[Advertisements⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 28 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 28
Tunda suka tafi koda wasa Sadeeq be taba gigin k’iran INdo a waya ba, bashi dama fa phone number dinta bare yace zai nemeta. A bangaranta itama bata ko tunaninsa tana gidanta hankalinta kwance babu abinda yake damunta. Ranar da su Sadeeq suka cika sati d‘aya da tafiya a ranar INdo ta fara fita, kullum tana gidan mak’ota bata nan layin bata can sam bata zama cikin kwanaki takwas mutanan unguwar sun santa maza da mata yara da manya. Yayin da a bangaran Sadeeq yana son ya kirata tunda yasan tana da hakki akan sa amma baya kaunar ya kirata tayi mai rashin kunya ko ta gaya mai maganar da zai kasa bacci dan ya lura akwaita da shuka magana ba kuma ta barinta indai harka gaya toh zata baka amsa hakan yasa ya shareta. 
Misalin k’arfe hud’u ta fito daga wanka tana shafa mai tajiyo me tallah a k’ofar gida, cikin sauri ta janyo doguwar riga a cikin wardrobe ta zura tare da d’aukar mayafi ta fita. A k’ofar gate d’in ta tsaya dan sake tabbatarwa da kunnuwanta abinda me tallar yake cewa still taji yana cewa. A sai kajin gidan gona matasa..!” 
INdo tayi saurin fita tare da kwala mai k’ira ya dawo baya kasan cewar harya wuce gidan nata. Tsayawa tayi suka fara ciniki zata siya har yace zai siyar mata a yadda cinikin ya tsaya, guda bakwai ta siya ta shiga gida ta d’akko mai kud’in ta bashi ya tafl ita kuma ta shiga da ‘yan kajinta sai kuka sukeyi iya-iya-iya tana ta murna taje ta zuba su jikin bathroom d’in tsakargida dama ba’a shigar sa. 
A hankali ta ci gaba da kiwonsu tana bayarwa ana siyo mata abincin su hankalinta a kwance su Haleema idan suka zo suyi ta mata dariya ita kuma tace da tayi kud’i saudiya zata tafi idan ta dawo a dinga k’iranta Hajiya INdo kasan cewar sunan ya bazu cikin gidajen mak’ota k’annan su Sadeeq ne kawai ke kiranta da aunty Humairah kamaryadda marigayi ke fad’a mata. 
Rayuwar INdo ta cigaba da canzawa sana’o‘i take yi kala-kala kajinta ma sunata girma har ta samu sun fara kwai tana tarawa taci takai gidan su Sadeeq sai da Mama tace ta fara siyarwa sannan ta fara. Da daddare tana kallon arewa 24 Sumayya tana gabatar da shirin tauraruwa taji yadda wata mata da ake hira da ita yadda rayuwarta ta faro tun daga tushe haryanzu da takai wannan matsayin nan da nan lNdo tayi sha’awar yin karatu itama tana son ta iya turanci sai dai tayaya zata iya? Sam kwakwalwarta bata gane turanci ba kuma ta iya rubutawa sannan ba ta iya maida hankali wajan koya tayaya zata iya zama tauraruwa kamaryadda taga ana haskilo mata masu aji ana kuma alfahari dasu, tasa a ranta zata fara koyan turanci 
kamaryadda marigayi yaso tayi kafin mai rabawa ta rabasu. 
Sannu a hankali tana jin takaicin Sadeeq nak’in nemanta tun ranar da Aminatu ta guntsa mata cewarai dan batajin turanci ne yasa Yaya Sadeeq cewa baxai tafi da ita can ba hakan yasa abin ya kuma ba ta haushi tsanarsa ta kuma hauhawa a cikin zuciyarta dama ya saba yi musu wulak’anci tun a tsefawa. 
M.M Haruna English academic taJi anata tallar makarantar a gidan redion express, ta fara tunanin yadda zata yi ta samu shiga cikin ta. 
Tanason zuwa tana tsoron kar da taje ta tarrar da garzazzu wad’anda basa Hausa sai turancin, wai shin ma meyasa aka maida turanci tamkar saukar alkur’ani da komai za’a ce in zaka yi sai ka iyasa? Ga larabci yaran annabi amma ba a dagewa da zuwa islamiyoyi ba’a basu muhimmanci kamar yadda ake bawa yaran jajayan farar fatar nan. idan aka kyaro 
baka iya bama sai ka zama wani hulugu ka zama abin raini da wulak’anci a wajan al’umma. Zata yi turanci itama za kuma taje ta koya badan wulak’ancin Sadeeq kad’ai ba sai dan wata rana itama ak’irata ayi hira da ita a kuma tambayeta tauraronta tace Abubakar ne,haka zakila kuma a Dama da ita ita duniya wannan burinta ne ba kuma zata canza shi ba koda Sadeeq zai saketa. a 
“Hello mubassheer, kana Ina yanzu.?!” “Ina majalisa ya akayi ta samu ne..?!” 
