[Advertisements⬇️]

GIMBIYA SA'ADIYA CHAPTER 11 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GIMBIYA SA’ADIYA 
CHAPTER 11
GIMBIYA Saadiyya ta daga kanta ta kalli Fulani Kursiyya, idanuwanta cike tafda kwalla. Sannan a hankali ta dukar da kan nata tana sauraron abin da bakin Kursiyya ke shirin furtawa. “Yerima Abu Sufyan dan sarkin Kubaisu na nan zai zo gobe, wurin yarlelena gimbiya Hafsa. Abin da nake so dake shi ne, karki kuskura ko leke ki fita daga dakin nan. Bana so ki gitta ko’ina da ke cikin gidan nan. Ke K0 mai martaba ya nemiganawa da ke ban yarje miki ki fita ba. Idan harshiya matsu to sai daiya zo nan din ya same ki. Bana son ki tambaye ni dalili. Kamaryadda bana son maganar nan ta fita daga cikin bakinki. Karki ce ban fada miki ba. ” 
Ta karashe maganar da karkace bakinta tana sakin murmushi, irin murmushin nan nata na mugunta. 
Gimbiya Saadiyya ta saka tafin hannunta ta share hawayen da ya gama wanke mata fuska. Duk yadda taso ta tsayar da hawayen hakan baiyiwu ba, domin kuwa wasu ne ke sintirin sauka. ‘ 
“Kukanki ba zai amfane ki da komai ba Halimatu. Bin umurnina ne kadai abin da zai 
taimaka miki.” Tana gama fadar haka ta fara takun kasaitar nata, tabar dakin, kofa bude. Bayan ta fita Sa’adiyya ta fada bisa gadon tayi kwanciyar rufda ciki. Gunjin kuka take yi da ita kanta ta tabbatar ba yada magani. Sai dai a gare ta, sosai kuka ke rage mata wani radadi daga cikin zuciyarta. A ranta take tunanin miye dalilin Fulani Kursiyya nayi mata shamaki da yalwatacciyar masarautar tasu? K0 tana gudun kar ta fita ne Yeriman ya canza zabi?A banza! Ta riya a ranta. Domin kuwa ta tabbata kamaryadda ba ta taba samun masoyi ba a duk duniya banda mahaifinta, haka take da yakinin ko giyar wake Yerima Abu Sufyan ya sha ba zaizabe ta ba matsayin wacce zai aura. ‘ 
Isowar shi. 
Da misalin sha biyu da rabi na rana ne mai martaba ya samu sakon isowar Yerima Abu sufyan a cikin garin Bilba. Fada wansa mutum gama ya tayar da dawaki domin su tarbo Yerima Abu Sufyan. Ba wai don hadiman Yeriman ba su san masarutar ba. Sun sani, domin kuwa sukan rako Sarkin Kubaisu a wasu lokutan idan ya kawo ziyara ga Sarki Sani. Mai martaba ya tura fadawan ne domin kara daraja Yerima Abu Sufyan. Ya tabbata zaiji dadin hakan. Saboda ya girmama shi matuka, ya kuma san zaiji dadin girmamawar. 
