[Advertisements⬇️]

HARSASHEN SO CHAPTER 23 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HARSASHEN SO 
CHAPTER 23
Da sallama ya shiga, kuma kowa na gidan yana tsakar gida. Amma ko Mama bata amsa masa sallama ba, kowa shiru yayi masa, sai Shalele data taso da gudu tayo wurinsa. Cikin farin ciki ta tsaya gabansa tare da cewa yaya me ya kawoka nan gidan da rana kowa yana kallonka, 
Hannunsa ta fara ja tare da cewa maza ka fita kafin Mai gida yasa ayi maka lullusar fitar hayyaci, kallonta yayi ba tare da yayi magana ba ya cire hannunsa daga cikin nata. Ya fara taflya don shiga cikin gidan gaba daya, Mai gida ne yace idan ka sake taku daya a Cikin gidan nan saina gundile maka kafafuwa, tsayawa yayi ba tare daya ci gaba da tafiyar ba kuma baici baya ba, a wurin yayi tsayuwarsa kamar an dasa icce. Cikin tsananin bacin rai Mai gida yace me ya kawo dan makiyi na  cikin gidana? Shalele tace nice nan nina kawoshi. daga inda mai gida yake zaune yayo wurgi da wata “yar fiririyar wuka wanda yaso ta soke a cikin bakin Shalele, wanda haka ya ayyana a ransa shi yasa yayo wannan saitin, amma kafin ta samu isa wurin Mubarak ya tare wukar ya riketa da da hannunsa. 
Tashi tsaye Mai gida yayi tare da cewa da kyau, da kyau jarumin jarumai wato uba zaiyi hukunci wa “yarsa kaine zaka hana k0? Da kyau da kyau, haka ake san mazaje su rika kasancewa masu zafin nama. 
Me ya kawoka cikin gidana? Mubarak yace zowa nayi na tambayi Shalele shin haryanzun tana sona ………. . ……… Da sauri Mai gida ya dakatar dashi tare da cewa rufa min baki rufamin baki ……… Idan ka sake maimaita wannan kallamar a gabana saina gimtse maka harshe, murmushi Mubarak yayi tare da kallon inda Shalele take yace ki fada a gaban babakin kina sona! 
Zaro idanuwa Mai gida yayi tare da goge zufar dake barowa daga jikinsa yabi Shalele da wani irin firgitaccen kallo banda dukan dubu dubu babu abinda gaban Mai gida keyi, cikin tsananin bacin rai ya zaro “yar karamar bindigar dake sake a cikin jikinsa, yace na rantse da Allah idan har kika furta kallamar so wa dan makiyina saina harbeki in kashe ki har lahira na kashe banza, Tun kafin Mai gida ya rufe bakinsa Shalele tace ina sansa, kuma ni nake sansa shi baya sona, kuma a haka naji na gani nace ya taimaka ya auren ni………. da sauri Mama ta taso dan Mai gida ya saita daidai kan Shalele zai sakar masa harsashe kan ya watse gaba daya. Mama ta janye Shalele harsashen yana fita, cikin tashin hankali Mai gida yace na rantse da Allah saidai ki mutu amma babu maganar auren dan makiyina, dan gajeran murmushi Mubarak yayi tare da juyawa ya fice daga cikin gidan, Mai gida yaci gaba da cewa ni zaki tonawa asiri? Shekaru nawa kika sani nake dakon kiyayyar abinda na tsana a cikin zuciyata?, da nasan zan ga wannan ranarda idona da tunda na haifeki na sare miki zuciya, baki da wani amfani sannan baki da banbanci dake da sakako, 
Shalele na tsine miki albarka Allah ya tsine miki ‘tunda har kika ci fuskata a gaban dan makiyina, kika wulakantani a gabansa kika nuna masa banda mutunci kuma bani da amfani,yace ki fada a gabana kina sansa kika fada,yau ni dan makiyina yakeyin murmushi a gabana? Yau ni dan makiyina yaga hawayena? Na tsanake na gogeki daga cikin jerin sahun “ya”yana dana san sun kasance a cikin jinina, idan har kika sake tunani nine ubanki ko a zuciyarki kikayi wannan tunanin ban yafe miki ba, daga yau ki rika kiran sunana kai tsaye kawai kice ‘MANSUR’ kema kina jerin sahun abinda na tsana a duniya …….. 
