[Advertisements⬇️]

HARSASHEN SO CHAPTER 29 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HARSASHEN SO

CHAPTER 29

Uhum ai halin Mansur saishi, ni ina sansa ina kuma tausayawa rayuwarsa, domin
rayuwar daya daukawa kansa rayuwar wahala ce da halaka,
Har zuciyar Bashir baiji dadin hakan ba, amma sai yayi murmushin karfin hali yace yarinta ce yake damunsa kuyi masa uziri zai daina in Allah ya yadda.
Gyara rufin kanta tayi tare da cewa babu wani yarinta iskancinci ne wallahi, haka kwanaki naje gidanku saida yayi min duka wannan abu yamin ciwo, kuji sharrin mata, baifa daketa ba amma tace yayi mata duka.
Kasaitaccen murmushi Bashir yayi tare da cewa to ya isa haka kiyi hakuri, ai yanzun dai bai sake dukanki ba k0? Tace Ey yace to insha Allah bazai sake ba, ya tsina fuska tayi dan ba haka taso ba, taso su taru su zage Mansur har sai yaji babu dadi,
A dakin ango Mansur da amarya Maryama kuwa, Bashir na fita ya kalleta tare da gyara zaman agogon hannunsa yace dan ubanda ya haifeki tashi  dago kai tayi ta kallesa cikin dakiya tace Yaya ina zanje ne? Duk gidan ubanda zakije ki fita shegiya agola dan masu gida yana zaune a wuri kina zama, daka mata tsawa yayi tare da cewa waje nace ……. da sauri ta tashi ta fita kofar daki tana kuka.
Kukanta Bashir yaJIyo daga dakinsa dan haka ya fito tare da tambayarta lafiya? Da sauri ta goge hawayenta tace ba komai, to miye ya fitar dake daga daki a cikin wannan dare ne
Eye? Maryam tace ba komai iska zansha, Bashir yace wane irin iska kuma? Koma daki kinji,
Bata da yanda zatayi dan haka ta koma daki, tun bai tafi ba yaji Mansur yana cewa idan kika sake shigowa dakin nan wallahi saina ci uwar …………. ki ….. , waje dan ubanki, da sauri ta sake fita tana kuka.
Bashir ya sake cewa koma waikai Mansur miye haka ne? Daga cikin daki yace ubanka ne haka dan mara zuciya ba nace ka daina min magana ba? Matar kace na koro ko tawa? Idan
ka sake min magana dani da matata saina ci uwarka kaima wallahi Allah na fada maka.
Murmushi Bashir yayi tare da cewa Allah ya baka hakuri, baka dai da kunya kake zagina ko Mansur? Naji na zaga ko zaka rama ne? Da sauri Bashir ya daga hannunsa tare da cewa
A. a,Allah ya baka hakuri ni na isa in zagi dan uwana? Ai karantar tayi yawa gara dai kai na bari kayi ta zagina dan farin cikinka kaji ko! Ke Maryam wuce muje.
‘Dakinshi suka tafi danshi Maryam kanwa ya dauketa tunda tun tana goye Gwaggo tazo da ita, tunda Hauwa“u taga Maryam ta fara bata rai, Bashir yace ku kwana da Maryam anan, Hauwa”u tace haba wannan wane ma irin tsari ne? Ni wallahi babu jakar da zata kwanamin a daki danma ka sani.
Bashir yace ai ba rokarki nakeyi ba umarni ne na bayar saboda nan gidana ne kuma gidana gidansu ne, dan haka ku kwana da ita nace a daki daya, yana fadar haka yajuya ya Fita daga dakin, gaba daya ma gidan ya bari,
Yana fita Hauwa ta sauko ta shakare wuyan Maryam tace shegiya dan ubanki ni zaki nunawa kishin sauri irin wanda matar kani da yaya sukeyi ko, to ki sani dai har abadan duniya mijina yafi naki ko gidan nan nashi ne shegiya har Iefe ma mijina ne yayi miki “yar gidan matsiyata,
Murmushi Maryam tayi tare da sauke hannun Hauwa”u daga wuyanta, tace kece matsiyaciya dan duk wanda ya gaji arziki baya gori matsiyaci shine yake gorin arziki ki kama
kanki dan wallahi ubana yafl ubanki kuma kin sani kowa yasan haka dan haka ki samu
natsuwa ki bari mu zauna lafiya shine akwai shawarata a gareki, tana fadin haka ta haye
saman gado tayi kwanciyarta,
Lallai kuwa tasan banda kaddara babu abinda zaisa Maryam ta auri Mansur domin ubanta mai arzikine na Iissafl a cikin masu kudi mutuwa ce tayi musu hanzari, tana ciki wata biyu babanta ya rasu, kuma ita kadai Gwaggo ta aifa a duniya, bayan ita bata sake ba, ta auri Babansu Mai gida kuma bata sake aihuwa ba har yanzun.
ltama rabawa tayi ta kwanta tanajin bakin ciki a ranta a cikin wannan dare mai tarin sirrika da dama taso ace ta kasance tare da mijinta datafi so da kauna a duniya amma saboda makircin Mansur ya koro matarsa dan shi bayasan ya kwana daki daya da ita wato itama kada Bashir ya kwana da ita, kwafa tayi tare da cewa sainaci maka mutunci in Allah ya yadda.
