[Advertisements⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 25 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 25
Har sukaje gida Abba be sanar da Sadeeq ba, suna zuwa Abba ya shiga gida shi kuma Sadeeq daya kagu yaje gida ya juya kan motar ya tafi. Abba na zuwa fuskarsa cike da fara’a 
ya cewa su Umma. “Toh hajiya Au an daura aure yau.” “Alhamdulillah Allah ya sanya musu albarka ya kauda fitina ya basu zaman lafiya.” 
Cewar Umma nan da nan fa gida ya cika da murna lNdo kuwa bacci take a lokacin sai 
bayan da ta farka ne Mama tace. “Aisha jeki wanka kizo kuje gyaran kai.” 
Da sauri INdo ta mike cike da murna domin tunda ta dawo gidan bata sake koda lekawa kofar gida ba, sam sun hanata ko unguwa Mama zasu sai ta kafa mata doka akan idan ta kuskura ta leka waje, yau gashi zata fita kusan kwananta dari da takwas raban data kalli waje bare taga abinda yake wakana. Tayi kyau tayi haske fatar jikinta tayi luf-luf sannan tayi kiba da yake hankalinta a kwance yake suna kula da ita sosai dan ko ‘ya’yan gidan basu kaitajin dadi ba. 
Wanka tayi tana fitowa taga saban dinki an dakko mata a can gidan Abubakar da takalmi da jaka da mayafi su dankune sarka da kayan kwalliyar su Haleema. Zama tayi tana kallon kayan tare da shafa jakar da takalmin sai hawaye a fito mata tace. “Allah sarki dacta kai ka saimin su..” 
Tashi tayi tasa kayan sai ga Mama ta shigo cikin wasa tamkar ba suruka ba tace. “Toh wa kika tambaya da kika dauka kika sa? ldan kuma nawa nefa..?!” Dariya lNdo tayi tana rufe baki tace, 
“Ai Mama ina ganin jakar na gane su, lokacin da zai kaimu gidan abokanansa da nadakko 
zan rataya yace min basu yi match da kayana ba na ajiye ta.” “Allah sarki Abubakar Allah yayi masa rahama Allah yayi baxaku yi tsawon kwanaki tare ba.” Cewar Mama tana dakko mata humra ta ajiye mata a kusa da kayan tana cewa. “Daga yau zaki iya sanya komai Aisha sai dai zaki ci gaba dayin abubuwa irinna matan aure domin yanzu kema Matar aure ce.” Sam INdo bata gano inda zancen Mama ya nufa ba, a tunaninta tunda ta taba aure toh zata ci gaba da suturce jikinta da kuma dora mayafi aka. Tana gama shiryawa Mama ta bata kudin gyaran kai tasa suka tafi dasu Haleema. Lokacin data fara zura kafarta a waje ji tayi tamkar yau aka haifeta. Wata ajiyar Zuciya ta sauke tare da kallon ko’ina na wajan taga mutane kowa yana harkar gabansa, wasu kuma da suka santa suna sake yi mata gaisuwa tana amsa musu har suka kai bakin titi Haleema ta tare musu napep suka shiga. 
Shagon saloon suka shiga sun dan jima sannan suka fito suka dawo gida. Da dare bayan 
Abba ya dawo ya kira Sadeeq sannan ya kira INdo, Mama da Umma duk suna zaune a dakin. Cikin muryarta medan karadi tayi sallama tare da shiga ta zauna tana gaida Abba. 
