HARSASHEN SO CHAPTER 32

Advertisements

_____

HARSASHEN SO 
CHAPTER 32
Kasa daurewa Shalele tayi ta lallaba ta kwanta, momy tace yadai? Murmushin karfin hali Shalele tayi tare da cewa ba komai. 
Momy tace to Allah yasa, Shalele ta amsa da amin, 
Wayarta ta dauka ta turawa Mubarak sako cewa don Allah bata lafiya ya taimaka yazo ya kaita asibiti. 
Gajeran tsaki yayi bayan ya gama karanta sakon sannan ya tura mata cewa, bazan je ba, 
Sake tura masa tayi cewa, aini kasan banda zuciya, kayi hakuri ka kaini, karfa ka manta diyar ko dan nan da zan aifa bafa nawa bane ni daya. 
Abinda ya rubuta mata cewa shine, idan kin aifa ki dauka duka na baki wallahi. Kuma karki bari suce min Baba ko Dady domin duk duniya wannan kalmar na tsana a kirani da ita, kici gaba da fadar Mubarak dan suma su rika kirana da sunan. 
Murmushi Shalele tayi amma bata bashi amsa ba saboda murdawar da mararta yakeyi. 
Saukowa tayi daga saman kujera ta kwanta kasa, wai a haka boyewa takeyi dan kar Momy ta gane mata. 
Murkushe murkushe takeyi sosai har ta kasa boyewa, ganin haka yasa Momy tace Suleim 
kodai in kaiki asibiti ne? Cikin jajircewa Shalele tace babu komai zan samu sauki in Allah ya yadda. 
Momy ganin Shalele da gaske haihuwa zatayi yasa tace gaskiya tashi muje na kaiki asibiti, Shalele da wahala ta isa tace tom, waya tayiwa Mubarak dan neman izinin fita amma bai dauka ba, “ 
Sako ta tura masa cewa zataje asibiti tunda shi baya da hali, rubutawa yayi cewa nidai idan kinje bada izini na ba, kuma wallahi ban yafe miki ba. 
Murmushin takaici Shalele tayi tare da mantawa da lamarin Abak. Tashi Shalele tayi ta nufi toilet domin jinta takeyi kamar zatayi bayan gida. 
Da rarrafe ta ida shiga toilet din, tana shiga ta fara kokarin mikewa tsaye, tayi ta mike tsaye amma ta kasa mikewa, jin kamar zata zarce lahira yasa ta fara kiran Momy tana kuka, da gudu Momy ta shiga toilet in tare da cewa nace miki muje asibiti aihuwa zakiyi, Shalele cikin jigatuwa tace ba bukatar zuwa asibiti insha Allah zan samu …….. Wata irin kara ta kara saki sosai wanda ta hanata ta karasa fadar maganar da tayi niyya. 
innalillahi wa”inna ilaihir raji”un mutuwa zanyi, cikin tausayawa Momy tace baza ki mutu ba Suleim. 
Rike Shalele Momy tayi tana shashshafata a hankali tare da mata maganganu masu sa 
natsuwa, cikin rarrashin tace kiyi nishi sosai domin Momy ta lura Shalele gab take da ta sako babynta yazo duniya. 
Rike Momy Shalele tayi sosai tana maijin kuna a ranta, da Momy bata zoba kenan da saidai ta mutu, wata irin tsanar Mubarak taji a ranta ji takeyi kamar ta kamoshi ta kasheshi. 
Wata irin kara ta saki a lokacin da babynta ya fado duniya, lokaci daya kuma kukan jariri 
ya fara tashi, da sauri Momy ta fita cikin farin ciki, jakar kayan da tazo dashi ta bude ta fiddO reza ta koma toilet domin ta hado duk wani abu da mai aihuwa zata bukata, 
A lokacin data koma tuni Shalele ta kara halbo wani babyn zuwa duniya, cikin farin ciki Momy ta yanke cibi, ta dibi ruwan zafi ta wanke jarirai fes ta zugesu a cikin kayan data siyo wa Shalele, 
Ruwa ta zubawa Shalele itama ta daureye jikinta, Momy ta wanke toilet din ta goge tatas ta watsawa dakin kamshi, Shalele kuwa waya ta bugawa Mai gida ta haihu. Dariyar mugunta 
Mai gida yayi tare da cewa Allah ya raya, Shalele tace amin, 
Suna gama waya da Mai gida ta turawa Mubarak sako cewa ka hau online zan baka babban albishir, tattara yaran tayi ta rumgumesu ajikinta tana mai farin ciki Momy ta daukesu hoto. 
Shalele ta turawa Mubarak, wuta kuwa daukewa Mubarak tayi a lokacin da yaga hoton yaran da Shalele ta tura masa, wani irin bakin ciki ya tokare masa zuciya a zuciye ya fito dan tafiya dakin Shalele a daidai lokacin da Mai gida ya shigo gidan. 