Da safe Mansur na dawowa daga masallaci yaga Maryam ta fito daga dakin Hauwa”u tayo dakinsa, idanuwa ya zaro sosai tare da kwance belt din kugunsa yace dakin makiyina
kika kwana dan ubanki? Banza tayi masa ta shige cikin dakinta.
Cikin bacin rai ya bita yaci gaba da dukanta tare da cewa duk wanda ya rabi abinda na tsana a rayuwata burina ganin bayansa, ihu Maryam takeyi tana bawa Mansur hakuri amma bayaji kuma baya gani, Bashir ne ya shigo gidan da sallama yaji kukan Maryam Mansur yana dukanta yana tambayarta abinda yakaita dakin makiyinsa, kamar uba yana dukan “yarsa. shiga dakin Bashiryayi cikin bacin rai ya kwace belt in yaci gaba da dukan
Mansur shima tare da tambayarsa zaka sake dukanta dan ubanka?
Juyawa fadan yayi tsakanin Bashir da Mansur suka fara zage zage da gore gore, can kuma suka fara dambe to karfi ba daya ba saida Bashir yayi ma Mansur dukan tashin hankali yayi masa dameji da fuska har kamanninsa suka bace, sannan yace daga yau duk wanda ya ragawa wani a cikinmu nida kai baikai da ba, idan har ka haifu ga Ummu suleim mu zuba dani dakai ko an fada maka nima ban iya rashin mutuncin bane Eye? Kyaleka
nakeyi saboda kai dakiki ne wawa jaki dakai dan iska sakaran banza marartunani.
Yana fadin haka ya fice a dakin, Cikin tsoro Maryam tayi waje da gudu dan tasan kanta zata kare, kofar daki tazo ta rabe tana jiran hukuncin da Mansur zai mata, shi kuwa Bashir
bai sake bi takan Maryam ba ko Masur dan yana da zuciya Mansur kuwa saida ya gama kukansa, sannan ya fit daga gidan. gidansu yaje ya fadawa Mama wai baima Bashir komai ba yayi ta dukansa tun daren jiya harda safe yanzun ma dakel ya kwace dan so yayi ya kashe sa, ita kuma Mama yanda taga wannan dukan
ranta ya baci sosai dan haka ta kulafi Bashir a ranta.
Ganin tahau yasa Mansur yaci gaba da cewa kuma da nace zanzo na fada miki cewa yayi ai bayajin tsoronki wai daya baki kudi mantawa zakiyi da wannan zance, wannan abu yayiwa Mama bakin ciki, sosai kuma tahau akansa ta zauna, Mansur yaci gaba da zugata yana dorata taci gaba da hayewa a matakinsa kamar tana hawa saman bane. Baba dake kokarin shigowa daki yaji flrarsu daga waje yace idan dai Mansur ne saiya kasheki anyi jana”izarki, shiga yayi cikin dakin yace wannan da bakaji dadin halinka ba wallahi.
Turo baki yayi tayi yana gunguni, gaba daya halittarsa ta canja shima Baba daya ganshi a haka saida tausayinsa ya kamashi amma bai nuna ba dan Mansur baya zaunuwa kwata kwata,
Kudi Mama ta bashi ya tafl asibiti, zama Baba yayi tare da cewa Umma karki biyewa Mansur ki bari Bashir din yazo kiji abinda ya hadasu, Mama tace wallahi bazanji komai ba dan na tabbata Mansur baya masa karya, dama tunda ya dawo naga yanamin wani kallon hadarin kaji shi yaje yayi kudi, tou wallahi komai sai an rabashi an bawa Mansur nashi tunda bashi kadai ne daba.
Duk yanda Baba yaso ya kwatantawa Mama taki hawa tana nan daram akan maganar
Mansur, dole ya hakura ya barta ya tashi yayi tafiyarsa Office.
Mansur kuwa yana dawowa duk wani abu dake dakin Maryam gaba dayansa ya tartara ya fitar a tsakar gida. Ke wannan jakar zo nan, da Hauwa“u yake, kallonsa tayi amma batayi magana ba, Mansur yace idan dakikin mijinki yazo kice ga tsiyarsa nan. Kuma daga yau
idan Allah yasa tsautsayi yasa kika zo ta kofar dakina wallahi saina karya miki kafa kinji
nace wallahi. ’
Gida ya koma ya fadawa Mama yana kuka yace Bashir ya kwace duk abinda ya siya masa an barsu a tantagaryarsuminti basu da anikin ko ledartsakar daki, Mama bataji dadin haka ba, dan haka tacewa Mansuryaje ya siyar da wani gidanta ya siyawa Maryam komai
da komai har lefe yayi mata, kuma kada ya bari Gwaggo taji wannan magana,
Bayan kwana biyu ya samu gida ya shige, amma ko allura bai siyawa Maryam ba yaje ya raba kudin da abokansa sukayi bushasharsu. Dan babu abinda ya dameshi da Maryam.
shiga goma fita goma  saiya garbeta koya mareta.
