[Advertisements⬇️]

HARSASHEN SO CHAPTER 25 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HARSASHEN SO
CHAPTER 25
Wata kafirarriyar mota ya hau mai tsananin kyau da tsada uwa uba daukar hankali da burge duk wanda ya gani tana tafiya tana hucin naira. 
Tuki yake cikin natsuwa da burgewa, motar nan kuwa ta dauki sanyi mai sanyaya zuciya, kamshin turarensa da kamshin turaren motar ya hadu ya bada wani sirrintaccen kamshi. Sai sautin waka dake fita a hankali. ‘ Wayarsa ya dauka ya fara kiran Sulaiman, babu wani dadewa ya dauka, cikin girmamawa 
ya fara gaishe da Abak. Bayan gaisuwa Mubarak ya fada masa ya taho. Addu”ar sauka lafiya Sulaiman yayiwa Mubarak, shi kuma ya ajiye waya. 
Suna gama wayar ne Sulaiman ya nufi dakin Shalele a lokacin harta fara bacci, sallama 
yayi sosai wanda ta tashi Shalele daga bacci. Sulaiman yace Shalele mai gida Mubarak yace ki taho. Kallonsa Shalele tayi tare da cewa in taho kamarya? Sulaiman yace yana zuwa ne yanzun shine yace in fito dake zamu hadu dashi a hanya zaku tafi. 
Cikin daburcewa Sulaiman yace ki taho don Allah kafin “yarlabai ya dawo, dan gajeran tsaki Shalele tayi tare da gyara kwanciyarta taja bargonta ta lullube, rasa yanda zaiyi da ita yayi dan haka ya fita ya kira Abak ya fada masa yanda sukayi da Shalele. 
Mubarak yace to babu damuwa barta zanzo da kaina amma kaci gaba da dubamin shigowar baba, Sulaiman yace babu damuwa, kashe wayarsa yayi tare da fita yana “yan hange hangensa. Mubarak kuwa a kofar gidansu yayi parking, Sulaiman ya bude masa cikin girmamawa, Mubarak bai sauraresa ba ya fada gidansu kai tsaya. Dakin Shalele ya nufa cikin sauri dan karsu hade da Baba b, ita kuwa tuni baccinta yayi nisa da sallama Mubarak ya shiga cikin dakin tuni Shalele tayi nisa sai rago takeja Bakin gadon ya tsaya tare da yaye bargon data Iullube dashi, cikin tashin hankali Shalele ta tashi zaune dukanta gaba daya, dan a tunaninta wani kato ne,jawota yayi cikin sauri ba tare da yayi magana ba. Cikin muryar bacci tace Yaya ina zamuje ne? Ba tare daya kalleta ba yace ba kince zaki je ki zauna dani ba? Shalele tace Ey , kallonta Mubarak yayi tare da cewa to kizo muje kinje ko? Murmushi Shalele tayi tare da saukowa daga saman gadon. 
Rike hannunta yayi a hankali suka fara tafiya, Shalele sai raba idanuwa takeyi kamar ta kada kishiya, cikin dabara da sanda suke zame har suka fita, saida ya sakata mota sannan yayi sallama da Sulaiman, shima zagaya wa yayi ya shiga mota Sulaiman yana ta musu fatan alkairi tare da musu addu”ar Allah yasa a sauka lafia Godiya Mubarak yayi tare da fara tafiya, ita kuwa Shalele shigarta motar nan duk sai taji gajiya ta lullubeta dan haka ta gyara kawai taci gaba da baccinta, tafiya mai nisa Mubarak yayi kafin ya Fita bakin titi dan suna da nisa da hanya sosai,juyawa yayi ya kalli Shalini dake bacci parking yayi tare da kwantar mata da kujerar da take kai dan taji dadin bacci, a hankali ta bude idonta ta kalli Mubarak, kyakkyawan murmushi Mubarak yayi ba tare da yayi magana ba. Murmushi Shalele tayi tare da lumshe idanuwanta a hankali taci gaba da baccinta cikin natsuwa. 