Yana gama fadin haka, Mama tace maza ki tattaro duk abinda kike so dani dake yau zamu bar masa gidansa. dama amfanin aihuwa da yawa kenan, yau ga ranarta tazo. cikin tashin hankali Mai gida yace A, a, mamana kiyi hakuri raina neya baci, Mama tace idan har ka sake daga murya ko magana akan tarayyar Mubarak da Shalele zaka ga hukuncin da zan yanke, dakel Mai gida ya hadiye yawun bakinsa tare da goge hawayen bakin ciki, baida yanda zaiyi dole ya sakawa sarautar Allah ido. 
Mubarak kuwa yana fita gidansu ya koma, Bai samu Baba ba, sai babban yaronsa mai suna Sulaiman, wanda duk abinda ya faru a gaban idonsa akayi komai, Baba Bashir ya yadda dashi 100% babu wani sirri na Baba wanda shi Sulaiman bai sani ba, Dan haka shine ya fara kwantarwa da Mubarak hankali cewa yayi hakuri insha Allah shi da kansa zaije ya nema masa auren Shalele da kansa yanzun nan kuma basai anjima ba, dan gajeran murmushin Mubarak yayi danshi dai yasan basan Shalele yake ba kwata 
kwata, amma zai bari a nemi auren nan kodan ya kalli yanda wasan yake tafiya. 
Sulaiman kuwa fita yayi daga cikin dakin dan tafiya gidansu Shalele, girgiza kai Mubarak yayi tare dayin murmushi da gefen bakinsa, dan zamewa yayi ya kwanta saman kujera, wayarsa ya ciro ya kira Khadija cewa bazai samu dawowa ba yau, Khadija tace me yasa ne? Mubarak yace shima dai Oho, yana fadin haka ya kashe wayarsa. 
Sulaiman tsaye a gaban Mai gida cikin gidansu Shalele, Sulaiman yace, ni yaron Bashir Abak ne Sulaiman. Mai gida yace na samu labari kan cewa kanaji da karfi sosai a hannayenka, Sulaiman yace nayi nadama akan faruwar waccan al’amari, Mai gida yace Ina ina? Sam sam ba nadama ce ta kawo ka nan ba, kazo nan ka gaya mana cewar wuyan zuri‘ar mu babu karfi, Sulaiman yace idan har kana san ka dau fansar wuyan danka sadiq zaka iya sare nawa wuyan, ya karasa maganar yana mai sadda kansa a gaban mai gida. Mai gida yace kaga karka wani sunkuyar min da kai ban taba cin itatuwar tankwararren reshe ba tabbas ina binku bashin karyamin wuyan babban dana da kukayi kuma zan fanshe nan bada jimawa ba zan fanshe bashi na. Sulaiman yace, malam mansur na hada hannayena ina rokon wata alfarma a gareka da fatan bazaka barni na tafi hannu biyu rabbana ba. Mai gida yace sam karka sake ma ka nemi wata alfarma a wurina wacce mai yuwuwa ma zata iya sawa ka rasa hannayenka. 
Sulaiman yace ina nemawa dan ubangidana Mubarak auren “yar wurinka Ummu suleim, cikin tashin hankali Mai gida yace rufamin baki makiyi rufemin baki, fice min daga nan nace fice ya karasa maganar jikinsa har kyarma yakeyi saboda bacin rai. Cikin sanyin murya Sulaiman yace bafa zaginka nayi ba malam Mansur, kai ubane ga yarinya budurwa kuma koda bakaji dadin wannan alfarma ba ya kamata ka duba su waye suke neman wannan alfarma, ka tuna gidan Bashir Abak ne, Jinjina kai Mai gida yayi tare da tattaro natsuwarsa yace lallai zan kuwa duba, zan duba wannan magana da kyau, cikin tashin hankali kuma ya sake daga muryarsa tare da cewa fitar min daga gida makiyana lallai dana samu birbishin cewa a zuri’armu an taba kashe bare a gidan nan dasai na gimtse maka harshe na tura a gidan makiyina gangar jikinka karnuka sun cinye,balaga ……………. da gudu suka iso wurin, Mai gida yace ku fita dashi daga gidan nan cikin mutuntuwa har karshen iyakarmu baki daya. 
Fizgejikinsa yayi daga rikon dasu Balaga sukayi masa sannan ya fita daga gidan ransa a bace. duk abinda ya faru ya fadawa Baba B, dan ya dawo daga inda yaje, dariya Baba b, 
yayi sosai tare da cewa wato yaji tashin hankali da fargaba dama yana san “yarsa, lallai Jini na yana da karfl, 
Kallon Mubarak yayi dake tsaye a gabansa, dafa kafadarsa yayi tare da cewa dakyau dana , da kyau da kyau wannan itace zuciyar karfe da kuma ketar ta gulla wannan shine launin jini na gaskiya, da kyau dana ka fade soyayya da “yar makiyina da kyau dan nan da kyau da kyau, Yanzu koda kogin jinine zai gudana auren “yar gidan Mansur sai ya zamo naka, ina mai tabbatar maka, Sulaiman a shirya doki dakaina zanje har gidan Mansur na hadu dashi. 