Bashir kuwa ya rasa inda zaisa kansa baisan abinda yayiwa Mama ba, idan zai kwana gaishe ta bata amsawa. idan ya kawo abu bataci kuma bata karba, wannan abu ya dameshi dan haka ya samu Baba ya fada masa, Baba dakansa yayi ma Mama fada amma sai tace
idan ya gaji da zama da ita ya bata takardarta. Cikin damuwa Bashir yace A, a, Mama kiyi
hakuri abun duk baikai haka ba, Baba ka barta ba komai Allah ya huci zuayarki Mamana. Iya damuwa Bashir ya shiga damuwa, harya koma Mama tana gaba dashi, kuma da zai tafi yayi tafiyarsa da matarsa. yana tafiya Mansurya siyar da gidan ya lashe kudinsa, Maryam kuwa ya mayar da ita gida, ita kuma taji dadin haka, Mama kuwa ta shiga damuwa siyar da gidan nan da Mansur yayi amma sai yace da Bashirya tashi tafiya ya siyar wai yace yaga gidan da zai zauna. Wannan abu ya sake dabaibaye Mama wato so yakeyi asirin danta ya tonu a idon duniya, ai ji take k0 bata raye Bashir mai rike Mansur ne, dan shekaru 10 ne tsakanin Bashir da Mansur a aihuwa.
Dole ta shiga ta fita ta samo kudi dakel ta siyawa Mansur gida dakel ta tattara ta mayar masa da matarsa, amma saboda tsabar iskancin Mansursatin gidan biyu ya siyar dashi, da Mama tayi magana sai yace mata ai wani malaminsa yace hannu aka saka masa, Kuma duk inda aka buga masa kasa cewa akeyi Bashir ne, haka ya jagalgali Mama ya kaita wurin malamin dan Mansur ya gama tsara masa yanda yake so a fadawa Mama,
malamin ya bada siffar Bashir tatas yace shine yakeyi wa yaronki asiri duk abinda ya samu ya lalace,
Mama tace dana ne fa, Yayansa ne fa, dukansu ni na aifesu, Malamin yace sosai hajiya ai bayasan Mansur baiki ya mutu ba fa, Mama tace innillahi, kai amma Bashir ya bata wayansa, Malamin yace sosai ma dan yana can asiri kadai yake kusawa Mansur.
Cikin mutuwar jiki Mama ta dawo gida da damuwa sosai a zuciyarta, kuma bata da sauran kudin da zata siyawa Mansur gida, Mansur ganin kudin Mama ya kare ya shiga cin dukiyar Baba ba tare da Baba ya sani ba, duk inda Baba yake da wani gida ko mi Mansur yaje ya siyar dasu yakai kudi banki ya ajiye wai kada Baba ya mutu a raba gado da Bashir yafishi kudi.
Ana haka ne Allah ya bawa Maryam ciki, tana shan wahalar cikin sosai ga babu wani wadataccen abinci dan azaba ta karshe yake ganawa Maryam haka zaiyi mata shegen duka
kuma ya hanata wadataccen abinci duk ta fitittike ta lalace gaba daga Mansurya bigeta.
Hardai ta aihu tana cikin wahala, Allah ya albarkace ta da samun da namiji, Bashir yaji dadi daya samu labarin haihuwar Mansur kudi masu yawan gaske ya saka masa a account dinsa ba tare daya fada masa ba wai dan ya kara yayi hidimar suna cikin kwanciyar hankali, amma Mansuryana gani alart ya mayar masa da kudinsa.
Bashir ya sake maido kudin kuma ya Kara musu yawa amma Mansur ya sake maida masa, Clkin damuwa Bashirya sake mayar da kudin ya kara linkasu so adadi mafl yawa a bisa lokacin daya tura daga farko, Mansurya sake mayar masa da kudinsa tare da ansar numbersa wurin Gwaggo ya rubuta sako na wulakanci ya turawa Bashir.
Bashir baiji dadi ba amma dole ya hakura, bai fadawa kowa ba, yabarwa zuciyarsa da rayuwarsa, kuma koya kira Mama bata daukar waya wannan abu ya hana masa zaman lafiya, dan baiga amfanin kudinsa ba yayi kudi dan “yan uwansa suji dadi shine amfanin arziki kayi dan naka ya huta, yayi kudi na tashin hankali harma ya rasa abinda zaiyi dasu danshi yanda ya raina kyautar miliyan hamsin yanajinta ne kamar naira hamsin ne, yaso Mansur ya dawo da hankalinsa a jikinsa danshi baya da abinda zaiyi da kudi. Mama bata so
Baba kuma yana da kudinsa sai Mansur ne yake fama da talauci yana haukar banza.