“Kai dan rainin wayo ne, kazo dan Allah zamuyi sirri.” 
“Toh aunty Humaira gani nan zuwa amma fa zaki ban jakar kunun aya guda biyu.” “Dallah idan baxakazo ba sai na kira khaleefa wallahi.” 
“Sorry Matar broth ina zuwa.” 
Kashewa yayi yana dariya sannan ya d’auki abokinsa guda d’aya suka tafi gidan a mashin. A falo suka zauna ta kawo musu kunun ayar da zobo da jallop d’in taliya suka ci sukayi dam sannan mubashsheer ya kalli INdo yana cewa. 
“Toh meye sirrin Matar broth, tunda kin bamu munci. Sai data hararesa sannan tace mai. 
“Dallah kaga ni ba surutu na tambaye ka ba,jujun labo store zaka dan Allah ka siyo min farm (form) d’in shiga makarantar M.M Haruna English menene ma dayan na gaban ma oho na manta.” 
Ah Matar broth wai kina nufin shiga zakiyi..?INdo tace “Eh ya ranka? Zakaje kayi min duk abinda za’ayi na fara zuwa kokuwa wulak’anci zaka yi min Kai ma..?!” 
“Ah Matar broth na isa, kawo kud’in toh sai muje muji ya za’ayi, amma tukunna kin sanar da broth Sadeeq d’in zaki fara ne dan karya zo yayi min masifa.” 
“Kai zaka siyo min ko kuwa na saka wani?!” 
Ahh nina isa kawo kudin muje muji ya za,ayi
“Toh nawa zan baka..?!” 
“Haba ki kawo ten thousand muje mu fara manage dasu.” 
“Kana nan nawa kenan?!” 
“Kai Matar broth dubu goma zaki kawo naga kina min wani kallo.” “Tab goma fa kace? Wallahi ku tafi na fasa ai ba dole bane.” 
Ta fada tana shiga cikin d’aki Mubasheer ya dinga yi mata magiyarta fara bada ten thousand d’in tace ta yafe bazata ba sai da yace. 
“Toh kawo five thousand, dubu biyar wallahi Matar broth kin fiye san Kud’i da yawa, duk sati dubu biyar broth yake badawa a kawo miki ga kud’in zobo ga kunun aya ga gullisuwa da kwan kaji dan Allah mekikeyi da kud’i bayan duk akwai abinci a gidan..?!” 
Dubu biyar d’in ta bashi ya karba ya kirga sannan suka tashi zasu tafi”: INdo tace.  
“Dan Allah kanin miji a rage sa ido, duk lissafin ka yana kaina toh da ba kudin zaka ci naman dakaci a cikin abinci ne? K0 zaka ci harda vegetables din ne d’an rainin wayo.” Tayi “Magana ta wuce bari muje mu dawo.” 
Yana fada suka fice ita kuma ta shiga daki. Ko Ina tas-tas a gidanta bata barin kazanta sannan kullum cikin kanshin turaran tsinke d’akin yake dan haka INdo tana samun customers a rana sai ta durajarkokin zobo dana kunun aya guda d’ari biyu amma baya kaiwa dare Allah yasanya mata nasibi a ciki. 
A ranar bataga Mubasheer ba har kwana biyu sai gashi yazo, tsayawa yayi yace ya gama mata komai zuwa kawai zata farayi domin sai da ya sanar da abban su ya kuma bada goyan baya sosai. Juma’a na zuwa ta fara zuwa cikin tsoro da fargabar yadda zata tun kari malamai da dalibai dan tasan duk sun fita kok’ari. 
“Matar broth ga class d’inku nan.” Mubasheer ya fad’a yana nunawa INdo ajinsu. Ido ta dinga kwalowa waje hannun ta na dama dafe da k’irji ta kalli Mubasheer cikin tsoro tace. 
“Anya bazan koma gida ba, Mubasheer tsoro nakeji wallahi.” “Kai Matar broth wallahi karkiji tsoro kowa fa da kika gani zuwa yayi a koya mai, idan kika nuna musu kinajin tsoro zasu raina ki kedai karki fasa yin abinda kike so ki shiga kawai.“ 
. ..,,”Toh Matar broth Allah ya bada sa’a.” 
A hankali INdo ta shiga tashin farko ganin yadda hall d’in yake yasa gabanta bugawa da karfi sannan ga dalibai nan a zazzau ne duk sai ta daburce ta rasa inda zataje cikin sauri ta juya zata fita sai taga Mubasheer a tsaye yana dariya, cikin tsananinjin kunya tace. 
“Maidani gida bazan shiga ba.” 
“Hahaha… Wallahi babu inda zaki, muje na shigar dake haka kurum dan ayi asarar kud’i 
sai da aka gama komai zaki wani ce kin fasa.” 
Yana gaba tana bayansa har ya k’arasar da ita tsakiyar kujerun sannan yayi wa wata 
budurwa magana cewar gata nan dan Allah ta fara helping d’inta ta wasu abubuwan. 
Karimatu tayi murmushi tare da mik’awa INdo hannu suka gaisa ta zauna a d’ari-d’ari 
kamar munafuka sai wulkita idanuwa take a haka Mubasheer ya barta yayi tafiyarsa. 
Malami na shiga ta fara sunkuyar da kai, nan aka fara gabatarda lesson kasan cewar ajin masu koyan turanci ne hakan yasa komai ake yi musu dalla-dalla cikin hikima da kuma kwarewar malaman ita dai lNdo tayi tsit bata ko kwakwaran motsi dan karma malamin yayi mata tambaya koya saka mata ido. Alhamdulillahi kuma ta tsinto abubuwa kasan cewar sai anta maimaita musu abu anji kowa ya gane an kuma fahimta sannan za’a shiga wani abun haka aka dinga yi musu tana kuma zuwa dukjuma‘a asabarda lahadi da safe. ‘
Wata daya da sati biyu su Sadeeq sukayi a kwara state sannan sukajuyo suka dawo kano. Lokacin satin lNdo biyu da fara zuwa makaranta, sam bata yi wani murna da dawowarsa ba sema haushi da takaici dataji. Sai da yayi kwana biyu a gidan Fateema sannan ya waiwayo yau zaijegidan da INdo take. a 
Kofar gidan ya tsaya wajan karfe sha biyu na dare, key d’insa na gidan ya zura ya dan bud’e abu ya gagara sai yahau buga mata tana kwance a kan gado da littafi a hannunta tana Home work d’in da aka basu, tanaji saidai batasan kowaye ba dan haka batayi ma niyartashi zuwa ta gano ba. Mtwwww yaja tsaki tare da ciro wayarsa ya nemo layin Haleema, mtwww ya kumajan wani tsakin jin tana amfani da ita ya sake kiran khaleel cikin sa’a ya d’auka murya a shak’e Sadeeq yace. 
“Dan turo min da numbern Aisha.” Khaleel yace “Yaya bani da ita sai dai ko yah Mubasheer.” 
“Cene masa ya turo min.” 
Ya fada a dakile sabida babu kowa unguwar sai shi kadai ga duhu. Yana tsaye yaji an turo ya kira number’n kamar bazata d’auka ba sai kuma tayi picking tare dayin shiru dan taji me maganar. 
“Ke zoki bud’e min gida kinaji Ina bugawa kikaki zuwa ki bud’e min.” 
Harzai katse yaji tace. “Waye kai din? Wa kuma kake nema..?!” 
“Au bakima san waye ba dan rainin hankali Aisha?!” 
Tace “Kai kaga kila wrong number ne go and check.“
Kafin yayi magana ta katse kiran ta cigaba da aikin ta, Sadeeq yabi fuskar wayar da kallon cikin mamaki ya sake buga gate din da karfi? cikinjin haushi amma taki budewa cikin bacin rai ya buga numbern Mama tana bacci Haleema ta d’auka tana dubawa taga Sadeeq dan haka ta dan janye wayarta daga kunne da takeyi da saurayinta ta kara tare da cewa. “Yaya lafiya? Mama tayi bacci fa.” “Yauwa Haleema kira number’n Aisha kice ta bude min gidan Ina waje.” “Okey tom Yaya sai da safe.” 
Tana kashewa ta kira layin INdo, tana kwance duk tama rasa yadda zatayi Home work 
dinta taga kira ta duba a tunaninta number’n dazu ce tayi niyar d’agawa tayi mai rashin mutunci sai kuma taga dacta da haka akayi mata saving sunan tayi murmushi tare da karawa a kunne tana shirin gaida ita taji Haleema na cewa. ‘ “Aunty Humairah Yaya fa yana kofar gida yace kije ki bud’e mai nidai sai da safe.” 
“Dama shine? No wonder naji ya fada da gadara zoki bude min gida, d’an rainin hankali ai na d’auka harka koma bazaka zoba.” 
Hijabi tasa ta dauki mukulli tayi waje, cire kwadon (pad lock) d’in tayi ta bude mai ya shigo sannan ta juya ta koma, shi ya bude gate din yasa motar sannan ya rufe gidan ya shiga ciki. Bata falo ya bita bedroom fuskarsa a had’e yana shiga ya ganta kwance da littattafai a gabanta da biro da alama rubutu takeyi baki bud’e cikin tsananin mamaki yace… 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]