FIRGITA SAMARI COMPLETE

FIRGITA SAMARI COMPLETE

 1. FIRGITA SAMARI 
 2. Da sunan  ALLAHMai rahama Mai jin kai
  BABI NA DAYA
  Kano
  Z
  umuxi ne tar a fuskar Yusuf, sam bakinsa ya qi rufuwa, komai na fuskarsa yana nuna farin ciki da jin daxi. A tare da shi kyakkyawar ‘ya ce, budurwa, mai kyakkyawan murmushi, mai suna Harira, suna tafe gwanin sha’awa, sun nufi falon mahaifin Harirar.
  Dole Yusuf ya yi farin ciki, bayan tsaftatacciyar soyayyar da suka kwashe shekaru suna yi da abar qaunarsa Harira, a shekaran-jiya ya aiko da kayan lefe gidansu, to yau kuma gashi an aiko ya zo. Kuma yana kyautata zaton za a gaya masa cewar jibi ko rana ita yau, ko kwanaki goma masu zuwa za a xaura musu aure, ai kuwa murna ta zama dole a gare shi.
  Suna tafe, suna tava hirar qauna, har Harira tana tsokanar sa, tana cewa, “Yanzu a ce an fasa da kai ya za ka yi?”
  Yusuf ya harare ta, “Sai in faxa rijiya.”
  Suka yi dariya, Harira ta ce “Haba dai, sai ka ce wani sokon saurayi ka ce za ka faxa rijiya?”
  Suka qyalqyale da dariya. Yusuf ya ce, “Kin manta na tava ce miki in ba ke ba sai rijiya.”
  Ta yi dariya, “Har ka tuna min wani sususun saurayi, wai don an hana shi auren budurwarsa, kawai sai watarana da rana tsaka ya shiga gidan su budurwar ta shi, ya leqa sai da ya tabbatar yarinyar da iyayenta da ‘yan uwanta suna tsakar gida suna harkokinsu, sannan ya shiga gidan da gudu yana gunji, yana cewa ‘wallahi na gaya miki idan ba ke ba sai rijiya’, yana isa bakin rijiyar gidan ya kama bakin rijiyar ya zura qafafunwan shi, wai shi a dole faxawa zai yi.”
  Suka qyalqyale da dariya.
  Yusuf ya ce “Lallai wannan shi ne Sohoro.”
  Harira ta karva, “Kuma abin da zai ba ka dariya ya san rijiyar fa ba ta da zurfi.”
  Suka isa bakin falon, suka yi sallama, Harira a gaba Yusuf a biye suka shiga falon.
  A cikin falon babu wasu muhimman abubuwa face mahaifin Harira, Alhaji Idi Tsohuwar Dukiya, sai mahaifiyarta mai suna Haule, sai kuma qanwar mahaifinta ita kuma sunanta Rakiya, wadda ake wa laqabi da Rakiya Raka-ni-kashi saboda halinta na sa ido ga al’amuran mutane.
  Bayan su, kuma sai sauran abubuwa masu muhimmanci, wato wasu set xin akwatuna (jakunkunan) kayan lefe guda takwas, maqare da kaya a jere, qarama bisa babba tun daga ta biyu zuwa ta takwas, a can kan ‘yar autar jakunkunan kuma kuxi ne, wato ita qaramar jakar Allah ya taimaketa ba a xora mata nauyi ba, kuxin dubu sittin ne ‘yan Naira dubu-dubu a kanta.
  Sai kuma tsugunne a gefen set xin akwatunan lefen nan, wata akwati ce guda xaya qirar da, wadda ake kira da fantimoti, ita ce dai jallin jal guda xaya da Yusuf ya kawo a matsayin kayan lefensa. Sai kuma dubu bakwai da suka yi goho a bisanta.
  Duk da haka, idan mutum ya nazarci falon a tsanake zai tabbatar da cewa a baya ya karvi tarin kayan alatu da qawa, ma’ana a da akwai kuxi a wurin mai falon, yanzu kuma yana cisgar wahalar duniya.
  Yusuf da Harira sun yi mamakin ganin set xin jakunkunan da kuxin nan na lefe, domin shi Yusuf ji ya yi wani gwanin iya kixa yana buga masa kalangu a qahon zuci, gabansa yana bugun uku-uku.
  A nata ran Harira tunani take, to su kuma waxannan kayan na waye, wa aka kawo wa? A gidan dai ita kaxai ce mace budurwa, yayanta ya daxe da yin aure, kuma ma ko aure zai yi ba shi da kuxin siyen waxannan kayayyaki, kai ba shi da kuxin auren gaba xaya ma, ya ma daxe da barin garin, ba a san inda yake ba, to ko dai Yusuf ne ya yi mata bazata, ya kawo ba ta sani ba?
  Da ta dubi fuskar Yusuf, sai ta tabbatar shi ma mamakin kayan yake yi. Ta yi zugum tana duban shi suka haxa ido, sannan suka dubi iyayen nata, don a gare su za su ji duk wani bayani game da kayan.
  Alhaji Idi ya yiwa Yusuf kallon biyu-banza, sannan ya nuna masa akwatunan ya ce “Me ka gani?”
  Yusuf ya kuma kallon akwatun nan, ya ce “Kaya na gani.” A ransa yana fatan a ce shi aka bai wa.
  Malam Idi ya yi dariya “Kaya ka gani ko dai kayayyaki?”
  Yusuf ya kuma kallon akwatunan tare da fantimotinsa, ya yi magana a hankali, ya ce, “E kayayyaki na gani.”
  “E haka ne, sai dai na ga kana kallo har da wancan fantimotin taka guda, kuma a ciki babu ita nake nufin kayayyakin.” Cewar Alhaji Idi.
  Yusuf ya xago cikin damuwa.
  Haule ta xan sunkuyar da kanta cikin takaici.
  Rakiya ta yi gyaran murya, ta ce “Yaro arziqi muke qoqarin nuna maka, a yayin da ka yi saurin zuwar mana da tsiya, mu kuma dole mu yi qoqarin kakkavewa.”
  Yusuf ya kalle ta, Harira ta kuma shiga damuwa, Haule ta yi murmushin basarwa.
  Suka yi shiru. Alhaji Idi ya qura masa ido, kana ya dubi Rakiya, “Bai fa gane ba, tun da kin san wannan rashin ganewar yana xaya daga cikin dalilin da ya sa ya yayimo fantimoti ya kawo mana, kuma ya ke jiran a wanke zankaxexiyar xiya a ba shi.”
  ”Uhm. To ai sai in yi masa tafsirin farfaru ko.” In ji Rakiya, sannan ta kalli Yusuf ta xora da cewa, “Yaro wannan kayayyakin arziqin da ka gani,” ta nuna setin jakukunan nan, ta ci gaba “Sune kwatankwacin kayayyakin da duk mai son auren Harira zai kawo don ya same ta, to tun da kai ka gaza, an samu wanda zai iya, kuma ya kawo, wato Ayuba.”
  Harira da Yusuf suka yi saurin kallon juna cikin mamaki da razana, saboda jin sunan da Rakiya ta ambata.
  Rakiya ta ci gaba da magana tana kallon fantimotin Yusuf, “Yo wannan fantimotin taka ai ko ni za ka aura ka kawo min ita sai na haxaka da ‘yansanda sun karvar min haqqin raina min wayo da ka yi, ba gwara ka kawo min kwalla ba.”
  Yusuf ya marairace, “Baba wallahi duk qoqarin da zan yi na yi, amma lefen bai wuce wannan da na kawo muku ba, ba ni da su ne.” Ya kalli Alhaji Idi, “Baba har ga Allah ina son Harira, itama tana qaunata, kar ku hana ni ita saboda kayan lefe.”
  Alhaji Idi ya harare shi, ya ce “Wai kai wane irin gauxe ne? Ana nuna maka batu kana wani zance daban. Uban wa ka ke tunanin zai xauki ‘yarsa ya ba ka a wannan lokaci da wannan ‘yan kayan da ka kawo? Yaro ai ko tunkiya za ka siya, musamman tunkiya mai daraja dole ka bayar da kuxaxe masu yawa, ba ‘yan kwabbai ba, xan rainin hankali.”
  Rakiya ta karve, “Ni ina ganin vatawa kanmu lokaci muke yi, da vata baki, wannan cacar baki ce mara amfani, mu da muke da wuqa da nama da kuma haqoran taunawa to me muke jira kuma?”
  Alhaji Idi ya yi ‘yar qaramar dariya mai kama da ta tsuntsu, ya ce “Muna gaya masa laifinsa ne kafin mu gaya masa hukuncin da muka yanke masa.”
  Hawaye ya zubo a idanun Haule, ta yi sauri ta goge don kar Alhaji Idi ko Rakiya su gani, duk da haka Harira ta lura da ita.
  “Kin ga yanzu tun da ya ji laifinsa, sai kuma ya saurari jin hukuncin da aka yanke masa.” Alhaji Idi ya faxa yana kallon Rakiya, sannan ya dubi Yusuf da gefen idanu ya ce, “Yanzu kuma sai ka tashi ka xauki fantimotinka da ‘yan kwabbanka ka ba mu wuri.”
  Hankalin Yusuf ya yi matuqar tashi, ya yi duru-duru, hawaye ya fara fito masa, da ya kalli Harira, sai ya yi sauri ya sunkuyar da kansa qasa, ya kasa magana, hannunsa har rawa yake yi, idan aka raba shi da Harira an yi masa mummunar illa.
  Alhaji Idi ya xaga murya cikin tsawa, “Ko ba ka ji abin da na gaya maka ba ne, ka yi mana zuru?”
  Yusuf ya xago a hankali cikin damuwa, ya ce “A yi haquri Baba….wallahi…”
  Alhaji Idi ya katse shi, “Kar ka sake ka yi min magiya a nan, domin ba zan yi abin da kake faxa ba, wato haquri, ba na yin haquri domin a mafi yawan haquri ana cutar mutum ne…”
  Suka kuma yin shiru, kan Yusuf a durqushe yana tunani, jim kaxan ya nisa, ya ce “To Baba ina neman wata alfarma guda xaya… a yi min afuwa in tafi haka, idan na je gida sai in turo a karva, domin idan na tafi da su a yanzu zan wulaqanta.”
  “Uhm.” Cikin mamaki Alhaji Idi ya buxe baki, ya ce “Lallai yaron nan ba ka da kunya, cewa fa ka yi za ka wulaqanta? To mu da ka kawo mana ashe wulaqantamu ka so ka yi?” Ya yi dariya yana kallon Haule, Haule ta yi saurin xauke kai, ya kalli Rakiya yana nuna musu Yusuf, “Kun ji fa qarara ya fito da sharrinsa a kanmu. To Billahillazi sai ka fita da fantimotin nan yanzu.”
  Kuka ya vallewa Yusuf, har kowa a falon yana ji, Harira ma ta fashe da kuka, ta tashi a guje, ta fita daga falon.
  Yusuf ya ci gaba da kuka yana roqon Alhaji Idi. “Baba ka taimaka min, na amince zan karvi kayana, amma a taimaka min idan na je gida zan aiko a karva…”
  Alhaji Idi ya katse shi, “Au, ba ka ji rantsuwata ba kenan? Ka dage sai ka mayar da mu qananan mutane, to ba ka isa ba.” Ya tashi, ya je wajen fantimotin, ya fincikota ya cilla wa Yusuf a jikinsa.
  Cikin tsautsayi fantimotin ta daki gefen hancin Yusuf, ta fasa masa hanci, sannan itama da ta kai qasa, ta faxi ta fashe, kayan ciki suka zube.
  “Idan ba ka xauka ta lumana ba ai ka xauka ta tsiya. Cewar Rakiya tana kumbura tana batsewa, wai ita a dole ta yi zuciya.
  A hankali Yusuf ya sa hannu ya shafo jinin da ke gefen hancinsa, ya dubi hannunsa ya ga jini, sannan ya zaro hankici ya goge, tare da hawaye, kana a nutsen ya tattara kayan da suka zube ya mayar cikin fantimotin, ya rufe, ya xauki xaurin kuxinsa na lefe da suka yi gefe ya sa a aljihu, ya miqe, ya xan rissina ya ce.
  “Ku yi haquri Baba da jayayyar da na yi muku, na tafi da ita.”
  Rakiya ta yi suruf ta ce “To Allah ya raka taki gona, Allah ya sa mun rabu kenan.”
  Yusuf ya fita. Alhaji Idi ya yi tsaki, Haule ta kawar da kai cikin takaici.
  Da Yusuf ya baro falon Alhaji Yusuf, ya yi fatan kar ya haxu da Harira domin idan suka haxu xin zuciyarsa na iya faso qirjinsa ta fito saboda baqi ciki, a vangare guda kuma zuciyarsa ce ke gaya masa irin cin amana da munafurcin da Ayuba ya yi masa, lallai Ayuba ya kai qarshe wajen munafurci da cin amana.
  “Ayuba shi ne mutum guda xaya da na yarda da shi, kuma na xauka a matsayin tsanin gina soyayyata da Harira. Ganin sa a matsayin xan uwanta kuma ya nuna min alamar zai taimake ni a soyayyar, na gaya masa dukkanin sirrukan soyayyata da Harira, ya zamo abokin shawarata, a kowanne fanni da ya shafi soyayyarmu. Ya zamo…..”
  Tunaninsa ya katse a lokacin da ya yi karo da Ayuba bai sani ba har suka bangaji juna, fantimotin hannunsa ta suvuce ta faxi qasa, ta qarasa rabe wa biyu, kayan ciki suka zube. Yusuf ya yi sauri ya kalli da wanda suka yi karon bai sani ba, ya yi idon huxu da Ayuba.
  Ran Yusuf a vace, ya fasa tsugunnawa don kwashe kayan ya xago suka kalli juna sosai. Ayuba bai yi magana ba, sai raba idanu yake yi, Yusuf ya ce.
  “Yanzu Ayuba abin da za ka yi min kenan? Yanzu kana tunanin…”
  Ayuba ya yi saurin dakatar da shi, “Kar ka tsawaita zancenka na san ranka a vace yake. Ka kwantar da hankalinka, na yi maka haka ne saboda na fi ka sanin darajar Harira. Ba doguwar soyayya ba ce sanin darajar mace ba, haxa mata kavakin lefe shi ne sanin darajarta. Yaushe za ka xauko wata fantimoti ka kawo a matsayin lefen Harira da wasu ‘yan ku…”
  Yusuf ya xaga hannu zai mare shi, Ayuba ya yi sauri ya ce.
  “Kul! Ka sa hannu a fuskata. Ka yiwa kanka kiyamullaihi, ka tattala ‘yan kuxinka ko ka riqi na liqe wannan fantimotin taka, kar ka je ka baiwa ‘yansanda a banza, domin kana marina ka mari dubu biyar…”
  Hawaye ya xigo a fuskar Yusuf, yana huci, Ayuba ya wuce shi. Sai da ya bi Ayuba da kallo, sannan ya dubi fantimotinsa, ta gama rabe wa biyu ta fashe sosai, sannan ya dubi kayan lefen da suka zube. Ya jinjina kai cikin takaici, durqusawa ya yi, ya sa gefen rigarsa ya tattaresu, ya tashi, ya tafi, ya bar fantimotin a nan. Har ya kusa barin wajen, sai ya yi wani tunani, ya dawo, ya sa hannu, ya xauki fantimotinsa ya tafi.
  *
  Haule da ke tsaye a can gefen kujerun falon, ta share hawayenta, tana kallon ‘yar tata cikin damuwa da tausayawa.
  “Haquri za ki yi ki daina wannan kukan, Harira.”
  Alhaji Idi ya kalleta ya yi tsaki, a inda yake zaune yana da tazara da Harirar, ya ce “Ai ni jira nake ta gama, ta ba ni labari ko ta ji cewa mu iyayenta mun kusa mutuwa ne take ta wannan kukan.”
  Haule ta matso kusa da ita, ta zauna, ta ce “Kukan me ki ke yi ne.” Ita kanta da ta faxi maganar ta san dalilin da ya sa take kukan, kawai qarfin hali ta yi, ta tambayeta.
  Harira ta yi qoqarin sassauta kukan domin samu damar bayar da amsa, ta dubi mahaifiyar tata ta ce, “Mama….Abba wallahi ina son….Yusuf, shima kuma yana sona, idan aka rabamu zamu fuskanci matsala…..”
  Alhaji Idi ya yi dariyar takaici, ya ce “Yaro dai yaro ne. Ai idan haka ne, mu mun fi ki sanin kina cikin matsala, tun lokacin da na fahimci kina wani abu wai shi so ga matsiyaci, na tabbatar kin shiga cikin matsala, dole sai mun tashi tsaye. Kuma da ki ke cewa yana sonki, ai sai ki gaya mana tsakaninmu da muka kawoki duniya muka tufatar da ke muka shayar da ciyar da ke da shi da ya ganki a raye da girmanki wanne ya fi son ki?”
  Ya zura mata idanu kamar na uwar mujiya.
  Harira ta ci gaba da kuka, ta kasa buxe baki bare ta yi magana.
  “Ke nake tambaya. Idan kuma ba amsa, sai ki vace min da gani kar in mauje miki wannan tsigalallen baki naki, mara kunya.”
  Harira ta fashe da kuka, ta tashi a guje, ta bar wajen. Alhaji Idi ya yi tsaki, “Ja’ira mara kunya, ba da zamani wannan ta isa ta zo min da wannan magana.” Ya yi qwafa.
  Tana zuwa cikin xakinta, ta faxa kan motsattsiyar katifarta, ta ci gaba da kuka, zuwa wani lokaci kuma ta fara tunani.
  Watarana da ta wuce
  Yusuf da Harira suna zaune suna hira. A tsarinsu, ba sa daxewa a yayin hirarsu, domin ba su iya yawan maganganun nan na masoyan zamani masu cike da qarya ba, sukan faxin muhimman kalamai ne su yi sallama.
  Harira ta ce “Haba ai yanzu muna zamanin da ke cike da wayewa da ci gaba, su kansu iyayen sun fi yarda da so da qauna kafin giftawar wani abu a yayin aure, don haka ka kwantar da hankalinka, ba na zaton iyayena za su zama cikas a soyayyarmu.”
  Yusuf ya yi murmushi, “Wannan shi ne kyakkyawan fatana.”
  Suka tsahirta da hirarsu kafin daga bisani Yusuf ya xora da cewa, “Idan da ina da arziqin duniya, zan iya bada sama da rabin shi don in mallake shi, rabin mu zauna mu ci tare da ke Harira da ‘ya’yan da za ki haifa mana.”
  Harira ta yi fari da idanu cikin jin daxi, ta ce “Na  daxe da fahimtar hakan daga gareka.”
