanin hanyarda zasubi su bullowa Ma’isha maganar komawa ‘kasa Nigeria suke, dakuma hanyarda zasubi su sufadamata batun Yar uwarta Ma’ina A Daren suka 
kammala duk shawarwarinsu. 
Da sassafe bayan sallar asuba Momy da Daddy duk suka koma dakin diyarsu Ma’isha suka kwanta tare da ita, tamkar barci suke har zuwa lokacinda ta saba tashi (Karfe goma) basafiya. 
A hankali tataso domin kada tatashesu, Cikin sananin Farin ciki ta rungumosu sannan tayiwa kowa kiss “I love you sooo much .parents, and thank God you all love me back” Da wannan managar tamike cikin Farin ciki tawuce bathroom anan tayi brush, tawasa ruwa ajikinta sannan tafito. Aiko tana fita taga babu kowa a dakin se Nanny (Saratu) wacce take kula da ita tun tana ‘kan’kanuwa. ‘Na bar Momcy da Dad anan kan gadona suna barci ina sukaje?Ma’isha tafada cikin rudani ‘Ke Saratu kurmace ke? ba tambayarki nakeyiba?‘ 
Murmusawa Saratu tayi ‘Kwantar da hankalinki Yata, Momy da Daddy suna nan Parlour suna jiranki ….. 
Ma’isha ce tayi saurin katseta ‘What? wa kike ‘kira Yarki, God Forbid, Over my Dead body, Ni ba Yar kowa bace face Yar gatan Gidan Sambo Maidugu, I mean Yar Safeenah da Sambo got it? Kuma babu wanda yabaki damar ‘kiran Momy na da Daddy na dawannan sunan dakikayi kuskuren ‘kiransu ayanzu domin nice kadei nakeda damar wannan. Dirty Woman, yi maza kiciromin kayanda zan saka.. Duk wannan maganganun da tayi Saratu bata tanka mata ba, Jan bakinta tayi, tayi shiru kamar wacce bata wajen domin tafi kowa sabawa da halin Ma‘isha, kuskure kadan zasuyi fada. ‘Spoil Brat’ Tafad’a ahankali yayinda take bude 
wardrobe din Ma’isha..
Doguwar bakar Riga ta sanya Wanda sukayi dedei da farar fatar jikinta, inda Kai tseye ta gudo Parlour tana neman Momy da Daddy. A tsakar falon tayi Kacibus da akwatunan kayyakinsu wanda already anrigada anyi packing komai, da dukkan alamu dei ita kadei akejira. Washe baki tayi tanacewa “Momcy Ina kuma zamu? Kodei Allah ya amsa addu‘a tace? 
Daddy dake fitowa daga cikin dakinsane ya sanya bakinsa cikin maganar tasu inda yake tambayarta addu’ar me kikeyi? 
Juyowa tayi tana cewa; Haba Dady ai Kai kanka yakamata ka gane cewa na gaji da zama 
guri daya, ko mantawa kayine tunda nataso ban taba barin ‘kasar nan ba, shiyasa ako 
yaushe nakanyi addu’a kan Allah yakai ‘sahon rai insamu inga gata kaga awannan 
lokacin babu wanda ya Isa yahanani yin abunda naga dama a Duk fadin duniya because narigada na samo Freedom…
Ya Isa haka Maisha: Mommy takatse ta “‘Maza kutaso mutafi, kuma kisani wurinda muke zuwa ayanzu ba lallai bane kisake dawowa nan Sabida bakida tarbiyyarmu ta hausa, ‘Dabi’un ki duk kin kwaso sune anan d’abi’un arna Baturai, wa’enda k0 kad’an babu imani a zukatansu. 
Da wannan magana tamike ranta abace tarike hannun diyarta suka wuce. Ma’isha ‘kasa magana tayi domin tunda take bata taGa ganin bacin ran Momy ba se yau. 
NIGERIYA
Ta Gangaren Ma’inah kuwa babu wani wanda yafad’amata dawowar Iyayenta Nigeria, asalima tunjiya take ganin Umman ta cikin damuwa kuma kamar akwai abunda take boye musu ita da Miemah sunyi kokarin tambaya but she is not interested. Abba kuwa baya zama a Maiduguri bare yasan halindasuke ciki a gari, ko yaushe Yana Kano yana kokari da sana’oinsa. 
Hada baki sukayi akan su ringa sanya mata ido k0 zasu gane damuwar dake damunta wanda ko kadan ba tason susani. 
Karfe hudu na yammaci Umman tasu tafice cikin damuwa taja motarta ta tafi. Ma’inah da Miemah kuwa bin motar nata sukayi da adedeita sahu inda ta tseya bakin wani babban offishin Lawyoyi tashige Kai tseye. Ma’lnah da Miemah suka sallami Mai adedeita sannan sakabi sahunta, a bakin kofa suka labe suna sauraronsu. 
