[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 13 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE 
CHAPTER 13
“Banza dan sa ido meye naka aciki, ana ruwa kuna kIrgawa, Wawa Talaka ahaka zaka ‘kare Mallam Garba Shashasha kawai. Amsarda Maisha tamaidowa Mai gadin gidansu kenan yayinda ya tambayeta dalilin fitowa datayi aguje babu mota kuma da akwatuna a hannu sekace wacce aka ‘koro ko wacce take barin gari. “Yarinya da tsufa na kike fadamin wannan munanan maganganun, Malam Garba dakike ambata yanzu mahaifi nane kuma Allah yayi Masa rasuwa, Aiko ba’ zaki bani girmaba kya baiwa mahaifina koh… 
Da sauri Maisha takatseshi ‘ To hell with mahaifin naka,Ai sunan kowani talaka kenan Malam Garba, a zuri’ar ku akafara ‘kafa tu’tartalaucin duniya, dangin matsiyata kuma Allah wadaran tsufan naka tunda dei harkai furfura bakada ko sisi. Dawannan tabankado kofa adedei fuskarsa tai waje. Shiru Malam Lado yai yana binta da kallo hartseda ta bacemasa “Aiko duk dacewa ba’na banbanta tsakanin yan biyun nan Ma’inah da Maisha na tabbata wannan masipappiyar Yar Amurka nan ne Maisha, indei haka yayan amurka suke toh Allah wadaransu da rashin tarbiya, Allah kuma ya shiryesu Dan darajan Annabi. 
Adedeita tsahu ta tseyar cikin masifar sauri taturo akwatunanta aciki “Malam ZMZ Private hospital zaka kaini, yi sauri dan Allah. Hajiya ina ne kuma jet m jet. Tsohu Mai adedeita ya tambaya, Kiyi magana yedda zan ga’ne ….. Doguwar tsaki Maisha taja ‘inna lillahi wa Inna ileihi rajiun Bawan Allah anan Abuja kake kuwa? Imagine ZMZ is the most popular private hospital across Nigeria amma baka san taba kana mai adedeita haba tsohu wani irin jahilci ne wannan, Kai banda talaucin ma gajahilci A’uzubillahi, asibitin Zaid Muhammad Zabir 
zaka kaini. 
Dariya mai adedeita ya tsakar mata “Ayyo se yanzu naga’ ne, Allah ya huci zuciyarki gimbiya ai maganar ta ‘kine kinayinta kaman turawa harshen ki a dunkule aimin afuwa. Da wannan yaja machine dinsa yafara tuki.
Idanuwarta a rintse suke tinda sukazo asibiti bata budesuba, se wasu zazzafan hawayen dasuke gangarowa kan tattausar fuskarta. Baki kirin take ganin zuciyarta dukji take ta tsani kanta, tse yanzu tafara gane dalilin tsanar da Maisha take mata tun suna ‘kanana, laifin tane, domin tin afarko Data cigaba da zama taredasu Umma a Maiduguri da zai fiyemusu kwanciyar hankali Ma’isha ce yar uwarta kwara daya wacce take matukarji da ita amma ta tsaneta bata kaunarta kuma bata alfahari da ita. Da wannan tunanin tadauwa ‘kanta Alkawari cewa zatayi iya bakin kokarinta don ganin ta ‘kauracewa duk wani abu dake batawa Yar uwarta rai kuma se tayi kokarin hada kawunansu. 
I love you so much Maisha. Tafada a bayyane sannan tabude idanuwarta ahankali tana ‘kara zubda kwalla. I can’t believe you Ma‘inah, duk wannan dukan datayi miki, you still love her. Zaid ya tabe baki cikin mamaki, guntun tsaki yaja “atunanina ta shi zakiyi kina tambayana Chinese Prison Wanda ya’kamata mu aika ta ko irin psychiatry’s (gidan mahaukata) din nan sabida da dukkan alamu hankali bai ishetaba …… 
Ya Isa haka Se yanzu tahangoshi chan yana zaune akujera se wani tutturo ‘karamin ‘bakinsa yake yana kashe idanuwansa duk haushi ta addabeshi “Maisha must pay for what she did se an koyamata hankali. 