  Suka yi shiru, lokacin da Yusuf ya yunqura domin ci gaba da magana, a lokacin Ayuba ya iso wurin, yana murmushi ya yi musu sallama, suka amsa, ya miqa wa Yusuf hannu suka gaisa, da zai wuce yana dariya ya ce da Yusuf.
  “Yusuf Allah ya sa mu a danshinku.”
  Yusuf ya yi dariya ya ce “Amin.”
  Harira ta yi ajiyar zuciya da ta yi wannan tunani, a ranta ta ce “Lallai xan adam butulu ne.”
  Irin wannan tunani da Harira ta yi, shi Yusuf ya yi, a tare ma suka gama tunanin. Yusuf ya yi ajiyar zuciya, ya dubi hoton Harira da ke gaban shi, a kwarmin idonsa akwai qwalla ta nadama. A ransa ya ce “Ashe manufar Ayuba kenan da ya ce Allah ya samu a danshinku. Ya yi nufin ya cutar damu, Allah ya isa, Allah ya bi min haqqina.”
  *
  Yadda Haule ta rungume xiyarta Harira, zai nuna maka cewar akwai tsantsar soyayya ta ‘ya da uwa. Sun xan jima a haka kafin a tsanake Harira ta zare jikinta, ta dubeta.
  “Umma, ina matuqar mamakin yadda ki ke yin biyayya ga Abba a yayin da ya ke qoqarin yanke duk irin waxannan hukuncin a kaina, sanin kanki ne za ku cutar da ni. Umma me na yi muku ne?”
  Haule ta yi sauri ta rufe mata baki, tana cewa “Na gaya miki ba na son irin wannan magana…” muryarta ta karye, kuka ya nemi qwace mata.
  Harira ta miqe ta dubi mahaifiyarta sosai, “Umma ina neman ki yi min gafara, na san ‘ya’ya suna bijirewa iyayensu musamman a lamuran da suka shafi irin wannan, a yanzu ba bijire muku zan yi ba, amma tsarin da ku ka xauka a cikin lamarina akwai abubuwan da suka cushe min qwaqwalwa, waxanda idan har ban samu warwarewar su ba, to babu yadda zan yi dole zan saki zuciyata, ta sarrafa ni yadda take so, ba mamaki har in kai ga sava muku ba tare dana so ba.
  “Umma tsarin Abba ba a kan hanya ya ke ba, kuxi da son rai sun fi tasiri a ciki. Ke kuma kina xauke da wani lamari da dole ina buqatar saninsa, a ganina kamar dole aka yi miki, kamar kina cikin xaurin talala ne, shi ya sa ki ka kasa goyon bayana. Umma….”
  “Ke saurara, ba na son wannan magana.” Haule ta dakatar da ita, kuma ta kasa yin magana, sai hawaye, ta yi sauri ta miqe, ta juyawa Harira baya, ta isa bakin tagar xakin ta tsaya.
  Harira ta juya a hankali ta nufi qofar fita daga xakin. Har ta je qofar fita, sai ta ji mahaifiyar tata tana kiran sunanta.
  “Kar ki fita.” Cewar Haule.
  Harira ta tsaya, amma ba ta juyo ba, kuma ba ta ci  gaba da tafiya ba.
  “Cewa na yi kar ki fita.” Haule ta nanata.
  “Ban fita ba Umma.”
  “To dawo ki zauna.” Ta umarce ta.
  Harira ta dawo inda take ta zauna, ta kawar da kanta gefe tana kallon wani waje daban.
  Haule ta share hawayen fuskarta, sannan ta dubeta.
  “Ni baiwa ce a gidan nan Harira!” Cewar Haule.
  Cikin hanzari Harira ta xago kai ta dubi mahaifiyarta, me take nufi da wannan magana? Ta kasa magana, ta bi ta da kallo kawai tana sauraron ta ci gaba.
  Haule ta ci gaba da magana, “Tun da kina son ki ji dalilin da ya sa ba na goyon bayanki, nake biye wa mahaifinki to zan gaya miki, ko kya yi min adalci a cikin lamarinki.”
  Harira ta xan motsa, ta kasa yin komai.
  Haule ta xora. “Lokacin ina budurwa, ina da samari masu yawa, a ciki akwai waxanda suke da burin su aureni, to amma mahaifina ya gindaya sharuxxan yadda lefena zai kasance ga duk wanda zai aureni, lefen kuma ba  na wasa ba. To hakan ya sa da yawa suka gudu suka bar ni, waxanda ma suke da qoqarin ganin sun samo abin da ya kamata a matsayin lefen sun yi, amma bai kai yadda mahaifina yake buqata ba.
  “Hakan ya sa na rasa duk wani saurayi da ya dace ya aureni. Na ci gaba da zama a haka, ba karatu ba aure, har shekaruna suka ja, na zama abin da wani marubuci yake cewa kisan boko ko ace kwantan gida. Kuma mahaifina ya qi sassautowa daga ra’ayinsa, har zuwa lokacin da mahaifinki Idi ya zo da kuxinsa, ya sa ya sayeni….”
  Ta yi shiru. Sannan ta girgiza kai, “Sayena ya yi kamar yadda na ji shi da mahaifina suna tsadance wa da shi. Mahaifina yana nuna masa ya yi tsufa, don haka zai ba da kuxi da lefe kamar yadda tun farko ya faxa. Idi ya amince da hakan, kuma shima sai da ya shimfixa sharuxxansa. A qarshe har wajena ya zo ya ke gaya min, yana cewa “Na riga na saya na biya, don haka sai abin da na ce, idan ki ka kauce wa faxata to za ki fuskanci wulaqanci, domin ina matuqar qawance da wulaqanci, sai ki bi ni a hankali. Abin da na ce a yi shi za a yi, abin da na ce kar a yi, to ba za a yi shi ba, ba ki da ra’ayi ba ki da ‘yanci…
  “Wannan fa ya faru ne tun kafin a yi auren. Kuma babu yadda zan yi, dole na bi, kamar yadda mahaifina ya tabbatar sayar da ni ya yi, haka ni ma na yarda sayar da ni aka yi. Kafin haka, daman shi mahaifinmu ba wai son haihuwar ‘ya’ya mata yake yi ba, mu ma da muka rayu a matsayin ‘ya’yansa, mun rayu ne bisa qudirar Ubangiji, ba wai don son ransa ba, don haka dole na karvi wannan hukunci da ya yi min, ina mai miqa lamarina ga Allah domin na sami sassauci…”
  Ita da Harira kuka suke yi a yanzu.
  “Don haka kamar yadda ki ka gani, duk wani abu da ki ka yana faruwa a gidan nan, da duk wani wulaqanci ko bauta, to suna faruwa ne tun farko a bisa doron yadda aka gina shi kamar yadda na gaya miki. Ba zan qi ba ki shawara ba, ki yi qoqari ki lallava lamarin da ki ka samu kanki kuma ki ci gaba da addu’a, ki saurari abin da zai faru, amma na san dole ko kin qi ko kin so ki yi abin da ya faxa, kin ma yi sa’a ke yana xan sonki…”
  Suka yi shiru tsawon lokaci, sannan Harira ta nisa, tana kuka tana cewa “Yanzu Umma a haka ki ke rayuwa, lokuta da dama kina voye min halin quncin da ki ke ciki, rayuwar rashin ‘yanci da qunci?”
  Girgiza kai kawai Haule ta yi. Harira ta miqe a hankali, ta je ta rungume mahaifiyarta tana cewa “Umma ki ci gaba da yi min addu’a.”
  “Ba zan daina yi miki addu’a ba har in mutu Harira.” Cewar Haule yayin da ta kuma rungume Harira suka ci gaba da kukansu.
  *
  Suna tsaye, sun yi shiru cikin damuwa, Yusuf ne da Harira, ita Harirar har da qwalla a idonta.
  Da muryar kuka take magana, “Yusuf ka sani ba sau xaya ba, ba sau biyu ba irin wannan ta sha faruwa samari su ce sun tafi don nemo kuxin aurensu, amma shi kenan sun tafi kenan ba sa dawowa….”
  Yusuf ya katse ta. “Haba Harira, idan duk samarin duniyar nan suna gudu su bar ‘yanmatansu, ni ba zan iya guduwa in bar ki ba. Ba ni da wata hanya,  ba ni da komai, ba ni da abin da nake yi na aiki, dole ne sai na fita na samo kuxin aurenki….”
  Ta katse shi ita ma, “Kawai dai kana nuna min dole ne sai ka gudu ka bar ni. Me ka ke zato muna cikin wannan hali ka ce za ka tafi? Wato ka xauki halin quncin da ka ke ciki ka haxa da wanda nake ciki ka jibga a kaina, ka bar ni in mutu kenan. Shin ka manta ne idan ka tafi, kamar ka bayar da damar da za a ce shi kenan ma, ya gudu ba?”
  Yusuf ya kalleta “Me ki ke faxa ne haka Harira?”
  “Ina faxar abin da za ka haifar, za ka tafi ka bar ni maimakon ka tsaya mu magance matsalar.”
  “Ta ya ya ki ke zaton anan zamu tsaya mu gyara matsalar? Anan xin a ina ki ke zaton zamu samu maganinta? Bayan kin san kuxi ne matsalar.” Ya xan tsahirta kafin ya ci gaba “Haquri kawai za ki yi Harira amma ba zan iya zama ba sai na bar garin nan na nemo dukiyar aurenki…”
  Harira ta dakatar da shi, “Idan har son da kake yi min na gaske ne, to  ban  yarda da wannan tafiyar ba, ka tsaya kawai mu tunkari matsalar mu magance ta.”
  Yusuf ya girgiza kai ya ce “Babu wata dama ta magance matsalar a nan, da ya wuce tafiyar da zan yi.”
  Harira ta fashe da kuka “Na fahimci inda ka sa gaba, na lura ka zare soyayyata daga ranka Yusuf…”
  “Ko kaxan ban yi hakan ba, kuma ba zan tava yi ba.”
  “To idan ba ka yi ba, nuna min a zahiri ka fasa tafiyar da za ka yi?” Ta ce da shi.
  Ya girgiza kai “Ba zan fasa ba, domin zaman ba zai magance ba. Ko kaxan so bai zama makanta a wurina Harira ba zai rufe min idanu na kasa gane mafita da inda maganin matsalar yake ba.”
  “Haka ka ce? Wannan ya tabbatar min da zargin da…” Ba ta iya ida maganar ba, ta fashe da kuka tare da juyawa da gudu ta nufi cikin gida.
  Yusuf yana kiranta amma ba ta saurare shi ba. Ya tsaya nan yana kallonta har ta shige, sannan ya yi ajiyar zuciya, a yanzu ya ji tausayinta ya lulluve shi sosai, ya dace ace ya bita ta lalama, ya kwantar mata da hankali, bai kamata shima don ransa ya vaci ya yi mata ta ‘yan maza ba, kawai sai  ya ji qwalla a idon shi, ya yi saurin gogewa. “Yanzu me ya kamata na yi?” Ya tambayi kan shi. “Kamata ya yi na aika a kirawota, don na ba ta kwantar mata da hankali ta fahimce ni.”
  Sau biyu ya aika, amma ta ce ba za ta fito ba. Yusuf ya buga qafa, qwallar da ta maqale a kwarmin idanunsa ta fito. Ya juya a hankali, ya tafi.
  A cikin gidan su Harira, Harira ta haxa kai da bango tana ta kukan nadama.
                                                        Bayan Sati Daya
  ‘Yan kwanakin da ba su fi cikin tafin hannu ba, duk Harira ta sauya, abubuwa da yawa sun tarar mata, takaici da qunci da nadama har sun kusa illatata. Ta yi yin duniyar nan domin ta yakice wani vangare na soyayyar Yusuf amma abin ya gagara. A xaya vangaren kuma ga takaici da baqin cikin da kusan kullum Ayuba ke cusa mata wai lallai sai ta so shi, wani lokacin ya zo mata da wai lallai sai ya juyata yadda yake so, a cewarsa tun da ya bayar da lefe da sadaki to fa kamar ya mallaketa ne.
  Dole Harira ta yi ta tunanin mafita, kuma ta samo hanyar da take ganin ita ce mafitar, ta hanyar zuwa wajen Kakarta Iya Atu ta sanar da ita halin da take ciki.
  Allah ya taimaki Harira, Iya Atu ta tausaya mata, kuma ta fahimceta, ta damu da halin da take ciki, ta sha alwashin samo mata ‘yanci.
  Washegarin ranar da Harira ta je wajen Iya Atu, Iya Atun ta iso gidan, tana zaune a bisa kujera, haka nan Alhaji Idi da Haule sune zaune suma a sauran kujerun, Harira kuwa a tsugunne a ledar falon da ta kokkoxe, wani waje kuma ya yayyage.
  Idanun duka ukun su yi wuri-wuri, idanun Harira kuwa sun yi hawaye. Yadda Iya Atu ke faxa a matsayin wadda ta isa ta yi faxan, haka Alhaji Idi ya ke mayar da martani, alhalin shi ake yiwa faxan.
  “Wato qarata ta kai wajenki ma?” Alhaji Idi ya ce.
  “To ban isa ta kawo qarar taka wajena ba ne, kake faxar wannan magana?”
  “Kin isa mana, amma ni ina magana ne a kan…..”
  “A kan me? Maganar banza kake, bari ka ji in gaya maka, ko ka qi, ko ka so, yarinyar nan ba za ka yi mata dole ba…”
  Cikin fushi Alhaji Idi ya miqe tsaye, “Iya wannan ba huruminki ba ne, hurumi ne na ni da ‘yata, ina da iko a kanta fiye da ke, don haka na riga na yanke hukuncin abin da zan yi…”
  Mamaki da takaici suka mamayi Iya Atu, haka Haule da Harira. A fusace Iya Atu ta miqe itama, ta fara faxa.
  “Na yarda ka fi ni iko da hurumi a kan ‘yarka Harira, za ka iya yi mata duk abin da ka so, to amma ina fatan ba ka manta da cewa nima ina da iko da hurumi mai qarfi a kanka a matsayinka na xana ba, don haka abin da nake buqata shi ne ka aura wa Harira wanda take so…”
  Alhaji Idi ya girgiza kai, ya dubi mahaifiyarsa, “Abin da ki ke so kenan Iya?”
  Iya Atu ta amsa, “E, abin da nake buqata kenan.”
  “To shi kenan na yarda, amma a bisa sharaxin, dole ne yaron sai ya kawo fiye da abin da Ayuba ya kawo na kayan aure, kuma nan da wata xaya da kwanaki ashirin, wato kwana hamsin kenan, domin shi ne daidai lokacin da na yanke na yi mata aure, idan ya yi haka zan bi umarninki, idan bai yi ba kuma dole in yi abin da na so….”
  Ya kaxa kai ya yi waje, ya bar su tsaye cike da takaici da mamaki. Wancan ta kalli wancan, babu wanda ya iya yin magana a cikinsu.
  *
  Yusuf ya kalli Harira, ya ce “Kin ga wannan shi ne abin da nake gaya miki, yanzu sharaxin da mahaifinki ya gindaya miki ya nuna sai na je na nemo kuxi.”
  Harira dai ta kasa magana, tun da ta gaya masa sharaxin da mahaifinta ya gindaya mata kafin ya amince da aurensu, ta yi shiru.
  “Ki kwantar da hankalinki, inda za ni ina da ido a wurin, abokina ne wanda muka yi karatu da shi, ya samu kuxi sosai, shi ya ce in je. Kin ga idan Allah ya taimakemu, sai ya ba ni duk abin da nake so, idan ya so daga baya na koma ya ba ni aikin ko ya ba ni jari.”
  Ta ji daxin abin da ya ce, amma ba ta yi magana ba.
  Yusuf ya xora da cewa “Yanzu kin ga tun da haka ne, zan tafi a wannan sati dama na gama shiri….”
  Har yanzu dai ba ta yi magana ba, ita gani take idan ya tafi kamar sun rabu kenan, sun rasa juna har abada.
  Yusuf ya yi shiru yana nazarinta, yana ji a ransa lallai idan ya rasa Harira, to ya rasa wani vangare na rayuwarsa da ya tabbatar zai yi mummunar jinya.
  Har suka rabu Harira ta kasa cewa komai, sai kuka take yi. Tabbas asarar masoyi babu daxi, ba kowacce zuciya ba ce za ta iya jurar haka ba.


  BABI NA BIYU
  ENUGU
  M
  otar da ke xauke da su Yusuf sai sharara gudu take a kan hanyar su ta zuwa Enugu, irin doguwar motar nan ce mai suna luxurious, masu barci na yi, masu surutu na yi, haka waxanda suka yi shiru kamar irin su Yusuf suna kallon yanayin hanya suma suna yi.
  Saboda irin azababben gudun da direban motar yake yi, da tsattsayawa a inda ya kamata a tsaya a hanya ko da tashohi, kafin awoyin da ya kamata su kwashe a hanya su cika sai ga su a cikin garin Enugu, sannu a hankali har suka isa  babbar tashar mota ta kasuwar Ogbete.
  Sale Aliyu Sale shi ne abokin Yusuf, wanda suka yi karatu, ba wata abota ce mai qarfi ba, amma dai sun san juna, kuma da yake shi Salen yana da zumunta, duk lokacin da ya ziyarci jihar Kano sai ya kaiwa abokansa ziyara, ciki har da shi Yusuf xin, a nan ne suka yi musanyar lambobin waya, har kuma ta kai dalili ya yi da Yusuf xin ya tafi gare shi don neman kuxi.
  Kamar yadda Sale ya gayawa Yusuf, idan ya sauka a tashar kusa da kasuwar Ogbete shagunansa ba su da nisa da kasuwar, da ya tambayi Sale & Sons Investment, za a nuna masa, don haka Yusuf bai damu da cewa zai sha wahala ba yayin zuwansa gare shi.
  Da motar ta tsaya, kusan a tare fasinjoji suka fara fitowa, waxanda suke barci aka tattashe su. Shi kam Yusuf bai yi wata rintsawar kirki ba, musamman a matsayinsa na baqo yana so ya ga hanya ya ga gari.
  Wani garjejen Inyamuri ne a gaban shi mai tsinannen surutun tsiya, shi ya fara sauka, sannan Yusuf ya biyo bayan shi, yana kallon yanayin garin. Tashar dai ta yi masa kama da tashar Sabongari da ke jihar Kano, yanayinta da mutanen cikinta, domin qabilu ne iri-iri, Ibo, Hausa, Yoruba da sauran qabilu. Haka nan yadda ake layin motoci irin na kowacce tasha ta motoci, haka suma tashar take.