Baba Bashir kuwa tafiyar su Mubarak ya iso kuma ya hangi motarsa, murmushin mugunta yayi tare da shiga cikin gidansa yana mai addu”a Allah yasa safiya ta waye muna da rayuwa, tun a daren ya fadawa Sulaiman cewa da sun dawo sallah asuba zasu fita, 
amma bai fada masa ina zasu jeba. Mubarak kuwa cikin jin dadi ya shigo gari, zuciyarsa dukunkune da farin ciki da nishadi. A bakin kofar gidansa ya tsaya tare dayin horn kafin ya sauke hannunsa daga inda ya dannan horn din tuni an yage masa get ya shige. 
Bayan yayi parking yana zaune a mota wayarsa a saman kunnensa yana meeting ne, ci gaban zamani lallai”””,,,,,,, har 12:30am bai gama ba, ita kuma Shalele bata farka ba sai 
01:04am har sannan bai gama wayar ba. 
Da kallo tabi Mubarak cikin yanayin bacci, sannan ta koma ta kwanta, shima ita yake kallo ba tare daya daina magana ba, da hannu ya nuna mata su tafl? Kai kawai ta daga masa alamar Eh, jinjina kai Mubarak yayi tare da kashe motar sannan ya bude ya fita, da kanshi ya fitar da Shalele tare da rufe motar. ‘ 
Har suka shiga ciki Shalele na rike ajikinsa, a gafen gado ya zaunar da ita bayan sun shiga ciki, shima zama yayi dan ya kusa karasa meeting,din saida ya gama sannan ya kalli 
Shalele tare da cewa swry ina miki aikin office a gida. 
Tabe baki tayi ba tare da tayi magana ba, murmushi Mubarak yayi da gefen bakinsa tare da kallon Shalele da wutsiyar idonsa, mikewa yayi ya shiga toilet shima ba tare daya sake 
cewa komai ba, 
Ya dade sosai sannan ya fito da towel daure a kugunsa da alama dai wanka yayi, ba tare 
daya kalli inda Shalele take ba yace kije kiyi wanka kizo mu kwanta. 
Simi simi ta tashi kamar wata munafika da hijabi jikinta ta nufi toilet, bai sake kallonta ba kuma baiyi mata magana ba, dan gajera tsaki yayi tare da girgiza kansa, niko nace duk 
abinda zakayi da dan kyauye saiya siyar da halinsa. 
Yana tsaye harta fito jagaljagal ta sake lafto kayan dakejikinta bayan tayi wanka, dan 
bata fuska Mubarak yayi kamar yaga kashi tsakaninsa ga Allah har ransa yaji kyankyami wallahi kamar zaiyi amai, cikin sigar lallashi yace haba Shalinina meye haka? Ke bakyajin tsikarjikinki yana tashi ne? Haba da Allah yi hakuri kije ki gyara wankan nan plz. 
Murmushi Shalele tayi ba tare da tayi magana ba ta sake juya ta koma cikin toilet in, tsaki Mubarak ya sakeyi mai sauti sosai tare da kallon yanda duk wani gashi najikinsa ya mike zirrrrre saboda kyama, a hankali ya shafa jikinsa da duk gargasar jikinsa ya koma ta kwanta kamar yanda take daga farko, Towel ya dauka ya nufl hanyar toilet, a bakin kofa ya tsaya ya dora mata a sama yace idan kin gama ki daura wannan towel din karki sake ki sake sako kayan nan don Allah badanni ba. 
Gyaran murya tayi sannan tace mi yasa ne? Mubarak yace banajin dadi ne, Shalele tace to a jikinka na saka ne? Ajikina nefa, Mubarak yace to nidai koma dai miye kiyi hakuri don Allah kuma kisa Allah a ranki don Allah kiyi wanka da gaskiya. Ya karasa maganar dai gashi nan dai wani iri. Shalele tace to jeka ina fitowa,juyawa yayi daga wurin ba tare daya sake magana ba amma har yanzun hankalinsa ya kasa kwanciya, zuwa can kuma sai gata nan ta fito, kallo daya yayi mata ya dauke kansa sai wani bin bango takeyi tana rabe rabe kamar wata barauniya. 
