[Advertisements⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 32 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 32
‘Dan zamejikin ta tayi daga nasa ta kallesa, “shin da gaske ni yake so ko kuma cikin dake jikina? Anya malam Sadeeq kana sona kuwa? Amma zamu gani idan gaske ne.” “Kin yi shiru.” 
Dariya ce ta subuce mata ganin yadda yake kallonta tamkar wani mara lafiya, ganin tana dariya yasa shi jin wani farin ciki har cikin ransa ya kuma janyo ta cikin jikinsa yana shafarta, ba zai mata komai ba dan karma tayi tunanin dan hakan yake sonta yanzu gara ya daure ya hakura ana dauke ruwa kawai ya gudu gurin Fateema tunda Allah ya kasa ya bashi biyu. “Kana ganin yanzu babu abinda ya samu cikina?” “Insha Allahu karki damu, ko kinajin wani ciwon ne?” “A’ah banajin komai ni sai yunwa.” “Okay sorry bari ruwan naga ya fara d’an tsagaitawa sai na samo miki wani abun kici. Bafa ki bani amsa ta ba Aisha baki ce kin yadda zaki zauna dani ba.” 
Dariya ta kuma yi tunowa da maganar Asma’u da tace tayi hakuri wata rana sai labari, shi gani zai yi kamar an shiga rayuwarsa ne shida Fateema amma tunda hadin Allah ne wata rana sadeeq zai kulata zai sota koda bekai na Fateema ba tunda har Allah ya kuma had’a su a bed gashi harda rabo.
“Aisha me kikema dariya ne? Ko gemun dana tara kikewa dariya.?” “Kai a’ah wallahi ni ina ruwana da wani gemu.” “Toh kina so kenan in barshi yamin kyau?!“ 
“Lalalah bance ba yadda kagani kai dai, kuma tunda ka barshi ai kowa yasan so kake yi taya za ai nace beyi maka ba ni lNdo.” 
Tayi maganar tana rik’e habarta cikin nuna kaskanci dan ta san bata kai wannan matsayin ba da har zata bashi umarni yabi ba. Yatsansa yasa a goshin ta wajan billenta yana shafawa ta lumshe idanuwa tana tuno Abubakar sabida duk sanda zai ganshi sai ya taba mata shi, sai dai idan ta d’aura d’an kwali ta cukaro shi ya rufe shine kawai ba zai taba ba. 
“lNdo malam Hamza…! Wai me yasa ake ce miki haka ne, a memakwan Aishat Hamza.” 
Ya fada cikin wani irin style wanda yasa ta kalli cikin idanunsa shi kuma ya kanne mata nasa tayi murmushi tare da cewa. “Haka mutane suke kiran baban mu, toh lokacin da aka sani a makaranta dama kowa INdo yake cemin banda Inna ita sai dai tace min ‘yar nan, shi kuma baba yace min uwata shine da aka kaini sai aka tambaye ni sunana baban mu yaki fada ni kuma karna fad’i sunansa sai nace INdo Malam Hamza shine kawai sunan ya zama haka.” 
“Ummm! Good, toh yanzu kuma fa a school? Ko har yanzu kina nan a INdo malam Hamzan?” “No..no..noooo, Aishat Hamza tun lokacin da Mubasheer yaje yamin registration ya saka min haka shikenan nima na cigaba da sawa.” Kallonta yayi yaji wani mugun tausayinta sai dai shi kansa yasan ya makaro, tun a baya ya 
kamata yaji tausayinta amma beji ba ganin batada nutsuwa a memakon ya tallafa mata sai ya kita sam baya karfafa mata gwiwa akan sha’aninta amma ya zai yi da sharrin zuciya dana shedan, yasan dai marigayi shine ya kwashe ladan gashi haryau da baya duniya ta kasa manta shi. Yana fatan shima wata rana tayi mai irin wannan abun ko yana da rai ko kuma lokacin yabi d’an uwansa. 
Uban ruwan daya jibgeta ne gashi kuma ya rungemata ajikinsa ta takure yasa wani daddad’an bacci ya sace ta ba tare da tasani ba. Shima sai da ya janyo ta yaji jikinta ya saki hakan yasa shi leken fuskarta kawai sai yaga ashe har tayi bacci, ya juya yadda zai dinga kallon fuskarta ya kura mata ido. 
Ya dade yana kallon kyawunta mai kwantar da zuciya kamin yayi murmushi tunowa da yayi sanda ta dauke mai naira darinsa daya je siyayya. A hankali yake sanya hannunsa saman cikinta yana shafawa zuciyarsa na tsananin harba mai cikin wani masifaffan son kasancewa tare da ita ya kai lips d’insa kan nata ya sumbace shi sannan ya mike a hankali ya sanya mata pillow a inda ya tashi tare da rufa mata lallausan bargo ya mike da sauri kasan cewar an tsayar da ruwan har an fara kiraye-kirayan sallar juma’a. Cikin sanda ya fitar da motarsa sannan ya kulle mata gidan ya tafi gidan Fateema da zafizafinsa. A kofar gida yayi parking motar ya tura gate d’in a kulle, wayarsa yajanyo ya kirata ringing d’aya ta d’aya cikin murna da zumudi tace. 
“Allah yasa dai baby haka zaka cemin ka iso cikin Kano..?!” 
Muryarsa cikin murmushi yace. 
“Fito ki gani ina gate.” 
Zaro idanuwa Fateema tayi tamkartana gabansa cikin sanyayya murya tace. 
“Baby kadawo kana waje? Please I’m so sorry kaga yanzun nan muka tashi yara sabida ruwa, dan Allah baby kajira ni in karaso.“ 
“Okey toh kiyi sauri kinga karna rasa sallahn juma’a.” “Toh godiya nake baby na sai na karaso.” 
Sallama tayi da sauran malamai matan da suka fito tare, cikin sauri ta tari Napep kafin wani sakannin har ya kawo ta. Cikin mota ta tarar dashi ya ziro kafarsa waje hannunsa rik’e da wayar marigayi yana kallon pic’s dinsa dana |Ndo wanda yayi mata tun tana lNdo 
suka yi a Munjibur park da wadanda yake mata a cikin gida sai dai duk babu hotan banza a ciki Fateema na karasawa wajan Motar yayi saurin zura wayan a cikin aljihunsa. “Oyo-yo baby nah, taho mushiga ciki.” 
Ta fada tana kallonsa cikin murmushi tare dayin gaba ta bude kofar gate d’in shi kuma ya biyo bayan ta. A parking lot ta tsaya yana shigowa suka rungume junansu cikin nuna kewa kafin yace. 
“Bari nayi alwala naje nayi sallah kafin na dawo ki samar min wani abincin kiyi da d’an yawa za’a kaiwa Aisha na biya naga ashe batajin dadi.” 
Kallansa tayi tana dariya tace. “Wai wannan uban kasumbar daka tara gashi hardasu gemu duk na meye.” Shafar faskar yayi yana tafiya yana cewa. 
“Baby wannan gemun na komai ne wallahi, hmmm danma Allah ya temake ku a iya tara gemu na tsaya, bari dai naje na dawo please ki d’ora girkin.” 
Dai-dai lokacin suka shiga cikin Falo ya shiga toilet ita kuma tayi bedroom d’insa dan kara masa kamshi duk da cewar kullum tana kamsasa shi. Yana yin alwalan ya tafl masallaci, ana idarwa ya wuce gidan su suka gaisa dasu Mama tana tayin murmushi a tunaninta be fara ganin cikin INdon ba tasan zai yi murna d’an kaniya da ana bashi yana nuna baya sonta. Yana dawowa ya tarar ta gama dama already tana da miya wadda tayi jiya sai kamshi takeyi. Rungume ta yayi cikin tsananin so da bukatuwa domin da kyar yayi sallah banda ta juma’a ce da bazai yi ba sai ya fara samun nutsuwa. Sannan baya son komawa gidan lNdo da wannan matsalar dan kar tayi tunanin hakan ne yasa shi cewa su shirya yanzu yana sonta, ya fiso ya fara nuna mata yanzu ita din yake so kafin ya fara nuna mata ainihin waye shi. 
Bedroom suka koma hakan ya tayarwa da Fateema hankali dan tasan a wannan yanayin ita yake muradi gashi ita kuma tana period ya zata yi mai? Ganin yadda yake mata zamzam yasa ta riko hannunsa tare da kwanto shi saman kirjinta murya a karye tace masa “Sorry baby.” 
“For what.?!” 
Ya tambaye ta yana matsarta da gashin kanta, nuna mai tayi hakan ya tayar mai da hankali duk iya kokarinta na ganin ya samu nutsuwa abin ya faskar sai dai kawai ya nuna mata yayi normal sabida baya son damuwarta yasan da zata iya dauke blood din da yanzu tayi. 
“Baby Ina abincin Aishan, kawo naje nakai mata zan biya can gurin Anas akwai abinda zan karbo a gurinsa.” 
Kallonsa tayi tasan kila yaje gurin Aisha, amma a ka’ida yau itace dashi sai dai baxata so ta ganshi cikin matsala ba, tayi murmushin yake tana shafar gashin da ya lullube kewayan bakinsa tace. “Yana falo na zuba.” 
Tashi yayi ya mayar da kayansa ta rakosa ya d’auki basket din kirjinta na bugawa dan tana zargin akwai abinda zai hadasa da INdo amma tasan basa shiri zai iya sharewa yajira har lokacin da zata samu tsarki. 
“Bye-bye baby ina dawowa zanci abinci nayi bacci dan agajiye nake munyi kwanan mota.” “Toh sai ka dawo ayi mata sannu, kona zo muje tare?!” Kallonta yayi na ‘yan dakika kafin yayi murmushi yace. “Yanzu kika dawo daga gurin aiki, sannan kice zaki fita bayan mijinki ya dawo daga ‘tafiya me nisa. No ki zauna ki tanadar min daddadar hirar da zaki min idan na dawo.” 
Fateema tayi dariya tare da daga mai hannu ya fita tana kallonsa kishinsa fal cikin kahon ziciyarta. 
Yana fita ya shiga mota yayi gidan INdo, yana zuwa a bude yaga gidan yayi parking a gefen gidan ya d’auki kayan abinci ya Shiga. Babu kowa harya shiga cikin bedroom dinta bayan ya ajiya abincin a falo. Tararwa yayi ta idar da sallah, ya tsaya a bayanta yau lNdo ce take sallah harda su addu’a, lallai Allah buwayi mai sauyin lamari kamar yadda ya sauya salon alak’arsu daga malamin ta zuwa mijin twinnie dinsa daga nan ya sauya zuwa mijinta. “Humairah.” 
Taji ya fada kirjinta yayi tsananin bugawa tayi saurin waigawa tana kallonsa ido waje. Murmushi ya sakar mata tayi saurin d’auke kai dacta ya fada mata jin muryar data fara kiranta da sunan. Anya ba munafuntarta akayi ba Sadeeq ya mutu aka raina wayonta aka ce Abubakar ne, anya shima ba yaudararta yake yi ba aka hada baki dashi zasu raina mata hankali. 
Bata gama dai-dai tuwa ba taji ya zauna a kusa da ita har suna gogarjuna ya leka fuskarta tare da cewa. 
“Tunanin me kikeyi haka? Ni ko Abubakar.” 
Ta zame hijjab dinta ba tare da ta kallesa ba. Shin me yayi mata a cikin rayuwarta da zata wani dinga tunaninsa, wanda yayi matan ya koma ga Allah ko kuma dan yayi mata ciki shine zai sa ta dunga tuna sa kila haka yake nufi. 
“Okey yanzu bazaki kulani bama.?” 
“Welcome back malam Sadeeq.” 
“Sai da na roka, ai ba haka kikewa M twinnie ba oya hug me.” “Kitchen zani ko indomie na dafa, nasan dai kai bazakaci ba.” 
“I said kiyi min Oyo-yo, kamaryadda kika min ranar danaje dakkoki kika yi tunanin marigayi ne, oya am waiting.” 