Shekarar yaron Mansur biyar wanda yaci suna Abubakar sadiq yaro ya taso cikin gata da kulawa sosai dan yana wurin Mama ne,yaro mai shegen kyau da shiga rai, lafiyayyen yaro mai burgewa baka gajiya da kallonsa Allah ya zuba masa madarar kyau, duk wanda ya gani
zaice Baba idan kuma mace ce zaice mata mama,
Mansur yana matukar san yaron nan sosai kuma ya shaku dashi bayajin zai iya rabuwa dashi a rayuwarsa, san da yakewa sadiq yasa yake kulawa da Maryam ya daina munana mata yana bata kulawa daidai gwargwado, itama Maryam zama da Mansur yanzu ya fara mata dadi dan babu wannan haukar ko hayani, komai yana mata cikin sanyin murya ‘taci albarkacin danta.
Wata dawowa da Bashir yayi wanda tunda ya tafi yafi karfin shekara bakwai baizo nigeria ba, ya tattaro yazo ganin gida, Bashirya mulke yayi kudi ya gage idanuwansa sun bude yayi kyau na burgewa ga duk wanda ya kallesa, a tunaninsa idan yazo gida zai samu kulawa amma ko kare bai masa sannu da zuwa ba daga gwaggo sai Baba sai kuma ma”aikatan gidansu, wannan abu baima Bashir dadi ba saida ya rubuta nadama da kansa yaji dama bai dawo ba
Daren wannan ranar Bashir baiyi bacci ba yana cikin damuwa da nazarin wane irin laifl
yayiwa mahaiflyarsa da dan uwansa wanda gaba daya suka juya masa baya haka!
Hauwa”u itace tayi ta bashi hakuri tare da kwantar masa da hankali, hakuri yayi amma abun ya kasa wuce masa a ransa, wani babban yaronsa dake kula masa da komai a nan nigeria ya kirawo mai suna Sulaiman, bayan sun gaisa ne yace masa don Allah yazo da safe
yana neman sa. Sulaiman yace insha Allah, sallama sukayi tare da ajiye wayar dukansu.
Tunda safe Sulaiman ya nufo gidan Bashir, wani katafaren gida ne na nunawa a idon duniya ya gina wanda karyar mutum ya shiga  gidan yace nigeria yake, an zuba kudi an ci uwar naira an bautatawa kasa, bayan yazo suka gaisa tare da yin “yar firarsu, daga baya kuma Bashir ya fadawa Sulaiman abinda yake damunsa, hakuri kawai ya basa dan
ba”ashiga tsakanin “yan uwa.
Suna nan suna fira har 12:42pm, tashi Bashir yayi yaje yayi wanka ya shirya, dashi da Hauwa”u da Sulaiman suka nufo gidansu dan su gaisa, Sadiq kuwa yana ganin Bashir ya ruga da gudu Oyoyo Baba …….. , zuciya a wanke Bashirya rungumesa ajikinsa yanajin kaunar dan dan uwansa har a cikin ransa, surutu yaron ya farayi masa irin dai shirmen yara,
Dariya Bashir yakeyi sosai yana jin san yaron yana shigar masa har akin zuciyarsa, a haka suka shiga dakin Mama, zama yayi a saman kujera tare da kara rumgumo Sadiq a jikinsa, gaishe da Mama yayi kamar yanda ta saba tayi masa banza, itama Hauwa’u gaisheta tayi amma saita basar, Sulaiman shima gaisheta yayi sai ta mike tsaye tare da matsawa kusa da Bashir ta dauki Sadiq, da sauri Bashirya riko yaron cikin muryar biyayyar yace haba Mama aike naima laifi me kuma zaisa abin ya shafi harda dana.