  A hankali, Yusuf ya isa wurin wasu motoci zungura-zungura, yana yi yana ‘yan kalle-kalle saboda neman inda zai je ya yi fitsari. A can gefe guda na tashar ya lura ana yin fitsarin, domin ya hango wani tsaye yana callara fitsari yana fito.
  Yusuf ya sami wani yaro Ibo mai sayar da ruwan fiyawata, ya saya, ya nufi wurin, ya je gefe ya tsugunna yana fitsari, daga can gefensa wani Ibo ne sanye da hula hana-sallah a tsaye yana fitsari yana kallonsa. Yusuf ya lura da kallon da yake yi masa, amma bai damu da shi ba, domin kamar yadda yake yi masa kallon baqo, haka shima yake yi masa.
  Wata jaka da ke ajiye kuma voye a qarqashin xaya daga cikin zungura-zunguran motocin daf da inda Yusuf ya yi fitsari ita ta ja hankalinsa, don haka bayan ya gama fitsarin, ya nufi inda take ba tare da tsoro ba, ya tsaya daf da ita, yana kallon gefe da gefe, ko zai hango mai ita, amma bai ga kowa ba, kuma bai ga alamun kowa ba.
  Ya yi jim kamar wanda aka baiwa gadinta, yana dube-dube, ko tarko aka yi da ita, sam babu alamun haka, kamar yadda ya lura. Kusan mintuna ashirin ya yi tsaye yana kallon jakar amma babu abin da yake tunani, kawai sai ya yi qunar baqin wake ya je, ya jawota daga qarqashin motar. Yana gama fito da ita, sai ga wasu xirka-xirkan Inyamurai su biyu xaya a gaba, xaya a baya sun nufo inda Yusuf yake a guje, kuma dukkaninsu sun yi gumi idanunsu jajur.
  Yusuf ya yi wulli da jakar ya faxi gefe guda, yana cewar “Hasbunallahu”. Inyamuran nan suna zuwa, na gaba ya taka qafar Yusuf ya wuce, shima na bayan yana zuwa ya tsallake shi ya bi na gaban suka wuce Yusuf nan kwance. Wasu mutane kamar bakwai da suke bin su, suka zo suka wuce ta gaban Yusuf.
  Ashe Inyamuran nan faxa suke yi, na gaban ya naushi na bayan ya gudu, shi ne na bayan ya biyo shi, ‘yan kallo suma suka bi su don ganin yadda za ta kaya, dukkaninsu babu wanda ya san da wani Yusuf, bare sanin me yake yi.
  Yana kwance ya yi ajiyar zuciya, ya gama kallonsu, bayan sun vace daga wurin, sannan ya dubi inda xayan ya taka shi a ransa ya ce “Allah ya isa.” Cikin hanzari ya dubi inda jakar nan ta faxi, ya je ya xaukota, ya yi sauri ya koma bayan wata mota ya lave yana huci.
  Sai da ya yi nazari wurin da yake sosai, ya gamsu babu wanda yake kallonsa, ko ya damu da shi, sannan ya zuge zif xin jakar ya leqa cikinta. Numfashinsa ne ya xauke, ya yi mutuwar tsaye. A ransa ya ce “Wayyo Allah.”
  Kuxi ne gamin gambizar Naira dubu-dubu na Nijeriya da Dalolin Amurka damqar a cikin jakar. Zuruf ya zuge zif xin jakar, ya yi ajiyar zuciya.
  “Allah mai iko ashe cewa aka yi in zo nan in xauki abin da ya kawo ni in koma.” Ya ji wani vangare na zuciyarsa yana faxa masa.
  Ya yi shiru yana raba idanu, yana sauraron tunanin zuciyarsa. Take ya tuna ya kamata fa ya je ya  yi sallah. To a lokacin kuma wani vangare na daban na zuciyar nasa yake ba shi shawarar cewa wannan kuxin ba na shi ba ne, ya nemi mai su ya ba shi.
  Ya yi ajiyar zuciya, “To ai ko ba nawa ba ne, ba ni su aka yi domin in koma gida in biya kuxin lefen Harira, in kuma gina kaina, in yi arziqi.” Ya ji wani vangare na zuciyarsa na raya masa.
  Ya goge gumin da ya karyo masa, “Tabbas duk irin son da nake yiwa waxannan kuxi ba nawa ba ne, zan iya zuwa in shiga mota, in koma gida, in biya buqatata da su hankali kwance, babu wanda ya ganni, to amma akwai mai ganin kowa ko da a cikin qasa kake, kuma zai nunawa mai kuxin ni na tsinta ban yi cigiya ba, na cinyesu, wato Allah. Ya ya kenan? Ba mafita face in nemi mai su in ba shi abin sa, tunda ba nawa ba ne, idan ya so Allah ya ba ni nawa na halak…”
  Gumi mai xumi ya ci gaba da karyo masa, ya fara dube-dube a cikin tashar. Daga bisani ya nufi wajen wasu da ya lura ma’aikatan tashar ne.
  *
  Dabarar da Yusuf ya yi wajen neman mai jakar nan ta sa ya yi ta nema ba a sami mai ita ba, da ace fitowa ya yi kai tsaye ya nuna kuxi ne ya tsinta, da tuni an samu waxanda suka ce nasu ne, ko kuma waxanda suka qwace, amma sai ya yi dabara ya ce jaka ya tsinta ta tsummokarai, mai kama kaza, ya voye waccan ta ainihin a cikin wasu tarin tayoyi na tashar.
  Wani ma’aikacin tashar ma dariya ya yi masa, xaya ne ya taimaka masa suka yi cigiyar. Da suka gama ba su sami mai ita ba, sai ya ba shi shawarar ya je ya kai ofishin ‘yansanda, ya kwatanta masa inda yake.
  Abin da Yusuf bai sani ba, asalin jakar wani xanfashi ne ya satota, kuma yana cikin motar da ta isa tashar kafin motar su Yusuf xin ta iso. Suna zuwa tashar sai ya lura ashe wasu mutane suna bin sa tun daga Kano, ya yi zaton ma’aikatan tsaro ne, don haka ya jefar da jakar a tashar ya gudu, suka bi shi. Ashe suma ‘yanfashi ne kamar shi, sun biyo shi ne don yin fashin jakar.
  Yusuf ya isa ofishin ‘yansandan, ya sami CRO (Charge Room Officer), ya ja shi gefe, xan qabilar Yoruba ne, mai suna Kayode. Ciki Turanci suka yi magana.
  Yusuf ya dube shi sosai, ya ce “Yallavai tsintuwa na yi kuma na rasa mai ita.”
  Insp. Kayode ya dubi Yusuf, “Me ka tsinta?”
  Yusuf ya xora jakar a gabansa, ya buxe ta. Idanun Insp. Kayode suka firfito, ya ce “Yeee, da gaske ko wani abu ka voye a qasansu.”
  Yusuf ya miqa masa, ya ce “Bankaxa ka gani idan wani abu na voye?”
  Insp. Kayode ya ture hannunsa, ya ce “Ba sai na bankaxa ba, rufe ta. Biyoni.” Da suka juya za su tafi, Insp. Kayode ya dubi wani xansanda mai muqamin kofur ya ce “Kofur Waaka ina zuwa.” Ya wuce zuwa wani xaki da ke cikin ofishin, Yusuf yana biye da shi.
  Bayan da Insp. Kayode ya zauna, sannan ya nunawa Yusuf wuri “Zauna.”
  Yusuf ya zauna, suka nutsu.
  “Zan yi maka tambayoyi kafin in xauki bayanin ka (statement)”
  “Ina sauraronka.” Cewar Yusuf.
  Insp. Kayode ya jawo dirowa, ya fito da biro da takarda, ya ajiye a gabansa, sannan ya kuma duban Yusuf, “So nake ka gaya min yadda ka tsinci kuxin, da kuma dalilinka na kawo su domin a nemi mai su a ba shi? Kuma gaskiya nake so ka gaya min.”
  Yusuf ya yi qaramin murmushi ya ce, “Saboda ba nawa ba ne, shi ya sa na kawo a nemi mai su a ba shi. Ni kuma baqo ne, yau na fara zuwa Enugu.”
  Ya kwashe labarin dalilin zuwansa da kuma yadda ya tsinci jakar ya gaya wa Insp. Kayode. Sannan ya xora da gaya masa ainihin inda ya zo a Enugu.
  Sai da Insp. Kayode ya daxe yana kallon Yusuf, sannan ya ci gaba rubuce-rubuce a xan littafin, yana kuma tambayarsa wasu abubuwa har ya gama, a qarshe ya kuma dubansa.
  “Ni ma nan da ka ganni Musulmi ne, haqiqa na yi matuqar mamakinka, ba kowanne mutum ba ne a wannan zamani zai iya abin da ka yi ba.” Ya dubi jakar, sannan ya ci gaba da cewa “Zan yi matuqar qoqarin ganin an nemi mai ita, ka ga ko nan xin da ka kawo jakar, kana bayar da baya ta zama babu, domin za a yi wasosonta ne, amma saboda irin halin da ka nuna zan yi qoqari iya iyawata, nima in gwada imani irin naka.”
  Ya tura masa takarda “Sa min lambar wayarka a qarqashin sunanka, idan da hali da adireshin gidanka na can Kanon.”
  Yusuf ya karva ya rubuta, sannan ya tura masa shi ma.
  Insp. Kayode ya duba, sannan ya xauki takardar ya ninke, ya sa a aljihu, ya miqe, ya xauki jakar ya buxe wata dirowa, ya sa a ciki, ya rufeta da mukulli, kana ya kalli Yusuf da yake zaune har yanzu.
  “Zo mu je.”
  Yusuf ya tashi ya bi bayansa suka fita zuwa kan kanta.
  Insp. Kayode ne ya sa wani sajen ya raka Yusuf inda ya zo nema, wato wajen Sale.
  KANO
  Ayuba ya kamo hannun Harira ya fincikota har sai da ta haxu da jikin shi, sannan ya bi ta da kallo.
  “Ni nake yi miki magana ki ke neman ki shige gida?”
  Ran Harira ya yi mugun vaci, fincikota da ya yi har sai da hannunta ya amsa, ta ji zafi, ta kalle shi cikin tsana, ta ce “Kai xin wane ne da zan tsaya da kai. Ka sakeni tun kafin ranka ya vaci.”
  Ran nasa ya fara vaci, “Ba ki isa ki yi min wulaqanci ba Harira, na biya abin da duk wani mai ikirarin yana sonki ya kasa biya, abin da na biya daidai yake da na saye ki, don haka ki shiga hankalinki, domin ke xin mallakata ce, kamar yadda zan sayi akuya in yi iko da ita babu wanda ya isa ya hanani, haka kike a wurina, ina da iko da ke…”
  “Ba ka isa ba, idan ma qaramin hankalinka abin da yake raya maka kenan, to ka yi kuskure…”
  Ya yi kamar zai mareta, ta fincike hannunta za ta gudu, ya yi sauri ya kuma riqota, riqo sosai.
  “Harira ki bi ni hankali, domin wallahi kina barazana ne da zaman lafiyar cikin gidanku, kar ki ga na jirkinta miki, kawai qyaleki na yi amma ba wai don jira ko qa’idar da aka ba matsiyacin masoyin naki na jirkinta miki ba, kawai don raxin kaina na yi haka, amma idan ki ka kai ni bango to za ki ga wulaqanci. Kuma bari in gaya miki wani abu da ba ki sani ba, na yi miki xaurin talala ne, domin na tabbatar matsiyacin naki ba zai tava iya samo sama da abin da na kawo miki ba, don haka ki zauna da shirin ranar cikar qa’idar, misalin qarfi takwas na dare za ki farar fuskantar wulaqancina, kuma zan nuna miki ni wane ne, sai kin yi nadama…”
  “Sai dai kai ka yi nadama, jahili!” Ran Harira a vace ta faxa wa Ayuba haka.
  Ya yi dariya, haqoransa guda biyu da suka wantare, xaya ya yi gabas xaya ya nufi yamma suka bayyana, ya ce “Madalla, a ranar za ki ga jahilci, don zan nuna miki shi.”
  “Allah ya yi min tsari da kai.” Ta faxa, yayin da ta yi sa’ar qwacewa ta yi cikin gida da gudu.
  Ayuba ya yi tsaye yana wangame baki a tunaninsa murmushi yake yi.
  ENUGU
  Sale da Yusuf zaune a xan qaramin wurin cin abincin, suna cin abinci. Teburin shaqe yake da abinci da lemuka iri-iri.
  Yusuf dai ya tarar da Sale fiye da yadda yake zaton shi, domin ya yi arziqi sosai, motocin hawa kusan tara, ban da motocin jigilar kaya. Kamfanin na Sale abubuwa da dama suke sayarwa, suna sayar da kayan wuta, irin su talabijin da firji da sauransu. Sannan akwai shagunan da suke sayar da dardumu da kafet-kafet, sannan ga waxanda suke sayar da kayan gini irin su tile, da kuma chrome da sauransu. A ransa ya tabbatar zai sami masharar hawayensa tun da dai shi Salen ne ya ce ya zo, to yana da tabbatar faruwar abin da ya dace.
  Sale ya dubi Yusuf, “Yawanci mutanenmu gani suke ba za su iya yin kasuwanci a cikin sauran qabilu ba, alhalin kasuwancin ma ya fi daxi da su, duk ana tare kuma ‘yan uwan juna ne, qasarmu xaya.”
  Yusuf ya ajiye kofin da ke hannunsa ya ce “Ai qasar tamu ce an lalata mana ita, masu rainon namu Turawa, sun rene mu tare da gurvatamu yadda ba zamu zauna qalau ba, sannan shugabanninmu sun ci gaba da tayasu mummunan aikin da suka xora mu a kan shi, shi ya sa.”
  Sale ya ce “Haka ne, amma in ban da haka ai da tuni mun manta da ci baya, mun ci gaba.”
  Suka yi shiru, suna cin abinci. Jim kaxan Sale ya numfasa.
  “Ka qi ka gaya min maqasudin abin da ke damunka, ka san ni tun a makaranta ina fahimtar cewa mutum yana cikin wani hali na damuwa ko na farin ciki.”
  “Zan gaya maka amma sai mun gama cin abinci.” Cewar Yusuf.
  Sale ya yi dariya, “Ka manta tattaunawa da samo mafita da jin daxin zance ya fi armashi idan ana cin abinci ba?”
  “Haka ne.” In ji Yusuf. Ya xauko ruwa ya kurva, sannan ya dubi gefensa, ya tabbatar babu wani a kusa da su, sannan ya kalli Sale.
  “Dalili xaya ne ya kawo ni, wanda ya haifi wani dalilin. Zan yi aure ba ni da kuxin auren, xan abin da na bayar aka nemi wulaqanta ni aka dawo min da su. Sannan kuma daman ina buqatar aikin yi.”
  Sale ya yi dariya, ya ce “Kai mu dai akwai mu da son yin aure Hausawa.”
  “Aure sunna ce, kuma dacewa ne.” In ji Yusuf.
  Sale ya girgiza kai, “Gaskiya, nima tsokanarka na yi, kuma aure shi ne mafita, domin sauran qabilun da ba sa yin auren da wuri kullum cikin aikata zina suke da yiwa mata fyaxe. Shi jima’i babu wata halitta ta jinsi da ba ta son yi, don haka hanya mafi dacewa ita ce a yi bisa tsari na addini da dalili, wato aure.”
  “A to.” Yusuf ya ce da shi. “To ka ji dalilin zuwana.”
  Sale ya nisa yana murmushi. Suka ci gaba da cin abincin, suna tunani, kowa da abin da yake tunani a ransa. Kafin daga bisani Sale ya katse tunanin.
  “Za ka iya yin harkokin kasuwanci a nan?” ya tambayi Yusuf.
  Yusuf ya yi ajiyar zuciya ya ce “Me zai hana, kai ba ga ka kana yi ba. Amma idan zavina ne, ni kifin rijiya ne na fi son zama a gida, wato a jihata.”
  Sale ya yi dariya, “Haka ne, kowa da ra’ayinsa, amma ni ka ga na fi son fita wasu jihohin ko qasashe in kasuwanci na.”
  Suka kuma yin shiru. Kafin Sale ya ce.
  “To yanzu dai kafin a je ga na biyun wato yin sana’a, bari mu fara gama na farko, wato kuxin aure. Tabbas ban ji daxin wannan butulci da suka yi maka ba, ba don harkokina ba da na bi ka Kano na ga wane ne uban wannan yarinya.” Ya xan yi shiru, “Ba zan iya zuwa ba saboda harkoki, amma duk abin da ya kamata in baka zan ba ka na harkar auren nan, sai ka ninka abin da shi abokin takarar naka ya kawo sau uku.”
  Yusuf ya dube shi da mamaki, ya buxe baki kawai.
  “Kar ka damu, fiye da haka ma zan iya ba ka. Sannan idan aka yi komai aka gama, ka nutsu, akwai shagunanmu a can Sabongari da Kasuwar Kurmi za ka karvi xaya, domin akwai xaya yaron ya fara fita Dubai, yana nema ya yi mana wasa da wurin, mun ce ya samo wani har yanzu shiru.”
  Yusuf kasa magana ya yi da wuri, sai daga baya ya samun bakin cewa “Na gode Sale, Sale Allah ya saka da alkairi.”
  “Kar ka damu ka cancanci fiye da haka, kana da kirki da mutunci Yusuf ba ka da matsala a halayya. Yi addu’a Allah ya shige mana gaba.”
  Yusuf ya xaga hannu sama ya fara addu’a, Sale yana cewa amin.
  *
  “Wa zan kira a waya ya haxani da Harira?” Yusuf ya tambayi kansa a zuciyarsa. Tun da Sale ya yi masa alqawari, ya ji duk duniyar babu wanda ya ke so ya gayawa domin farin ciki sai Harira, to amma ba ta da waya, haka ma mahaifiyarta ba ta da wayar, domin duk Alhaji Idi ya hana su riqe wayar, har gwara-gwara Haule, wani jiqon yakan bar ta ta saya da kuxinta, idan rikicinsa ya tashi, ya qwace ya sayar.
  Yana nan zaune yana ta tunani, har zuwa daga baya tunaninsa ya zaga ya zagayo, ya faxo kan abokinsa da suke layi xaya, wato Jafar. Tabbas Jafar zai taimaka masa ya yi magana da masoyiyarsa.
  Ya yi sauri ya lalubo lambar Jafar xin, ya danna kira, ya kara a kunne, ‘yan sakanni sai damuwa ta bayyana a fuskarsa, saboda gaya masa da wayar ke yi cewa waccan wayar ta Jafar xin a kashe take. Ya yi tsaki, yana duban fuskar wayar.
  Dole ya kuma yin tunanin wanda zai kira don ya yi masa wannan taimako, amma ya rasa.
