[Advertisements⬇️]

GIMBIYA SA'ADIYA CHAPTER 13 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GIMBIYA SA’ADIYA 
CHAPTER 13
Sosai Hafsa ke bin Saadiyya da kallo. Tana ji tamkar ta samu mashi ta caka mata shi daga nan inda take. Abun bai tsananta ba har sai da taga kallon da Yerima Abu Sufyan ke bin Saadiyya da shi. 
Shiru ne ya gitta a tsakaninsu, Shaheed ya dakatar da shirun ta hanyar cewa, 
“Ranka ya dade, Iokaci na tafiya. Ya kamata a ce kamar yanzu har mun kama hanyar 
Kubaisu.” Yerima Abu Sufyan yajinjina kansa. 
Abun ba wani na bata Iokaci bane ba ai. Gimbiya Hafsa, ko zaki iya hakuri ki bamu wuri mu gana da Gimbiya Saadiyya?” Ido ta zaro sosai. Duk da bai fito karara ya shaida mata inda zancenshiya dosa ba amma ta gane. Da karfi ta fasa kuka wanda babu yadda ba tayi ba don ganin ta dakatar da shi‘amma ta kasa. Duk hankalinsu suka dawo kanta, suna bin ta da kallo. 
“Wallahi ba zai taba yiwuwa ba. Babu yadda za a yi ka zabi wannan mayyar mai bakinjini bayan gani nina dace da kai. Don Allah ka rufa mini asiri Yerima…” 
Ta duke harkasa tana kuka, tamkar ba ita ce Hafsar nan uwarjiji da kai ba. Tun daga nesa ta tsinkayo sautin Kursiyya na fadin, “Ya isa haka Hafsa!” Sannan ta karisa takowa cikin izza ta iso cikin dakin. 
“Kin bani kunya Hafsa. Da isa da mulkinki da komai yau kika tsaya a gaban namiji kina masa kuka ya soki. Gaskiya albasa ba tayi halin ruwa ba. Namijin wa? Yau ko shi ne autan maza Hafsa bai kamata ki zubar da kwallanki a gabansa ba. Amma babu komai, kaddara ta riga fata! Tashi mu tafi.” ‘ 
Kiri-kiri Hafsa taki tashi, ta kuma ki daina kukan da take yi‘. Yerima Abu Sufyan dai k0 kallon Kursiyya baiyi ba. Kanshi a kasa yake har tayi ta gama. Sai dai ita bata sani ba, wannan maganganun nata sai suka kara zubar mata da kima a idanuwansa. Girman da yake ganin ta da shiya nema ya rasa. A yanzu ya samu tabbacin abin da yake zargi tun zuwan shi masarautar, cewa dakyar idan mahaifiyar Gimbiya Sa’adiyya na cikin gidan. Daga ganin yarinyar an san bora ce. lrin kallon da Hafsa ke yi mata, da kuma kalaman da suka fito daga bakin Kursiyya a yanzu. 
“Tashi mu tafi na ce ko! ” 
Taja hannun Hafsa da karfi? tare da mikar da ita tsaye. Tajuyo saitin Sa’adiyya ta mata wani irin mugun kallo, wanda yasa ta mikewa da hanzari tana kokarin bin bayan Kursiyya. Cikin kuka take fadin, 
“Ba da son raina ba na fito Umma. Sai da nace ma Kawu bani da Iafiya amma ya tirsasa ni, yace dani mai martaba ke nema na. Wallahi ba a son raina bane. Ni na san ma bani da farinjinin dako bawa zai so ni bare kuma dan sarki. Bada niya dace ba, da Yaya Hafsa ya dace. Don Allah ki rufa mini asiri ba zan sake ba.” 
Har tayi surutanta ta gama Kursiyya bata kula taba. Fara takunta yasa Yerima Abu sufyan ya dakatar da ita, ki zauna. ” 
Kanta ta gyada alamun ba zata dawo din ba. Da karfiya daka mata muguwar tsawar da babu arzki ta kwafe a daidai inda take. “Matso nan kizauna!” Jiki na rawa ta koma ainahin inda take zaune dazu. 