Kiyi hakuri don girman Allah Mama, bazance sai kin fadamin laifin da nayi miki ba ki yafemin ki daina fushi dani dan darajar annabin rahma, S. A. W suka fada a tare duka palon harda Mama,jan Sadiq ta sakeyi da karfi Sulaiman yace kiyi hakuri Mama ki barshi don Allah,
Rike Sadiq Bashir yayi sosai tare da mikewa tsaye yana jansa Mama tana jansa, Hauwa”u
tace kaga bar mata yaron nan don Allah. shi kuma Sadiq sai dariya yakeyi dan a tunaninsa
wasa ake masa,
Ashe Mama bata rike sosai ba sai Bashir ya saki yaron kuma yana daga tsaye, cikin tsautsayi da hukunci na Allah yaron nan ya fadi kasa ta sadda kai ya sulale kasa sai wuyansa ya karye, wani irin ihu yayi guda daya, idonsa a kan Bashir murmushi yayi tare da kwanciya a kasa sosai jini yaci gaba da bulbulowa ta hanci ta baki. Kafin su ankara tuni Sadiq yace ga garinku nan, Bashir cikin tashin hankali ya duka ya dauki yaron da sauri ya fita waje dashi, cikin rudewa ya shiga mota ya nufi asibiti, a gida kuwa Mama ta kurma wani irin ihu tare da cewa lallai wannan kiyayya da gaskiya ne yau a gaban idona Mansurya kashe dan kaninsa, wannan tashin hankali ya fiddo gwaggo, akayi ma Mansur waya dandanan gidan ya cika kowa da abinda yake fada,
A asibiti kuwa likitoci sun tabbatarwa Bashir da yaron nan bashi da rai, kafin likita ya rufe bakinsa Bashir ya fadi kasa somamme, gida kuwa ya cakude da tashin hankali da Fitina, Mansur kuwa sai masifa yakeyi yana karawa, tare da cewa wallahi idan har Bashir ya haifi dansa wallahi saiya kashe shi, kuma wallahi bazai yadda ba sai an biyasa dansa,
Baba kuwa yanajin labari ya nufi asibitin domin yasan asibitin da suke zuwa, a lokacin da yaje har an bawa Bashir gadi ana bashi taimako dan farfado da rayuwarsa, Baba ya dauki gawar Sadiq yayo gida da ita dan ayi mata sutura, amma Mansur ya kafe caf yace wallahi idan ya yadda Allah ya tsine masa albarka sai an dawo masa da lumfashin dansa, Dan karamin hauka Mansur yakeyi Mama tana kama masa, Gwaggo ce tayi ta masa nasiha, dan ita Maryam ma abun kasa cewa komai tayi shiru tayi da bakinta tanajin dacin irin mutuwar da danta yayi, Mansur kuwa cewa yakeyi ai bakin ciki yasa aka kashe masa da, dan anga ya haifi namiji zaiyi kudl shi yasa aka lallaba aka kashe masa da, Baba kuwa tura Sulaiman da Hauwa”u yayi suka nufi asibiti dan Iura da lafiyar Bashir, den a gidan rike Mansur akeyi amma ya rike
wukarsa yace saiya farka cikin Hauwa”u, Dakel aka samu Mansur yabar yaron nan akayi masa sutura aka kaisa makwancinsa na gaskiya, Bashir kuwa tunda ya farko kuka kawai yakeyi yana tuno lokacin da Sadiq ya rugo da gudu ya kakumesa yana Oyoyo Baba …….. surutunsa da yake masa da lokacin da yakeyin dariya da Mama takejansa, kuka yakeyi sosai kamar ransa zai fita, yana jin nadamar zuwansa nigeria,
Sallama aka basu dan haka suka rantafo gida cikin damuwa, Baba kadai yayi ma Bashir sannu da Gwaggo, cikin tashin hankali Bashir ya zauna a gaban Mansur yana kuka kamar ana zare masa rai, hada hannayensa yayi duka biyun yace Mansur ka gafarceni akan abinda ya faru na rantse da wanda rayuwata yake hannunsa ba da wasa yaron nan ya fado daga hannu na ba, kayi hakuri kuma na yadda kamar yanda kace idan na haifi dana zaka
kasheshi na yadda da hakan idan har hakan zaisa ka janye kiyayyata dake cikin zuciyarka.
Mansuryace ga banza anyi wa jaki wanka, ko ka yadda ko karka yadda aihuwa bata fi aihuwa ba, haka kuma da baifi da ba, yanda naji ciwon mutuwar dana a raina wallahi saina dandana maka kaima kaji kwatankwacin yadda naji, ka rubuta wannan ka ajiye sannan kuma zan sake aihuwar wani dan wallahi saiya shafemin labarinka dakai da zuri’arka a
cikin duniyar nan, Bashir ban kaunarka na tsanake ka duniya da lahira, Murmushin karfin hali Bashiryayi tare da tashi daga wurin ya nufi gidansa, Sulaiman da Hauwa”u suna ta bashi hakuri amma a banza, haka akayi zaman makoki har aka kare
Bashir bai sake lekowa gidan ba. Bayan gama zaman gaisuwa Mansurya shigar da kara, idan hankalin Baba yayi dubu ya tashi wai “ya”yansa daya haifa da cikinsa sune zasuyi shara’a, dan haka Baba yace Bashir
ya tattara ya koma idan hukuncin kisa ne shi ayi masa akansa. Haka Bashir ya tattara ya koma dashi da matarsa Hauwa’u tashin hankalinsa ma azumin da zaiyi na mutuwar Sadiq, wannan abu yayi wa Mansur bakin ciki don haka ya dauki gidan Bashirya siyar ya tafi can kauye yayi ginin gida na idon duniya da kudin, katon gida ne ya gina da abubuwan more rayuwa wanda k0 a cikin birni iyakar abinda za”ayiwa gidan kenan.