Tura baki tayi tana mamakinsa ganin irin yadda dacta yake mata abubuwa tace. “Ni a’a, ka kyaleni naje wallahi inajin yunwa.” “Na kawo miki abinci, amma sai kin min oyo-yo sannan zan baki.” 
A hankali ta juya ganin ya takura mata ta rungumesa bayan ta rintsa idanuwa. Jin kirjinta a nasa ya sashijin wani shock ya sanya hannunsa ya makalota gabaki dayanta jikinsa ya hau rawa tanajin haka ta kwace kanta ya samu da kyar yajata suka Fita falo. 
Da kanshi yaje ya dakko plate a kitchen ya zuba mata, tunda taji kamshin kifi takejin tamkarta cinye abin miyar ya zuba musu tare sai kallonsa take yi ganin yanzu yana mata 
wasu abubuwan da marigayi yake mata hakan kuma ya sa ta dan sakar masa tun yana 
bata a yangance taji ko abinda ke cikin nata besan ana bata abinci ba yasa ta cewa. ’ 
“Kawo ni na dinga baka gaskiya.” 
A tunaninsa ko ta fara sonsa yayi murmushi tare da sakar mata spoon da pork din, idan ta bashi sau daya sai tayi kusan spoon biyar sannan zata kuma bashi, ya dinga bin fuskarta da kallo yana jin wani abu tamkar magnet yana fisgarsa. Sai da suka koshi sannan ta kwashe kwanukan takai wajan wanke-wanke yana binta da kallo duk da cewar doguwar riga ce ajikinta sai dai komai na jikinta rawa yake yi Sadeeq yajingina da kujera shi kam bazai iya kwana a haka ba, tunda yasawa ransa idan ya dawo zai samu nutsuwa koda a gurin Fateema ne toh gashi tana off yayi 3mothns a wahale bazai iya kwana haka ba.
“Sir Sadeeq na gode sosai, a cewa Fateema itama na gode ga kwanukanta.” 
lNdo ta fad’a tana kokarin ajiye kwandon akan center table. Shi kuwa tamkar me bacci haka yayi nan kuwa yana kallonta ta kasan ido yaga tana kallonsa jin yayi shiru yasa ta shiga d’aki ta zauna a bakin gado tare da dakko jakar makarantar ta ta fito da books d’in wanda duk iya kunshesun da tayi a jiki saida ruwa ya taba su ta bubbude su akan gado tana turo baki ganin duk sun sha ruwa. 
Ta bayanta taji ya rik’o ta, sharesa tayi ta cigaba da hura book d’in hannunta da baki ya sa hannu ya karba ya ajiye akan gadon ita kuma ya jata suka kwanta akan gado INdo tace. 
“Ana kiran sallar la’asar.” “Uhmm naji Humaira but I need your help please.” “Tofa name.?!” 
“I need you, dan Allah humaira karki min wata fassarar karki hanani ina cikin matsala humaira wallahi I love you… I love you Aisha karkiyi tunanin kodan wannan abun ne.” 
Jikin INdo yahau rawa ta fashe da kuka tana jin yadda yake mata amma ta kasa hanasa domin tanajin hirar matan ajinsu akan mazajen su. Shi kumajin bata yi masa irin na farko ba yasa shi cikin karyar da kai da nuna tsantsar nadama yasa har ya cinma muradinsa akan ta sannan shima yahau yin nasa hawayen. 
_”Twinnie kasan nifa ni bazai yuwu nazo gidana naga matata ba sannan na kyaleta ba no Zuciya ta baza ta bari bama tunda nasan mallakina ce.”_ 
Ya tuno irin hirarrakin su da Abubakar cikin shakkiyar murya Sadeeq yace wa lNdo. Shkukran-laki Aisha Humaira. Do you love me? Please humaira love me as I love u koda na iya 
yau ne kawai.” “Malam 
Ya rufe mata baki da nasa cikin son katse ta da sunan da yaji zata kirasa sannan ya cire 
yace. 
“Don’t call me malam again. please change my name in dai har kin yadda zaki soni kamar yadda kike son twinnie dina.” 
Hannunsa zagaye da wuyan ta suna hada numfashi INdo tace ….. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]