Shidai Mubarak binsu yayi da kallo baice musu komai ba, fita Baba b, yayi ya haye saman dokinsa sai gidan Mai gida, Shi kuwa Mai gida fitar Sulaiman shima ya fita dan tafiya wurin bokansa, dan ko kasa da sama zata hadu baijin zai iya hada jinin diyarsa da kuma jinin dan makiyinsa, wannan auren duk bala’i bazai yadda ayishi ba saidai a busa kahon tashin alkiyama kowa ya mutu a huta. Baba b, kuwa da gudunsa ya shiga cikin gidan Mai gida, yana shiga ya fara kiran sunan sa, Mansurrrrrrrrrrrrr, daya kira sunan sai dokinsa yayi wata irin haniniya yana samarya yana bude bakinsa, gaban Mama saida ya fadi jin muryar Baba bishir, da sauri’ ta taso ta fito tana cewa menene kuma ya faru Bashir? ‘ 
Bashir yace ina sone na sani meye yasa akaki karbar Mubarak a matsayin surukin gidan nan? Mama tace shin Bashir yanzun batun wannan hadi yasa kaji kirjinka ya buga? Bashir yace me yasa kirjina zai buga ne Mama? 
Shi Mansur din kawuna biyu gareshi ko kuwa mai ne yake bulbulowa a jikinsa? Kojinin sa ya dara nawa ne? Shin nasabarsa takai tawa ne? Me yake dashi wanda yakaini ne? Kowa yasan dana Mubarak daya ne a cikin miliyoyi, akan mi yaki amincewa ne Eye? 
Bashir yaci gaba da cewa Mama karfa ki manta sarki ne da kansa yake neman auren “yarku, Mama tace Bashir shifa neman aure bafa haka kawai ake daukar diya ga ko wane irin mutun a bayar ba, karfa ka manta Bashir. duk fa wanda yake san wani abu roka yakeyi a bashi bada karfi”: yake kwata ba, akwai abubu da yawa da ake aunawa a lamari na aure, Bashir yace Mama, wannan fa neman auren dan gidan Bashir Abak ne, wannan aure yafi karfin a dorasa akan ko wane irin mizani, Mama tace shin koma dai miye diyarsa ce, inma ya yadda ko bai amince ba auren “yarsa ne, idan ya yadda zai bayar da auren Shalele wa danka, idan kuma yace baya so to fa babu mai masa dole, mune zamu auna danka mizani idan ya cancanci mu bashi zamu daura auren Shalele wa Mubarak. 
Bashir yace, inma kun amince inma baku amince ba hakkun za‘a daura wannan aure saman kawunan gawawwaki, domin tunda dana yake a duniya bai taba son abu ban 
cika masa ba, Mama tace bashir jininka yana da zafi shima na Mansur tafasa yakeyi, kabi a hankali kar kace zaka tayar da fitina ka bani lokaci zanyi nazari akan wannan magana, ba tare da 
Bashirya sake magana ba yayi wa dokinsa diddige ya fice daga gidan, A ransa kuwa keta da mugunta ce kwance, tunda har Mansur baya san auren nan hakika sai ya kafe kai da fata anyi sa, Mubarak kadai ya ishi “yar sa jidali, kuma a gidansa za’a ajiye Shalele bazai wani bari a tafi da ita birni ba, hakika da yasan Mansur yana kyamatar jininsa wallahi da tuntunin duniya ya huro masa wuta daya tattare kayansa tuni yabar garin nan …… 
Da gudu Mai gida ya shigo cikin gida, yana kiran sunan Mama, cikin sauri ya haura sama har cikin dakin Mama sannan ya samu wuri ya tsaya, cikin ladabi ya fara magana cewa, Mama naji ance Bashir yazo gidan nan wai a dole sai an bashi auren Shalele, Mama tace haka ne Mansur amma miye abun daga jijiyar wuya? Mansur yace wannan abune da dole sai an daga jijiyar wuya akai, Mama Allah shine ya halicci duniya kuma munsan dalili, idan akayi tsawa da walkiya munsan dalilin da yasa akayi, amma yanzu Mama meye dalilin da zaisa mu dauki Shalele mu bayar ga wa’annan mutane sai kace wata tsinuwa ta kama mu? Mama tace yaro na sam ban fahimta ba, bansan abinda yasa kake kallon komai a haggunce ba, Mansur yace Mama saboda sune suka kashe min babban dana, kuma sunzo suna neman auren “yata'” Mama tace wannan abun alfahari ne, mutanen da suke gaba dakai yau sune suke neman alfarma a wurinka! 