  Sai bayan awa xaya da mintuna kusan arba’in da takwas sannan Allah ya taimaki Yusuf ya sami lambar wayar Jafar xin a buxe, a cikin waxancan lokacin ya yi kiran wayar ya fi a qirga, duk a tunaninsa za ta shiga. Ba ta shiga ba sai yanzu.
  “Hello Yusi ta samu kenan?” cewar Jafar a lokacin da ya xaga wayar daga nasa vangaren.
  Yusuf ya yi murmushi ya ce “E, ta samu amma daga vangarena ba daga naka ba.”
  Jafar ya yi dariya ya ce “To ya aka yi ne, na san dai da magana, rabon da ka kirani a waya, har na manta.”
  “E, ka san ai ba kuxi ake sawa wayar ba, wannan ma dalili ta yi aka kira ka.” Cewar Yusuf.
  “Na sani.” Jafar ya faxa, “Kai nake sauraro.”
  Yusuf ya gyara zama yana murmushi, ya ce “Jafar wani taimako nake so ka yi min. Ina so don Allah ka je gidansu Harira, idan ka kirata kun haxu ka yi min filashin sai in kira, domin ina son yin magana da ita. Ka san ita ba ta da waya…”
  “Harira? Ta ya ya kenan?” Jafar ya buqata cikin mamaki.
  “E kamar dai yadda na gaya maka.” Yusuf ya amsa masa.
  “To ka manta halin mahaifinta ne Yusuf. Ka manta wulaqancinsa? Kana ganin zai bari a yi haka?….”
  Yusuf ya yi sauri ya ce “Ina sa ran in sha Allahu ba matsala ai qoqari za ka yi ka je lokacin da ka tabbatar ba ya gida.”
  Suka xan yi shiru.
  “Hello Jafar kana ji na…” Yusuf ya ce.
  Jafar ya amsa “Ina jinka, xan tunani nake yi.” Ya yi ajiyar zuciya, “Amma dai kar ka damu, zan yi qoqarin yin hakan. Ina fatan dai kamar yadda ka ce ta samu, ta samu xin, domin ba ma son ka rasa Harira abokina.”
  Yusuf ya yi dariya, ya ce “In sha Allahu ba zan tava rasata ba, ku ci gaba da tayani addu’a, abin da aka fito nema sun samu.”
  “Alhamdulillahi, Allah ya shige mana gaba, zan qoqarta.”
  *
  Jafar yana nan rave a qofar gidansu Harira, ya gota mintuna talatin, har ya fara saduda, sai ga ta ta fito. Ya yi sauri ya gyara tsayuwarsa da xan damuwa a fuskarsa.
  Harira ta qaraso gare shi, ranta a vace yake, ta yi masa sallama, sannan ta gaishe shi, ta yi shiru.
  Jafar ya dubeta ya ce “An hana ki fitowa ko?”
  Harira ta gyaxa kai, “E, da qyar mahaifiyata ta bar ni na fito.”
  Ya yi ajiyar zuciya, “Daman Yusuf ne yake so ya yi magana da ke, shi ne ya ce idan na zo na kiraki, in ki ka zo in kira shi a waya ko in yi masa filashin zai kira, sai ku yi magana.”
  Harira ta wangale baki cikin murna da farin ciki tana kallon Jafar.
  “Allah sarki Yusuf xina…”
  “Yusuf xin ubanki, me kike yi anan?” Alhaji Idi ya daka mata tsawa, yana tsaye daf da ita.
  Hankalin Harira ya yi matuqar tashi ta razana, Jafar ma ya yi matuqar tsorata, ya ja da baya.
  Alhaji Idi ya dube shi a wulaqance, yana magana da kausasshiyar murya ya ce da shi “Kai kuma xan tsito me ka zo yi gidan nan, mene ne haxinka da Harira?”
  Jafar ya dubi Harira, sannan ya kalli Alhaji Idi, bakinsa yana rawa ya ce “Ba komai…”
  “Ba komai? Varawo ne kai kenan.” Cewar Alhaji Idi yayin da ya tsattsara Jafar da idanu.
  Jafar ya kuma tsorata, yana rawar murya ya ce “Wallahi ni ba varawo ba ne Alhaji…..”
  “To me ya kawoka wajenta, yanzun nan zan sa ‘yansanda su kulle min kai, kuma wallahi sai ka wulaqanta.”
  Idan akwai abin da Jafar ya fi tsana a rayuwarsa da tsoro shi ne a haxa shi da xansanda, ya qi jinin wannan lamari. Abin da ya yi tunani kenan tun da farko, sai da ya gayawa Yusuf daman, ga shi abin da ya jawo masa. Ya fara matse-matsen idanu.
  Harira ta yi sauri ta dubi mahaifinta ta ce “Abba, Ayuba ne ya aiko shi wajena, shi ne ya ke gaya min.”
  Yanayin Alhaji Idi ya xan sauya, ya kuma kallon Jafar tun daga qasa zuwa sama, sannan ya dubi Harira ya girgiza kai, ya ce “Kar ki wuce minti goma.” Ya wuce ya bar su a nan.
  Jafar ne ya fara yin ajiyar zuciya, sannan Harira. Da ta lura Jafar ya haxa gumi ta so ta yi dariya, sai kuma ta dake.
  Cikin hanzari Jafar ya dubeta, kamar zai yi magana sai ya fasa. Ya duba wayarsa, ya nemo lambar Yusuf ya kira, ya kara a kunne da ta yi qara alamun ta shiga sai ya kashe, bai fi sakan uku da kashewar ba, dama shi Yusuf jira yake, kawai sai ya kira. Wayar tana fara qara, Jafar ya miqa wa Harira, ya ce “Sai ki yi sauri.”
  Harira ta karva, ta xauka, ta kara a kunne. “Salamu alaikum sahibi.” Suka fara gaisawa, suna gama gaisawa Ayuba ya qaraso wurin, ko sallama babu.
  Harira ta razana, Jafar da Ayuba suka yi kallon-kallo. Ayuba ya fara magana cikin kaushin murya, “Kai kuma fa, wa ya kawoka nan?”
  Jafar ya kalle shi a wulaqance, “Abin da bai shafeka ba na zo yi.”
  Ayuba ya fusata, “Ka san me kake faxa kuwa? Ka san wace ce a gabanka?” Ya dubi Harira wadda ke tsaye da waya a kunne ta yi sakato cikin razana.
  “Da wa ki ke waya?” Ayuba ya tambayeta.
  “Malam wannan fa ba huruminka ba ne, ina ruwanka.” Cewar Jafar.
  “Kai kar fa ka kawo min wasa, yanzun nan ranka zai vaci….” Ayuba ya ce da Jafar.
  “Kai xin banza…”
  Suka yi kan juna kamar za su yi faxa, Harira ta yi sauri ta shiga tsakaninsu, ta miqa wa Jafar wayar, tana cewa “Yi haquri, don Allah kar ku yi faxa.”
  Ayuba yana huci, Jafar yana huci, Harira a tsakiya cikin matuqar damuwa.
  “Ina fatan kun gama.” Jafar ya tambayi Harira.
  Ta girgiza kai, “Na gode qwarai. Je ka ba matsala.”
  Jafar ya yi qwafa, ya juya ya tafi. Ayuba ya yi kamar ya bi shi, amma Harira ta yi tsaye a gabansa, idan zai yi bi shi sai dai ya tureta.
  *
  Alhaji Idi ya harari Harira sosai, ya cije baki ya ce “Allah ya kaimu ranar Litinin xin, ki sani idan bai zo ba, to a ranar Talata zan xaura miki aure, ba Iya ba ko wa ki ka je ki ka gayawa, ba zan fasa ba wallahi.”
  Harira ta razana da abin da mahaifinta ya ce, amma dai tana ciki farin ciki ta tabbatar dai tun da Yusuf ya ce mata zai zo gidansu ranar Litinin xin ya kawo kayan aurenta, to zai zo.
  Hatta Haule sai da ta damu da abin da mijinta ya faxa, duk da ba wannan ba ne karo na farko da ya sha lafto magana a tsaye haka ba mutunci bare kara a ciki, amma wannan ya sha alwashin mahaifiyarsa ma ba ta isa ta hana shi abin da ya nufi yi ba, to me ya taka?
  Harira tana nan tsugunne tana ta tunani, a ranta ta ji wani xan abu ya xarsu, tana tunanin idan aka samu matsala fa, ya ya za ta yi? Me ya sa ba ta yi shiru ba kawai sai dai a gan shi, kuma ga hukuncin da ya yanke…
  “Me kuma ki ke jira ki ka yi min zaune?” Alhaji Idi ya katse mata tunani.
  Ta kasa motsawa. Ya daka mata tsawa. “Tashi ki ba ni wuri, ba na son ganin wannan munafukar fuskar taki.”
  Sum-sum Harira ta tashi, ta xan dubi mahaifiyarta, sannan ta fice daga falon.
  Haule ma tashi ta yi ta bi bayanta, Alhaji Idi ya bi ta da kallo cikin tsana, yana tsaki.
  Mintuna biyu da fitar su Rakiya raka-ni-kashi ta shigo falon, ba ta iya yin sallamar Musulunci ba sai dai ta gargajiya, ta ce “Gafaran ku dai.”
  *
  A farfajiyar gidan Alhaji Idi, Harira ce tsaye cikin damuwa, tana tunanin abin da zai faru idan aka sami kuskure. Sannan kuma tana tunanin yadda za ta sadu da Jafar, domin ta kira Yusuf, ta jaddada masa kar fa a samu matsala ranar Litinin xin, domin samun matsalar yana nuna tsinka igiyoyin soyayyarsu ne da na aurensu tun kafin a yi.
  Duk ta haxa gumi, tana tunanin qaryar da za ta yi, domin ta samu damar fita daga gidan.
  Ayuba ya qaraso inda take, a yanzu yana sanye da wasu kaya jajaye kamar xan sama-jannati. Ganin shi ya sa Harira ta tsaya tana kallonsa, shima kallonta yake.
  “Ke kanki ba kya farin ciki, don kin san me zai faru.”
  “Me zai faru?”
  Ya yi dariya ya ce “A, kin san cewa Yusuf ba zai iya kawo abin da aka nema ranar Litinin ba, da alama ma shi ya tafi kenan?”
  “Me ka ke nufi?” Harira ta tambaye shi.
  “Abin da na faxa shi nake nufi.” Ya amsa mata.
  Ranta ya vaci, ta kalle shi cikin xacin rai, ta ce “To aniyarka da mugun nufinka ya bi ka.”
  Ya qyalqyale da dariya, “Idan dai a kan Yusuf ne, babu wani mugun nufi sai kyakkyawa nufi. Bari ki ji Harira in yi miki ta babban mahaukaci…”
  Ta katse shi “Irinka ba.”
  “E, na ji. Ki kirawo ni koma me ki ke so. Amma ki sani idan ma Yusuf ya dawo, ba zai iya zuwa da sama da abin da na ba da na kuxin aurenki ba, idan kuma ya zo da su wannan gari, zan sa a raba shi da su. Ina fatan kin fahimta. Don haka dama kin cire wani batun Yusuf, tun da na dirko cikin rayuwarki kuma na kutsa na shiga tsakiya, to zance ya qare, sai dai haquri…”
  Ya girgiza mata kai, ya juya, ya barta nan inda take.
  Harira ji ta yi kamar ta bi shi ta maqure don baqin ciki, da ya bar wurin sai ta yi baya ta jingina da bango ta fashe da kuka.


  BABI NA UKU
  W
  annan karon qaramar mota, hayis mai xaukar fasinjoji bakwai Yusuf ya hau, wato uku a baya, uku a tsakiya xaya a gaba. Sai kuma karen mota.
  A bayan motar inda Yusuf ya zauna akwai wasu mata ‘yan qabilar Ibo su biyu, wadda take zaune a jikin Yusuf sunanta Amaka da ‘yarta mai suna Helen a hannu wadda take ta barci abin ta, xayar kuwa sunanta Ndidi, ita kuma tana xauke da jakarta a hannu.
  Shima Yusuf xin yana xauke da jakarsa a gabansa, a cikin jakar akwai kuxaxen da abokinsa Sale ya ba shi, ban da na mota dake aljihunsa.
  Fasinjojin da ke tsakiyar motar kuwa, wani xan qabilar Ibira ne da matansa guda biyu sun sa shi a tsakiya. Sai gaban motar inda shi kuma xan gwari ne, akwai wasu tsagu taya-taya a fuskarsa.
  Su Amaka da Ndidi suna xan tava hira, alamu suna nuna ko kaxan Amaka ba ta so ace a kusa da Yusuf suke zaune ba, yadda ta ke ta tsaki, tana ta wani jajjanye jikinta, don ma dai shi Yusuf xin nutsattse ne, babu ruwan shi da su.
  Shi ma xan Ibira sai hirarsa suke da matansa. Yusuf kuwa ya yi shiru yana tunani, dukkanin hankalinsa ya yi gida, yana tunanin yadda zai je wa Harira da irin wannan farin ciki, a ransa yana tunanin abin da zai yiwa Ayuba domin ya huce rashin mutunci da cin amanar da ya yi masa.
  Wani vangare na zuciyarsa, ya gargaxe shi da yin haka, yana mai ce masa “Haba Yusuf, bai kamata ka koma ta kan wani Ayuba ba, tun da dai Allah ya taimakeka ka samo abin da kake buqata ai shi kenan.”
  Ya yi ajiyar zuciya, ya gamsu da wannan tunani, don haka ya yi murmushi.
  Direban motar ya kuma sakin motar suka qara gudu, daman shi Yusuf abin da yake so kenan, da zai iya yin tsuntsuwa ma da tun daga Enugu tsuntsuwar ya yi ya je gaban masoyiyarsa da abin alkairin da ya samo.
  Da suka nausa sosai, masu yin hira suka yi shiru, wasu suka fara xan rintsawa, wasu kuma suka shiga kalle-kalle. Yusuf yana cikin masu xan duba yanayin hanya.
  *
  A can cikin gidan Alhaji Idi, Harira a tsaye a cikin xakinta, ta qurawa madubi idanu, kwalliya take son ta yi, kwalliya don farin ciki da jin daxin yau abin qaunarta Yusuf zai dawo, tana so ta yi masa tarba ta musamman,  amma haka kawai sai ta ji gabanta yana faxuwa.
  Ta jima tana nazarin kanta, tana kuma sauraron qwaqwalwarta, domin ta gaya mata mene ne dalilin jin faxuwar gaban, na murna ne ko kuma na mene ne? Idan mutum yana cikin farin ciki yana jin faxuwar gaba kenan?
  Ta rasa amsoshin waxannan tambayoyi nata. Ta yi ajiyar zuciya, ta xauko man shafawa domin ta fara shafa.
  *
  Motar da ke xauke da su Yusuf ta qara gudu sosai, tafiya babu kama hannun yaro. Tun Yusuf yana gamsuwa da gudun har ya koma yana jin haushin yadda direban nan yake ta sheqa gudu kamar baya son ransa.
  Sannu a hankali sai ga shi direban yana rage gudun, har ya daidaita tafiya daidai yadda hankalin kowa zai xauka, a haka suka ci gaba da tafiya, a nutse, kuma tafiyar ta fi daxi, waxanda suka yi shiru, suka ci gaba da hirar su.
  Daga baya ne Yusuf ya fahimci dalilin da ya sa direban ya yi ta gudu ba qaqqautawa, ya ji ne daga hirar da direban suke yi da fasinjan da ke gaban motar. Ashe dajin ne cike yake da ‘yanfashi, suna yin gudun ne saboda tsoron kar su haxu da su.
  Amaka da Ndidi suka ci gaba da hirar su, cikin yarensu na Ibo suna ta zagin Yusuf, suna danganta shi da baragurbi a qasa. Yusuf baya jin Ibo, don haka hirar ba ta dame shi ba, duk da shi ne dalilin hirar ta su.
  Amaka da yi tsaki, “Na tsani mutanen nan Hausawa, kawai dai ina zaune ne a Kano daidai da ace in zauna a wuta. Duk wani rikici da rashin ci gaban qasar nan su suke jawo mana. Shi ya sa ki ka ga ba na iya yin sati biyu sai na je qauyenmu.”
  Ndidi ta xan vata rai, “Har yanzu Amaka kina cikin wannan halin naki, ya kamata ki saki jiki ki fahimci mutanen nan Hausawa, tun da kina cikinsu, za ki fahimci cewa vata gari da jahilan cikinsu su suke haxa rikice-rikicen da ki ke faxa…”
  “Sace mana kuxi a qasar nan fa?” Amaka ta tambayi Ndidi.
  Ndidi ta yi qwafa, “To kuma su kaxai ne kawai a cikin gwamnatocin qasar? Ya kamata ki lura, shugabannin qasar ai ba Hausawa kaxai ba ne, kowanne vangare akwai su a ciki, idan su Hausawa sun sace kuxi, su ragowar ina suka kai kuxin. Idan Hausawan sun kasa kawo wa qasar nan ci gaba, su ragowar fa?”
  “Haba Ndidi, kar ki manta fa su suka fi kowa mulkar mu?” Cewar Amaka.
  “E, haka ne. To amma iya sune kawai suke mulkin? Kar ki manta fa, idan shugaban qasa Bahaushe ne, to mataimakinsa ko shugaban majalisar dattijai ai ba Hausawa ba ne, haka sauran madafan iko, ba zai tava yiwuwa a ce su ne mafi rinjaye ba….ki duba ki gani mana…”
  Amaka ta katse ta, “Ba fa wani abu da za ki yi ki wanke su, wai ke ko don kina da saurayi Bahaushe shi ya sa ki ke son su?”
  “Ko kaxan, ni dai ina fatan mu fahimci junanmu, idan abu yana faruwa, ko ya faru mu san mene ne dalilin faruwarsa, me ya haddasa shi, kar mu yi son ransa, wanda shi yake rufe mana idanu, ya sa mu yi hukuncin da a kullum yake hanamu fahimtar cutarmu bare mu yi maganinta…” Ndidi ta faxa, tana girgiza kai.
  “Ai kuma sai ki yi…” in ji Amaka “Amma ni da su na gaya miki sai dai su saya in sayar musu, amma wani abu da ya shafi mutunci da salama babu su.”
  Ndidi ta yi dariyar takaici, “To ai kamata ya yi ki zauna a qauyenku ki nemi kuxin a can.”
  Helen da take barci kamar matacciya, ta farka, ta callara kuka. Amaka ta yi sauri ta shiga lallashinta, ta cusa mata mama a baki, yarinyar ta shiga cancanxa, Amaka tana shafa mata kai cikin lallashi.