Gaishe shi Mubarak yayi cikin girmamawa, Mai gida kuwa yayiwa Mubarak barka, amsawa yayi dai ciki ciki, Mai gida yace rakani wurin ita Shalinin mana, Mubarak yace to, shiga yayi 
gaba Mai gida yana biye a bayansa har zuwa dakin mai girma Shalele. 
A palo Mai gida ya zauna, Mubarak kuwa ya shige cikin dan fiddo da Shalele, ko inda yaran 
suke Mubarak bai kalla ba yace idan kinga dama kizo Baba yana kiranki, 
Murmushi Shalele tayi tare da cewa Momy muje Mai gida yazo, itace ta dauki yaro daya Momy ta dauki daya har palo, gaisawa sukayi da Mai gida ya sakeyi musu barka suka amsa, ya anshi yaran dukansu yayi musu addu”a, bayan ya gama ya kalli Mubarak yace Allah ya raya, 
Kauda kai Mubarak yayi ba tare da yace amin ba, Mai gida ya kalli Momy yace to Yaya ki tashi muje, kema Shalele ki dauko mayafinki domin makaranta zaki koma, 
Da sauri Mubarak ya dago kansa ya kalli Mai gida yace Baba ya za”ayi ta koma makaranta dajarirai, Mai gida yace inji wa yace maka ana zuwa makaranta da jarirai ne.Ai ajiye maka “ya “yanka zatayi. Cikin tashin hankali Shalele tace Mai gida ya za”ayi haka kuma? Mai gida yace ai ba “ya “yanki bane ki barwa ubansu su ki tashi mu tafl …….. ya karasa maganar cikin tsawa Da sauri Shalele ta mike tana kuka ta koma daki don dauko hijabi, 
Cikin tashin hankali Mubarak yace haba Baba wannan wane irin hukunci ne? Mai gida yace ta bar maka duka ka dauka idan baka so ka zubardasu a daidai lokacin da Shalele ta fito tana kuka. 
Mubarak yace Shalele wallahi idan ma kika bar yaran nan babu abinda ya dameni nan zan barsu suyi ta kuka babu ruwana, Momy tace Mansur wai miye haka ne? Mai gida yace babu ruwanki dan haka ki fitar da kanki a cikin wannan hukunci. Cikin hargowa Mai gida yace fita muje, simi simi ta wuce tana kuka Momy tabi bayan Shalele, cikin damuwa Mubarak yabi Shalele da gudu ya riketa yace Shalele karki biyewa Baba wallahi “ya “yanki zasu mutu babu abinda ya dameni, ‘ 
Cikin bacin rai Shalele tace da Allah su mutu ko ance maka idan sun mutu nima mutuwa zanyi, ta fizge hannunta tare dayiwa Mubarak tsaki ta wuce, yana bin bayansu yana magayi har suka shiga mota suka tafi”, 
A hanya Momy tacewa Mai gida mi yasa yayi wannan hukunci hakan bai kamata ba, Mai gida yace yaron dan iska ne, idan ba haka nayi masa ba babu ranar da Shalele zatayi mutunci a idonsa, saboda shi kudi suna kai masa karo yakeyi iskanci ki barni dashi kiyi kallon ikon Allah, gobe idan Shalele ta sake samu cikin bazaice zai zubar dashi ba. 
Mubarak kuwa da gudu ya koma dakin Shalele jarirai sai ihu sukeyi, wayarsa ya ciro jikinsa har kyarma yake ya kira Khadija yace ta sameshi dakin Shalele, 
Bayan tazo ya fada mata cewa Shalele ta haihu kuma Baba ya tafl da ita ta dauki yaran nan taci gaba da kula dasu, Khadija tace Allah ya sawake wallahi bata dauki ciki ba babu dalilin da zatayi wahala da dan da bata haifa ba, 
Juyin duniya da magayi Mubarak yayi amma Khadija ta murje idonta tas tace wallahi bata daukar yaran nan, 
Waya ya bugawa Mama itama tace wallahi bata san zance ba, gwaggo ma tace bata daukar yaran nan, Mubarak ya shiga tashin hankali ga yara sai kuka sukeyi shi kuma baida abun basu, Nannade kafar wandonsa yayi ya dauki daya yana rurrugawa zuciyarsa tana masa suya kamar zata fito, idan daya yayi shiru saiya ajiye ya dauki wani, ganin zai samu warwarewar tunani yasa yayiwa wani abokinsa waya ya fada masa halin da yake ciki. Shi ya samawa Mubarak mafita domin shi likita ne, madara mai kyau da tsada ya kawowa Mubarak ya nuna masa yanda zaiyi amfani da ita, godiya Mubarak yayi tare da cire rigar jikinsa daga shi sai gajeran wando da singlet, dama madarar yayi ya zuba a piader ya fara bawajarirai. 