Har KUrSlyya ta isa bakin kofa, hannunta rike da hannun Hafsa, ta sake waiwayowa ta kalli Gimbiya Sa’adiyya, tayi kwafa sannan a fusace suka bar dakin. 
Ya isa to, daina kukan.” Ba ta daina ba sai ma kara tsananta da yake yi. 
“Ban damu da sanin komai ba a yanzu, saboda ba shi ne ya kawo niba. Nazo nan ne domin zabar matar aure, kamaryadda muka yi da mahaifina. Dan haka na zabe ki, na zabe ki Gimbiya Sa’adiyya, a matsayin abokiyar rayuwata. Ban damu da duk wani abu da zaije ya dawo ba. Kuma aure tsakanina da ke ba gudu baja da baya. Sai dai wani iko daga Allah.” 
A razane ta dago ta kalle shi. Yajinjina kai alamar yana mai tabbatar mata da hakan. 
“Shaheed ka zama shaida, ni Yerima Abu sufyan na zabi Gimbiya Sa’adiyya a matsayin wacce zan aura. Daga nan zuwa kowanne Iokaci aka bukaci kasantuwar auren, a shirye nake.” Cikin kuka, jikinta sai famar rawa yake yi ta fara magana, 
”Don girman Allah ka rufa mini asiri ka canza zabi. Ni dai wallahi ba zan iya aurenka ba. Yayata Hafsa ke kaunarka tun kafin ta fara ganin ka. Me yasa zakaki maikaunarka? Niba na sonka, Allah ya sani. Kuma na tabbata kai ma din ba sona kake yi ba, kamar yadda ban taba samun mai so naba bayan mahaifina. Kar ka cutar da rayuka uku, rayuwarka, rayuwar Yaya Hafsa, da kuma tawa rayuwar. Komai zai iya faruwa a sanadin haka. Ina mai rokon alfarmarka, dama ba ka riga da ka fada wa Abba ba, ka taimaka kace masa Hafsa ce zabinka. Hakan ne kawai zai tseratar dani daga rayuwar kunci. Na roke ka da girman Allah da kuma darajar iyayenka.” 
Ta sake dukar da kanta tana kuka sosai, kukan da duk wani maabocin imani idan yaji shi dole ya tausaya mata. Shi kanshi Yerima Abu Sufyan din ba karamin tausayinta yaji ba. A zuciyarsa yake nazarin wannan rayuwar ta yanzu. Rayuwar da idan ba mutum ya  ba duk kusancinsa da shi ba zaijawo shi a jiki ba, ba zai gwada masa kauna ba, ba zai nusar dashi dana kowa bane. Rayuwar da kowa nashi ya sani bai san na wani ba. 
“Ba zan iyajanyewa ba Halimatu. Domin kuwa kece waccejin muryarki kadai nayi yayin da kika yi sallama na tsinci kaina a wata duniyar. Kece wacce nayi tozali dake na jini a wani yanayi wanda ban taba tsintar kaina a cikinsa ba. Ki cire duk wani tsoro da fargaba. Na miki alkawarin babu abin da zai faru sai alkhairi. Ina son ki da zuciyata daya. Zan baki duk wani farin ciki wanda kika rasa a baya. Zan zame miki matsayi, in gwada miki dukkanin 
sayayyar da kika rasa daga wurin mutane.” 
Duk da hakan Sa’adiyya bata yi shiru ba, haka kuma ba ta daina fargabar abin da zai faru ba. Kanta sunkuye kasa tana zub da ruwan kwalla, tanajin yadda kanta ke sara mata, har 
yake barazar barewa. Jijiyoyin kan nata sun mata rudu-rudu. ldanuwanta sunyi jajur. Mikewa yayi a bisa kafafuwansa, hakan yasa Shaheed ma ya mike. “Yallabai tafiyar ce .Kai kawai Yerima Abu Sufyan yajinjina ma Shaheed yana mai ci gaba da taku. 