A hankali Sadeeq ya dago ya kalleta sannan ya kawar da kai cikin ransa yana tambayar dama tana da ladabi ko kuwa har lokacin mutuwar mijinta najikinta ta dai kusa tafiya shima ya samu ‘yancin shiga gidan ubansa. Abba ne ya kira sunansa ya amsa tare da kallonsa abban yace. “Toh Sadeeq kamar yadda ka sani tagwai dinka Allah yayi masa rasuwa ya bar matarsa, yau kuma Allah ya nuna mana cikar wa’adin takabar ta kamar yadda addini ya dora mata. Sadeeq kaine mutum na farko daya kamata ya rufawa matar dan uwanka asiri ka dubi halin da zata shiga idan ta koma garin su ka kuma dubi kankantar da tayi a matsayin bazawara bawai munaja da ikon Allah bane a’a duba da yadda rayuwarta zata fada yasa muka yanke wani hukunci akai.” 
“Babu komai Abba ni dama tuni nayi alkawarin zan dinga tura mata kudi sannan zan dinga yi mata abinda take bukata idan har baifi karfina ba damajira nake ta kammala iddar sai na tambaye ta abinda yake matsalarta.” 
Sadeeq ya fada ba tare da ya kawo komai ba dan sam beyi tunanin wani aure tsakaninsa da ita ba, Fateema yake so kuma ita ya aura baya tunanin zai yi ‘MUSAYAR ZUCIYA’ da watanta nan gaba bare kuma nan kusa daga yin aure wata biyar. “Toh Sadeeq ai wannan abubuwan daka fada koni zan iya yi mata shi, mu yanzu fatan mu ka rufa mata asiri a matsayin ta na mace me rauni kuma matashiya domin a dazu daka kaini Sumaila kauyan su naje ne mun daura muku aure dakai da ita ka maye gurbin dan uwanka… A matukar razana Sadeeq ya zaro idanuwa yana kallan Abban shi, zuciyar sace take rawa jikinsa na tsuma ya kalleshi yace. “Abba wani auran zan kuma yi? Abba ko wata biyar ban cikasa ba ace na kuma yin aure? Tayaya zan iya zama da mata biyu Abba bayan yanzu nayi dayan? Abba matar twin din zan aura? Ya akayi mutuwa tayi min haka…” “Kai ya isa haka karkayi min sakarci kaji ko? ldan baka aureta ba ya kakeso tayi bayan tana bukatar temako da kuma mai lallashi da tausayawa a gareta…?
“Amma Abba yau yau dinnan fa tayi takaba amma ace ayau za’a daura mana aure ko fuskanta juna bamuyi ba? Abba ya Fateema zataji wannan labarin.” Ya fada tamkarwani maraya Abba ya wurga mai harara Cikin bacin rai’ yace, 
“Da kuma ace kaine ka rasu akace Abubakar ya auri Fateeman zakaji dadi ko kafison ta tafi ta auri wani bare..?!” 
“Wallahi Abba gara ta auri bare haba-haba sai kace jira, dan Allah Abba kuyi tunani ni 
wallahi…” Bekarasa ba Abba yayi saurin katse sa ta hanyar cewa. “Toh shikenan sakarta ni sai na aureta shikenan hakan yayi maka.?!” ‘ Cikin tashin Hankali Sadeeq ya kalli mahaifinsa sai zuba uban gumi yake baki na rawa yace.”Innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un Abba ai babu aure tsakanin ku gara nidin.” 
“A’ah aini tausayinta nakeji Sadeeq kuma abinda zanyiwa Abubakar kenan yasan nayi mai kara ka sake ta sai na aureta ko kuma uncle dinku Ahmad.” ‘ “A’a Abba dan Allah ka rufa mana asiri na karbi auran Allah yajikan twinnie yasa can 
tafiye masa nan.” 
Duk suka amsa da amin banda lNdo wadda tunda taji maganar da akeyi tayi kicin-kicin zuciyarta banda bugawa babu abinda takeyi wani radadi na shigarta. Abba ya maida hankali wajan ta ya kalleta cikin kulawa yace. “Aisha muna fatan bamuyi miki shishigi a cikin rayuwarki ba, muna fatan zaki yadda da 
auran Sadeeq gashi nan komai nashi iri daya ne dana marigayi…” Da sauri INdo tace “A’ah Abba wallahi ba halinsu daya ba koda can kafin mu saba.” Abba ya kalli Mama itama shidin take kallo sannan tace. “Aisha ai shima Sadeeq zai miki abinda marigayi yayi miki kiyi hakuri idan kuma bakya sonshi shikenan aike yanzu babu batun yi miki auran dole gareki a wannan karan ma. Dama munyi haka ne dan karki shiga damuwa ko da idan kinga Sadeeq din.“ Shiru tayi batace komai ba su kayi-sukayi tayi magana amma tayi shiru Umma tace. 