  Helen ta daxe tana shan nonon, kafin ta qoshi, ta saki. Sai kuma ta fara wasa. Ndidi ta miqa hannu ta yi mata wasa, ta yi qoqarin ta xauketa, amma da yake Helen akwai ta da tsinanniyar qiwa sai ta qi zuwa wajenta, ta kawar da kanta, don kar ta xauketa.
  Idanun Helen ya kai ga Yusuf, ta kalle shi, ta kalli hular zitar da ke kansa, ta yi murmushi, sai ta fara qoqarin kai hannu cikin wasa domin ta tava hular, hannunta bai kai ba, sai kuma ta fara miqa hannu domin ta je wajensa ya xauketa.
  Yusuf ya lura da haka, sai ya yi murmushi ya fara yi mata wasa, yana da son yara, yadda ya ga Helen tana yi masa murmushi sai ya ji yana son ya xauketa ya yi mata wasa, ya miqa hannu kamar yadda itama  ta miqo don ya xauketa, cikin zafin nama Amaka ta doke hannun nasa, ta shiga masifa da cin mutunci. A wannan lokacin tana haxawa da xan guntun Turancinta da Hausa, domin Yusuf xin ya ji abin da take faxa.
  “Wa za ka xauka? Kai xin banza, Hausa ka xaukar min ‘yata, Allah ya kiyaye, tir jaki kawai, akuya…”
  Yusuf ya tsaya cikin mamaki yana kallon Amaka. Ndidi kuwa ta kawar da kai saboda takaici.
  Ta ci gaba da la’antar Yusuf. Ko kaxan Yusuf bai ga dalilin da ya sa za ta yi masa irin wannan cin kashi da wulaqanci ba, sannan kuma bai ga dalilin da zai tanka mata ba, domin yin hakan kamar shima ya zama ita kenan.
  Maimakon ya tanka mata xin, sai kawai ya ba ta haquri cikin Turanci, sannan ya yi shiru abinsa.
  Ndidi ta kalli Amaka, ta ce “Kin gani, kina ci wa mutum mutunci amma shi ya ba ki haquri.”
  “A banza ai. Ni fa na gaya miki Ndidi, ni da waxannan mutanen gaba ce ta qarshen ruhi…”
  Ndidi ta yi tsaki, ta ce “To Allah ya kyauta.”
  Tafiya sannu-sannu kwana nesa, suna wuce garuruwa da qauyuka, sai ga su, sun iso jihar Kano, Yusuf ji ya yi kamar an yaye masa dukkan baqin cikin da ya tava samun rayuwarsa a ciki, ya ji wani sanyi a ransa. Tun da ya ga an sa ‘Barka da Zuwa Kano’ ya ji fari tas a ransa.
  Suka ci gaba da wuce qauyuka da wasu qananan hukumomi na qauyukan Kano, domin isa cikin birnin Kano. Suna cikin tafiya, sun isa qauyen qarshe wanda daga shi sai unguwanni da qananan hukumomin da ke cikin birnin Kano, kawai direban su bai ankara ba, sai ganin wata qatuwar mota Shorido ya yi a gabansa, ba tare da shiri ba, kawai sai ya xauke kan motar, a lokacin wurin taka birki sai ya take totur xin motar, motar ta yi wata irin qara mai tsanani, ta rufta, ta je ta doki wasu bishiyoyi da ke tsaye su biyu.
  Motar ta hantsila, ta yi adungure, ban da qarar motar za ka jiyo ihu daga cikin motar, sannan kuma sai kalmar Inna Lillahi da Hasbunallahu daga bakin Yusuf, sai kuma kalmar Jesus-Jesus.
  Motar ta yi kaca-kaca, ta watso fasinjoji uku, xan Ibira da matarsa guda xaya da Ndidi, ragowar kuma suna cikin motar. Dukkanin waxanda motar ta watso sun mutu, haka nan a cikin motar ragowar sun mutu, sai mutune uku da ba su mutu ba, akwai direban motar, wanda ya yi ta kicin-kicin ya fito daga motar, yana fitowa ya ruga da gudu ya nitsa daji a susuce.
  Yusuf da ya ji mummunan rauni a ko’ina na jikinsa, wani vangare na motar ya danne masa qafa. Amaka da Ndidi sun mutu, amma a cikin motar a kan cinyar Amaka, Helen ce tana ta callara kuka jini yana fita daga bakinta.
  Duk da halin da yake ciki, Yusuf ya kalleta cikin tausayi, yana ta qoqarin ture qarfen motar da ya danne shi, ya kasa.
  Illahirin wurin babu jama’a, sai xaixaikun motocin da suke wucewa, su kuma tun da aka yi hatsarin wani mai Honda ne ya wuce, shi kuma bai tsaya ba. Ganin haka ya sa mai motar da ya haddasa musu hatsarin ya gudu abin sa.
  Yusuf yana cikin wannan hali, ya lura da wani vangare na motar ya fara kamawa da wuta, hankalinsa ya yi mugun tashi, cikin hanzari ya dubi Helen, tausayinta ya kuma kama shi, ya ci gaba da addu’a, ya dage tun qarfinsa ya ture qarfen, ya mirgina gefe, ya yunqura domin ya tashi sai ya ji ya kasa, wannan ne ya tsorata shi, ya yi tunanin ko karyewa ya yi.
  A qwaqwalwarsa ya ji kukan Helen yana qaruwa, idanunsa kuma suka hango masa wutar nan na kuma ruruwa. Ya sake qoqarin yunqurawa, wani mugun raxaxi ya karaxe jikinsa, amma a haka ya qoqarta, ya tashi, yana jan qafarsa ta hagu ya isa cikin motar nan, ya sa hannu ya xauko Helen, ya juya da qyar ya bar wurin motar, ya koma can gefe ya faxi shi da Helen.
  Faxuwarsa ta yi daidai da kamawar motar da wuta gaba xaya. Shi kuma ya suma. Wasu manoma da mutanen gari da ke can nesa da wurin suka iso a guje da suka hango tashin wuta domin kawo agaji.
  Ba su damu da Yusuf da ke gefe ba, sai da suka yi qoqari suka kashe wutar da ke cin motar da qasa. Sannan wasu daga ciki suka isa wajen Yusuf suna duba shi.
  “Ai babu wanda ya yi rai a cikin motar, ina jin sai wancan mutum da ‘yarsa.” Cewar wani dattijo, yana nuna Yusuf da ke rungume da Helen, a tsammaninsa Helen ‘yar Yusuf ce.
  Wanda yake gayawa xin ya ce “Ina jin qoqari ya yi ya fice da ‘yarsa…”
  Mutane masu tausayi suna kuka, wasu kuma suna dube-dube a cikin motar da wajenta.
  ‘Yansanda ba su qaraso wajen ba sai bayan wajen mintuna hamsin, su kuma mutanen wajen sun kasa yin komai, face sun lulluve gawarwakin da ganyayyaki.
  Da suka zo, suka kwashe gawarwakin da Yusuf da Helen suka tafi asibiti da su.
  A asibiti bayan Yusuf ya farfaxo, ya ji cewar ashe tsagewar qashi ya yi, sai kuma muggan raunukan da ya ji a jikinsa, da buguwa. Haka ita kuwa Helen buguwa ta yi, da kuma gigita irin ta yara. Likitoci suka duba su, suka yi musu magani, suka kwantar da su.
  *
  Misalin qarfe tara da mintuna arba’in na daren, Harira tana zaune a tsakar xakinta, idanunta sun qeqashe saboda kuka da ta sha, tun yamma take kukan, kuma tun lokacin gabanta yake faxuwa.
  Da yamman mahaifinta Alhaji Idi ya gaya mata cewar Yusuf bai zo ba, don haka ta zauna da shirinta.
  Ita kanta ta san shi kenan tata ta qare, domin tabbas Yusuf xin bai zo ba, kuma babu abin da za ta yi da ya wuce ta yi kuka, har zuciyarta ta gaji ta mutu.
  Tana nan zaune, ta jiyo an shigo xakin, a tsammaninta mahaifiyarta ce ta shigo, domin ko xaga kai ba ta yi ba, bare ta ga wane ne ya shigo xin, sai da aka zo daf da ita, aka daka mata tsawa, sannan ta fahimci wane ne ya shigo, wato mahaifita Alhaji Idi.
  A sanyaye amma a razane ta xago ta dube shi, ta miqe tsaye.
  Alhaji ya dubeta a wulaqance, ya ce “Da ki ka tashi ina za ki je kuma?”
  Ba ta yi magana ba, ta koma ta durqusa.
  Ya yi dariya, “Kamar yadda na gaya miki mayataccen mutumin naki ba zai zo ba, domin ba zai iya biyan kuxi aurenki ba, to ga shi ta tabbata, don haka sai ki shirya, gobe idan Allah ya kai mu qarfe tara zan xaura miki aure da Ayuba, domin yanzu haka daga duk inda ya kamata in je nake, kuma mun gama komai har da liman…”
  Ya juya, ya nufi qofar fita. Cikin hanzari Harira ta tari gabansa, ta faxa kan qafarsa tana roqonsa. “Abba don Allah ka yi min rai, wallahi ba na son Ayuba, ba na qaunarsa, ka qara yi min jinkiri…”
  Alhaji Idi ya xagota a hankali kamar abin kirki, sai da ya tabbatar ta gama xagowa, sannan ya sheqa mata mari a hagu da daman kuncinanta, sannan ya yi mata varin makauniya, sai da ta faxi qasa magashiyan, sannan ya durqusa a gabanta.
  “Wallahi ko da za ki mutu ba zan fasa xaura miki aure a gobe da na faxa ba. Kuma wallahi ko da Iya za ta sake dawowa ta hana ni, ba zan hanu ba sai na yi miki wannan auren. Don haka sai ki shiga taitayinki. Babban abin farin ciki na a rayuwa shi ne ace ma ban aurar da ke ba, da zan iya wallahi da na je na jefar da ke na huta, ina ma ki bar min gida da na huta tun tuni.” Ya shureta da qafa, sannan ya fice.
  Harira ta fashe da wani sassanyan kuka na takaici, zuciyarta ta yi mata zafi, wane uba ne yake yiwa ‘yarsa haka idan ba ubanta ba? Wane mahaifi ne bai damu da farin cikin ‘yarsa ba, idan ba mahaifinta ba? Tsananin tsanar Ayuba ta ji a ranta, ta ji matuqar xaci a ranta.
  Wacce mafita gareta yanzu? Ta ci gaba da kukan tana tunani. A qarshe ta gamsu da hukuncin da zuciyarta ta yanke mata. Kawai ta gudu ta bar gidan nan, gidan da ya zame mata kurkuku, gidan da take fuskantar tsana da wulaqanci, ji ta yi kamar Alhaji Idi ba mahaifinta ba ne. Idan mahaifinta ne me ya sa yake yi mata waxannan wulaqanci?
  Ta tuno labarin da mahaifiyarta ta ba ta na yadda mahaifinta ya aureta, “wannan shi ne dalili” ta ce a ranta, don haka ba ta ga dalilin zamanta ba.
  Haka ta qoqarta, ta tashi, ta gyara jikinta, ta xauki mayafinta, ta fice daga xakin, tana dube-dube ta fice daga gidan.
  Lokacin da Harira ta yi nisa da gidansu, sha xayan dare ta gota, tana tafe ita kanta ba ta san inda za ta je ba, ba ta san inda ta nufa ba. Ta yi doguwar tafiya mai yawa, wadda ita kanta ba ta san ta yi wannan tafiyar ba, amma dai ta ji a jikinta ta gaji sosai, duk da tana tunanin ta sami wuri ta zauna domin hutawa amma sai ta qi yin haka saboda qoqarinta na barin ilahirin unguwarsu.
  Tana cikin tafiyar, inda take nufa xin wasu samari ne  su uku ke nufowa gareta, dukkaninsu a cikin maye suke, sun sha giya, sai dai ba sa nuna alamun buguwa sosai a tare da su, saboda sai da suka xan nutsu, sannan suka taso suka taho.
  Katsam! Sai ta gan su a gabanta, cikin hanzari ta yi gefe, suma cikin sauri suka yi kanta, suka sa ta a tsakiya.
  Xaya mai siffar raqumi saboda tsayinsa, ya kalleta yana gwale idanu, ya ce “To ina kuma za ki je?”
  Harira ba ta yi magana ba, ta ci gaba da qoqarin kauce musu.
  “Babu wata hanya fa yarinya, da ma tsayawa ki ka yi, ki ka amsa tambayoyi.” Shi xin dai mai siffar raqumin shi ya yi maganar.
  “Ka ga Tahir, ba fa ma yin jira a irin wannan kai ka sani.” Cewar mafi gajartar cikinsu, mai suna Jabir.
  Tahir xin ya yi dariya, wanda bai yi magana ba, mai suna Nasir ya taya shi, shi Nasir duk cikinsu ya fi su baqi a launi.
  Kusan a lokaci guda suka miqa hannu domin kama Harira, ta yi qoqarin kubcewa, tana ihu da kuka, sai dai lokaci ya qure mata, domin suna daf da ita.
  Tahir da Nasir ne suka sami nasarar damqe hannayenta, shi kuma Jabir gaba xaya ya dadumeta, ya ruqunqume, ya matse tam da hannayensa guda biyu.
  Kici-kicin, Harira tana qoqarin qwace kanta, a yanzu ba ta da damar yin ihu, domin Nasir ya rufe mata baki, su kuma suna qoqarin cire mata kayan jikinta. Abin ka da mazaje uku a kan mace xaya, cikin qanqanin lokaci suka cimma burinsu, suka yi mata tsirara, suka kuma jigatata, wanda har sai da ta shixe, ta fita hayyacinta, sannan suka shiga biya wa kansu buqata a gareta, xaya bayan xaya, har suka gama.
  Tahir ya yi miqa, ya lanqwasa hannayensa guda biyu cikin jin daxi, yana washe baki, ya dubi abokansa da suke gyara jikinsu, ya ce.
  “Lallai yau dawa ya yi nama.”
  Suka yi dariya gaba xayansu. Sam ba su damu da Harira da ke kwance cikin jini a sume ba.
  Jabir ya ce “Dawa kam ya yi nama, an kama barewa.”
  Suka kuma yin dariya, sannan suka kaxa kawunansu suka bar wurin.
  Duk abin da ya faru a wurin, ya faru ne a kan idon Karime mai xanwaken dare. Idan ta gama siyar da xanwaken, sai ta shiga rumfarta, ta yi lissafi, ta yi kintse-kintsenta, sannan ta tafi gida, da yake gidan nata babu nisa da inda take sana’ar.
  Tana cikin lissafi ne ta jiyo wannan balahirar, har ta koma ta vuya, sai ta fuskanci me ke faruwa, ta leqo ta ‘yar rumfar tata ta ga duk abin da ya faru. Dukkanin samarin ta sansu, ta san gidajensu, domin suma ba su da nisa da inda take, kuma kusan kullum nan ce hanyarsu, idan sun yi sha ko ba su yi ba.
  Ganin haka, don kar ta jawa kanta jarfa, a gurguje, ta tattara abin da ya kamata ta tattara na kuxinta, ta qunshe, ta sumama ta bar gurin.
  Harira kuwa a kwance a sume, ko juyo wa Karime ba ta yi ba, har ta isa gidanta gabanta yana faxuwa, tana ta fatan yarinyar ba ta mutu ba, kuma a ce ta bar wurin kafin safiya. A wannan daren kwana ta yi tana kuka.
  *
  Misalin qarfe biyu, hantsi ya yi sosai, Karime xauke da kayan haxin xanwakenta, irin waxanda take xaukowa, kamar qulli, yaji, mai da sauransu. Tsananin son kuxin Karime ya yi yawa, hakan ya sa ita take xauko kayanta, kafin ka ga Karime ta xaurawa almajiri kaya wai don ya kai mata wani wajen don ta biya shi, sai dai idan ta tabbatar kayan za su hallakata, ko kuma wani tsautsayi.
  Komai idan har ba dole ba, to Karime ba ta iya sayensa da kuxi, kuma ba ta iya sawa a yi mata ta biya, ba ta iya bayar da sadaka bare kyauta.
  Da ta iso daf da wurin, sai ta ji gabanta ya faxi, hankalinta ya koma daren jiya, tana tuna abin da ya faru. Babu Harira a wurin da ta ga ta suma, to wannan yana nuna ko addu’arta ta karvu, yarinyar ba ta mutu ba kuma ta bar wurin ko an xauketa, domin da ta mutu ta ga alama, da tuni ta ga masu baqaqen kaya.
  Ta ajiye  ragowar kayan a gefen rumfa, sannan ta shiga rumfar ta xan dudduba, domin ganin abubuwan da ba ta kintsa su ba jiya, ta kintsa su a yanzu, ta ci gaba da shirin abin da ya kawota.
  Har ta yi duk shirin da ya kamata ta yi, ta xaura tukunya a kan wuta, ta ci gaba da dama qullin xanwake, ruwa ya yi zafi, kafin ta fara saku, masu siye suka fara zuwa, domin idan an gama a zuba musu.
  Kwashewar farko, ta siyar, domin ta zuba a kwanukan da suka rigaya suka iso, ta fara saku na biyu, a daidai lokacin da za ta saka qula-qulan xanwake na biyar, hannunta ya gaza cilla xanwaken cikin ruwan zafi, gabanta ya faxi, idanunta suka tsaya cak a kan Harira da ke zaune quri ta tanqwashe qafa, kanta babu xankwali, fuskarta a daddauje, tana ta wani furzar da yawu daga bakinta.
  Hankalin Karime ya kuma tashi, a ranta ta ce “Yarinyar nan ba ta mutu ba, amma ta haukace, Inna lillah….” ba ta qarasa ba, ta ji zuciyarta na raya mata ta haqura da sana’ar xanwaken nan yau, domin lamarin yarinyar akwai tausayi da rikitarwa, lokaci guda bisa wani dalili yarinya ta haukace. A ranta ta yi wani tunani, sannan ta tambayi kanta, “Ko dama mahaukaciya ce yaran nan suka yi mata fyaxe?”
  Ita kanta ba ta yarda da haka ba, domin a jiya da ta ganta ba ta ga wani alamu na hauka ba, to alamu dai sun nuna dalilin abin da ya faru jiya ne ya haddasa mata. Ta girgiza kai, ba don masifar son kuxin Karime ba, da ta haqura da sana’ar nan ta yau.
  Haka ta saduda tana jefa xanwaken, amma duk jifa xaya, sai ta kalli Harira, don haka da mutum zai qirga iya adadin xanwaken da ta yi har zuwa dare, to da shi ne iya adadin kallon da Karime ta yiwa Harira.