Baiyi mata magana ba yadan tabe bakinsa tare da jan pillow ya kwanta, ita kuwa Shalele a wurin ta daskare sai kace wata dusa, saida ta bushe ta tsane tsaff harjinin kanta ya fara dawowa a kafafuwanta sannan tace Yaya na bushe fa, ba tare daya juyo ba yace yo waye ya 
shanyaki ne? Shalele tace nima ban sani ba, Mubarak yace to bare kuma ni, daga haka bai sake mata magana ba, ta kara dadewa sosai sannan tace haba nafa gaji ka bani kaya in saka, Mubarak yace ni ba mace ba meye kuma zai hadani da kayan mata? 
Juyowa yayi ya kalleta sosai sannan yace ni ba’a kwanciya a kusa dani da kaya, ya dan turo lebensa na kasa tare da dan girgirza kansa sannan yaci gaba da cewa sannan kuma ba‘a hawar min gado da towel, sai ki zaba kwanciya kusa dani ko kuwa dai ya zakiyi shawara ya rage naki. . 
Zaro idanuwa Shalele tayi tare da kallon kanta sannan ta kalli Abak, dan bude idanuwansa yayi duka tare da gyara kwanciyarsa ya juyo dukansa yana kallonta sannan ya lumshe idanuwansa cikin nishadi yaya dai? Kinyi shiru kice wani abu mana. Ya karasa 
maganar yana mata shu”umin murmushi. Karar wayarsa ce tasa shi juyawa ya bata baya dan ganin waye yake kiransa a daren nan ne? Khadija ce, a ransa kuwa cewa yayi me yasa ita take san kiransa a irin wannan lokacin ne? 
Dogon nazari yayi sosai wanda shi kadai yasan nazarinsa, uhumm ya fada tare da ajiye 
wayar, juyowa yayi tare da cewa taho ………… Ya mika hannunsa tare da binta da wani irin rikitaccen kallo, cikin daburcewa Shalele ta juya tare da boyewa gefen wadrof, cikin gajiyayyar murya yace Shalinina kizo mana ……….. maganar ta kare cikin warwarewar haruffa, a hankali ta leko ta kalleshi, murmushi yayi tare da daga girarsa daya ya kare yana mai nuna mata tazo da kansa. 
Fitowa tayi ta nufi bakin gadon, amma kafin ta kaida hawa yace don Allah kiyi hakuri karki haumin saman gado da towel, cikin jin kunya Shalele tace saboda me? Mubarak yace wallahi kina haumin gado da abinda kika fito toilet wallahi yau bana iya bacci, Shalele tace to ka bani kaya na saka mana, Mubarak yace wallahi banda kayan da zaki saka kizo ki kwanta kawai da safe kafin ki tashi za’a kawo miki kaya, nan gidan banda kayan kowa saina uwar gida ko a baki ki saka ne? 
Kishi harda su Shalele 0h, wai A, a, ta fada tare da rufe idonta dan ta rasa ta yanda zata rabu da towel in, gajeran murmushi Abak yayi tare dayin wasa da idanuwansa sannan ya juya dan bacci ne sosai a idonsa, ita kuma kashe fitila tayi sannan ta cire towel in tahau gadon da sauri cikin jin kunya taja bargo ta lullube,. 
A hankali yajuyo idanuwansa a rufe ya lalabu Shalele ya kamkameta a jikinsa tare da sauke wata irin gajiyayyar ajiyar zuciya waddajin sautin ta yasa chargyn wayata ya kare, da sauri na nufi jikin soket na saka chargy amma kafin na samoshi na dawo dan baku labari tuni komai ya faru dan kuwa Mubarak ya kashe boss ya raya sunna a cikin wannan dare wanda shima yana daya daga cikin dararen da bazai manta dashi ba a rayuwarsa, a 
bangaren Shalele ma haka ne. Sirrin ma’aurata sai su. 