Gaba daya ma sunki su sha sai ihu sukeyi gaba daya sun firgita gidan, Shalele ya turawa sako cewa kinsan Allah kizo ki dauki “ya “yanki har yanzun kuka su keyi, Sharewa tayi da lamarinsa tayi kamar bata ga sakon nasa ba, a zuciye ya fita daga dakin ya nufi dakin Khadija, cikin bacin rai ya shiga yaci gaba da ‘siyaya mata masifa wai saboda rashin imani tanajin yara suna kuka amma dan iskanci bazata zo ta daukesu ba, ‘ 
Khadijia tace wallahi Mubarak bazan dauki yaran nan ba, uwarsu ma ta barsu ta tafi bareni, lalashinta Mubarak yayi amma saima ta fara tattara kayanta tana cewa na gaji da zaman gidan nan ma. 
Ganin haka yasa Mubarak bai sake magana ba ya fita ya koma dakin da yaran suke, har yanzun kuka sukeyi, dauko madarar yayi cikin fushi yace da Allah kuyiwa mutane shiru bana baku madara ba kun wani tsaya kinibibi a daidai lokacin daya sakawa daya fida a bakinsa, 
Kin kamawa yaron yayi yaci gaba da kuka, tashin hankali Mubarak ya shiga ya sake daukar daya cikin lallashi yace kai sha kaji ko, matsawa yaron madararyayi cikin ikon Allah ya rika lashewa, Mubarak yace yawwa to sha, haka ya basu daya bayan daya har suka koshi. 
Kwanciya yayi a gajiye ya tattara yaran a gabansa yana sauke wahalalliyar ajiyar zuciya. 
Shalele kuwa ta shiga damuwa da tashin hankali lallai yau ta tabbatar Mai gida baya da imani, kiri kiri ta aihu amma ya rabata da “ya “yanta, da tayiwa Mai gida magana sai yace idan masu rayuwa ne zasu rayu domin itama bata rayu da uwarta ba. 
Dole ta hakura, Momy kuma tana tare da Shalele domin itace take mata wankan jego. 
Mubarak kuwa jarirai sun hana masa baccin dare, ya rasa abinda sukewa kuka ya rasa abinda yake masa dadi, dole tasa yayiwa Mai nasara waya cewa dashi da matarsa suzo yanzun nan yana nemansu, 
Tashi sukayi suka nufo ciki dan ansa kiran Mai gida Abak, cikin ladabi suka gaishe da Mubarak su dukansu, bayan gaisuwa Mubarak yace ni yaran nan sunki suyi bacci. 
Murmushi matar Mai nasara tayi sannan ta tashi ta matsa wurin yaran, pampers ta cire musu ta canja musu wata, sannan tacewa Mubarak a kawo madarar tashi yayi yaje ya 
kawo, basu tayi suka sha, sannan ta kwantar dasu sukaci gaba da bacci, 
Godiya Mubarak yayi su kuma suka tashi suka tafi suna fita ya dauki wayarsa ya kira 
Shalele amma taki ta dauka, online ya hau dan ya fada mata bata abinda ke ransa 
Tana online abinta, kallon agogo yayi yaga 12:40am a bayyane yace lallai yarinyar nan 
mahaukaciya ce, typing ya farayi kamar haka. _Salam_ 
_shiru_ _Wallahi baki da wayau Shalele_ _shiru_ 
In banda rashin tunani irin naki saiki zubar da “ya “yanki ki kama gabanki saboda ke shedan ya doka miki ganga ko?_ _To ina abinda ya dameka dasu ne? Ko nace dole saika dauke su ne?_ _Ke kika sani, danni bana nan ma ina nan Lagos_ _Matsalarka_ _Nidai shawara nake baki idan kina san “ya “yanki kije ki dauki abinki,_ _Mai gida yace ka zubar dasu_ Motsi daya ya farayi shine dalilin da yasa ya sauka online. 
Da sauri ya tashi ya dauko pampers ya canjawa jaririn dan a tunaninsa shine zai daina kuka, 
Kuka yaron yaci gaba dayi, da sauri Mubarak ya sake cire pampers din da ya saka masa yanzun ya sake canja wata, ihu yaron yaci gaba dayi babu ji babu gani, kukansa ya tashi dayan gaba daya suka rikice suka mayar da dakin kamar dakin allura, 
Wohoho abinda Mubarak ya fada kenan tare da kiran sunan Allah, bakar zuciya garesa shine dalilin da yasa yayi zuciya bai sake neman Khadija ba, haka kuma yayi zuciya da sake kiran Mama ko Gwaggo ya daukarwa ransa ko zai mutu bazai sake cewa wani ya dauki yaran nan ba. 