  A cikin wannan hali, ta tabbatar da zarginta cewar yarinyar ta haukace, sannan ta ga lokaci da wani ya taimaka ya ba ta abinci ta ci, ta ga yadda mutane suke kallonta, ta ga irin yanayin da take ciki na haukan, ta ga yadda take furzar da yawu, ta ga abubuwa da yawa. Sai dai kuma ta rasa me za ta yi, na taimakon yarinyar, ko na faxin abin da ya faru da yarinyar.
  Yadda Karime ke da masifar son kuxi, haka take da masifar tsoron, don haka ta yi shiru da bakinta, kar ta je ta ce ga abin da ya faru, ta shafa wa kanta kashin kaji.
  Akwai abin da ya fi ba ta tausayi ga Harira, shi ne tun da ta zauna ba ta iya tashi ba, sannan ga ta fuskar tausayi, wani abu a kan haka, ta lura ba don mutumin nan ya ba ta abinci ba, da babu inda za ta je ta nema ta ci, idan har ba kuskure wa ta yi ba, ta lura a nan xin har fitsari Harira ta yi a zaune, ko da yake mahaukaci mene ne ba zai yi ba.
  A xan lokacin ta yi tunanin ko ina iyayen Harira, ko daga ina ta fito? Ita dai ba ta da amsa.
  *
  Haka kawai Yusuf ya ji ya damu, kuma gabansa yana faxuwa, ba damuwa ko faxuwar gaba saboda hatsarin da suka yi ba, haka kawai shi ya rasa dalili. Zuciyarsa tana ta zayyano masa yadda abubuwan suka faru.
  Yanzu babu wani abu da yake gabansa, da ya wuce ya je ya ga Harira, idan ya rufe ido ita yake gani, idan ya buxe ma haka, idan zai yi magana sai ya ji kamar maganarta zai yi, idan ya yi shiru kuma tunaninta yake.
  Ya dubi likitan da ke ta rubuce-rubuce ya ce “Yallavai ka ce na sami sauqi, kuma an sallameni, amma ka hanani tafiya…”
  “Ba likita ba ne ya hanaka tafiya ba, hukuma ce.” Kafin likitan ya yi magana, wannan maganar ce ta fara ratso ofis xin. Kana daga bisani, kofur Bala ya shigo. Idan mutum yana cikin nutsuwa, gashin bakin kofur Bala yakan iya sa shi yin dariya ta wuni guda, amma idan ranka a vace yake, to gashin bakin yakan iya sa ka fashe da kuka, an ce idan an yi mutuwa ba a so ya zo wurin, domin za a iya qara samun wata gawar, ko kuma gidan mutuwar ya zama wurin dariya.
  Ya isa daf da teburin likita, ya ja kujera ya zauna, sannan ya kalli Yusuf.
  “Faruwar hatsarin da ku ka yi yana buqatar lokacinka sosai…”
  Gaban Yusuf ya faxi, gaskiya ba shi da lokaci, ban da kwanan da ya yi a asibiti, kuma ya qara wani lokaci? “To har tsawon yaushe?” ya tambaya.
  “Ba adadi…” Cewar kofur Bala, “domin sai abin da ka gani kawai, yanzu ka xauka lokacin naka yana nan…”
  Yusuf ya kuma damuwa a fuskarsa, “Yallavai zan iya zuwa gida in ga….”
  “Za ka je gida amma ba yanzu ba.” Kofur Bala ya ce da shi. “A cikin motar da abin ya faru, ku uku ne kawai ku ka rayu, duk ragowar sun mutu, ku xin kuma da ku ka rayu, xaya ya gudu har yanzu ba a gano shi ba, haukacewa ya yi, ko kuma guduwa ce ya yi, mu dai muna bincike. Xayar kuma ‘yar qaramar yarinya ce, sai kuma kai babba, don haka za mu je ofis ne da ku…” ya dubi likita, ya miqa masa hannu suka yi musabiha, “Likita mun gode qwarai da gaske.”
  Likita ya amsa da ba komai.
  Kofur Bala ya miqe tsaye, ya juya, ya nufi qofar fita, “Zo mu je.”
  Babu musu Yusuf ya bi bayansa, yana dogara sanda.
  Ofishin ‘yansanda
  “Za mu haxaka da ma’aikatanmu za ku je can garin su Helen ku nemo ‘yan uwan mahaifiyarta da sauran danginsu.” Cewar kofur Bala.
  Yusuf ya zare idanu, ya yi ajiyar zuciya, “Yallavai ba zan iya zuwa gida ba?”
  “Kai da alama ba ka jin magana. Na gaya maka za ka je amma ba yanzu ba.” In ji Kofur Bala.
  Yusuf ya qara shiga damuwa, “Don Allah….”
  Kofur Bala ya dakatar da shi ta hanyar xaga masa hannu ya ce “Kana matsayin kullalle ne, halin da ake ciki fa kana matsayin wanda ya kamata ace an kulle, amma ba a yi haka ba, kuma kana so ka vata wa mutane rai, ka nutsu ka ji.”
  Yusuf xin ya nutsu, yana tunanin to me ya sa za a kulle shi?
  “Kamar kana tunanin me ya sa zan ce kana matsayin kullalle ko? To hukuma da mutane za su iya xaura maka zargin cewa kai ka yi sanadiyyar kashe mutanen da suka mutu a cikin motar da ta yi hatsari, don haka dole sai an yi bincike, ka ga ke nan kai xin a kulle ka ke, ko ba haka ba?” Kofur Bala ya furta hakan, kamar ya shiga ran Yusuf.
  Yusuf ya kalle shi cikin mamaki, ya kasa magana.
  Ofisa Goshi da ofisa Meri aka haxa da Yusuf domin zuwa Enugu binciken iyayen Helen. Suna tafe a mota bana-ba-harka ta Ofisa Goshi xin, shi da Meri a gaba tana xauke da Helen, sai kuma Yusuf a baya, za su je tasha su ajiye motar a ofishin ‘yansanda na tashar, sannan su hau motar zuwa Enugu.
  Dukkaninsu sun yi jugum-jugum rai a vace, da alama su ofisa ba su so yin wannan aikin ba, haka shima Yusuf ransa a vace yake, ya dawo Kano, bai je gida ba, ga shi zai koma Enugu. Sai dai kuma ya kamata ya gode wa Allah tun da shi bai mutu ba a hatsarin, da ko wannan tunanin ba zai yi ba.
  Suka ci gaba da tafiya. Goshi ya katse shirun da suke yi. Ya ce da Yusuf.
  “Kai ya kamata ka godewa Allah ba ka mutu ba, ba ka yi asara ba, domin da ganinka ba ka taho da komai ba…”
  Gaban Yusuf ya faxi, sai yanzu ya tuno da kuxin aurensa da ya taho da su, wanda abokinsa Sale ya ba shi, suna ina? Ya yunqura zai yi magana, sai ya fasa, don tunanin idan ma ya yi su Goshi ba za su yi masa magani ba. Nutsuwa ya yi yana tunanin inda ya kamata ya ga kuxinsa, tsawon lokaci bai tuna komai ba.
  Hawaye suka zubo masa, ya girgiza kai, take ya koma tunanin masoyiyarsa Harira.
  Har suka iso tasha, Yusuf tunani yake, yana tunanin yadda rayuwarsa ta gudana shi da masoyiyarsa da iyayensa da iyayenta, da yadda aka hana shi aurenta, saboda rashin lefe.
  Goshi ya yi fakin motarsa a qofar ofishin ‘yansandan, tun kafin su fito wani xansanda ya yi dariya yana duban motar ya ce “Vavurka motar xansanda da ke da babu duk xaya.”
  Goshi bai ji shi ba, saboda yana da xan nisa da shi, amma ya fuskanci yana yi masa wani kallon raini, da ace ya ji shi, da ya mayar masa da martani shi ma, domin baya bari ta huce.
  Goshi ne ya shiga ofishin, ya je ya yi bayanin ajiyar motarsa da zai yi, sannan ya fito, tuni Meri da Yusuf sun fito daga motar, ya wuce suka bi bayan shi.
  Da suka je ofishin yankar tikiti, sai suka ba Yusuf kuxi ya shiga ya yanko tikitin, su kuma suka tsaya a waje.
  Yusuf ya shiga. Jim kaxan da shigarsa, Meri ta dubi Goshi ta ce, “Gaskiya Kofur Bala bai san abin da yake yi ba, ko waye ya gaya masa haka ake yin aiki, ya haxamu da yarinya wai mu je neman iyayenta, idan ‘yan uwanta suka far mana fa?”
  Goshi ya yi murmushin takaici, “Ai mahaukaci ne, idan ya sha giyarsa ta raya masa sai ya yi abin da ya ga dama. Amma ki sani, ni wannan aikin kamar hutu aka ba ni…”
  Meri ta dube shi cikin mamaki, “Kamar ya ya hutu aka ba ka?”
  Ya yi dariyar mugunta ya ce “Kina tunanin zan je wani Enugu ne a yanzu, mahaukaci ne ni?”
  “To ya za ka yi?” Meri ta buqata.
  “Za ki ga yanda zan yi. Kuma ke ma idan za ki bi tawa to ki gaya min….”
  Kafin Meri ta ba da amsa Yusuf ya fito da tikiti, ya ba Goshi, sannan ya nuna masa motar da aka ce za su hau.
  Goshi da Meri suka kalli juna, a cikin kallon Meri ta gaya wa Goshi cewa ta amince da batun shi. Suka rankaya zuwa wurin motar.
  A cikin motar a kujerar tsakiya, Yusuf xauke da Helen, amma babu Goshi babu Meri. Ko da suka shiga motar daman Goshi bai shigo ba, shi da Meri ne suka shiga, da suka zauna a kujerun kusa da juna kuma ko minti goma ba a yi ba, sai Meri ta miqa masa Helen ta ce ya riqe mata ita tana zuwa.
  Yana nan zaune, sannu a hankali mota tana cika, shi kuma yana tunanin su Goshi suna jira ne motar ta cika sannan su shigo, amma har mota ta cika, saura wurin su amma ba su shigo ba. Direban motar ya shiga, ya tashe ta, ya ba ta wuta, nan ma shiru su Goshi, hakan ya sa Yusuf ya fara zargi, karen motar su uku suka shigo, suka rufe motar, amma babu su Goshi ballantana alamun su.
  Lokacin da motar ta fara tafiya domin fita daga cikin tashar, Yusuf ya yi tunanin ya tsayar da direban ya ce an manta wasu, amma ya kasa, idan ya yi haka gani yake kamar zai jawo hankulan mutane gare shi su ga yarinyar da ke hannunsa kuma shi ba mace ba.
  Motar ta nufin babbar qofar fita daga tashar, Yusuf ya dubi qofar ofishin ‘yansandan nan inda Goshi ya ajiye motarsa, ba ta nan, wannan ne ya kuma tabbatar da zargin Yusuf cewa Goshi da Meri guduwa suka yi suka bar masa Helen, to yanzu shi ya ya zai yi kenan?
  *
  Duk irin tsananin son kuxin Karime da mammaqo, sai da ta tausaya wa Harira, ta xebi xanwake, ta zuba a wani tsohon kwano mai lamba ta je ta kai mata a nan inda take a zaune.
  Da ta ba ta sai da ta nutsu ta kalleta, ta lura bayan matsalar hauka da Harira take da shi, alamu sun nuna ba ta da lafiya, ta kuma jin tausayinta ya kamata.
  Harira ta ja kwanon xanwaken ta fara ci, alamun sun nuna yunwa ta ci qarfinta, kafin ta gama Karime ta kawo ruwa a moxa ta ba ta, abin da ta lura da shi shi ne, idan har ba ba ta abinci ko ruwa aka yi ba, to ba za ta tava tashi ta je ta nema ba.
  Hakan ya sa Karime ta fara tunanin, ya kamata ta samar wa da Harira wurin kwanciya, domin a nan inda take a nan take kwana, kuma ga sanyi, ga rashin nutsuwa.
  Can dare, bayan Karime ta kammala kintsa duk abubuwan sana’arta ta je wajen Harira, ta kama hannunta, ba musu Harira ta tashi, ta bi ta, Karime ta kawota cikin rumfarta, ta zaunar da ita, sannan ta nemi wani tsohon zani da wata busasshiyar tabarma ta shimfixa mata, zanin kuma ta ba ta don ta lulluva. Daga haka ba ta kuma cewa da ita komai ba, ta xauki kayanta ta tafi.
  Ita kuwa Harira ta kwanta a kan tabarmar, ta xan lulluva da zanin da Karime ta ba ta, ta rufe idanunta, cikin sauri ta buxe su hawaye suka shiga sintiri daga idanun nata. Tun daga lokacin da matasan nan suka yi mata fyaxe, ta gaza yin barci, domin duk lokacin da ta rufe ido abin ne yake bayyanar mata, don haka qwaqwalwarta ta kasa saituwa, ta zama zautacciya. Idan ka ga ta yi barci, to sai dai idan ya zo mata dole ba ta shirya ba, ya ci qarfinta ya tafi da ita.
  Xan lokacin nan duk ta fara jemewa, ta fara yin baqi, yanayinta ya sauya gaba xaya. Yau ita ce a cikin wannan hali, ita ce ta zamo kamar ba ta da kowa, ba ta da iyaye, anya iyayenta sun  yi mata adalci, mahaifinta ya koreta, sannan bai nemeta ba, haka ma mahaifiyarta ba ta nemeta ba.
  *
  Haule ta tsirawa Alhaji Idi idanu masu xauke da hawaye, bakinta yana rawa tana cewa “Ba zan iya yin haquri in qyale ace ka qi sa wa a nemo min ‘yata ba.”
  Ya harareta, “‘Yar ki? Lallai kin sake, wato har kina ina buxa baki ki ce ‘yarki, alhalin ina raye. Shakka babu rashin mutuncinki ya fara bunqasa, don haka zan yi gaggawar ganar miki da kuren ki kafin abin ya wuce yadda zan iya tsammaninsa. Ni nan da ki ka ganni, na fi kowa farin cikin guduwar Harira, fata ma nake Allah ya haxata da wani bala’i.”
  “Allah ya kiyaye, bakinka ya sari xanyen kashi…”
  Haule ba ta gama maganar ba, sai ji ta yi ya yi mata mahangurva, kan ka ce me, jini ya biyo baya, ta kife nan tana gunji. Alhaji Idi ya yi tsaki ya ce,
  “Wannan kaxan ke nan. Kuma wallahi a yau ko Harira ta dawo gidan nan, to ba ‘yata ba ce, sai dai ta nemi wani uban amma ba ni ba, kuma ko da wasa idan na ji wani ya tafi nemanta, ko ya sa a nemeta sai ya ga wulaqanci  a rayuwarsa. Ke xin kuma wannan kashedi ne a gareki, kin dai san matsayinki a wannan gida, to ki ci gaba da rufa wa kanki asiri kar ki kawo qarshen buxe idonki a gidan nan….”
  Ya fice, ya bar ta nan kwance cikin kuka.
  *
  Motar da Yusuf ke ciki tana ta sheqa gudu a jeji, Helen ta farka daga barcin da take yi, ta fara sheqa kuka, daman tuni wasu sun fara zargin Yusuf, suna yi masa wani irin kallo. Yanzu da Helen take kuka, Yusuf ji ya yi kamar ya nutse a qasa, saboda damuwa da yadda mutane suka zuba masa idanu.
  Ya ruxe, ya rarumo wani yogot da ya saya a tasha, ya danna a bakin Helen, ta yi wani juuum, ta shiga tsotson yogot xin, har ta shanye shi, sannan ya xauko ruwan fiya wata ya ba ta, shi ma ta sha yadda za ta iya, da ta gama kuma sai ta zuba masa idanu qurrr!
  Gaban Yusuf yana dakan uku-uku a ransa yana ta addu’ar Allah ya sa kar ta kuma fashewa da kuka. Yadda take kallonsa, haka wasu mutane a cikin motar suke kallonsa, Helen kamar tana tunanin inda ta san shi. Shi kuma addu’a kawai yake yi.
  Jim kaxan kawai sai ta fara uhum-uhum don yin kuka, Yusuf ya shiga yaqe baki yana yi mata dariya da rarrashinta, Allah ya taimake shi kukan da ta sa ba mai qarfi ba ne, ba kamar na xazu na yunwa ba. Babu yadda zai yi, haka ya rungumeta yana jijjigata cikin lallashi, ita kuwa sai uhum-uhum xinta take yi.
  Yanzu Yusuf ya ci gaba da tunanin abin da ya kamata ya yi, tun da abin ya zama haka, dole ya haqura ya nemi qauyen su Helen ya sadata da danginta, ya nuna ma shi ne xansandan kawai. Ya yi saurin kawar da wannan tunani, domin ko kaxan bai yi kama da xansanda ba, kuma ba shi da wata shaida. Duk da haka tun da babu mafita, dole ya san abin yi.
  Ya tuno da hirar su Amaka mahaifiyar Helen da Ndidi, ya tuna cewar sun ambaci sunan qauyensu ya fi a qirga, sai dai ya kasa tuno sunan “Bissau….kai ba Bissau ba, Bojjo…..Bojjo…., a’a…” Yusuf ya girgiza kai a lokacin da yake qoqarin tuno sunan qauyen, amma dai ya kasa.
  “Ba mamaki a can idan na faxa a samu wanda ya san sunan qauyen na daidai…” Ya ce a ransa, hawaye suka fito daga idanunsa, ya sa hannu ya goge, ya ci gaba da rarrashin Helen, yana tausayin kansa, yana kuma tausayin Helen, rayuwa kenan, yarinya tana tare da mahaifiyarta a xan lokaci ta rasata, Allah kenan, akwai nufinsa a wannan lamari, yarinya ba za ta iya yin komai ba a rayuwa, amma Allah ya karvi mahaifiyarta, lallai akwai abin da yake nufi da rayuwar Helen da ta Yusuf.
  Babban kuskuren da Yusuf ya samu shi ne, rashin sanin ainihin inda su Amaka za su je a Kano, sannan  kuma da ya sani da tun a tasha ya sauka shi ma ya koma ofishin ‘yansandan. Sam ya rasa me ya ke cushe masa tunani ba.
  Wani obatakin da direban motarsu ya yiwa wata motar xaukar ayaba ita ta ja hankulan dukkanin fasinjojin motar, suka duba, masu addu’a na yi, masu surutu na yi, har da masu rintse idanu. Direban ko a cikinsa wai an tsikari kakkausa, ya ci gaba da zabga gudunsa.
  *
  Sannu a hankali, yau da gobe, Karime da Harira suka fara sabawa, a da Harira ba ta uhm ba ta uhm’uhm, amma yanzu idan Karime tana yi mata magana tana amsawa amma ba kalmomi da yawa. Ita Karimen ce ke ba ta abinci, sai kuma mutanen da suka lura da buqatarta.
