[Advertisements⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 37 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA 

CHAPTER 37Sumaila kauyan Sani ….. 

Cikin ikon Allah INdo taci gaba da kula da Ayman cikin d’an ilimin data samu. Sam bata barin aje mata yawo da d’ah a memakwan ta dingajin kunya sai Inna ce kejin kunyar dan sam bata bari taga an mai wani abun abubuwa take yi cikin dai-dai wayewarta da saninta. 
Zuwan su Hawwa dasu Haleematu uku a cikin sati biyu, duk sun kagara ta koma sabida ba karamin sonta suke yi ba. Maman su kuwa kullum sai tayi mata waya sun gaisa sannan ta tambayi Ayman. 
Sadeeq kuwa raba dare suke yi idan ya fara bugawa Fateema suka gama shan hirarsu sai ya buga mata itama susha hirar love din su. Ayman yana ta wayo kamanninsa dabanne dan sam baya kama da iyayensa kyakkyawa ne fari ga suma (lNdo dai ba gashi] gareta ba dan Fateema ta fita nesa ba kusa ba) gashi da son wasa dan haka yake shansa gurin Nafeesa da Shehu. 
Watansa daya da sati biyu ya dawo kano, sosai fateema tayi murna da ganinsa. Abba ne ya kirasa lokacin chuchu na gidan sam ya tsani yarinyar musamman tun ranar da taso kushe mai matarsa uwar ‘ya’yansa. “Yaya welcome back.” Yayi banza da ita sabida zaune take da daurin kirji ko kunyar mazan gidan bata yi, Mama na kallansa da yadda ya shareta ya wuce ya gaida Umma sannan yayi shigarsa zuwa gurin Abba. 
“Sadeeq ranar Friday aka raba gadon marigayi.” 
Kirjin Sadeeq ya buga sabida sam ya tsani yaji anyi zancen gado abin yana bashi tsoro, daga wannan sai wannan ya mutu an bayar da matarsa yanzu kuma za’a bayar da duk abinda ya tara bayan yasha matukar wahala a wajan samu. 
“Kayi min shiru.” “Yi hakuri Abba am..am inajin ka ai.” 
“Toh an ware na Aisha, inajin kawai ma idan ta dawo daga sumaila kawai ta wuce can gidan marigayin tabar wancen kaima kaga an rage maka wahala ko.?” 
Hawaye Sadeeq ya share, kada kai kawai yake yi yana amsawa Abba amma besan abinda yake gaya masa ba har sai da Abba yazo yana mai-maita masa tambaya. 
“Yaushe Aishan zata dawo toh? Nace Yaushe zata dawo ne? Kai Sadeeq, haba tunanin me 
kake yi ne? “Abba Allah yayi mai rahama, yasa aiyukansa na alkairi su bishi.” 
Sadeeq ya fad’majikinsa duk a sanyaye, Abba ya amsa da amin tare da cewa. “Tambayar ka nakeyi yaushe ne Aisha zata dawo.” 
Sadeeq ya dan kalli Abba sannan ya maida kansa k’asa yace. 
“Abba ranar Sunday zata dawo, sauran sati d’aya kenan insha Allahu.” 
“Toh Allah ya nuna mana, idan kaje sai ka sanar dasu, yanzu sai kasa aje gidan a gyara shi Allah yayi muku albarka shi kuma Allah yayi masa rahama.“ 
“Amin Abba Allah ya amfana.“ 
Fita yayi zuciyarsa fal tunanin twinnie dinsa, gani yake yi tamkar bazai yafe mai ba sabida duk ya handame komai nasa. Yana zuwa kofar gate yaga chuchu tsaye sanye cikin abaya tayi rolling kanta idanunta sanye cikin wani shegen shade tana tsotsan loli pop Sadeeq ya murtuke fuska shima ya zura dark shade dinsa yazo zai gifta ta, ba zato yaji ta riko masa hannu yayi saurin fizgewa ta turo baki. 
“Haba Yaya Sadeeq ya zaka dinga wulakanta ni? Ai ko bakomai ni ‘yar uwarka ce be kamata ka dinga min haka ba. Please meye aibu na da baka sona?!” 