Sake Baki Ma‘inah tai tana ganinsa da idanun mamaki wai me ma Zaid yakeyi anan asibitin tareda ita anya kuwa Zaid Muhammad Zabir ne ZMZ Bulders CEO take gani Ko dei gizo ldanuwanta suke mata “Me kakeyi anan Sir? Nan take yami’ke cikin sassanyan murya yace “Ma’inah from now on please call me Zaid because we are teaming se mun samo miki Justicel mean Maisha must pay for her deed. 
Dasauri ta girgiza Kai “No sir, Maisha Yar uwa tace kuma ba nason ayimata komai sabida kai ba’rene cikinmu bakagama sanin ha’laiyar muba tukunna, Nice mai laifin anan, so please you just have to mine your own business Sir. 
Ku’kurl, kurkukkur!, Kakeji ‘karar adedeitar da Maisha take ciki, se yanzu suka ‘karaso 
asibiti. Babu abunda kakeji cikin keken se mugun tsakin da Ma’isha take tun shigewarta 
tana huci haushin Adedeitar takeji tamkar ta  kowa yahuta. “Wannan banzan machine din naka wallahi gwara kawai ka ballabata kahuta da wahala domin 
iskace kawai take wahalar da Mai kayan Kara. ‘ Mai Adedeitar bai amsaba, haka ta kwaso akwatunanta tafice “Malama kudin fa? Muguwar tsaki ta tsakar masa “Ba’nida kudi toh, dawannan akolar keken naka kake wani tambayata kudi, Money hungry. Murguda masa baki tasakeyi sannan tafara tafiya. Allah ya Isa, Amsarda ya maido mata kenan sannan yaja machine dinsa yatafi. Ko ‘Dar Maisha batajiba haka ta’karaso cikin asibiti tun akofa akasa ta ijiye tarkacenta sannan ta’karaso, gun reception tafara zuwa tana tambayansa ko akwai wata mai kamada ita wacce akayi admitting a asibitin, Aiko dasauri ya amsa mata cewa sunanan sama daki mai lamba shida tareda CEO Asibitinsu. Ko godiyarta bai samuba haka tahauro sama a guje tana Allah Allah suhadu da Zaid tun kam ta ‘karaso ciki sabida ganin Ma’inah awannan lokacin zai iya sata hawanjini domin akan Zaid zata Iya hallaka mutum har lahira. 
Aiko tana sa ‘kafa karshen matakala se ga Mutumin “Zaid” tafada cikin farin ciki, wayar dake hannuntane ya fado ‘kasa yayinda ta’kara kuremasa ldo tanacewa I‘m sorry Zaid please karkayimin haka, Zaid wallahi Sanka nake, Kuma kai ne tsanadiyar fadan damukayi Ni da Mainah, wallahi zan iya jure komai Amma banda rashin ka, please you need to Understand me Sir I love you so much, lnaga kawai kafadamin abunda zanyi maka wanda zaka yarda dani har muyi aure Kuma idan kanason nabawa Ma’inah hakuri fine wallahi 
zanyi adalilin ka….. 
Bai tankamataba wayarsa yafitar cikin aljihu Kai tseye ya’kira layin Security, minti daya Basu ‘karaba nan da nan suka ‘karaso wajen “Take her out” yafada cikin sanyin murya Wanda idan bakasa hankali akansaba ba lallai ne kagane abunda yakecewa ba. Babu musu suka kwaso Maisha sama, wacce batasan hawaba bare sauka jinta tai kurun ahannun katti 
inda suka sauketa kasa hargate din fita, akwatunanta suka jefota dasu sannan aka rufe gate. 
“lnnalillahi wa Inna ileihi rajiun, Yar Sambo Maidugu yau ake wulakanta, Maisha Sambo Maidugu yarinya Mai millioyi da kadarori aka wulakanta ayau. Toh Wallahi this will be the first and last wannan bazata ‘kara faruwa dani ba. 
Mikewa tai cikin tsananin bacin rai ta gingimo akwatunanta tamkar mahaukaciya ta tseida mai taxi. Tukin awanni biyu ne kacal suka ‘karaso gidanta shima wannan mai taxin Saida sukayita rigima har suka tara jama‘a awajen dalilin biyan kudin mota, akarshe wani mutumi ne yabiyamata sannan kowa ya watse. 
“Banza dan wahala. Tana fadin wannan tafara bubbuga kofar gate din gida tun tanayi a hankali har tanemo sanda tanata bibbigewa tana ihu cewa Mai gidan ce abude mata. 