  Amma zuwa wannan lokacin duk wanda ya kalli Harira ya ga mahaukaciya, domin tuni ta yi datti sosai, fuskarta ta yi baqi, kayan jikinta sun yi dauxa, to ba ta wanka, ba ta wanki, ba ta wanke fuska, ita dai daga zama sai kwanciya, sai cin abinci da shan ruwa.
  Wani lokaci Karime takan yi mata wasu ‘yan tambayoyi amma bata samun amsa daga gareta, don haka ta qyaleta. Akwai wani saurayi da ya xan fara damuwa da lamuran Harira, har yakan tambayi Karime, to amma Karime ta taka masa birki saboda sanin halinsa, mace ko wacce iri ce idan za ta zani, to zai iya nemanta, hatta mahaukaciya, domin yana cikin irin mutanen da suke da camfin wai kowa ya nemi mahaukaciya zai yi arziqi.
  Karime ta yi masa kyakkyawan jan kunne, don ya shiga taitayinsa. A fili kamar ya xauka, amma a zuciyarsa yadda ya ga Harira kyakkyawa to ba zai iya qyalewa ba, tunda ita Karimen ba mahaifiyarsa ba ce da za ta hana shi yin abin da ya ga dama.
  *
  Fasinjojin motar suka fara firfitowa, har zuwa lokacin da shi ma Yusuf ya fito, ya kuma kallon yanayin tashar, tana nan kamar yadda ya bar ta a kwana biyu da suka wuce, waccan zuwan ya zo da ‘yar jakarsa, wannan zuwan kuma ya dawo da Helen a hannunsa.
  Da ya sauka sai yake ganin kamar yadda mutane suke yi masa kallon zargi a cikin motar, haka suke yi masa a wannan kallon a wannan tashar, kamar yadda ya danne a cikin motar, haka ya danne a cikin tashar.
  Ya sami wani Ibo mai sayar da taba, ya tambaye shi cikin Turancin Nijeriya (broken English) duk da shi mai sayar da tabar baya ji sosai, ya gane tambayar. Ya dubi Yusuf sosai, ya kwatanta masa yadda ba zai sha wahala ba, ya kuma ba shi shawarar ya hau okada kai tsaye ya kai shi qauyen.
  Yusuf ya yi godiya, sannan ya nufi wajen da ya ga tarin ‘yan okada a tsaye. Lokacin da yake zuwa gare su, ya fara tunanin ya kamata ya je wajen abokinsa Sale ya sanar da shi halin da ake ciki. Wata zuciyar ta raya masa bai kamata ya yi haka ba, domin Sale zai ga kamar yana son ya qara masa wasu kuxin ne, tun da waxancan sun vata. Don haka ya yanke shawarar kawai ya bari sai ya kai Helen, kafin ya koma gida ya je wajensa, sai dai da ya sani ya je wajen abokin nasa kafin ya je qauyen su Helen.
  Shi kansa xan okadan sai da ya kalli Yusuf sama da qasa cikin mamakin Bahaushe da ‘ya Inyamura, sannan ya gaya masa kuxin da zai kai shi, Yusuf ya amince, sai dai kuma gabansa ne ya faxi, domin ya tuna ashe ba shi da kuxi, ya yi saurin laluba aljihunan rigarsa, babu komai a ciki, sai da ya zura hannu a aljihun wando, sannan ya jiyo wasu ‘yan kuxaxe, ya yi tunanin yadda ya same shi, ya tuna tun kafin ya bar Enugu yake da su.
  Sannu a hankali okada yana tafe da Yusuf a baya, shi kuma Yusuf xin yana kallon gari da yanayinsa, xan okada bai tsaya ba sai da ya shiga tsakiyar qauyen sannan ya tsaya, ya dubi Yusuf, ya ce “Nan noe mun jo.”
  Yusuf ya yi mamakin yadda xan okadan ya iya Hausa, ya bi shi da kallo cikin mamaki, yana zaro kuxinsa zai ba shi.
  Xan okadan ya fahimci Yusuf yana mamakin sa, sai ya ce “Kana mamakin na iya Hausa ko? Ai na jauna a Kano a unguwar Inyamurai, Sabongari.”
  Yusuf ya girgiza kai ya ce “Na ga alama.”
  Har xan okada ya yunqura zai tambayi Yusuf game da Helen, sai ya fasa, ya karvi kuxinsa, ya wuce yana tunanin yadda haxin gambizar nan ya afku.
  Bayan xan okada ya bar wurin, sai Yusuf ya nufi wajen wani matashi da ya gani a kusa da wajen, yana aikin gyaran wasu shuke-shuke. Ya yi masa sallama irin ta su, matashin ya tsaya da saran shukar da yake yi, ya dubi Yusuf ya amsa masa da barka, sannan sai mamaki ya kama matashin lokacin da idanunsa suka ga Helen alamun ya santa, bai yi magana ba, har sai da Yusuf xin ya riga shi da cewa.
  “Don Allah ni ma’aikaci ne daga Kano, na zo neman ‘yan uwa ko dangin wannan yarinyar ne.” Ya nuna masa Helen. Sannan ya xan yi masa bayanin abin da ya faru na hatsari.
  Matashin ya kuma yin mamaki, ya ce “Chineke!” Sannan ya jefar da addar da ke hannunsa, ya kuma duban Yusuf.
  “Ai nan ne qauyensu, xan jira ni ina zuwa.” Ya ba shi wuri a  gefen inda yake aiki, ya nuna masa wani xan kututturen itace ya ce ya zauna.
  Yusuf ya yi godiya, ya zauna. Shi kuma ya tafi. Yusuf ya nutsu yana tunani, yana godiya ga Allah da bai sha wata wahala ba, ga shi har ya sami inda iyayen Helen suke, don haka yana gamawa da su zai je wajen Sale ya yi masa bayanin halin da ake ciki, ko da bai qara ba shi wasu kuxin ba, ya san abin yi, ko da yake lokacin da aka xiba masa ya kai kuxin sun wuce, ko a wane hali Harirarsa take ciki?
  Ya ji gabansa ya faxi, a ransa ya ce “Allah ya sa ba a yi mata aure ba.” Sai kuma wani tunani ya zo masa, ya fara tunanin yanzu idan mutanen qauyen nan suka yi masa wani mummunan tunani a kan iyayen Helen fa?
  Wannan tunani ya yi  tasiri a gare shi, to ko ajiye Helen zai yi a wurin ya gudu? Da ya dubi fuskar Helen wadda take ta sharvar barcinta, sai ya tausaya mata, ya ga cewar idan ya yi mata haka bai kyauta mata ba, ita dai yarinya ce, ba ta da wani nauyi a kanta.
  “Tsayawa kawai zan yi komai ta faru, haka Allah ya qadarto.” Ya ce a ransa.
  Bai jima da rufe baki ba, sai ganin matashin nan ya yi da sauran matasa a tare da shi xauke da sanduna sun nufo wurin da yake, Yusuf ya yi sauri ya miqe tsaye yana faxin “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un…” Ya juya domin guduwa, a bayansa ma wasu ya kuma gani, haka ya rungume Helen qam-qam, ya fara ja da baya.
  Suka qaraso, matashin nan ne ya fara yin magana yana nuna Yusuf ya ce “Ga shi nan, sune suka kashe su Ndidi da Amaka…”
  Wani mai jajayen idanu da askin ‘yan iska a cikin samarin ya iso wajen Yusuf ya qwace Helen daga hannun Yusuf ya miqawa wani a gefe, sannan ya dubi Yusuf ya ce “Kamar yadda ku ka haxu ku ka kashe uwar yarinyar nan da qawarta, yanzun nan za mu kashe ka kai ma, mun fara xaukar fansa…”
  Yusuf ya yi sauri ya fara magana yana cewa “Haba idan ni na kashe su ta ya ya zan kawo muku Helen? Kuma……”
  Kawai sai wannan qaton ya kutufe shi a fuska, kafin ka ce mene ne wannan sun rufar masa da sanduna da naushi, suka yi masa laga-laga, har sai da ya daina motsi, duk sun farfasa masa jiki, sun yi masa jina-jina, kamar ya mutu, waxanda ke kusa da shi ne kawai suke ganin numfashinsa.
  Sannan suka xauko taya da sauran itatuwa, suka xora masa, wani ya zaro ashana, ya qyasta, ya jefa a kan itatuwan, wutar ashanar ta mutu, ba ta kama ba, ya kuma qyastawa, yana shirin  jefawa, Igwe Onyebuchi na qauyen da mutanensa suka iso wajen, da sauri Igwe Onyebuchi ya hana, sannan ya sa mutanensa suka cire tayar da itatuwan daga kan Yusuf.
  Wasu daga cikin matasan suna ta guna-guni suna cewa su sai sun qona shi.
  Igwe Onyebuchi ya dube su ya ce “Ko ba ku qona shi ba, kun kusa kashe shi, kuma bai kamata ku qona shi ba, idan kuka qona shi a ina zamu samu bayanan Azubuike mahaifin Helen xin? Kuma ai ya kamata ya yi bayani kafin a kashe shi.”
  Ya dubi yaransa, ya ce “Ku xauko shi mu tafi da shi.”
  *
  Igwe Onyebuchi ya yi tsaki lokacin da Yusuf ya gama ba shi labarin duk abin da ya faru, haka nan yaransa su biyu ma, sai huci suke yi cikin fushi.
  Igwe Onyebuchi ya miqe tsaye, ya xan taka ya yi gaba kamar zai fita daga xakin, sai ya juya ya kuma duban Yusuf, ya ce “A ce duk kowa a motar ya mutu amma ban da kai kaxai da ita Helen xin, wannan ma ai qarya kake yi, ba zamu tava yarda da kai ba, ni fa so nake ka gaya min zahirin abin da ya kawo ka, ka san mu nan ba wawaye ba ne, muna da hankalinmu.”
  Yusuf ya girgiza kai, ya cije baki cikin takaici, hawaye ya fara xigo wa daga idanunsa, ya dubi yaran Igwe Onyebuchi sannan ya kalli Igwe xin, ya ce “Idan har wannan ne tunaninka, to ba ka yi min adalci ba, me zai hana ka aika can Kanon, ka aika ofishin ‘yansandan da na  gaya maka ka tabbatar…”
  Igwe Onyebuchi ya juyo ya kalli Yusuf sosai, sannan ya tave baki, ya girgiza kai, sai da ya xan yi tunani, kana ya yi tsaki ya ce, “Wannan ba aikina ba ne, aikina shi ne a yanzu in sa a kulle min kai zuwa lokacin da na so, sannan kuma in sa a kasheka a qarshe.” Ya kalli yaransa, “Ku kulle shi, kuma a ci gaba da lura da shi kar a samu matsala.” Ya kaxa kai, ya yi tafiyarsa.
  Tun kafin ya bar wurin, masu fushi da fushin wani suka daqumi Yusuf, suna duka suna komai suka mayar da shi cikin xakin da suke kulle da shi.
  *
  Haule cikin matsanancin kuka, ta durqusa har qasa ta riqo qafar Alhaji Idi, har ma kukan yana neman hanata yin magana, da qyar take faxin, “Ka qi ka nemo min ‘yata, in san a halin da take ciki, ni ma ka hana ni in nemeta, ya ya ka ke so in yi da rayuwata?”
  Alhaji Idi ya kalleta ya ce “Ko ma ya ya ne ki yi da ita mana, mene ne ya shafeni, bari in gaya miki a karo na qarshe, in maimaita miki babu inda zan je neman tsinanniyar yarinyar nan, kuma ke ma babu inda za ki, domin ba zan sake kina matsayin hajata ki vace min ba, ita ki rabu da ita ta je can ta vata, daman ai ribar qafa ce, tun da ta zavi wannan yanayin na rayuwa, to babu ruwana da ita, duk abin da zai faru da ita ni bai shafeni ba…”
  Ran Haule ya vaci, ta ce “Ai ni ya shafeni, domin ‘yata ce, ba zan iya rabuwa da ita rayuwarta ta salwanta ta wulaqanta ba.”
  “To ai sai ki yi abin da za ki yi.” Ya daka mata tsawa. “Har wani maganar salwanta da wulaqanta ki ke yi, ba ki san wannan shi ne abin da na fi so ba ke nan a rayuwata, a yau idan Harira za ta yi muguwar wulaqanta, ai shi ne abin da na fi so. Shin kin manta wulaqancin da yaron nan Ayuba ya yi min, ya zo ya ce sai na ba shi dukiyar aurensa da ya kawo mata, alhalin na kashe su? Ko kin manta?”
  Haule ta girgiza kai, ta ce “Ka fi damuwa da kuxi ko dukiya fiye da ‘yar cikinka Alhaji?”
  “Qwarai kuwa, na fi damuwa da su fiye da Harira, da za a ba ni kuxi kwatankwacin wanda Ayuba ya kawo zan iya sayar da Harira, in bayar da la’ada. Kuma kar ki manta ke xin da kuxi na saye ki, yadda ki ke matsala a tare da ni, da zan sami riba kai ko faxuwa ne ma zai iya karva in ba da ke.”
  “Ka gaya min duk abin da ka so, don ba wannan ba ne karo na farko ko na biyu ko na xari ba, na sha ji, amma yanzu ina magana ne a kan ‘yata da ka kora daga gidan nan…”
  Marin da ya sauke mata a fuska, shi ya katse ta, ta kife ban da hawaye har da majina ta fitar, saboda qarfin marinsa. Ya nuna mata da hannu.
  “Na koreta, kora kuma da babu dawowa, sai ke ma ki shiga taitayinki…” Ya wuce ya bar ta nan tana cewa.
  “Babban abin da na fi so ke nan ka koreni.” Ta fashe da kuka, ta faxi a nan inda take rigingine tana gunjin kuka.
  BAYAN WATA
  TAKWAS
  BABI NA HUDU
  D
  aidai lokacin da Karime ta kammala komai tana shirye-shiryen tafiya gida, naquda ta kama Harira, hankalin Karime a tashe ta fara xawainiya da taimaka mata, ta daxe da sanin wannan rana tana nan zuwa, ta ji tsoron kar ta zo a lokacin ba ta nan, domin ta san halin da mai naquda kan shiga.
  To ga shi ranar ta zo, kullum kwanan duniya kuma tsawon watanni takwas da ‘yan kwanakin da Karime ta yi da Harira sai ta tsinewa matasan nan da suka yiwa Harirar fyaxe, a tsawon lokacin ta tabbatar Harira ba ta da gata a duk inda take, idan kuwa tana da gatan to akwai wanda ko wacce take yi mata qullalliya a rayuwarta. Kuma ta zo ta haxu da azal, waxannan marasa imani suka yi mata fyaxe, suka kassara rayuwarta, suka sa ta zautu.
  Allah ya taqaita mata naqudar, cikin mintuna kamar arba’in ta haifi xiyarta mace kyakkyawa da ita. Dukkanin abubuwa da ya kamata Karime ce ta yi mata, ta kintsata, ta gode Allah da ba da rana abin ya faru ba.
  Ta miqa wa Harira ‘yar, lokacin da ta ga ta nutsu.
  Babban abin da ya ba Karime mamaki shi ne, maganganun da ta ji Harira tana yi, tsawon lokacin da suka yi a tare ba ta ji ta yi maganganun da suka wuce kalmomi biyar ba a lokaci guda, amma a yanzu sai ga ta tana yi mata wani dogon jawabi.
  “Karime na gode da dukkan irin taimakon da ki ka yi min, haqiqa sai dai Allah ya saka min. Zan ba ki amanar xiyata, idan ta girma ki ba ta labarin abin da ya faru da ni, kar ki voye mata komai, ki gaya mata waxanda suka aikata min wannan abu. Sannan don Allah ina son ki sa mata sunana wato Harira a ranar da ta cika kwanaki bakwai a duniya. Sannan ki rinqa kiranta da Hari kawai.” Ta yi shiru.
  Karime tana kallonta cikin mamaki. Sannan Harira ta ci gaba.
  “Ki yi haquri Karime, akwai abin da zai faru ne. Don haka kuma ina son ki ba ta labarin irin yadda kakanta, mahaifina ya xauki matsayin rayuwata da rayuwar mahaifiyata…” Ta yi shiru tana kuka. Sai da ta yi shiru, sannan ta baiwa Harira labarin ko ita wace ce, da ainihin unguwarsu da gidansu da labarin mahaifinta Alhaji Idi.
  Karime ta yi mamakin yadda ba su da nisa amma sam ba a nemeta ba, ashe daman haka mahaifinta ya so ya ganta. Tana cikin tunani, Harira ta katse mata shi.
  “Ba na son ki kai ta gidanmu, domin ba nan ba ne asalin gidan iyayenta ba, kawai ki ba ta labarin da na gaya miki, ita ta san yanda za ta yi, da ki kai ta gidanmu, gara ki kai ta gidan marayu ko kuma ki jefar da ita a bola.”
  Ta yi shiru, daga haka ba ta kuma cewa komai ba, ta miqawa Karime jaririyar da take ta kuka, kana kuma ta juyar da kanta gefe. Haka itama Karime ta yi shiru, ta kasa cewa komai cikin mamaki.
  Da Karime ta ji shirun ya yi yawa, sai ta fara cewa, “Ikon Allah, amma fa Harira lamarinki akwai ban mamaki.”
  Nan ma ta kuma jin shiru, sai ta xan tavo ta, babu alamun motsi, cikin sauri ta juyo da fuskarta, sai ta ga idanunta a rufe, ta kara hannu a kan hancinta, babu numfashi, ta yi saurin sa hannu a qirjinta, babu numfashi a nan ma.
  “Na shiga uku, Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un.” Haka Karime ta ce.
  Jaririya Hari ta qwallara qara kamar ta san mahaifiyarta ta mutu, haka Karime itama ta fashe da nata kukan.
  *
  Tsawon watannin nan Yusuf yana qwaqume a cikin xakin da Igwe Onyebuchi ya sa a kulle shi, duk ya rame, ya koxe ya zama wani iri saboda wahala.
  Abincin da suke ba shi tun baya iya ci har wuya ta sa ya koyi ci, kullum jira yake ya ji sun ce yau za su kashe shi ko ya huta.
  Duk lokacin da za su zo kawo masa abinci, sai ya yi qoqarin neman su aikata masa abin da suka yi nufi ko ya huta, amma ko sauraronsa ba sa yi, shi kuma Igwe Onyebuchi xin ko zuwa wajensa baya yi, tsawon wannan lokacin ya je gare shi sau xaya, daga nan bai kuma ba.
  Dukkanin irin tunani da dabarun da ya kamata ya yi, Yusuf ya yi domin ya kuvutar da kansa ko ya nemi su kashe shi ya huta, amma a banza. Xaurin da suka yi masa alhalin yana cikin xakin, shi ya fi komai muni a wurinsa, wata sasari suka sa masa hannu da qafa, a hannun kuma sun mayar da shi baya, saboda rashin adalci, abinci ma sai dai a ba shi a baki.