Mansur yace A, a, Mama A, a, ba auren Shalele suke so ba tozarta ta sukeso suyi, karki 
manta shi Mubarak ba shine yake san Shalele ba ita Shalelen take sansa, Mama tace kaga irin gardamar taka, shin baka tunanin yanda za’a samu maslaha tsakanin gidaje biyun nan? Kullum kana yawo da takobi a hannunka da kafi a harshenka, Mansur yace Mamata wannan sakamakon zazzafan jinin Babana ne yake gudana a jlkina, sai kuma kyautatuwar shayarwarki, Mama tace to ka sassauta wannan zazzafan jinin kayi tunani idan Shalele ta zama surukar gidan Bashir ……………… 
Da sauri Mai gida ya rumtse idanuwansa tare da runtse dukan hannayensa ya matse jikinsa kamarwanda aka watsawa tafassashen ruwan zafi, sannan yace A ,a, Mamana A, a, A ,a, don Allah kada ki shiga wannan zancen ki yarda kawai ki tafi aikin hajji, Mama tace daurawa diya budurwa aure yafi maimaita hajji, alkawali na yadda da maganar Bashir na bawa Mubarak auren Shalele ……………. Kuma babu wanda ya isa ya hana,juyawa tayi ta shige cikin dakin baccinta tare da rufo kofarta. Balaga dake tsaye a gefe yace mai gida, ka amince ni zan kwalkwalewa duka dangin ango idanuwa, cikin sanyi Mai gida yace A, a, Balaga wannan hukunci bana Mama bane akwai wani abu. Nima dole saina bi yanda take so idan ina san zama lafiya. 
Balaga yace Mai gida karka damu wallahi zan iya warware wannan magana, Mai gida yace A, a, yaro yanda baza ka iya warware Babanka ka nada wani ba haka wannan maganar bazata warwaru ba,… 
Mubarak kuwa a gidansu ya kwana, Baba b, kuwa ya rubuta a rubuce ya tura cewa auren Shalele da Mubarak ya tsayar da kwanakin aure kwana ukku casss haka ya iba kuma haka za’ayi fada musu yayi bawai shawartarsu yakeyi ba. 
Mama kuma ta amince da hakan ta kuma yadda kuma tace babu fashi ba canji bare daga lokaci kwanakin da Bashir ya iba haka za’ayi, idan hankalin Mansur yayi dubu ya tashi, Ya koma ya fadawa boka amma boka yace wannan auren bazai taba auruwa ba, ya kwantar da hankalinsa,a sikwane Mai gida ya dawo gida. duk wanda ya gansa yasan yana cikin tashin hankali da damuwa, wannan abu kuwa yayi bala”in ma Bashir dadi sosai abokin gabarsa ya shiga dimuwar rayuwa dama haka yake so kuma hakan take ta kasancewa, Khadija kuwa labarin auren Shalele da Mubarak ya iskota idan hankalinta yayi dubu, to da kwara kwara saida ya tashi, tayi kuka kamar zata kashe kanta, dan haka itama ta fantsama malamai, kuma duk inda taje ana bata tabbacin babu wannan auren babu baza ayi saba. 
Yau ta kama ranar daurin auren Mubarak da Shalele, a gidan Mai gida kuwa dashi da zaman mutuwa babu banbanci. Baba bashir yaji labarin haka yaji dadi sosai abokin kiyayyarsa yanajin ciwon rabuwa da “yarsa, kuma a rasa a ina zata je sai a gidan babban makiyinsa, Abinci “yan gayu masu shegen dadi da tsada Baba bashir yasa aka kawo daga birni, yaransa yasa su dauka dan sukai gidan Mai gida, ran Mai gida a hade yace wannan kuma fa daga ina? Abinci ne Mai gida Bashirya bada cewa a kawo, Mai gida yace ku juya dashi sannan ku fada masa cewa ni ba mayunwanci bane bana kwadayin duk wani abu da yakejin yana takama dashi, ku koma dashi, daga sama Mama ta leko tare da cewa ku shigo ku ajiye. Shiga sukayi suka ajiye sannan kowa ya samu wuri ya zauna yana jiran lokacin daurin aure yayi, Shalele amarya kuwa babu abinda takeyi sai aikin faman kallon agogo dan baifi 
saura minti 30 ba ta zama matar Abak. 
Hmm ko me zai faru😀

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]