[Advertisements⬇️]

TAGWAYE CHAPTER 10 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TAGWAYE 
CHAPTER 10
shushu Shaid who IS she? Yarinyar tanuno Ma’inah tana tambayan Zaid dake tseye ya tabe baki tareda girgiza kai “Look Muna I don‘t know her either, but this is my uncle Sambo Maidugu. Ya nuno Daddy dake murmushi yana binsu da kallo “Dana kwana biyu, l realiy miss you Mr Zabir… Haba daddy ka saurareni mana, wannan mutumin ba mutumin arziki bane kyab dan maciciji ne sunansa, Zaid gabansa fari bayansa baki please don’t trust him father… 
Zaid bai bata lokacinsa agun ba, Gaisawa da Daddy yayi kurun sannan ya mike tareda Muna sukayi waje. 
‘Daddy a ina kasan shi?. Ma’inah ta tambayesa cikin sanyin murya ‘Meye kuma alakarka dashi wanda har kake ‘kokarin dan’ka Yarka a hannunsu? 
Gyara murya yayi, sannan yafara Bata labari “lokacin da nafara aika ‘kayana zuwa ‘kasar China, Muhammad Zabir wato Mahaifin Zaid wanda Ni kaina zan iya ‘kiransa Mahaifi. Ma’inah wannan Mutumin ba’wan Allah ne kuma Mutumin arzi’ki and he is the most richest man in China. Ya taima’kamin alokacinda nake matukar bukatan taimako. Duk wanda yasan Beijing wato babban birni a ‘kasar China, zai sheda miki cewa abu mafi wahalar samu a garin shine wurin zama either apartment rent, Uwa uba kuma sayan gida ko fili tawannan Gangaren sunada tsada matuka hakan yasa duk magidanci a Beijing mai kudi ne nafitan hankali. 
Muhammad Zabir yagayyatoni gidansa lnda yabani wani bangare cikin gidan nazauna dasu, Ya kuma taimakamin da tsana‘ata hartseda nayi suna achan Chinese sannan ya sayamin gida daga baya, anan nacigaba dazama ina ‘kasuwanci ahankali ahankali. Bayan wasu yan rigimar da suka faru achan yasa nabar Beijing nakoma Amurka. 
Iya abunda zan iya fadamiki a yanzu kenan dafatan kin gamsu kuma zaki yarda nabarki anan kifara wata sabuwar rayuwa tareda zuri’ar Muhammad Zabir?. Cikin nunfashi daya jero bayanan nasa inda azuciyarsa yake Allah, Allah Ma‘inah ta gamsu da yan bayanin dayayi mata. 
Kura masa ido tayi tun yana magana har sanda ya kammala bata dauke idanuwarta 
akansa ba,. Duk dacewa ba’tasan amsa wannan bu’katar tasaba, kawai daurewa zatayi ta amince don gudun bacin ransa, ta Umma, data Maisha domin ba santa suke agidan ba 
dama. Kuma koda dan cutar dayake fama da ita, aganinta idan tayi nisa dasu zai fiye masa kwanciyar hankali Sabida babu wani abunda zai bata masa rai dazaran tarabu da Momy da Maisha..
‘Yata karki damu, Kamin muzo nan na’rigada na gabatar dake gaduk mutanen gidan nan kuma sun amince, munyi magana da mahaifin Zaid shima ya amince kizauna dasu yanzu kawai naki amsar Mukejira:. Wannan maganar da Daddy yayi, shi yakatse mata tunaninda take inda ta gyada kai, idanuwarta suna kokarin zubda kwalla amma ta daure, dakyar tarikesu ‘Daddy na amince zancigaba da zama anan taredasu amma agaskiya ina tsoron Zaid, I mean I‘m not feeling comfortable around him Kuma Ni kaina bansan dalilin hakanba.. “Wannan ba abun tada hankali bane Miss Ma‘inah Zaid haka yake yanada tsananin farin 
jini da daukar hankali Wanda idan kana taredashi kamar yadda kika fada you will not feel comfortable“,. Asad yakatseta, Kai tseye yashigo suka gaisa da Daddy sannan yajuye bangaren Ma’inah yana zolayarta  Miss Ma’inah Zaid is really amazing isn’t he? 
Shiru Ma’inah tayi tana masa kallo da idanun mamaki, daganinsa akwai fara‘a kuma yanada hankali, toh amma taya akayi sukayi hannun Riga da dan uwansa Zaid Kodei shi 
wannan ba dan nan gidan bane? Gashi se wani dariya yake yana washe hakora.. 
“Miss Ma‘inah don’t think too much. Asad yakatse mata tunanin, inda yajefo mata wata doli dolin yara yanacewa: zaki iya wasa dashi it’s really fun idan kinmasa magana zai bibbiye ki, Kinga kenan shi zai ringa debe miki kewa ako da yaushe and trust me you won’t 
feel lonely around him,l mean the Teddy. Yafad’a Yana nuna dolin dake hannunta. 
Murmushin karfin hali tayi ‘nagode sosai’. Never mind miss, sunana Asad babban abokin Boss, the mighty Zaid, karki damu dahalinsa dazaran Ina nan taredake babu abinda zai ‘kara miki da yardan Allah, And nice to meet you Miss Ma‘inah. Ya mika mata hannu domin su gaisa. 
Dasauri ta basa hannu “nice meeting you too Asad, Muryar wata mata ce takatse gaisuwar dasuke, Matar Zatayi akalla shekaru talatin zuwa talatin da Biyar, kekyawace kalar larabawa cikin fara’a ta ‘karaso lnda suke yayinda suka gaisa tareda Daddy sannan tajuya bangaren Ma’inah suka gaisa da ita. Sunanta Aunty Rahila; Asad yanuno matar ‘itace tamaye gurbin mahaifiyar Zaid ‘kanwar mahaifin sane she is the head of this family bayan Uncle Zabir, Abba kenan. Kawu Sambo yar ‘ka Mainah kekkyawa ce sosai kuma kunada kamanni matu’ka kamar an tsaga ‘kara… Aunty Rahila ta’kara kurewa Ma’inah ido tanacewa; Kuma daganinta akwai Kamun Kai. ‘Kwarai da gaske, Yata kekkyawa ce kinsan dama hausawa sunce kyan da ya gaji ubansa. Daddy yafada inda yake murmushi yana bin Yarsa da kallo. Hoton Maisha yazaro cikin jakarsa ‘Yar uwar Ma’inah kenan, Maisha sunanta, ita tana gidana tareda mahaifiyarta. 
Wow!!! Identical twins, Maisha tayi kyau Masha Allahu: Aunty Rahila tamaida masa da Hoton sannan tace ‘Uncle Sambo kada kaji komai aranka, Insha Allahu zamu rike yarka amana kawai ka kaddara ma gidanka Ma’inah take sabida zan maya gurbin mahaifiyar ta 
domin na gamsu da dukkan bayannan dakayimin babu komai ‘Da na kowa ne ai. 
Na’gode Rahila, wallahi bansan dame zan biyakuba because i owe you alots na’gode sosai da sosai, Kuma kaman yadda namiki bayanin cewa Ma’inah will be safe here shiyasa nakawota, babu wasu y’an uwan danakejidasu anan Abuja bayan ku. Thank you. Da wannan magana Daddy yami’ke yana hawaye, bai ‘kara wata magana ba daganan yafice. Kuka Ma’inah take nafitan hankali bata tse dashi ba ahaka yafice yabarta anan tana zaune 
tana tsana‘arta na kuka. 
Aunty Rahila ce ta matso kusa da ita ‘Feel at home babu komai Yata. Mahaifinki zai ringa zuwa yana ziyartarki, ‘Karki damu sabida bayan Mahaifinki ya sanar dani halinda kike ciki agidanku yasa nanemi alfarmarsa cewa yadawomin dake zan ‘rike masa ke Amana, Ma’inah ni Nan dakike gani banida aure bare yaya, Zaid shine kadei zan iya ‘kira ‘Dana. Anan ne Rahila ta ‘kasa ‘karasa maganar, inda tafara zubar da hawaye cikin karkarwan murya tace ” Ki gafartamin Ma‘inah inada wasu sharud’an danake so kibi dazaran Zaki zauna damu anan please and Please you have to respect my son Zaid kada kikasance sanadiyar bacin ransa koda kuwa kallon dabayaso kada kiyimasa domin mu anan gidan binsa muke ahankali tamkar yadda ake rike Kwan Kaza… 
“””””””
A’uzubillahi, kamar kuka kunnuwata sukaji kekiyi, haba Safeenah meye yafaru agidan naku yau kuma cikin wannan daren? Saminu ya‘kara daga muryarsa yanacewa‘ Kinajina kuwa Safeenah? “Inajinka Yaya. Safeenah ta amsa cikin sanyin murya sannan ta’kara dacewa “Dan uwanka yadena ganin darajata kwata kwata baya Jin maganata barre yasaurareni uwa uba Kuma baya’ma ganina da idanun daraja ya rabani da Yata Ma’inah Wai acewarsa.. Bata ‘karasa maganaba Yayi saurin katseta ‘Kinga Safeenah wallahi ni kaina kwanan nan ba‘na ganemasa Hankali bata isheshi ba wallahi, Sambo bashida mutunci, macucine kuma azzalimi amma babu komai da yardan Allah zanyi Masa magana… 
Da wannan yakatse wayarsa bai ‘kara cewa uf’fan ba, katse wayarsa yayi bayan yagama magana, bai bata lokaciba Kai tseye yafara gwada layin Sambo. 
Mamakin maganganun dasukayi Momy tashigayi ‘ace yau Saminu dakansa yake fadan muggan ‘kalamai akan dan uwansa Sambo? taya hakan yafaru… 
Yana isowa dakinsa, Bathroom yashige Kai tseye yayi wanka sannan yad’aura alwala. Fitowarsa yaja sallaya ya tada Sallah n Isha anan wayarsa tafara ‘karadi ‘kiransa ake ba’a fasaba har seda ya idar nanma bai kula wayarba kwanciyar sa yayi yana jan charbi yana tuna Y’arsa “Ko awani hali take ciki a yanzu oho’. Waya se ‘kara take tun dazu tamkar bashi ake binsa dakyar ya mike yanacewa ‘Mutanen kasuwancin nan kwata kwata basuda hankali, daren ma da albarkarsa baza abar dattijo yahuta ba haba Dan Allah wannan wace irin jaraba ce da masifa. Kai tseye yasa wayar akunne “Assalamu Aleikum wanene? ‘wannan ne wanda kamance dashi yake fama da karayan arziki tun watan jiya. 
Saminu” Daddy ya’kira sunansa cikin mamaki ‘yaushe ‘karayan arziki ta sameka kuma meye yasa baka kiraniba i hope kuna nan lafiya dakai da Iyalinka dakuma Miemah. 
“Wannan kam bata shafekaba amma Miemah tana nan tana fama da rashin lafiya kuma 
agaskiya ba’nida isassun kudin jinya ko zaka taimaka Mana. 
What… Meye ya sameta? And why didn’t you inform me… Kaga Sambo wannan shirmen naka ya isheni kawai inzaka taimakamana kafadamin idan Kuma bazaka taimakamana ba, ka sanardani tunda akwai masu arziki a ‘kasar nan bayan kai… Saminu tabe baki yayi tamkar,,,,,
Shiru Daddy yayi na dan wasu mintuna sannan yace: nawa ake bukata zamuzo ganin jikin nata se mukawo maka kudaden. Bai karasa maganaba yai saurin katseshi “Ban gayyatoku gidanaba kuma banson waninku yazo batun kudi kuma Million biyar ce kadei kudaden aiki sekuma kudin magani dubu d’ari da saba’in… 
Million biyar da dubu d’ari da saba’in: ya nanata cikin tsananin mamaki “wannan kuwa wani irin cuta ne? Kudaden sunyi tsada ni Kai na sena shirya kamin nasoma wannan kudaden domin yawancin business dina na tsayar dasu musamman confanunuwana yawancin su are on bankruptcy taya zan hada maka wannan kudaden? Fine, fine Saminu yafashe da dariya “Just imagine your life Sambo bakada tausayi aranka kwata kwata, Amma babu komai zan cigaba da bara kamar yadda natsaba domin nasamo kudaden ka San dama ni almijiri ne, Dama dan arzikin danake maneji dasu ne ku yan bakin ciki bakuso. 
Daddy baiyi maganaba shiru yai yana sauraronsa “Matarka ta ‘kirani dazu take fadamin cewa karabata da diyarta Ma’inah Kuma baka sauraranta, Amma ni wannan matsalar kuce dazaran kana kula’min da amanata shikenan. 
Wace amana kake magana? Daddy ya katseshi cikin sanyin murya sannan yace: Batun kudi kuma dan Allah karufamin asiri kada kayi bara zagina za’ayi a gari, zan turo maka kudaden da yardan Allah. 
Saminu bai tankamasa ba ya katse wayarsa Kai tseye Daddy yashiga tinani inda yami’ke yahada coffee sannan yafita zuwa kitchen domin yasa sugar, Maisha yahango chan tana dirkowa se wani sauri take tamkar korota ake “Ma’isha Ina Kuma Zaki cikin wannan bakar Daren? ya tse da ita da mamaki a fuskarsa. 
“Ofishin yan Sanda za’ni. Ta amsa kai tseye. 
Yan Sanda? Meye yafaru Maisha kuma ‘kararwa zaki Kai. Cikin tsananin daurin kai ya’karaso Inda take “are you okay my dear. 
‘Daddy will you please stop pretending ‘karar ka zan kai wajen hukuma domin su kwatarwa Mahaifiyata wacce kabari tun jiya take kuka yancinta you know human rights I guess, haka kawai Daddy zakabar Matarka cikin damuwa, hawan jini kakeso kajanyo mata ne haba wallahi Koda bakayi karatun arabiya ba na tabbata cewa kanajin tarihin Manzon Allah (SAW) yadda yake terereyar matansa yake Kulawa dasu Yana nuna musu soyayya, Kai ma Daddy ba haka kake ba alokacin damuke America Kuna zaman lafiya abar sha’awa amma meye yasa daga haduwar ka da wannan tsinenniyar so called daughter nan taka ka chanza Baki d’aya kakoma wani abu daban…. 
Tun datafara magana bata kallesaba se yanzu takai idanuwarta akansa “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ a kwance yake a ‘kasa rigingine kuma a sume,jini ne ke bulbulowa cikin bakinsa suna zuba abun tsoro… 
Ta bangaren Ma’inah kuwa bayan Aunty Rahila ta jero mata sharudodi da ka’idodi tatafi, Asad ya’zo bayan sallahn isha ya zagaye da ita cikin gida yanuna mata wasu gurare dakuma wasu bangarori agidan tun tana mugu mugu dashi har seda tasake jiki tamkar sun saba dajimawa. 
“Wan_chan bangaren”. Ya nuno wata Bangare chan nesa sannan yai murmushi ‘Part dinsa kenan Zaid da Muna. babu mai shiga bangarensa se ni dakuma Aunty Rahila wataran itanma gaskiya Zaid bayaso ta ringa shigowa, wato kinsan ra’ayin Mutumin nawa is complicated. Tabe Baki Ma’inah tayi “Really, wama zai shige masa bangare, Muna fa wacece ita? “His adopted daughter. Yafada kai tseye. What? Ma’inah takatseshi ‘Meye yasa zaiyi adopting Kodei san yara gareshi? Shiru Asad yai sannan yace Yar mahaifiyar sace. 
Daga nan Ma‘inah tashiga tunani, babu wanda ya’kara cewa komai cikinsu, Asad yawuce bangaren Zaid, Ita Ma’inah kuwa bangarensu tanufa kai tseye… 
lYA ABUNDA YA SAWWAKAA YAU KENAN A  

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]