Komai dai nasu a tsaftace sukayi shi domin dai Mubarak tsohon hannune kuma yasan kansa, shine ya taimakawa Shalele ta gyara jikinta, kayan bacci ya dauko mata sabbi ya bata ta saka sannan ta koma ta kwanta sai shashshekar kuka takeyi cikin yanayin wahaltuwa, shima tsarkakejikinsa yayi sannan yazo ya kwanta cikin farin ciki tare da jawo Shalininsa ya riketa ajikinsa, basu dade da kwanciya ba dukansu bacci yayi gaba dasu. A bangaren Baba Bashir kuwa wannan dare rumtse bai rumtsa shi ba koda wasa sai round yake yana safa da marwa a cikin tankamemen palonsa, zuciyarsa kuwa ji yakeyi kamar zata fasa jikinsa ta Fito, tunani kawai yakeyi da ayyanowa duk abinda ya faru ya riga ya gama faruwa, haka ya kasance har asuba, alwallah yayi ya nufi masallaci, daga masallaci suka kama hanya dan zuwa gidan Abak dashi da Sulaiman, 
Hankalin Sulaiman ya tashi sosai ganin sun fito kauyansu lallai yasan gidan Mubarak zashi, kuma babu dama ya fadawa Mubarak suna zuwa dashi da Baba baida abinyi ko 
mafita dole ya hakura. Mubarak kuwa yana dawowa daga masallaci bai koma bacci ba, ita kuma Shalele ta zaune a saman abin sallah da zabgegiyar hijabinta kanta a duke, shi kuma Mubarak yana 
kwance a gefen gado yana waya. Ganin Shalele ta mike yasa shi kashe wayar tare da saukowa daga saman gadon ya nufo wurinta cikin farin ciki, a hankali ya jawota zuwa cikin jikinsa tare dajanta suka matsa jikin gado, zama yayi tare da zaunar da ita itama, 
Cikin jin kunya ta dukar da kanta kasa, murmushi Mubarak yayi tare da dago mata fuska ya tallabeta da lallausar hannunsa, idonsa a cikin kwayar ido Shalinina ina miki murna da wayuwar gari a cikin sabuwar rayuwa, Shalele tace nima inayi maka murna, murmushi Mubarak yayi tare da cewa na gode sosai ………. 
Mubarak ………… Yaji muryar Babansa daga palo yana kiransa, murmushi yayi tare da cewa tashi muje, har ta tashi ya sake zaunar da ita, saida ya sumbace ta sannan ya mike yaja hannunta suka fita, A palo suka samu Baba bashir dashi da sulaiman. Mubarak yace barka da safiya Babana, shiru yayi bai bashi amsa ba, Sulaiman yace ubangida na yana gaisuwa. Baba bashir yace Sulaiman daren jiya ya kasance mafi dadi gareni, 
Cikin damuwa Sulaiman yace miya faru ne “yar labai? Baba Bashir yace tunda nake ban taba samun kunar zuci ba irin kunar da naji kamar ranar daurin auren Mubarak ba, Sulaiman yace kuna kuma? Kunar me “yar labai ya tambayesa cikin yanayin damuwa, Baba Bashir yace kunar da take samar da raunuka a zuciyata kunar da take caccaka da kwankwatsar zuciyata, kunar dake haramtawa jiki duk wani hutu, haka zalika barauniyar sukuni, Sulaiman yace wannan wace irin kunace haka “yar labai harta hanaka bacci? Baba Bashir yace, kunar tabamin kimata da akayi Sulaiman, kunar da Mansurya cusamin a matsayin sadakin “yar sa, Sulaiman yace idan dai har haka ne ka bari ni dakaina zan dasa masa bakin cikin da yafi wanda kaji a taka zuciyar, Baba Bashir yace a, a, Sulaiman kunar da nasha a daren ranar ina so na rama fiye da haka, cikin daga murya yace Mansur wayewar garinsa cikin farin ciki ta kare. 