Amma duk wannan ihun da takeyi babu amsa ko motsi aciki. daganan ne tafara kwalawa Mai gadi ‘kira, har yanzu dei babu motsi cikin gidan alamu sun nuna cewa duk an korosu. Layin wayan Habu mai gadi tasaka, cikin damuwa tayita goda layinsa bubu network shima da alamu ya koma ‘kauyensu. 
Salati Maisha tafara saukarwa tana mamakin Saminu, yaushe sukayi maganan gidan har yafara tsara dokokinsa aciki, Kuma shi waye da zai koramata masu aiki wa’inda suka dade da juna tun tana kankanuwa. ‘ 
Abba har ka fito, yajikin naka? Asad yami’ke cikin girmamawa yana kokarin karbomasa jakardake hannunsa. “Kai gafara nan Malam bakada hankali ne Kodei makaho ne kai? Makaho kuma? Asad ya’kara kuremasa ido cikin mamaki yace Abba ban gane abunda kake nufi ba kuma… 
Bai ‘karasa maganar tasaba Saminu yaja masa tsaki a fuska “Ba’ka gani ne kodei dan shaye shaye ne kai? Ka taba ganin Sambo cikin shiga irin wannan kodaddun kayan? Sunana Saminu dan uwansa amma ni ba azzalimi bane irinsa sabida ban tabacin gadon marayu ba. Amsarda ya maido masa kenan. Asad Koh shiru ya tsaya tamkar gunki yana binsa da kallo har tseda ya bacemasa, har yanzu mamakin bai ishesaba lekansa yakeyi 
sanda yashige dakin da Daddy yake sannan ya sauke ldanunsa yashiga tunani. 
“Sambo inada wata muhimmiyar magana danakeso muyi ni da kai. Saminu yafada kai tseye babu tsoro ko tausayi a fuskarsa. “Haba Kawu bakaga halinda yake ciki bane, bashida lafiya dakyar likitoci sukayi dashi sannan yatashi daga Suma wacce ….. ” Ke Safeenah ba dake akeba kawai kirufe mana baki. Saminu ya katseta. Se yanzu Daddy yabud’e bakinsa yai magana inda yakecewa “Sambo indei batun kudaden jinyar yarkace (Miemah) toh kayi hakuri bazan iya bakasuba. Me kace? Saminu ya’kara bude kunnuwansa yana tambayansa Kila k0 baiji sosaiba “kace bazaka iya bani kudaden ba? Kwarai da gaske haka nafada. Rasa abun fada yayi, Nan take zuciyarsa yafara dukan Uku uku, Saida yashare zufandake fiskarsa sannan yace “Wallahi sena tona maka Asiri Sambo. 
Daganan yafito aguje sukayi karo da Asad a bakin kofa,juyowa baiyiba bare yacemasa sannu yana fitowa bakin asibiti yashiga motar taxi. Daganan airport yanufa domin idan yacigaba dazama anan Abuja Maisha zata iya dauresa sabida k0 sisi bashida ita bare million bakwai daman wajen Mahaifinta zai samosu gashi yanzu shima yafara shakka akan maganganunsa. Gidan da ake magana akai kuma ya rigada ya sayarwa wani attajiri, kud’aden duk ya biya basussukanda ake binsa, wannan ake ‘kira tsaka Mai wuya. 
‘karar wayarsa ne ya katsemasa tunanin, Yana dubawa sunan Maisha yagani “Innalillahi wa Inna ileihi rajiun’ Salati yafara saukarwa yayinda yasa wayar a silent yanata zabga addu’oi 
har suka Kai airport inda yafito cikin masifar damuwa yamikowa Mai mota kudinsa 
Jakarsa yake turowa yanaja se jujjuyi yake yana gannin bayansa tamkar gudun wani 
yakeyi. Mutanen Airport kowa kallonsa suke kaman mara gaskiya. 
Karo sukayi da ‘Yarsa Miemah yayinda yabude lifta yana kokarin shigewa ita kuwa tana fitowa. Kallonta yai sama da ‘kasa tana Jan ‘jakarta alamun yanzu tasauko daga jirgi all the way from Maiduguri. “Me kike anan? Tambayarda yafara mata kenan. Cikeda Farin ciki ta tarungumeshi “Abba tun shekaran jiya mukayi magana da Kawu Sambo he is so worried about me na fad’a masa lafiyata ‘kalau amma ya ‘karyatani yace ba’zai yarda da maganataba har tse nazo gida Abuja sannan ne za’muje wajen likita yatabbatar masa da 
maganata, kuma har kud’in jirgi shi ya aikomin ….. 