Hafsa data sha ado ce zaune bisa kayatacciyar kujerardakinta na daban. Idanuwanta a saitin mudubi tana sake bin kanta da kallo. K0 da ba a fada mata ba, ita kanta ta san tayi kyau. A takaice ma, tun da take a rayuwarta bata taba ganin kyanta kamar na yau ba. A yau ta kara gasgata cewa ita kyakkyawa ce abar so. Ta karajaddada kaunar mahaifiyarta a cikin ranta, a kan tsayuwarta tsayin-daka don ganin tilon yarta ta haskaka, ta zama abaryabo ga Yerima Abu Sufyan. Kararkararrawar da taji ne yasa ta sauke ajiyarzuciya hade da sakin wani kayataccen murmushi, wanda ita kadai ta san ma,anarsa. Wannan kararrawar ana kada ta ne a duk lokacin da aka samu manyan baki a cikin masarautar sarki Sani. Jin da Hafsa tayi an kada ta kuwa, ta tabbatar da isowar Yerima Abu sufyan ne. Da hanzarin Zabbau ta iso dakin, har tana cin tuntube da duk abin da ya tari gabanta. Da shesshekarta take fadin 
“Sun isa.,.Yeriman naki ya iso ranki shi dade. Fulani ta ce nace miki ki zama cikin shiri. Sannan kar ki manta da abubuwan da ta fada mikigame da shi, cewa Yeriman yana da isa da kasaita. Dole ke ma sai kin zama isasshiya sannan za ku daidaita. Nuna zumudinki a kansa zai iya sakawa ya raina ki, ki tabbatar da kin daga darajar ki a idonsa.” ‘ 
Kai kawai Hafsa tajinjina alamar gamsuwa. “Bari in je. Zan saka su Fauziyya gabatar da kayan makulashe a gabansa ne. ” Sai a sannan Hafsa ta ce, “Daga zuwan shi? Haba Zabbau. Idan fa yaga haka zaiga kamar an mayar da shi mayunwaci ne?” Zabbau ta murmusa, irin murmushin nan na gwanayen munafukai. . Tace”Kar ki damu. Hakan ma duk cikin karamci ne. Duk fa abin da za kiga an yi don a siya miki darajarki ne. ” “To da yaushe zan ganshi?” 
Zabbau ta dafa kafadar Hafsa. Da sauri Hafsa ta janye mata hannu cikin bacin rai tace, 
“Wannan wane irin hauka ne? Ba kiga yadda aka laga mini alkyabbar bane? Wannan ba irin sauran alkyabba da kika sani ba ne. Zata iya zamewa ta fadi. Kuma na tabbata ko za a kashe ki ba zaki iya nada mini ita ba.” Saida maganganun Hafsa suka daki Zabbau, suka sosa mata rai. Daya daga cikin abubuwan dake hada ta da Hafsa ke nan. K0 kadan yarinyar ba tada kunya, sam bata san darajar mutane ba. Ba tada yadda za tayi da ita ne dai kawai. Kuma idan har tana son Kursiyya ta kyautata mata, to fa dole ta kyautata ma Hafsa.Ki fadi abin da za ki fada ina sauraren ki.” Da kyar Zabbau ta iya zakulo magana daga kasan makashinta, ”Ba yanzu zaki fita ba tukunna. Bari za kiyi har a neme ki sannan.” “Zaki iya tafiya.” 
Hafsa ta fada tana kallon Zabbau. Da saurinta kuwa ta fice, domin ta san ba abin mamaki ba ne ba taji saukar mari a bisa kumcinta idan har ta cika zakewa. 
Zaune yake bisa kayatacciyar kujerar da ta kawatu da wasu irin karafa kalargwaldin. Wanda dukyake da karancin ilimin sanin zinare, zai iya rantsuwa da Allah cewa kujerar ta zinare ce. Fuskar nan tashi babu annuri ko kadan, idanuwanshi na bisa pocket diary din da ke bisa cinyarsa, hannuwansa kuma rike da karamar biro.
Daidai sadda ya dora biron zai fara rubutu yaji ana masa magana, “Ranka ya dade, ku ci abinci haka nan k0?” Waziri‘ ya fada, wanda ya iso dakin yanzu, bisa ga umurnin mai martaba Sarki Sani. Kansa ya jinjina cike da izza. Hakan yasa wani makusancinsa ya gaggauta karbar diary da biron ya soka a aljihunshi. Kimanin awanni biyu suka shude, duk da cewa Yerima Abu Sufyan da ahalinshi sun gama cin abincin, sai dai bai ba su izinin aikata komai ba. Rubutu yake yi a diary din nashi har sai da ya cika shi taf, sannan ya mika shiga Shaheed, yardajje kuma amintaccen hadiminsa, wanda ya dauka tamkar aboki a gare shi, kasantuwarshi din ba ma ‘abocin tara abokai ba ne. 