Juya kallonsa ga Mubarak yayi tare da cewa Mubarak ni wane irin uba ne a gareka? Murmushi Mubarak yayi sannan yace wanda na zabesa fiye da girman duniya da abinda yake cikinta, Baba Bashir yace shin dakwai wasu muradai da kake dasu k0 wani muradi kwaya daya da ban cika maka shi ba? Mubarak har yau babu wani abu wanda bakayi min shi ba Baba, nuna kansa yayi sannan yaci gaba da cewa saboda ni ka juya gaba zuwa zumunci ta hanyar bani Ummu suleim, 
Baba B, yace a madadin wannan farin cikin dana baka idan na nemi wani farin ciki daga gareka shin zaka bani? Murmushi Mubarak yayi sannan yace ko raina ne kace na baka shi zan bakashi cikin murmushi, Baba bashir yace to idan ya kasance abinda zaka bani kafi sansa akan rayuwarka fa? Mubarak yace Baba duk wani numfashina naka ne, domin farin cikinka har guba zan iya sha Baba, Baba bashir yace tunda haka ne ga Al’Qur”ani nan ka dafa, sannan kayi alkawari cewa abinda nace kayi shine zakayi. 
Matsawa yayi kusa da Al’Qur’anin ya dafa, sannan ya fara cewa, na rantse da Al’Qur”ani mai girma duk abinda kace nayi shi zanyi bazan saba maka akanshi ba. 
Baba bashir yace Mubarak idan ya kasance kana matukar san motocin dake cikin gidan 
nan dukansu, ka siyosu ne saboda ka hau ka more rayuwarka dan kana so ka siya, sai ya kasance kalolin motocin nan sun kasance suna sukar zuciyar mahaifanka tamkar dubun harsasai ya zakayi? 
Mubarak yace Baba gusar da tunaninin wannan motocin zanyi a zuciyata, cikin daga 
murya Baba bashir yace to in haka ne ina so ka kori Shalele daga gidan nan. Zaro idanuwa Mubarak yayi tare da kallon mahaifinsa sannan yajuya ya kalli Shalele cikin tashin hankali, sake juyowa da kallonsa yayi ga mahaifinsa cikin kuka yace Baba? Baba Bashir yace kardai ka manta ka rantse da alkur’ani mai girma kuma ka sani kur”ani ya wuce gaban wasa. Sulaiman yace “yar labai ya haka? Baba Bashir yace manta Sulaiman, Mansur yaci zarafina a gaban dandazon al”umma ya dorani akan mizanin kare kima, 
Mai Nasara, da sauri ya shigo ciki wanda tun kafin shiga Baba Bashir shima saida ya fito dashi, da sauri ya shigo cikin palon yabi ubangidansa da kallo, Shalele kuwa tayi mutuwar tsaye, dan gaba daya ganinta ya dauke, makullin mota Baba mansurya bawa Mai nasara tare da cewa, Wannan makulin motarda babanta ya saka ne a cikin kudin sadakinta, akwai kudi a cikin motar naira miliyan biyar da takardar filinta ka kaita har gurin Mansur, Kallon Shalele yayi sannan yace idan kinje ki fadawa Babanki Mubarak ya biya farashinki. Cikin kuka Shalele tajuya ta kalli Mubarak shima hawayene ke ratata daga cikin idonsa, a hankali ya dauke kansa daga kallon Shalele juyawa tayi ta kalli Sulaiman shima cikin kunar zuciya ya kauda kansa daga gareta, ba tare data kalli Baba bashir ba ta tunkari hanyar fita, Mai Nasara yabi bayanta har waje, cikin kunar zuciya tattare da danasani ta shiga motar Mai Nasara yaja suka tafi Baba Bashir ya juya tare da cewa muje Sulaiman ……….. Mubarak yana kallonsu har suka fice daga cikin palon. 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]