Muryan wani dattijo ne yafara magana “Mrs Saminu muna sane da zuwanki nan domin kinbi duk offishin Lawyoyi kina basu ‘qaranda ke kanki idon ke lawyer ce dawuya amshi irinsa. Sambo yanada arziki kuma ki yarda ko kar kiyarda yarigada yabiyamu kudi masu yawa Daman yasan irin haka zama iya faruwa. Muryar Umma sukaji tana kuka “Lawyer kataimaka. Wallahi Ma’ina tarigada tazama Yata domin Nice nashayar da ita Kuma shi kansa Sambo yace yabani itane har abada, believe me daga baya ne yachanza magana dasukaga Yarsu dake chan batada tarbiya Kuma tafara kauce hanyar musulunci. Kuma Ma’inah tarigada ta saba da yata Miemah bazasu iya rayuwa babu….. 
Umma bazan koma wajen Momy ba; Ma’inah tashige oflshin tana hawaye masu zafi. Miemah dake labe a bakin kofarma shigowa tayi tana kuka “Umma baza’a rabamu ba koh, Dan Allah Umma kifadamusu cewa Teddy na ba’tason rabuwa damu Sabida ita yarkice Kuma ‘Kanwata ko Umma. Bata ‘karasa furucinta ba, Ma’inah ta rungumota “Teddy wallahi babu inda zanje ina nan taredaku da Umma dakuma Abba… “Ku dakata; Wani dattijo yamike yanacewa; Mrs Saminu yakamata ki kwaso Yayanki kutafi gida Sabida nan ofishine ba wajen shirya Fina finai ba. Jikin Umma a sanyaye tamike, tashare hawayenta sannan ta rike yayanta suka fita ofishin suna kuka kaman waenda aka kaiwa sa’kon mutuwa. “Karfe biyar zamuzo gida mudauki Ma’inah musata a jirgi takoma Abuja Gidan mahaifinta” wani saurayi yabiyosu da maganar sannan yakoma cikin office. 
ABUJA NIGERIA””‘“'””‘””” 
Daddy is this my house? Wow thank you Dad I love you sooooo much: Ma‘isha tafada cikin mamaki; Mommy you don’t have to worry, I will be happy here as far as our family is complete karku damu na yarda muzauna a Nigeria nidei matsalata kawai bansan ganinku cikin damuwa… Duk wannan maganganun datake, Mummy Bata Tankamataba, Sabida hawayendake kokarin zubo mata Wanda ko kadan batason su subuce. 
Princess we have a su rprise for you “Daddy yayi ajiyar zuciya yafada. Shima yana komarin rike hawayensa. 
What surprise? Daddy meyasa kake kuka? Mumcy meyasa daddy yake kuka: Ma’isha ta tambaya cikin rudani, awannan lokacin itama hawayen suna kokarin tsirarowa a idanuwarta domin tunda take bata taba ganin lyayenta cikin damuwa irin hakaba. Safeenah ce tayi saurin katseta “Ma’isha ki gafartamana” Ta ‘kasa rike hawayenta awannan karon. Rungume yarta tayi tana cewa: Alhaji maybe this is not the right time. yakamata ka shiryamana Viza gobe mukoma America. Inaa, Shine kadei abunda Sambo yafada Sannan yafice. Bai dade da fitowa ba, yadawo tareda Ma‘inah: yayi ajiyar zuciya yanacewa 
“Ma‘isha Surprise, this is your twin sister, mun boye miki wannan maganar ne sabida yanayin lafiyarki, kinsan ba muson ganin bacin ranki. We love you so much Ma‘isha shiyasa bamu fad’amikiba tun a farko ba… Whatttttt
Ma’isha ta yi matukar kaduwa dajin wannan sirrin da suka dade suna boyemata. A ranar babu irin halinda batanuna musuba. Nuna musu tayi zata iya kashe kanta dazaran sun hadata gida tareda Ma’inah saboda duk duniya babu wacce tafi tsana irinta. Hakan yasa Samba ya sai mata gida takoma chan tareda masu kula da ita, Ma‘inah koh tazuna tareda lyayenta, duk dacewa batasan hakan tilastawa kanta tayi Sabida kada tabatawa lyayenta rai… 
“FLASHBACK ENDS”””‘ 
TAKAITACCEN LABARIN MA’INAH DA MA’ISHA KENAN, KUBIYONI CIKIN LABARIN KUJI YEDDA ZATA KASANCE. 
DO NOT GIVE UP, KEEP ON FOLLOWING LABARIN TANADA ABUBUWAN TAUSAYI, MAMAKI DAKUMA AL’AJABI AKWAI KUMA BABBAN DARASI WANDA ZAKU FAHIMTA IDAN LABARIN TAYI NlSA. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]