Zufa Saminu yafara sharewa daga fuskarsa “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun yar nan kin tona’min asiri na shiga uku. 
Yaso sukoma Maiduguri tare Amma bashida issasun kudin jirgi ahaka yai tafiyarsa se ‘kara Salati yakeyi. Makokoronsa duk ta bushe tsaban damuwa. 
Abba lafiya? Miemah ta tambayesa cikin rudani, Uffan bai tankamata ba wucewa yai abarsa yabarota awajen. Tabe baki tai ‘tohhh Allah ya keuta. 
Ma’isha tanata bubbuga gate din gida har tseda yan Sanda sukazo wajen inda suka sanar mata cewa gidan tarigada tazama mallakim Alhaji ‘Kadiru Shetima, kuma ya bada umarni a rushe sa gobe da yardan Allah za’a fara aiki. 
Mutuwar tseye tai tana kokarin musu bayani amma babu mai sauraranta ahaka tabar wajen cikin sananin damuwa tawuce gidan abokinta Auwal wiski wanda yake unguwar tasu shima spoilt brat ne kamar Maisha mahaifinsa ya mallaka masa komai babu abunda 
yarageshi dashi tafannin dukiya. 
Dashike gidan babu nisa nan da nan ta’karaso. Sa’ar datayi kuwa tanashan kwana Sega Mutumin da’kananan kaya alamun motsa iini yafito (Exercise). 
“My one I really miss you Miss Maidugu. Ya washe baki wanda da dukkan alamu sun dade basu had’u da juna ba. Duk wannan damuwar datake ciki bai hanata masa murmushi ba “Haba Auwal ina kashiga kwana biyu. 
Jiya nadawo daga Qatar. Ya amsa mata kai tseye “Waisu chan ‘kasashen larabawa basason yan iska irinmu, toh shine kawai suka ‘koromu ganin muna batamusu yan matan gari. Guntun tsaki Maisha taja tareda girgiza kai “Ai ni shiyasa bansan irin wannan kasashen larabawan. Jinjina Kai yai “gaskiya kam sunada matsala. 
Tai shiru nadan wasu mintuna sannan tace Auwal ba ma wannan ba tukunna inada wata muhimmiyar magana danakeso muyi ni dakai. 
Wow!!! haka gidan nan yakoma, Masha Allah gaskiya dei Kawu Samba yanajin dadi tareda iyalansa, Teddy na tananan tana more rayuwarta a daula gida irin wannan sekace ta aljannah. Ahaka Miemah tacigaba da mamaki ta_sake ba’ki tana kallon gidan har ta’karaso gate. Kai tseye tashige da sallamar musulunci “Assalamu Aleikum”. 
Aguje Malam Lado mai gadi yafice daga dakinsa “Hajiya Ma‘inah sannu sannu da dawowa 
yau kuma dei akafa haka ba mota? Murmushi Miemah tai sabida ako yaushe idan ana cewa suna kama da Ma’inah dadi takeji har cikin ranta dukda cewa ita kanta ta’san hakan Sedei kuma ta d’aya bangaren idan ta tuno kamanninsu da Ma’isha se taji kamar suje su chanza kamanni ita da Teddy (Ma‘inah). 
“Malam ba Ma’inah bace. Tafada cikin murmushi da Farinciki ‘amma zaka iya ‘kirana dasunan sabida duk daya muke we are twins. Ta sa ke yin wata murmushi. Mamaki Malam Lado yashigayi “Tohh yarinya ai abun ne da mamaki Maisha ce da irin wannan shigar Kuma babu hayaniya haka. 
Bacin rai taji azuciyarta sabida ako yaushe idan ta tuno cewa Ma’inah ba asalin Twin inta bane takanji bakin ciki sosai domin alakar Teddy’ inta da wannan Macijiyar (Maisha) ta’fi ‘karfi samada alakar dake tsakaninsu. “Malama Maisha lafia kika shiga tunani haka? Indei hakuri kikazo ba’ni wallahi na yafe tun tuni. Maganar Malam Lado ne yafitar da ita cikin tunaninda takeyi. Dasauri ta girgiza kai “Ba Maisha bace Miemah ce yar Saminu Maidugu. 