Peyts fitar zawo duk ya watse masa jiki yana kokarin canjawa yaron pampers, da gudu ya nufi toilet yana maijin kyankyamin jikinsa, cire kayanjikinsa yayi tare dayin wanka sannan ya fito da sauri ya dauki yaron yaje ya wanke masajikinsa, saida ya sake maida masa pampers sannan ya cire zanin gadon ya wanke, 
Saidai yayi tsaki tare da cewa wallahi yarinyar nan kidahuma ce, haka ya kwana kiri kiri 
Bacci ya haramci idonsa da safe da kansa yayiwa yaran wanka da ruwan zafi yako basu azaba don yace ance idan anama yaro wanka da ruwan zafi yafi karfl da karko to haka ya wankesu cikin ruwa mai zafin gaske, 
A lokacin daya ciresu daga ruwa duk sunyi laushi domin wanka yayi musu irin wankan da inyamurai sukeyi wa yaransu, duk wanda ya cire daga cikin ruwa sai yayi bacci saboda gajiya. 
Shima wanka yayi ya saka kayansa, ya koma gefe ya zauna domin dai yanzun fita tafi karfinsa, idan ma meeting ne yake da k0 wani abu saidai yayi waya yana gida kamar matar kulle. 
Ganin yara suna bacci yasashi kiran wayar Baba Bashir yace Baba ni wallahi nafa gaji tunda kake don Allah ka tabajin namiji da kula da yara? Baba bashir yace Eh idan ya aifesu ba 
dole ya kula dasu tunda shi ya haifa abinsa, 
Kai yanzun tunda ka bude idonka a duniya waka gani kuma waka sani idan bani ba? Amma zan kira Mansur din in bashi hakuri idan ya yadda saiya dawo maka da matarka domin nidai kam wannan fitina na gaji dashi wallahi Mubarak. 
Kukan jariri yasa shi yin bankwana da Baba tun kafin dayan ya farka, madara ya dauko ya bashi yasha, rirritashi yayi harya koma bacci, komawa yayi daga gefe ya zauna ya zabga tagumi duk abin duniya ya dameshi, “ Yaso ya kira Shalele amma bakar zuciyarsa ta hanasa, yana dai addu”a Allah yasa ta dawo dan cikin satin nan zaiyi tafiya idan kuwa bata dawo ba wallahi saidai ya tafi da yaran 
nan dan baisan ina zai ajiyesu ba. 
lta kuwa Shalele Momy tana kula da ita sosai tare da gyarata yanda ya kamata, dan tace bazata tafl ba sai kwana arba”in ya cika cif, kuma tace ta tafi da ita Mai gida yace A, a, shine 
dalilinta na zama harsai Shalele ta gama wanka. 
Baba bashir kuwa kasa kiran Mai gida yayi domin dai baisan wace matsala zata sake kunno kai a tsakani ba, dama a wurin Mama ya ansa numbersa saboda a zauna lafiya yasa bai kirasa ba ya hakura, Bayan kwana biyu Mubarak ya kirasa Baba b, dan tambayarsa yanda sukayi da Mai gida amma sai Baba b yace kayi hakuri Mubarak kawai kayi ta addu”a amma banaji a jikina 
yarinyar nan zata sake zama dakai a karo na biyu. 
Mubarak yayi salati tare da cewa tou wallahi nidai maida mata yaran nan zanyi saboda ina da abinda zanyi na kashe komai nawa na zauna ina raino yara sai kace wani dan daudu, Baba bashir yace hakuri zakayi, 
Godiya dai yayiwa Baba amma ba haka ransa yaso ba, dole ya hakura, yana so yayi shawara da Shalele yaran nan ya saka musu sunan iyayensu amma saiya barta kawai ya barwa yaran sunansu ‘Al’ hassan da Al’ husain. 
Baya da yanda zaiyi ya fara shiri dan tafiya Hollond,zaiyi kuma da yaransa zai tafi ya dauki 
hakuri Allah ya raya masa su. 
Amma Mama da taji labari tayi kokarin hana Mubarak tafiya da yaran nan amma yace 
dasu zai tafi, tace ya kawo yaran wurinta shima ya zuciya dan haka yace baya bukatar barinsu kawai abarshi zaiji dasu. 
Shalele da taji labarin Mubarak zai tafi da yara hollond bataji dadi ba amma dole ta hakura dan tasan tanayin magana Mai gida zaiyi fada.
Hmm 

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

HARSASHEN SO CHAPTER 30

Advertisements _____ HARSASHEN SO  CHAPTER 30 Kashe sigarin hannunsa yayi sannan yace idan kuma kina …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *