[Advertisements⬇️]

GIMBIYA SA'ADIYA CHAPTER 14 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GIMBIYA SA’ADIYA 
CHAPTER 14
Banda je-ka-ka-dawo babu abin da Kursiyya ke yi tun dazu a cikin dakinta. Sautin kukan Hafsa daya gama mamaye dakin kuwa, jin sa take tamkar ana rura wutar darma ana malayar da ita a Cikin kunnuwanta. A rayuwarta ta tsani jin kukan tilon yarta. Takan aikata komai ma, duk tsananinsa in daiza ta saka yarta a Cikin farin ciki. Ta lura sosai soyayyar Yerima Abu Sufyan tayi tasiri a Cikin zuciyar Hafsa. Ban da haka, da sai ta roke ta ta saka wa zuciyarta salama, ta fita batun shi tun da baya da raayinta. Amma hakan ba zaiyiwu ba, ta yi alwashin cika ma Hafsa burinta, ko mata wacce hanya ce sai Yerima Abu Sufyan ya auri Hafsa. 
Runtse idanuwanta tayi bayan ta zauna kusa da Hafsa. Ta dafa mata kanta. 
“Bana son zubar ha wayenki Hafsa. Duk kwallarki daya da zai zuba daidaiyake da azaba kala goma da zan gana wa waccan mayyar yarinyar. Ki kwantar da hankali, in dai Yerima Abu sufyan ne wallahi sai kin aure shi; k0ta wacce hanya ce.” Cikin kuka Hafsa ta ce, 
“Ta wacce hanya kike tunanin Yerima zai soni bayan ya gama ci mini mutunci a gaban yarinyar can? Umma na tsani kaina, kuma wallahi ba zan taba yin aure ba matukar Yerima Abu Sublan bai aure ni ba.” Shiru Kursiyya tayi na wani lokaci, kafin ta ce, 
”Ni nasan hanyar da zata bullar da mu. Abu daya nake so daga gareki yanzu dai, kiyi shiru ki daina kukan nan. Alkawari na daukar miki, wallahi ba zai auri Halimatu ba ke zai aura.” 
Nannauyar ajiyar zuciya Hafsa ta saki, sannan ta kokarta tsayar da kukanta. 
“Yauwa ko kefa. Kijira niyanzu zan fita ni da Zabbau. Karki sake in same ki kin kuma yin kuka, zuciyata ba zata yi mini dadi ba.” 
Kai kawai Hafsa ta daga tana kara share kwallarta. Kursiyya ta bazo yalwatacciyar sumarta bisa gadon bayanta, sannan ta yafa mayafi mai matukar kyau da daukar ido, ta bar dakin. 
Bata ko tsaya neman izinin mai manaba ba, sai dai ta isar da sako ga Khalili, ta kuma 
umurce shi kan cewa karya kuskura ya sanar da mai martaba fitar tata har sai ya tabbatar sunyi‘ nisa. Ya amsa da to cike da al’ajabin hali irin na Kursiyya. 
Drebanta daya kasance dukkanin Iamurranta da suka shafi tafiye-tafiye yaja su, 
bayan ta sanar da shi inda suke son zuwa kai tsaye suka nufi wurin Boka Fartsi. 
Kamar koyaushe, dukkanin al’amurran da suka saba yi idan sun ziyarci boka Fartsi ne suka wanzar; cikin dan dakiku saiga su a cikin dakinshi, bayan sun shajini, sun kuma yi zane da shi a fuskokinsu. 
Kasan dakin ya hau girgiza, ya tsatssage hade da wata irin kara mai razanarwa, sai ga boka Fartsi ya bullo daga kasan, fuskar nan tashi kamar kullum babu annuri a cikin ta. 
Bayan ya daidaitu a mazauninsa, ya saita idanuwanshi bisa kwaryarjinin nan, ya kalle ta na kimanin mintuna biyar, sannan ya fara maganar shi mai cike da razanarwa. Abin da kike so ba zai taba yiwuwa ba. ” Da sauri Kursiyya ta dafe kirjinta sanadiyyar bugawa da taji yayi. “Ranka ya dade Boka Fartsi, amma maiya sa duk bakinjininta shidin baiki taba? K0 kuwa hakanyana nufin wancan dadadden asirin namu na neman kwancewa ne?” 
Ya watsa yatsunsa na hannun haggu a saitin kwaryar, saigajinin cikiya canza launi dagaja zuwa kalarkasa mai tururuwa. “Wancan asirin na tsawon shekaru goma sha bakwai ba ayi shi ga wanda ba dan masarautar ba. Zai iya shafar har wanda ba a cikin masarautar ba, matsawar a cikin garin Bilba ne. Don haka, wannan Yeriman ba dan garinku ba ne, ba Iallai bane wancan sihirin ya shafe shi ba.” 
Jinjina kai’ Kursiyya ta hau yi‘ alamar gamsuwa, tabbas maganarsa haka ne, domin kuwa ba Yerima Abu sufyan kadai ba, shi ma kanshi abokin tafiyar shi taga tsantsar kula war Halimatu a tattare da shi, sabanin mutanen masarauta da kuma garin Bilba. ‘ 
“To yanzu boka miye abin yi?” Ta tambaye shi cike da damuwa. “Tabbas rayuwar Yata zata shiga kunci, matukar ta rasa Yerima Abu Sufyan. Haka kuma rayuwata zata shiga kunci, madamar rayuwar yata na cikin kunci. A taimaka miniya boka, k0 nawa kake so zan baka, duk abin da kake so nayi alkawarin zanyi maka shi, indai harza ka karkato hankalin Yeriman ya dawo ga Hafsa yata. ” ldanuwansa ya zaro yana kallon ta hanyar da kasa ta tsage ya fito sai ga wani dunkulelen abu ya fito, tamkar mage, tamkar kuma kare. Sai dai dukka girmansa ba zai wuce na 
magen ba. Yatsarsa manuniya ta hannun haggunsa ya saita ga halittar dabbar, a take ta rikide daga kalar baki tana komawaja, tana murzajikinta a kasa da Iya karfinta, dukkanin 
gashinjikinta na ficewa harya gama fita baki daya, ta koma zallarqashi babu k0 tsoka a 
jikinta. 
Sake mayar da idanuwansa ga kwaryar yayi, sai gata ta tashi sama, tana zuwa saitin da 
dabbar nan take ta karkace, duk wannan jinin daya sauya kala ya hau zubajikin dabbar. 
Wani irin kuka take saki, wanda ya tabbatar da cewa tana tsananinjin radadi da azabar abin da ke zuba a jikinta. Da haka ta rinka sussulbewa tana talewa, hargabobinjikinta suka 
rabu kashi-kashi, karshenta ke nan. Kwaryar ta koma mazauninta ta zauna  Boka Fartsi ya daure fuskarsa kuma, yayi kasa-kasa da idanuwanshi. 
“Zaku iya fassara mini abin da ya faru a nan?” Da saurin su duka biyun suka gyada masa kai. Ya danyi shiru jim, kafin ya cigaba da cewa, 
“Ya riga ya kamu da kaunar yarinyar, ba kuma zamu Iya yi masa komai don ya daina son taba. Sai dai zamu iya yi masa wani abu domin yaso Hafsa, idan babu gilmin Halima kenan.” 
Kwata-kwata kansu ya gama daurewa. Sun kasa gano madosar Iamarin nashi. Kuma sun sani sarai, boka Fartsi yaki jinin a ce komai saiya warware shi, yafiso idan ya baku haske 
to ku dauka. Ba irin mutanen nan bane masu yawan magana. “Kunga wannan dabbar data fito?” Suka daga kawunansu da sauri. Yayi murmushi, “Kun ga yadda nayi da ita?” nan ma suka sake daga kai. 
“Hakan yana nunar muku da cewa abin da ya faru da ita ne kadai zai iya sakawa Yeriman ya auri yarki. “Ya tauni lebensa na kasa, wanda ya kasance dabi ‘arsa ce dama. 
“Ta fito daga kasa da izinina. Na raba ta da rabin rayuwarta, domin kuwa dabba babu gashi a jikinta sunan tanarayuwa ne, amma a kowanne Iokaci zata iya rasa rayuwar tata. Bayan nan, da kayan tsafina na tarwatsa mata abin da yayi saura na daga gangarjikinta. Wanda kun ganta a baje akasa, ba kuma hakan na nufin ta mutu bane. Sai daiya nunar da cewa a karkashin ikona take, idan naga dama zan miyar da ita yadda take, sai dai bayan na miyar da ita yadda take, zata cigaba da zama a karkashin mulkina, zata aikata dukkanin abin dana umurce ta dashi. Kenan dai ta rasa farin ciki da walwalarta kenan.” 
Saiyanzu Kursiyya ta dago hasken. Murmushin gefen baki ta saki, sannan tace, “Abin da ya kamata ayi ma Halimatu ke nan?” Yajinjina kansa. 
“Hakan na da kyau Bokana. Tabbas bani da tamkarka, hakan yasa na dauki alwashin ba zan taba barinka ba har abada. Ba zan taba butulce maka ba. Duk kuwa ranar da na butulce maka, na roke ka da ka aikata naka ikon a kaina, kayi mini duk hukuncin da kaga ya dace dani. Domin kuwa na zama maciyya amana babba ba karama ba.”
Ya tulle da dariya da iya karfinsa, wacce dukkanin gangar jikinsa ke amsawa, yace”Kar fa watan wata rana haka ta faru ki nemi na gafarta miki, domin kuwa ni bana yafiya, kuma na tabbata hakan na zuwa nan gaba duk daren dadewa.” 
Ta saki murmushi hade da gyada kanta. “Ba dai daga gare ni ba ya bokana. Yanzu dai ba wannan ba, muyi maiyiwuwa dare keyi.” 
“Wannan aikin na yanzu mai matukar tsanani ne. Dole zaki ma yarinyar wayo k0ma ta yaya ne ki kawo ta nan, ke kika san yadda zaki tsara kayanki. Babu wata hanya da za a iya bi sabanin da a kawo ta nan din.” 
Jimmm Kursiyya tayi tana nazari’, To boka, zan san duk yadda zanyi don ganin mun zo nan tare da Halimatu, da kafafuwanta.”
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]