Babu wanda yasan Mansurya gina wannan gidan sai wani yaron gidansu anan gidan yake aiki mai suna Balaga shima dan iska ne lamba daya saida ya gama lalacewa iyayensa suka kawoshi almajiranci, daya zo ya samu aiki a gidansu Mansur, Mansurya mayar dashi uwarsa ya mayar dashi ubansa domin yana bashi shawarar banza, idan ya gansa zai jinjina masa yace Mai gida ……. Yanajin dadin Mai gida sosai dan Mansur Allah yayi nasa baiwar kyauta duk abinda ya samu na jama”a ne, yaga damar yana da dubu daya itace kadai ta rage masa a duniya ya dauketa ya bayar shi ya zauna babu, to da kyauta ya kama mutane
sosai har ya hada zugar “yan daba.
Abas kuwa ganin iskancinsa yayi yawa yasa Yayan Babanshi ya tafi dashi Katsina dan gina masa rayuwa mai kyau, Bashir kuwa yana can kasar waje arziki sai dada bunkasa yakeyi yayi kudi harya rasa abinda zaiyi dasu dan haka yacewa Hauwa,u shidai zai daina komai ya zauna wannan kudin sun isheshi rayuwar duniya zai koma gida ne ya zauna cikin “yan uwansa, Hauwa”u tace ina ai neman kudi yanzunma aka fara shi, ya nemi dukiya kamar bazai bar duniya dan
kudi zasu kara martaba da mutunci akan zuri”arsa idan ya aifesu ko bayan baya lumfashi.
Mansur kuwa daukar Balaga yayi ya mayar dashi kauye ya zuba dawakai da karnuna masu yawan gaske, Balaga yake kula dasu ya daina wani karatu ya koma ya tare wurin Mai gida dashi da sauran “yan iskan da suka gagari iyayensu.
Yau kuwa Baba ya tashi da tashin hankali dan sai yanzun yaji labarin duk wata kaddara da yake takama da ita Mansur ya siyar da ita kakaf harta gidan da yake ciki Mansur ya siyar dashi, yana zaune ya gama shan shayi Gwaggo na zaune a gabansa akayi masa waya aka sanar dashi wannan bakin Iabari, mai kula da duk wasu harkoki nasa ya sanar masa, ya kara da cewa kuma ashe ma gidan da yake ciki Mansur ya siyar dashi haya yake biyan gidan duk shekarar duniya, wani irin ihu Baba ya kwada tare rike Gwaggo gadagam da gudu duk
wanda ke gidan yayo palon Baba dan ihu ne yakeyi bana zai bari ba.
Rike yake da Gwaggo yana cewa wallahi ban yadda sai kun biyani komai nawa idan kuwa ba haka ba mutuwa zanyi kuma wallahi kece kika kasheni, tashin hankali. faduwa Baba yayi kasa tare da daukewar lumfashi, da sauri aka daukeshi akayi asibiti dashi babu rai, ma“ana baya numfashi wanda zai tabbatar wa mutane cewa yana da rayuwa. Mama ta fito daga daki dan a lokacin tana wanka taji ihun Baba, lokacin data fito an tafi asibiti dashi, sai Gwaggo dake ihu, riketa Mama tayi tare da tambayarta abinda ke faruwa amma sai ta rika cewa wallahi bani na kasheshi ba, Mama tace waye? Gwaggo tace shine ya mutu, Mama tace wa mi waye ne? Ai Gwaggo ta dimauce saboda fargaba Fita tayi daga dakin ta nufi kofar gida duk wanda ta gani saita rikesa tace tsakanin ka da Allah ni na kasheshl?
A asibiti kuwa taimakon gaggawa aka bawa Baba dan ceto lumfashinsa, tunda ya farko da wannan bakin cikin kudln ya dawo duniya, ganin haukarsa yayi yawa yasa likita ya dura masa allurar bacci,
Mansur kuwa yana can yaji labarin Gwaggo ta kashe Baba, babu kunya ba tsoron Allah abin duniya ma yasa ya manta da surukarsa ce, dan haka ya kira wani abokin Baba dake katsina ya fade masa matar babansa ta kashe Babansu kuma zata gudu, shima waya yayo nan kaduna ya fadawa wasu “yan sanda babu binciken komai aka damke Gwaggo akayi gidan yari da ita.
Mansur kuwa shiga yayi dakin Baba duk wasu kudi da wata “yar takarda ta fili wanda bai sani ba ya gansu yanzun saida ya kwakwaleta, wani littafi ya gani dan haka ya dauka ya
bude ya fara dubawa,
Mai kiwo, wani ne yakewa Baba kiwon shanu, lambarya gani a rubuce dan haka ya rubuta ta da sauri ya kira mutumin, bayan sun gaisa yace masa yana ina ne? Mutumin ya fada masa. Mansuryace tou duk ka siyar da shanun nan inji Baba zanzo na amsa kudin, ai mutum yanajin haka ya kashe wayarsa tare da tattara duk abinda yake so ya kora shanu sukayi gaba, dan Baba ya bashi labarin Mansur komai ba bako bane a wurinsa kan Iamarin
Mansur yasan dai Bashir bazaiyi haka ba dan natsuwarsu ma ba iri daya bace Ci gaba Mansur yayi da parking duk wani abu daya san yana so saida ya dauke sannan ya
dauki Mama a mota da sauran masu aikin gidansu suka dawo wannan kauye suka boye.