‘Karasowa sukayi har cikin falon Auwal inda duk sukasamu wuri suka zauna kan wasu maka makan kujeru na gani afad’a. Auwal ya hura sigarinsa yanasha itama yabata nata amma bata ansaba cewa tayi ba’tashan sigari se shisha, sabida aganinta sigari na ‘kananan mutane ne. 
Shi Saminun ne yake duk wannan iyayin dakike magana? Auwal yafad’a cikin mamaki “This 
man is unbelievable danfaranki yai neh? 
Gyara murya tai sannan tafara magana “Na seyar masa da gidana Million Goma, na mallaka masa takardun gidan da komai harda makullai amma mutumin nan baisan ko wacece ake ‘kira Maisha ba, yayi min wa’sa da hankali million Uku kachal yahad’ani da ita yai tafiyarsa yanzu ba’nida wani gida, ka san cewa na bar gidan iyayena yau gashi nadawo 
nan kuma ko ina a rufe, Kuma nayi masa Miss Calls kusan arba’in bai dagaba, me yake nufi, 
7 million naira kudadena dake wajensa yanzu. ‘ 
Gyada Kai Wiski yai yana hura sigarin dake bakinsa yayinda yace “Na fahimceki Maisha cool down, Me kikeso ayi masa? 
Kudi na nakeso, ko tawani hali kawai ku ansomin kudina Koda gidansu dake Maiduguri zaku sayarwannan duk bai shafeniba, kawai million Bakwai dina nake bukata Auwal…. 
Nawa zaki bamu? Auwal ya tabe Baki yana tambayarta. Million Ukun daya bani shi zan baku sabida ba’nasan kuskure awannan aikin. Million Bakwai chip! nake bukata babu ‘kari bakuma ragi. 
Anan tamiko masajakar kud’i kamin sutafi. 
IYA ABUNDA YA SAWWAKA A YAU KENAN “
PART 15 SPOILER 
Gidan duk an chanza tayi kyau matuka ko ina flawowi kake gani yana walkiya dakuma fire works masu tsananin kyau da tsada. Har ba’kin kofa dreba yatsei da motar tasu ‘kirar 
BMW XLR. Ana bude masa kofa yawuce kai tseye yasa hannayensa yarike Ma’inah inda tafito cikin sanyin jiki. Sama da ‘kasa tafara bin gidan da kallo duk an chanza gwanin sha’awa “Welcome back Ma’inah Sambo Maidugu”. A rubuce adeden kofar shiga kumada manyan baki aka tsara rubutun. . 
Thank you so much Sir. Tai murmushin ‘karfin hali “I really appreciate. Murmushin Zaid yamaido mata “I’m glad you like my job Bae. Yakashe mata kyawawan idanun nan nasa “Thank you bae, na’gode sosai. 
MaiJidda Nan ne gidan Wallahi. Ma’isha ta’kara rusa kuka “Shikenan Auwal ya danfareni kudi na million Uku na mallaka masa kawai sabida suyimin aiki because I trust him ban taba tunanin zai iya tafiya da kudadenaba sabida shi ba matsiyaci bane he is Rich enough. 
Rasa abun fad’a MaiJidda tai, jinjina Kai taketayi tun tuni ” Wai kina nufin Auwal Wiskin dakansa kika baiwa kudaden, abun mamakin anan shine he is Rich enough banga dalilinda zaisa yadanfareki ba. 
Duk ya kakkatse layin wayoyinsa gashi kuma munzo nan gidansa ance yariga daya siyar  yazanyi besty na shiga uku. 
I’m sorry Besty. Maijidda tafada cikin sanyin murya “Maisha ya’kamata muyi handling case inki na gida tukunnan kamin muzo Bangaren Saminu da Auwal. Yes you are right besty. 
l can’t believe this crazy brat, Ma’inah meye kuma kikeyi anan gidan mu? Ina Tsamman kin 
koma gidan dadi kuna cin amanata tareda Zaid. 
“Zaid kuma? Miemah ta tabe baki. Cikin tsananin mamaki tamike tana tambayarta waye shi Muryarta na karkaruwa, mamaki dukya cika Mata Ido “Miemah meye kikeyi anan “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun” Doura hannu aka Maisha tai tafara Salati, kema gajiya kikayi da Matsiyacin Mahaifin naki kika dawo nan to claim that Sambo is your real Father ……. 
Bata ‘karasa furucin nataba yayinda Miemah tadaga hannu, babu tsoro ta sauke Mata mari afuska “Mind your tongue Maisha Sambo Maidugu. 
Hmmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]