A kufule Sadeeq yana kokarin fita yace mata. 
“Sabida bana sonki, idan kina sona ni bana sonki ko ana so dole? Kije can ki nemi wani Sadeeq din amma wannan daga kan Aisha humaira ya rufe.” 
Wata uwar harara ta wurga mai tana kallonsa ya shiga mota yayi tafiyarsa. 
“Hmmmm wallahi Yaya Sadeeq zaka ga mijin da zan aura, ko dame matan naka suka fini…’ Mtwww 
Tayi maganar tana kallon jikinta, har ya kule bata bar gurin ba kasan cewar cewa tayi dasu Haleema bari taje ta karbo one thousand a gurinsa yanzu kuma da kunya sukaga ta koma famfam-fayau. 
Washe gari Sadeeq ya shirya ya tafi sumaila. Yau tunda INdo ta tashi take murna sabida zuwan Sadeeq. Kaninta shehu ta aika yayo mata cefane a cikin gari, da kanta ta shiga yi mai girki Inna nata mamaki ganin INdo na son farantawa miji lallai a koda yaushe ba’a fidda samun rahamar ubangiji akan komai. 
Tsab ta shirya mai wainar shinkafa miyar egusi da naman rago sai kamshi take yi. Pineapple juice tayi sannan ta dama mai fura da nono da madara tasa su a flask d’inta da ta siyo tana zubawa bak’inta na birni da suke zuwa a ciki ta zubawa Sadeeq ta gyara cikin d’akin baban su sabida yafl fili babu tarkace kamar dakin Inna. 
Share gidan tayi k’asa ce amma gidan yayi fes kamar ka kwanta kayi bacci a gurin. Inna tayi mawa Ayman wanka wanda ‘yan kauyan sabida tsabar rashin iya fadar sunan yasa suke cemai Ama INdo tayi masifar tayi Allah ya isa duk wanda ya sake cemai Ama amma ina harta hakura dan wani lokacin itama har fad’a takeyi. 
Wanka tayi sannan tacewa Inna bari taje ta dawo. Shagon Maman Tessy taje wanda Abubakar ya fara kaita, ba karamin mamaki Tessy tayi ba lokacin dataga lNdo har suna ‘yar hira cikin Hausa suna d’an watsa turanci Tessy tayi mata murna sannan ta cancada mata makeup tayi kyau sosai sannan ta dawo gida. Me mashin yana ajiyeta ta Shiga zaure motar Sadeeq na karyo kwanar layin gidan. 
Waya ya dakko ya kirata ta d’auka yace gashi a kofar gida. 
Inna yazo.” 
“Toh ‘yar nan, Nafeesah jeki ce masa ya higo ciki ai hi yanzu ya zama dan gida.” 
Tashi tayi tare da d’aukar Ayman, fita tayi tana zuwa ta tarar dashi ya bude kofar mota ya zuro kafarsa wasu yara sunzo sun zagayeshi banda zarni babu abinda suke yi Sadeeq ya kalli Nafeesah tare da sakin murmushi bayan ya mika mata hannu dan ta bashi Ayman. 
Bashi tayi tana dashare baki ya kalli dan yaga ya kura mai ido tamkarya sanshi Sadeeq yayi murmushi ganin wai d’ansa ne ikon Allah, Allah yayi shine zai haihu da Aisha hakan yasa aka d’auke Abubakar, ita kuma Fateema ya fara auranta amma aka hanata haihuwar Allah kenan buwayi gagara misali me yadda yaso a sanda yaso duk lokacin daya so. “Allah 
ka kara mana tsoranka” Sadeeq ya fada a ransa duka a cikin ‘yan dakikai. “Anfa ce ka higo ciki ka tsaya sai kallon danka kakeyi.” 
Nafeesah ta fada tana rike da kofar daya bude. Ayman kawai yake kallo yanajin kauna da soyayyar dan na shiga cikin jininsa kafin ya kalli Nafeesa yace. 
“Zagaya ki bude baya ki shiga da kayan ciki gani nan zuwa.” 
Da sauri ta zagaya ta dauki ledojin ta shiga dasu. Ya dade cikin mota yana kallon dansa tare da yi mai hotuna kafin ya tashi ya shiga cikin gidan tare da sallama. 
‘Dakin malam Hamza Nafeesah ta nuna mai ya shiga kamshin d’akin danajikinsa suka hadu suka bada wani daddadan kamshi ya zauna akan tabarmar da aka shimfida sannan gefe kuma kayan abincin da aka shirya mai ne 
Tana gama shiryawa ta fito ta shiga dakin. Sadeeq idonsa na kan kofar tana shigowa besan sanda ya mike tsaye ba ta kallesa suka yi four eye’s cikin shauki kuma suka sakarwa juna murmushi. 
Alama yayi mata da hannu ta saki labulen da aka nannade aka dora akan kofar dakin. Murmushi tayi tare da zaro idanuwa tana girgiza kai alamar a’a, ganin haka yasa shi matsawa yana kallon kofar ganin babu me kallonsa yayi saurin sauke labulen INdo tace. 
“Kai.. Kai… Kai! ba ruwa na nidai Inna ce fa ta daga shi wai sabida akwai zafi.” 
Hannu yasa yajanyo ta kusa dashi yana kallon fuskarta, ya kaleta ya kalli Ayman a hankali ya kai bakinsa saman goshinta ya sumbace ta INdo tasa hannu ta bayansa ta rungume shi 
itama sannan ta kallesa tace. “Ka zauna ka tsaya.” Hannunsa cikin nata suka zauna yana kuma rike da Ayman. 
Kwantar da Ayman yayi a gefe kasan cewar yana cikin towel sannan yajuya yana kallon INdo wanda ke kallon kirjinsa dan wani iri taji da yadda yake mata wani irin kallo. ‘ 
“Sannu da zuwa, ya gurin su Mama?” 
“Kin yi kyau cutie na, kinyi kamar ba mejego ba dan babu wani alamun da zai nuna hakan meye sirrin?” “Inna ce.” 
Ta bashi amsa tana wasa da yatsun hannunsa yayi murmushi tare da matso da ita kusa dashi yana makalota jikinsa. 
“Ko kawai ma idan zan wuce mu tafi tare tunda kun gama wanka ai kin fara sallah ma ko 
cutie?” INdo ta zaro idanuwa tana kallansa yayi murmushi yana d’aga mata girarsa kafin yaji tace. 
“Tab… In bikafa kace? So kakeyi insha zagi kenan a cikin garin nan, kasan mu bazan koma 
gidan ka ba dole sai an yi garar barka sannan za’a maida ni.” 
Kallonta yayi cikin rashin fahimtar maganarta ta sannan ta dan zame tajanyo kayan abincin ta tsiyaya mai lemo ya karba har yana cewa. 
“Cutie ban gane abinda kike nufi bane wace irin garar suna? Kuma wazai kai? Wa za’a bawa.?!” 
“Kayan abinci ne ake kawowa gidan su mejego,su anan sun maida hakan kamar ibada dan haka idan miji beyi ba sai abin ya zama gori harjikokin mutum.” 
“Ikon Allah, Allah guda daya amma garuruwa daban-daban ni ban tabaji ba koda wasa wallahi. Toh idan kuma mijin bashida halin yi fa sai ayi yaya cutie?” 
lNdo tana gyara kafar Ayman ba tare data kallesa ba tace. 
“ldan miji beyi miki ba shikenan sai a rabu dashi baza a mayar da ita ba. Idan aka ga ya takura da zaryar zuwa gidan su kuma sai ad’auke ta a kaita inda bazai sake ganinta ba har sai ya kawo kayan.” 
Sosai mamaki ya cika masa zuciya, lallai akwai dimbin gyara a cikin kauyan nan amma banda haka ya za’ayi a hana miji matarsa akan abinda ba aIkur,ani bane ya wajabta shi ba. 
Lallai yadda ya kagu ta koma su tafi kwara state tare dole yaje a harhado a kawo,yarinyar tayi tsada da yawa daga wannan sai ace maka wannan. 
“In zuba maka yanzu ko sai kayi sallan azahar naga an kusa kirawo wa.” “Bari sai nayi sallah cutie, dawo nan in dinga jin duminki a jikina.” 
Matsawa tayi ya rungumeta, yana yawo ajikinta da hannunsa ita kuma ta lumshe ido tana sauraransa. Sallamar su Uwani sukajiyo Sadeeq yayi saurin zame hannunsa daga jikinta yana yatsina fuska yace.. “Su waye?” “Inajin su Maryam ne naji muryar su da Uwani da Sahura.” 
“Kai nashiga uku ni Sadeeq, wai hardasu nake aure ne da kullum na shigo garin nan sai 
sunzo sun samin ido? Ko ‘yan uwanku ne cutie?” 
“A’ah kawaye nane amma kuma su haka suke duk inda sukaji labarin wani abun tofa sai ka gansu sabida dama ba wani tambayar miji fita suke yi ba.” 
“Ai munafukai ne wallahi.” Ya fada a kufule kafin ya matsa sun shigo cikin dakin bakunansu a washe. 
Zama suka yi daga bakin kofar amma hakan be hana warin ranarjikinsu da kaurin icen girki shiga cikin hancin Sadeeq ba ya tuna da tuni itama INdon haka take amma Allah ya daukaka ta. 
Da kyar ya amsa musu a ciki-ciki sabida yadda suke kallansu suna rike haba sabida sunga sun manne jikinjuna. 
“Cutie zanyi alwala.” “Okey toh bari akawo ruwa kofar gida, ko zaka yi anan ciki.” “A’ah Inna na nan da dai bata nan sai nayi.” 
Tashi yayi suka d’an rabe ya wuce sannan lNdo ta fito suma suka bita a baya, tunda tazo gida suke bibiyarta ganinta suke tamkar Matar wani shugaban me rike da wani mukamin. 
Ruwa ta zuba tasa mayafi takai mai wajan mota sannan ta koma ciki. 
Hira suka farayi har aka Idar da sallah Sadeeq ya dawo daga massalaci dan har tsayawa yayi suka danyi hira da principal din tsefawa makarantar su lNdo daya bari. 
Nafeesah ce ta kuma fita ta shigo dashi sannan INdo ta bishi su kuma su Uwani suka ci gaba da hira da Inna duk da bata cika sanya musu baki ba. 
“Cutie Ina baby na kika kaishi?” “Inna ta goyashi kona karbo shi?!” “Ah no kyalesa kar ace nayi rashin kunya.” 
Waina ta zuba masa da miya sannan ta matsa kusa dashi, hade hannuwa yayi a kijinsa tare da bude baki alamar ta bashi da kanta. ‘ 
Murmushi tayi tana girgiza kai ta fara bashi kunnuwansa har motsawa suke yi sabida yadda miyar tayi mai dadi idan ta bashi sau daya itama sai ya tura mata wanda ta kuma debowa yasa mata a baki haka suka dinga yi har suka kusa cinyewa yace ya koshi. 
“Cutie gaskiya ranar Sunday zaki koma zanyi duk iya yadda zanyi na tabbatar da an kawo kayan nan, sannan direct za’a wuce dake can gidan marigayi acan zaki ci gaba da zama an raba gado Abba yace idan kin koma zaizo yayi miki bayani kinji.?!” 
Kifta idanuwa ta shiga yi alamar hawaye take son karsu fito ya janyo ta tare da kamo 
fuskarta yana san saka kwayar idanunsa cikin nata. 
“Karki zubar min da hawaye kinga nima ina tattala nawa, keda ma ba’ayi miki da yawa ba tunda an baki me kamadashi iri d’aya sak sannan kina cikin zuciya ta kamar rai. Ni kuwa tare muka taso mu kwana tare muyi fad’a mu shirya ba tare da kowa ya sani ba, shine ni nine shi amma yau babu shi.” 
“Ka d’auka kaima a ranka nice shi tunda dama silarsa ce ta sa muka zama abu d’aya dakai, na zame maka shi kaima karka sake yin kuka mun riga munyi ‘MUSAYAR ZUCIYA’ ni da kai fatana a yanzu shine na zama tauraruwa kamar yadda yake so yaga na zama kayi min addu’a malama Hannatu tace addu‘ar miji akan matarsa tana saurin karbuwa.” 