“Ai kamata yayi a sanar da mai martaba kun gama tattaunawa, kaga yana da kyau yaji zabinka daga bakinka.” 
“Ba zaiji komai ba idan yaji furucin na?” 
Da sauri Saadiyya ta dago kanta tana gyadawa. A ranta tana jinjina kalaman na Yerima. Kenan yana nufin ita borar mai martaba ce? Da ace bakinta zai iya dauriyar tankawa a daidai wannan gabar, da ta gusar masa da tunanin cewa Hafsa ce mowar Sarki Sani. Domin kuwa mahaifinta na son ta ita ma, yana kuma gwada mata kauna. Sai dai fargaba da yakeji a wasu Iokutan, wanda hakan na daya daga cikin dalilan da suka sa kowa ya raina ta. Inda ace yana fitowa a gaban kowa ya nuna irin kaunar da yake mata duk da ba haka ba. Ta sake fashewa da kuka hade da mikewa zata bar dakin. 
“Halimatu! ” Yerima Abu Sufyan ya fada da karfi Ta tsaya cak ba tare data waiwayo ba. 
“Kar ki fita kina kukan nan. Bari in baki wata shawara. Idan har kina son ki siya ma kanki daraja da mutunci a idanuwan kowa, ya zama dole ki kiyayi kowa na ganin kwallarki. A karshe, ki cire fargabar bayyanuwar soyayyarmu. Domin kuwa hakan ba zai amfane ki da komai ba face wani cin mutuncin. Ki fito karara ki nuna kin aminta dani, hakan zaisaka su fargaba, su kuma tsorata da ganin sauyuwar ki a lokaci kadan.” 
Yana kai wa nan ta fice daga dakin tana share hawayenta. Sosai take jinjina kalamansa. Tabbas gaskiya ya fada nata. Ba zata iya mantawa ba, tun tana yarinyarta bata da wani aiki da ya wuce shiga kunci da damuwa, wanda har hakan yayi silar da take fuskantar tsana daga wurin mutane, musamman kuma kuka da yakan kufce mata a wasu Iokutan a gaban idanuwan mutane. 
Bayan Yerima Abu Sufyan ya koma ya zauna, ya umurci Shaheed da ya shaida ma masu gadin kofardakin bakin, cewa yana son zai yi sallama da mai martaba. 
Babu wani bata Iokaci mai martaba ya iso tare da waziri. Yama waziri alama da hannu kan cewa ya basu wuri, haka Shaheed ma ya gaggauta barin dakin. “Yerima Abu Sufyan dana, ba dai har tafiyar ta tashi ba. ” Dan murmushi yayi bayan ya sadda kansa kasa, “Ta taso Mai martaba.” “To madalla. Wacce ka zaba a cikinsu?” Sosa kansa yayi cikinjin nauyin furucin da zai fito daga bakinsa, “Mai martaba, na zabikaramar, Gimbiya Sa’adiyya. ” 
Sassanyan murmushi Sarki Sani ya saki, wanda ya tabbatar dajin dadinsa. Sai dai kuma a Iokaci guda ya canza yanayi, hakan bai rasa nasaba da halin da yake da tabbacin gimbiyar tashi zata shiga a silar zabar ta da Yerima Abu Sufyan yayi a matsayin matar da zai aura ba. 
“Ma sha Allahu! Tabbas da Hafsa da Halimatu duk daya suke gare ni, kuma babu wacce tafi wata a wurina. Naji dadi sosai da kake da ra’ayin cika mana burinmu ni da aminina Sarki Abdurrahman. Allah yayi maka albarka.” ya amsa da ’ameen Abba. Bari in tashi kar dare yayi mana.” 
Ya mike fuskarsa kunshe da annuri’. 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]