Baba kuwa yana farfadowa da hankalinsa yaga babu kowa a wurinsa babu matarsa babu Mansur wannan bakin ciki yasa ya karya layinsa ya sulale daga asibiti babu wanda yaji kuma babu wanda ya gani ya koma lagos yaci gaba da rayuwarsa.
Bashir kuwa yaji labarin komai daga bakin Sulalman, yaso yazo to amma matarsa ‘nada ciki ita kuma tace wallahi bata dawowa ta aihu Mansur ya kashe abinda ta haifa, ko ranar
da zata aihu kukanta akan Mansur ne, cikin tsoro da fargafa ta aihu ta samu yaronta namiji, Taji dadi sosai kuma ta roka alfarma ko bayan bata raye don Allah karda ya mayar mata da da Nigeria,shima yayi mata alkawari bazaiyi haka ba. suna zaune lafiya sosai da Hauwa”u yanajin dadinta dan itama mace ce mai hakuri da biyayya ta rasu ne Mubarak yana da shekara biyu mota ta takata ta mutu a wurin bata ko shura ba. Bayan rasuwar Hauwa”u da shekara biyar Bashir ya tattaro ya dawo nigeria amma bai taho da Mubarak ba sannan kuma bai fadawa kowa ya aihu ba, koda ya dawo shima kauyen ya koma saboda ya rika jin kamshin “yan uwansa, danshi bai wani rikesu a ransa ba, saida ya dawo kauyen sannan ya fara binciken ina mahaifinsa ita dai Mama yasan tana gidan Mansur, ’
Shi kuwa Baba saida ya koma lagos da dadewa ya samu labarin gwaggo tana gidan yari amma hauka takeyi, dan har a lokacin bai dainajin bakin cikin abinda Mansur yayi masa ba, amma yaje gidan yarin shi yasa aka kaita gidan mahaukata, yaso ya tafi da ita tun a wannan lokacin amma abokinsa yace yadan barta domin duka yaransa sunzo daga Mansur har Bashir amma kowa shi daya yazo, kuma sunce kar a saketa, shi Mansur bala”insa daya wai ta bashi kudin Babansu, Bashir kuma yace kaci abinda kaci wannan kudin duk duniya babu maisu saini, shima Bashir fita tasashi yayi haka dan yana da kudln da yakejinsa idan aka daga nigeria zai iya sayenta, yayi hakan ne dan ya kulla fitina yanda zasuyi masifa da Mansur, wannan maganar kudi ya kara kulla har kalla tsakanin Bashirda Mansur danshi yanzu Bashir haushin Mansur yakeji fiye da tunanin mai karatu, bakin cikinsa daya matarsa ta mutu tanajin tsoron kada danta ya kasance a nigeria, dan haka ya tsaya saman kafafuwansa saiya shafe labarin Mansur a duniya dan dansa ya dawo yayi rayuwar farin ciki a cikin “yan uwa da kuma dangin mahaifiyarsa, wannan dalili yasa shima ya barbaza “yan daba a cikin gidansa dan
su tayasa yakar Mansur.
Tou ana cikin wannan futar ne Shalele tazo duniya, abinda yasa tazo a matsayin namiji saboda wai ya nunawa Bashir Allah ya bashi namiji daga farko an kashe sa dan bakin ciki, yanzun ya samu wani a karo na biyu.
Bayan tasowarta ne Mansurya nuna mata cewa Bashir makiyinsa ne, mai masa hassada baya kaunarsa ya kashe masa dansa na farko da yake tsananin so da kuma kauna,yana so kuma ya cinye dukiyarsa, shima Bashir ya biye , sukaci gaba da fitinar rayuwar, da kuma
masifa ta ciyosa ya kwace gidan da Mai gida yake ciki domin dai dama gidansa ne, tunda Lokaci lokaci Bashir yana zuwa wurin Mubarak, danshi ya bari can duka ya dawo nigeria yayi fitina, Mubarak baisan kowa ba a duniya sai Bashir sai kuma matar dake kula dashi, ya taso cikin gata da wadatuwar arziki dan babu abinda ya nema na rayuwa ya rasa,
Duk karatunsa a can yayi tashinsa a kasar waje bai hana Bashir gina masa rayuwa da ilimin addini ba, a saudiyayya yayi karatunsa saida yayi hardar Al’Qur”ani mai girma yasan koma sannan ya fara karatun prmry, sosai yana da ilimin addini dana zamani.
Saida ya zama mutum sannan Bashirya barshi ya fara zuwa nigeria domin yasan idan dai
ta kama gwabzawa Mansur da yaransa basa iya tsintar komai daga Mubarak,
Shidai Mubarak yasan dangin Mamansa amma dangi Baba babu, wannan abu ya damesa shine ya tambayi Yayar Mamar labarin ahalinsa na wurin uba, bata boye masa ba ta bude masa komai, daya gano Shalele “yar uwarsa ce yaji dadi sosai amma bata wani burgeshi ba, kawai dai zai nuna ta yace diyar kanin Babansa ne.