“Toh da alama ta yadda Allah ya bada zaman lafia.” Tashi Sadeeq yayi ya fita Mama da lNdo suma suka fita aka bar Umma kasan cewar itace da girki a ranar. Dakyar ya iya kai kansa gida, lokacin daya shiga Fateema na kwalliya cikin bedroom taji shigowarsa amma bata ga ya shigo dakin ba, shi kuwa guri ya samu a falo ya zauna kan kujera tare da dafe kirji kanshi na barazanar fashewa ya tarwatse. 
Fateema ce ta fito cikin shirin bacci tayi kyau ta kuma fari kai da kaganta kasan tana cikin kwanciyar hankali, karasawa tayi kusa dashi ta dare kan cinyarsa tana kokarin dago mai kai. Janyo ta yayi jikinsa da karfu tare da sanya ta a kirjinsa ya matseta da hannuwansa tamkarzai maida ita ciki ita kanta dakyar take numfashi zuciyar ta cike da mamakin yadda taganshi. 
“Wayyo Allah baby zaka karya ni.” Ta fada tana kokarin kwatar kanta sabida ba karamin azaba takesha a matsar ba. A hankali ya sassauta mata rikon dayayi mata cikin sanyin murya Fateema ta kallesa tace.
“Baby wai meyake damunka, haka kashigo fa ba sallama kuma naga dukjikinka a sanyaye meya faru..?!” “Bakomai kinci abinci dai k0?!”Ya tambaya yana shafar cikinta, kada kai tayi tana kallon shi ya lumshe idanuwa tare da kwantota jikinsa yace. “Toh why?!” “Baby kasan dai bana iya ci harsai kana nan, meyasa yanzu kake tambaya na…?!” “Kinsan ai bana son kina zama da yinwa, kinga gobe ina da lecture 9 to 11 kuma gashi banajin dadin jikina ya zanyi ne..”Fuskar sa ta tallafo sukayi kallon cikin ido ta sakar masa murmushi tana shafar gashin dake habarsa tace. “Yanzu ai lokaci bekure ba goma da rabi saura minti uku kayiwa class captain waya kace musu bazaka samu damar zuwa ba suyi hakuri zaka samu wani time din sai kuyi musu 
amfani dashi…” “Ai kuma baby ban musu lectures bafa tunda aka koma gashi har an fara tambaya na exam questions, zanje ko abu daya ne nayi musu tashi muje kici abinci.” “lnci abinci k0 dai muci abinci?!” Ta tambayesa tana sake lafewa a jikinsa, suna zama yana cewa. “Kinsan Abba neya kirani so munci abinci tare dashi.” ‘Dan hararasa tayi tare da cewa “Ai kasan dai nima nawa yana jiranka dan haka sai kaci 
babu wani batun kunci da Abba ko zakayi amai kuwa.” 
Shi sam yarasa ma mezai yi yinwar ma bajinta yake yi ba shi yasa yace mata haka amma 
dan karta shiga damuwa sai yace. “Toh baby na ya zanyi amma nasan yau babu abinda zan iya tabukawa.” Shi dai dakyar ya samu yaci duk tunanin yadda zai bullo mata yake yi a cikin zuciyarsa, sai daya tabbatartaci ta koshi sannan ta rakashi yayi wanka ta bashi sleeping gown ta maza yasa sannan suka bi lafiyar gado. Kamar yadda ya sabar mata koda bazai yi komai ba toh sai sunyi wasa haka yauma har sai da yaga ya kwantar da kanta kan kirjinsa zata yi bacci ya bude baki dakyar ya kira sunanta. “Zarah…” Tayi jimmm jin yadda ya kira tsohon sunan da yake kiranta dashi tun suna saurayi da budurwa, can dai ta amsa mai tana shafar kirjinsa shi kuma yana shafar himilin gashin kanta domin akwai suma yace. 