Bakinsa da yake ta motsi tun d’azu shi ya zura cikin nata cikin wani mugun tausayinta da wata azababbar kaunarta da soyayyarta da ta taso mai. Kissing din ta yake cikin wani irin salo wanda yasa INdo ta kasa gane kansa, ya shagala kawai sukaji muryar malam Hamza a tsakar gida amma Sadeeq ji yayi tamkar a tsakiyar dakin yayi sabida tsabar tsoro. 
“Na tafi cutie kar nayi abun kunya a gidannan a dakin baba dan naga kema ba hanani zakiyi ba.” 
Dariya INdo take yi sosai wanda tasa Sadeeq kallonta yana hararata dan har rike ciki takeyi ya matsa can bakin kofa-tare da maida hularsa yanajiran shigowar malam Hamza dakin dan yaji Inna tana cewa suna ciki. 
“Matsoraci kawai Abu Ayman, uhm…uhm..uhm..” 
INdo ta fada cikin dariya ya juya yana mata gwalo shima. muryar malam Hamzan yaji a bakin k’ofar Sadeeq yayi saurin d’aga labulen ita kuma INdo ta fara matsar da kayan da suka ci abinci kamar masu gaskiya. 
“Baba sannu da shigowa, gashi duk mun tsare maka dakin.” 
Sadeeq ya fada yana gyara zama tare da turo hula gaba yana kuma mai da ita baya alamar kunya ya keji. 
Malam Hamza yayi dariya tare da karasawa cikin dakin ya zauna a bakin gadon sa yana cewa ba komai Gaidashi Sadeeq yayi cike da girmamawa har suka dan fara hira ita kuma INdo ta kwashe kayan ta fita dasu can su Uwani aka ci ragowar anajinjinawa INdo ganin duk da kudinta tayi wannan shagalin. 
Malam Hamza da Sadeeq sunjima suna hira kafin malam Hamza ya fita iNdo ta shiga tare da dora mai ayman akan kafarsa kasan cewar ta karbo masa shi dan tasan yana son ganinsa. 
“Cutie ni kikawa dariyar mugunta ko? Hmmm zan rama ai zaki zo inda nake.” “Toh ai kaine da abin dariya wallahi.” “Za dai mu hade you will see.” 
Kallon ayman yayi tare da cewa. 
“Cutie wannan dawa yake kama sam na kasa ganewa?!” 
“Ban sani ba nima kasan ance ba’a gane kamanin jarirai harsai sun fara girma.” “Ki dinga karanta mai ayatul kursiyu kina tofa mai a madigarsa ai kin iya ta k0?” Tana kallonsa yatsan hannunta karami a cikin bakinta tace. “Eh na iya mana.” “Matso nan toh kiyi min inji ko dai-dai ne.” 
Cikinjin wani iri dan kar ta kakare ta matsajikinsa ya rikota, a hankali ta fara karanto mai inda yaji zata bata wani gurin sai ya gyara mata harta gama sannan yace. “Yauwa ki dinga yi mai Allah ya kare mana shi daga sharrin shaidanu.” “Amin abu Ayman.” “Zan wuce sai kinzo cutie kiyo shiri sosai dan wannan karan hmmmm.” 
Dariya ta kuma yi sannan ya zaro kudi 10k ya bata ko zata yi wani abun idan zata dawo sannan ya mike itama ta tashi suka rungume juna kamar basa son rabuwa cikin yanayi na ba haka aka so ba Sadeeq ya bata Ayman sannan ya Fita suka yi sallama da Inna su Uwani sai subirbida mai addu’ar sauka lafiya suke yi dan har lokacin suna gidan. 
Azaure Sadeeq yaga malam Hamza kan wata guntuwar tabarma yana gyaran redio suka yi sallama bayan ya ajiye mai 5k yana ta godiya. 
Yana shiga mota INdo tazo nan ma suka yi sallama ji yake tamkarya tafi da ita amma ba yadda zai yi dole ya fita yaja motar ya tafi cike da kewarta ji yake ma tamkar basu hadu ba kamar yanzu nema yake kan hanyarzuwa ya gansu…. 


Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]