Sai ya samu labarin Gwaggo, da abinda ya kaita gidan yari. dalilinsa na tura Shalele dan ta samo masa bayanai a inda Baba yake zama, bata samo komai ba, dan haka shine ya shiga ya fita ya gano Baba dakel.
Tsayawa firarsu tayi domin dare yayi, amma Mansur yace ko za”a tara taron tashin duniya Shalele ta gama zama da Mubarak saidai idan baya lumfashi amma matsawar yana da rayuwa yanda uwarta tabar duniya tabar Mubarak.
Gwaggo tace gaskiya Mansur baka da dabi”a wallahi, dariyar “yan tasha yayi sannan yace ai ina tunanin wannan tun kuruciyata kika gane, kedai diya kika aifa kika bani, kuma ta mutu dan haka wannan kuma nine na aifeta da kaina dole a barni nayi iko da abata. ‘
Baba yace ikon banza ikon wofi ai ta iko ta kare tunda da aurenta, kallon Mama yayi tare da cewa ke kuma kiji tsoron haduwarki da Allah ranar da duk Allah ya binciko littafinki karyarki ta kare domin dasa hannunki gaba ta yadu tsakanin “ya”yanki bawai Uwa kadaice take da hakki akan danta ba shima dan yana da hakki akanki domin dai Bashir
babu abinda yayi miki san zuciya kawai yasaki aikata haka.
Juyawa tayi a hankali ta kalli Mansur, tabe baki yayi tare da kunna sigarinsa wuta ya dage hanci sama yaci gaba da fitar da hayaki, Baba yace kai Bashir nemi gafar mahaifiyarka, matsawa yayi ya rike kafafuwan Mama tare da neman yafiya akan duk wane lalfi da yayi mata, da taimakon Baba da Gwaggo Mama ta washe, dan haka Baba yace dukansu su tattara su tafi gidan Bashir acan za”a kwana. da Mama da Baba da Gwaggo da Bashir suka mike dan tafiya wannan umarni Baba ne domin yace Mama acan zata kwana hakan zai tabbatar masa data saki Bashir a ranta.
Gaba daya suka fice a palon, sai Mubarak da Shalele da Mai gida, inda take zaune Mubarak ya matsa tare da cewa mu ai anan zamu kwana ko? Ya karasa maganar yana zama a kusa da ita, idon Mai gida a rufe dan yanajin dadin sigarinsa yace. kai idan na tashi uwarka zanci na fada maka, bude idonsa yayi tare da cewa ko itama kujerar ta ubanka ce tunda ance gidan nan nasa ne? Mubarak yace kayi hakuri Baba nidai babu ruwana mata ta
nake ma magana tana tashi zan bar maka gidanka.
Saida Mai gida ya sake jan hayaki sosai sannan yace ita matar nace ko itama da kudin ubanka na siyota ne? Murmushi Mubarak yayi a ransa yace sosai na tunda ubana ya biya sadakin uwarta, amma a fili yace kayi hakuri nidai ban sani ba, Kankance idanuwa Mai gida yayi ga bacci ga hayakin sigari, ya lumshe su sai kace wani mashayi sannan yace in Allah ya yadda ina tashi harbinka zanyi da bindiga wallahi, mlkewa Mubarak yayi dan yaji labarin Mai gida idan yace wallahi to fa lallai saiya aikata kamar fadar Allah.
Saida ya mikar da Shalele tsaya ya rungumeta ya sunbaceta ya wani kara kamkameta a jikinsa yana wani sauke ajiyar zuciya a hankali wanda Shalele kadai kejin lurnfashin shi kadai yasan dalilinsa nayin haka babu kunya babu tsoron Allah a gaban Mai gida wanda shi
bai dauki wannan wani abu ba saboda rayuwan da yayi a cikin yahudawa,
Zaunar da ita yayi a saman kujera sannan ya dauki kafafuwanta ya dora sama ya kwantar da ita daidai da daidai yana duke a gabanta yace kiyi addu”a Allah yasa Baba karami yayi hakuri, Mai gida yace ubanka ne karami dan iska fitar min daga palo tun ranar dana dora idona akan uwarka na tsaneta  na tsani abinda zata aifa. Dariya Mubarak yayi tare da cewa ashe kuma sirikinka ne za’a haifa baka sani ba, yana kaiwa nan yayi fucewarsa daga dakin, a daren bai kwana kauyen ba ya koma cikin gari.ba
Mai gida kuwa yasha shigari tafi kwali biyu, dan dama shan sigarinsa tafi yawa idan yana cikin bacin rai, Kallon Shalele yayi data fara bacci yace Shalele na rantse da Allah idan na fidda hannuna daga lamarinki sai kin zabi mutuwa fiye da rayuwa na fada miki. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]