“For example nine na rasu ba Abubakar ba idan aka ce ki auresa zaki iya..?!” Ya karasa maganar yana dan dago mata kai. Shiru tayi na tsawon lokaci tana tunanin abinda yasa shiyi mata wannan tambayar marar dadin ji bare sauraro, sai daya sake tambayar ta sannan ta numfasa dakyar tace. 
“Haba baby ya zaka min wannan tambayar tunda dai bakai ne ka rasun ba?” Yace “Eh so nake naji zaki yadda idan akace ki auri twinnie dina ya zakiyi.” “Gaskiya bazan auresa ba haba ai bashi na aura ba.” “Toh idan aka tursasa kifa ko aka aura miki shi ba tare da kin sani ba ya zajiyi..?!” “Tabdi wallahi baby saiya sakeni uhm’um ni dan Allah ka dena yin irin wannan tunanin please.” 
Jikinsa ya sake janyota yana shafar bayanta, so yake ya sanar da ita yau basai taji a bakin wani ba amma ya rasa hanyar fadarya dai daure yace. 
“Toh idan hakan ta faru tunda ni bakya sona mutu akace na auri Humairah ya zakiyi?!” “Bama zata yiwu ba sabida lNdo bata sanka har agabana ta fada.” Shiru suka yi na tsawon lokaci gashi dare ya tsala ko’ina yayi shiru sai karargen dinsu kawai akeji. Numfasawa Sadeeq yayi tare da janyota yace. “Kiyi hakuri baby na yanzu dawowar da kikaga nayi Abba ne ya sanar dani cewar an d’aura min aure da ita ni kaina ba…” Jiyayi ta mike zaune a razane daga ita sai bra domin rigar ta zame Fateema ta bishi da kallo hannunta dafe da kirji ya kalleta bayan shima ya tashi zaune. Wata shegiyar harara take wurga mai cikin zafin rai ta fara magana jikinta na rawa. “Yanzu kana nufin har an d’aura muku aure?” 
Sadeeq ya daga mata Kai alamar eh yasa hannunsa yajanyo ta a hankali ta fada jikinsa ta saki kuka me ban tausayi ya fara lallashinta shi kansa ji yake tamkar yaje ya bindige lNdo. Babu yadda zatayi ita kuma haka tata kaddarar take daga yin aure sai kishiya suna cikin more rayuwarsu. 
A bangaran lNdo kuwa wani uban nishi ta dinga saukewa duk iya kokarin Mama na ta gaya mata matsalar ta sam tayi shiru taki yin magana har gari ya waye bata yiwa kowa magana ba Mama ta rasa dalili dan ta saki ranta yasa Mama cewa. “Aisha gobe za‘a kaiki gida kije kiyi kwana biyu kam Sadeeq din ya ware yadda zai yi.” Sai a sannan INdo tayi magana tana dariya tace. “Toh Mama amma dai ba shine zai maida niba…?!” “Toh ai Aisha yanzu dai komai yana hannunsa sai abinda yace kiyi mai biyayya kedai anan zaki samu aljanna.” Ba zato cikin subutar baki tace. “Tan dijam..” Mama ta kalleta cikin mamaki amma sai taga lNdon na mutsu-mutsu da baki alamar magana take a ranta lallai yaran nan da alama zasu basu mugun mamaki sam basuyi zaton INdo zataki Sadeeq ba ganin yadda suke kammani da mijinta ba…. ‘ 
Hmm koya zata kaya 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]