Sallamar waziri da Khalili ce ta saka shidago kanshi daga latsar wayar da yake yi. Yana hada ido da waziriya sadda kan nashikasa, domin shi fa hada ido da mutane ma wani 
babban aikiya dauke shi. Dukawa Waziriya yi Cikin girmamawa, Yace Ranka ya dade, barka da hutawa. Dama mai martaba ne keson ganawa da kai, idan babu 
takura. Domin yaji sakonka cewa ba a nan za ku kwana ba. To baya so kuyi dare ne.” Yerima Abu Sufyan ya saita muryarsa, yace, “Mu na zuwa yanzu. ” Da fadin haka sai Waziriya mike. Yace da Khalili ya tsaya domin yayi musu jagoranci zuwa babban dakin bakin da aka kimtsa masa, inda za su gana da Hafsa. 
Cikin takun nan nashi na kasaita ya mike, Shaheed yabi bayanshi, sai Khalili a gaban su, harsuka isa dakin. Mai martaba Sarki Saniya ba shi izini da ya zauna bisa kujera, amma Yerima ya kekashe ya ce sam ba zai zauna sama ba sai dai kasa. Shi ba haka aka saba musu ba. Babu yadda za a yi sarki a saman kujera shi ma kuma ya hau. Hakan daya yi ba karamin faranta wa Sarki Rai yayi ba mai martaba yace”Mahaifinka ya shaida mini kun yi duk wata magana da shi k0?” Yajinjina kanshi, sannan ya sunkuyar da kan kasa. “To ma sha Allah. Ina fatar babu takura Sufyanu. Ko kadan bana so a yi maka abin da zai zamto ya takura maka. Auren dole ba shi da dadi. Ba zan so a yi maka ba.” Murmushi yayi, “K0 kadan maimartaba.” “To yayi daidai. Khalili a turo mini Hafsa yarlele.” Shiru Yeriman ya dan yi jim, domin shi ba haka suka yida mahaifinsa ba. Sun yi ne kan cewa akwaiyan mata biyu a gidan, za a kawo mishi su duka biyun ya zaba. Kodayake, bari 
dai harya gani tukunna. Bayan minti goma sai ga Hafsa tafe da kuyangu hudu biye da ita. Alkyabbar nan tata naja harkasa, kamshin turare na dakar hancin Yerima Abu Sufyan. Bai k0 dago kansa ya kalle su ba, sai daiyaji matsinta alamun ta zauna bisa kujera. Sosai mamaki ya cika shi. Ta yaya don tana yar sarki za ta zauna a kujera daya da sarki? Bai taba tsammanin hakan na faruwa ba saiyanzu. 
Mai martaba yace “To Hafsa, gaki ga Yerima Abu Sufyan dan babban aminina. Abun kunya ne gare mu a ce dukyadda muke da Sarki Abdurrahmanu na Kubaisu wai yayanmu wasu basu taba ganin junansu ba saiyau. Sai dai komaiya kau, tun da dai ga shi muna shirin hada auratayya a tsakaninku. Ina fatar zaku daidaita kanku. ” Daidaiya mike zai tafi Yerima Abu Sufyan ya daure ya furtso maganar da tun da Sarkin ya ambaci sunan Hafsa kadai yake son fiddo ta. Sai dai kwarjinin sarki Sani yasa ya kasa fadar ta saiyanzu. ‘ Amma…mai martaba, Abba yace mini yan mata biyu ne zan zaba. K0 dai dama guda dayarce?” Yana fadin haka Hafsa ta dago kanta ta kalle shi, gabanta na tsananta duka, fargaba na dada mamaye ta. A cikin sakwanni kadan kuma ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Tuna cewa yar uwar tata mai bakinjini ce. ‘ 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]