  Yana zaune, yana yin tunanin irin rayuwar da ya tsinci kansa saboda soyayyar Harira, tsawon lokacin nan sau tari yakan ji gabansa ya faxi idan ya tuno da iyayensa da halin da za su kasance a ciki, haka nan idan ya tuno da Harira, duk da ya saduda da batun aurenta, amma yana ji a jikinsa tana cikin wani hali mafi muni a rayuwa.
  Ya yi kukan, tun kuka yana yi masa daxi, har ya daina yi masa daxi, ya zame masa abinci kuma abin sha. A tsawon lokacin nan ya yi Allah wadarai da aiki irin na su Kofur Goshi da Meri, ‘yansanda, waxanda suka juye suka zama masu cutar wa ga al’umma da yaudara.
  Yana nan zaune abu goma da ashirin ya yi masa cunkus, ya dame shi, abin da ya ke sa zuciyarsa yin sanyi shi ne idan lokacin sallah ya yi, ya yi ta, ta hanyar rayawa, hakan yana sa shi jin sanyi a ransa.
  Dare ya yi a yanzu, aqalla goma sha biyun dare ta gota, ya fara qoqarin kishingixa don kwantawa, sai ya jiyo tafiya, hakan ya sa ya fasa, ya yi shiru yana sauraron mai zuwa, ko abin da zai faru.
  Yana ji, aka zo aka tsaya a bakin qofar da yake ciki, aka fara qoqarin buxewa, yadda ya ji ana buxe qofar ya tabbatar masa ba waxanda suka saba zuwar masa ba ne, ya qara nutsuwa yana sauraro.
  Aka gama buxe qofar, aka turo aka shigo. Igwe Onyebuchi ne, yana cikin wani yanayi. Yusuf ya tsaya yana kallonsa, ya fara raya mamaki a ransa.
  Igwe Onyebuchi xin ya zo daf da shi ya tsaya sannan ya dube shi, ya ce “Za ka fita daga nan ka tafi garinku, kana son haka?”
  Yusuf ya dube shi kamar yana son ya gane dalilin maganarsa, bai yi magana ba.
  “Mamaki ya hanaka magana ko? Na san za ka yi hakan, to amma ba wani abu bane, musamman idan ka ji dalilin ya sa na ke son na sakeka ka gudu.”
  Yusuf ya yi ajiyar zuciya, har yanzu bai yi magana ba.
  Igwe Onyebuchi ya ci gaba da cewa, “Tsawon lokaci, tun bayan da na sa aka kulle ka na yi nazari, na tabbatar da gaskiyar abin da ka faxa, to amma da na nemi a sakeka, sai abin ya zama rigima da sauran dangi, wanda a qarshe suka yi barazanar kashe ni idan na sake ka. Wannan dalili ne ya sa na kasa sakinka tsawon wannan watanni, amma fa ina ta tunanin hanyar da zan bi, sai yanzu na samo.” Ya tsagaita.
  Yusuf ya kawar da kansa yana sauraronsa.
  “Zan sake ka, ka gudu a yanzu nan, amma akwai sharaxi wanda zai hana nima a kashe ni, sannan kai kuma ka gudu.”
  Yusuf ya motsa baki a hankali, “Wanne sharaxi ne?”
  Igwe Onyebuchi ya dafa kafaxarsa ya ce “Za ka gudu ne tare da Helen…”
  Yusuf ya yi saurin kallonsa “Kamar ya ya?”
  “E, za ka gudu da ita ne can Kanon, ka san yadda za ka yi da ita ko a hanya ka san yadda za ka jefar da ita, ko kuma dai yadda ka yi ruwanka. Wannan shi ne sharaxi na farko. Sai kuma…”
  Yusuf ya katse shi, “Kafin ka ci gaba, ta ya ya zan gudu da Helen?”
  “Wannan ya fi komai sauqi, domin na ba ta maganin da za ta yi ta barci na tsawon awanni goma ma, idan har kana tsoron kar ta rinqa yi maka kuka a hanya.”
  Yusuf ya girgiza kai.
  “Sannan sharaxi na biyu, kar ka kuskura ka sanar da ‘yansanda, ko ka koma wajen ‘yansandan da suka turo ku, domin yin hakan kamar ka kuma dawowa ruwa ne, ka san kuma hukuncinka shi ne kisa.”
  Yusuf ya gamsu da bayanan Igwe Onyebuchi a fuska, amma a zuci bai yarda ba. Idan dai har ya samu ya gudu daga wannan uquba, daga wannan qauye, to zai iya jefar da Helen xin, “yarinyar da ta zame min bala’i.” ya ce a ransa. Sai dai bai ga wanda zai hana shi gaya wa ‘yansanda irin zaluncin da suka yi masa ba, hatta suma can ‘yansandan nan sai ya san yadda za a san abin da suka yi na cin amanar qasa da cutar al’umma.
  Igwe Onyebuchi ya fito da kuxi daga aljihunsa ya miqa masa, Yusuf ya karva, bai duba yawansu ba.
  “Idan ka fita daga nan, akwai yarona a kan mashin kuma Helen xin tana wajen shi a cikin jaka, zai kai ka har tashar bayan gari, anan za ka hau mota ku tafi, domin suna yin lodi ne tun dare har zuwa asuba lokacin da suke tafiya, idan ka shiga motar za ka iya zama a ciki har ta cika ku tafi. Ina fatan ka kiyaye dukkan abin da na gaya maka?”
  Ya girgiza kai, “Na gane.”
  Igwe Onyebuchi ya kunkunce wa Yusuf sasarin gaba xaya. Da qyar Yusuf ya shafa wuraren da sasarin ya jijji masa ciwuka, sannan ya fara hawaye. Igwe Onyebuchi ya dafa kafaxarsa, “Ka yi sauri, kuma ka yi haquri tun da ba ka mutu ba. Ka kiyaye abubuwan da na gaya maka. Zo mu je.”
  Igwe Onyebuchi ya wuce gaba, Yusuf ya bi bayansa suka fito har harabar wurin, sannan suka bi wata hanya, suka yi ‘yar tafiya, har suka fara hango mai mashin xin, Igwe Onyebuchi ya tsaya, ya nuna wa Yusuf shi, sannan ya ce “Je ka hau, zai ja ku tafi, idan ku ka je tashar zai ba ka ita sai ka tafi.”
  Yusuf ya ce “To.” Har ya wuce, sai ya ji Igwe Onyebuchi ya riqo hannunsa yana cewa.
  “Kar ka yi kuskuren qin bin tsarin da na tsara maka, idan ka yi haka, ka xauki kanka matacce.”
  Yusuf ya girgiza kai kawai, ya yi sauri ya je ya hau mashin xin, mai mashin xin ko kallonsa bai yi ba, ya ja suka tafi.
  Su Yusuf suna vacewa daga wurin, wata tanqwasasshiyar tsohuwa, wadda ta yi xaurin qirji, kuma tana xaure da wuri (irin kuxin Nijeriya na da kafin zuwan Turawa) a wuyanta, ta iso daf da Igwe Onyebuchi ta dafa shi tana dariya ta ce.
  “Ka ga xana wannan abin da ka yi shi ne kawai mafita, shi ne kawai hanyar da za ka iya ci gaba da mallake dukiyar xan qanin mahaifinka, wato mahaifan Helen, Azubuike, amma idan Helen tana raye, tana tare da mu ta ya ya ka ke zaton za ka mallaki dukiyar?”
  Igwe Onyebuchi ya yi murmushi, ya rungume tsohuwar, ita kuma tana buga masa ganyen isga a doron baya. Sannan ta ci gaba da magana.
  “Mutuwar Amaka ai abar fahari ce gareka, shi kuma Azubuike ai ka san ba zai kuma dawowa wannan qauyen ba, saboda zuwan sa kamar kabarinsa ya zo shiga.”
  Suka yi dariya gaba xaya, sannan suka juya zuwa cikin gida.
  Kamar yadda Igwe Onyebuchi ya tsara wa Yusuf, haka komai ya faru, mai mashin xin ya kai shi tasha, ya karvi Helen da ke cikin jaka, ya shiga mota, ya biya. Amma bai yarda ya sa jakar a bayan mota ba, domin haka kawai ya ji baya son a nakasta Helen.
  Mota ta xauki hanyar Kano, duk da irin tsaye-tsayen da suka yi a hanya Yusuf bai jefar da jakar da Helen ke ciki ba, wannan ne kawai Yusuf bai yi ba, kamar yadda Igwe Onyebuchi ya tsara masa.
  Da suka isa tasha a Kano, Yusuf ya sami mai babur mai taya uku, ya hau, ya ce masa “Fagge za ka kai ni.” Har sun yi nisa da tafiya, sai kuma ya sauya shawara, ya kwatanta masa unguwar su Harira, wato Gwammaja.
  Mummunan labarin da Yusuf ya ji, ya sa sai da ya kusa suma a wurin, ya ji dama bai dawo daga Enugu ba, dama ya daxe da mutuwa, domin ya sami labarin Harira ta mutu. Da qyar mai babur xin ya kwantar wa da Yusuf hankali, ya zaunar da shi a cikin motar, ya ja suka nufi Fagge.
  A nan ma babu sauqi, wani mummunan labarin ya ji, mahaifinsa ya rasu watanni huxu da suka wuce. Mahaifiyarsa kuwa ta tafi nemansa.
  Yusuf ya jawo jakar da Helen ke ciki, ya wulwulata zai jefar, lokaci guda kuma ya ji jikinsa ya yi matuqar sanyi, wata qwalla mai xumi ta fara zuruftu daga cikin idanunsa, ya dire jakar a hankali, ya fashe da kuka.
  Mai babur xin yana tsaye yana kallonsa cikin tausayawa.
  Yusuf ya sa hannu a hankali, ya buxe jakar, Helen ce kwance tana ta barci kamar yadda Igwe ya gaya masa, tausayinta ya kama shi lokacin da ya ga kamar tana murmushi. Ya yi sauri, ya rufe jakar, ya juya, ya kalli mai babur xin, ya ce “Mai da ni tashar da ka xauko ni.”
  Ya je da jakar a hannunsa ya shiga cikin babur xin, mai babur xin ma ya shiga, ya tayar ya ja suka tafi.
  BAYAN SHEKARU SHA BIYAR
  BABI NA BIYAR
  G
  inin gidan ya tsaru gwargwadon tsaruwa, tun daga kan ruwan madarar fentin zuwa kayan alatu da waje da farfajiya da cikin gidan ka san an kashe masu gidan rana.
  Iya farfajiyar gidan da ke xauke da shuke-shuke da tsari mai kyau ya wadatar da bayar da gamsuwa ga mai fasalta kyawun gidan.
  Sai dai mummunan yaron mai kama da tsamiyar biri, mai suna Sunusi wanda ya kwashe shekaru talatin da ‘yan kwanaki a raye, sai dukan kyakkyawar yarinya Hari wadda a qiyasin shekaru ta kai shekaru goma sha shida da ‘yan kwanaki yake yi da belt idanunsa a rufe, idan ta yi can sai ya bi ta, idan ta yi nan ma ya bi ta. Duk ya farfasa mata jiki. Tana kuka mai tsanani, kuma tana kallonsa, kallon kana zalunta. Dukan wulaqanci yake yi mata, har sai da ya gaji, sannan ya qyaleta, yana huci, yana cije baki, ya juya, ya tafi.
  Jim kaxan da tafiyar Sunusi, sai ga Zinatu matashiyar budurwa, baqa, amma ba xixim ba kamar Sunusi, ita tana da xan kyau, amma ganinta zai tabbatar maka da qanwar Sunusi ce, mai kimanin shekaru goma sha bakwai a raye, ta fito xauke da bokitin ruwa, ta zo kan Hari ta xaga bokitin nan, ta sheqa mata ruwan da ke ciki, tun daga kanta. Hari ta yi qara sosai, ga zafin duka, ga takaicin da tuquqin baqin cikin kwara mata ruwa da Zinatu ta yi, sannan ta toshe kunnuwanta, sai kuma ta fashe da dariyar takaici, ta yi ta yi, har dariyar ta sake komawa kuka, alamun kamar ta samu matsala a qwakwalwarta.
  Qarar Hari ya yi daidai da tahowar Hajiya Silima, da gani babu tambaya ita ta tsugunna ta haifi su Sunusi, tana tafiyar qasaita, ta iso gaban Hari tana yi mata wani irin kallo na wulaqanci, sannan ta kumbura baki, ta fara magana.
  “Shegiya. Na gode Allah don da alama kin haukace. Haka kawai yarinya kin zame mana annoba a gida. Kawai Alhaji ya je ya tsinto yarinya, ‘yar qauye, jaka, ta zo gida muna zaune lafiya cikin kwanciyar hankali, ta zame mana bala’i. Tun da ki ka shigo gidan nan zaman lafiya ya qaurace mana, muna zaunenmu lafiya. To bari shi wanda ya kawo kin ya dawo ya san inda zai kai ki. Don ba za mu zauna da mahaukaciya ba.”
  Hari ta kalli Hajiya Silima cikin takaici tana goge hawayen da ke fuskarta, ta ce. “Ni ba mahaukaciya ba ce. Kuma zan yi farin ciki da hakan, zan fi so ya kai ni duk inda zai kai ni, da dai ace kune ku ka kaini inda ku ke son kai ni.”
  Hajiya Silima ta kalleta cikin mamaki, ta ce “Ina za mu kai ki?”
  Hari ta yi qwafa ta ce “Lahira mana.”
  Hajiya Silima ta qara matsawa kusa da ita ta durqusa a gabanta, tana harararta, ta ce “Ina magana ki na magana?”
  Ran Hari ya vaci ta ce “Ina da bakin yin maganar da ki ke da shi ne, shi ya sa. Kuma za ta iya yiwuwa bakin nawa ya fi naki iya furta yawan kalmomi. Don haka babu dalilin da za ki hana ni yin magana, wannan abu….”
  Hajiya Silima ta sheqa mata mari tana faxin “Yawan kalmomi marasa amfani daga bakin mara amfani ba.”
  Hari ta dafe kuncinta a hankali. Sannan Haj. Silima ba ta ankara ba, sai ta ji tass! Hari ta rama marin da ta yi mata, kuma tana faxin.
  “Ba ke ba ce alqaliyar amfani ko rashin amfanin kalamaina ba, kunnuwan da suka ji, sune mahukuntansu.”
  Hajiya Silima ta dafe kuncinta tana kallon Hari. Suka yiwa juna kallon-kallo sosai.
  A fusace Zinatu ta yi kan Hari za ta buga mata bokitin da ke hannunta, cikin sauri Hajiya Silima ta riqeta, sannan ta dubeta a nutse, ta girgiza mata kai, ta ce “Kar ki soma.”
  Ta kama hannunta, ta ja ta suka koma cikin gida.
  Washegari
  Hari kwance a kan daven hanyar zuwa banxaki, a takure take saboda tsananin sanyi da take ji, wasu koxaxxun kuma yagaggun kaya ne a jikinta marasa kyau, tana barci.
  Alhaji Jabir ya fito daga xakinsa yana sanye da kayan barci, daga barcin ya tashi. Ya taho zai wuce, sai ya ga Hari a kwance a wurin. Cikin mamaki ya tasheta. Hari ta tashi, ta zauna tana kallonsa, tana murza idanunta na barci.
  Alhaji Jabir ya kalleta sosai, ya ce “Hari me ya faru? Ya ya na ganki a nan a kwance?”
  Hari ta yi tsaki cikin takaici ta ce “Anan na kwana.”
  Alhaji Jabir ya yi sauri ya kalli qofar xakin Zinatu ransa a vace. Ya qwala mata kira.
  “Zinatu! Zinatu!!”
  A can cikin xakin Zinatun ce a kwance, lulluve da kyakkyawan tattausan bargo, a kan gado mai kyau, tana ta sharvar barci abinta. Muryar Alhaji Jabir sai ratso cikin xakin take, yana kiranta.
  Zinatu ta xan motsa kaxan sannan ta qara qudundunewa da bargo. Can kuma sai ta ji ana qwanqwasa mata qofa. Ta yaye bargo, ta yi tsaki ta yamutsa fuska. A haka ta xan tako zuwa bakin qofar xakin tana magana tana lullumshe ido saboda barci. Tana magana a wulaqance.
  “Wai wane ne?”
  Muryar Alhaji Jabir ta ratso cikin xakin a fusace yana cewa “Ubanki ne!”
  Alhaji Jabir yana tsaye a qofar xakin. Zinatu ta buxe qofar, ta fito, tana fitowa ta yi wata irin miqa ta gantsare a gaban mahaifinta ba tare da ta ji komai ba, ko ta damu ba. Cikin sauri Alhaji Jabir ya kawar da idonsa daga kallonta.
  Babu damuwa a tare da ita, tana wani tattare fatar saman idanu ta ce “Abba lafiya kuwa?”
  Alhaji Jabir ya harareta, sannan ya kalli inda Hari take, ya sake juyawa ya kalli Zinatu ya ce “Ba cewa na yi a xakinki Hari za ta rinqa kwana ba ki ke korota take kwana a waje? Kuma kayan da na ce ki bata ta sa ba ki ba ta ba kenan?”
  Zinatu ta shagwave masa, tana cewa “Haba Abba ni ya zan yi in kwana xaki xaya da wannan qazamar, kawai in xauki wata cutar in mutu a banza. Gaskiya ba zai yiwu ba, kuma ba zan iya ba ta kayana ba.”
  Hajiya Silima ta iso wurin ba su ga zuwanta ba, sai maganar da ta yi suka ji, itama tana sanye da kayan barci, alamun ba ta jima da tashi daga barci ba.
  “Gaskiyarki. Kawai da ganin yarinya a juji ka kwaso ka kawo mana gida, ba ka san wacce irin jaraba ka xauko ba? Kuma ni tunda ka kawo yarinyar nan na san ka kawo mana bala’i ne. Ba ka san irin halin da muke ciki ba a gidan nan.”
  Alhaji Jabir ya yi mata wani kallo cikin sauri, ya ce “Ni na tsara haka. Kuma abin da na ce shi za a yi domin gidana ne, don haka babu fashi dole a yi.” Ya wuce, ya bar su a nan a tsaye.
  Hajiya Silima ta bi shi da harara, tana cewa “Ai ba komai kake da iko da shi ba. Don haka abin da ka faxa qarya ne.” Ta kalli Zinatu. “Koma ki yi kwanciyarki babu mai shiga rayuwarki.”
  Zinatu ta koma cikin xakin, ta rufo qofar da qarfi.
  Hajiya Silima ta harari Hari, sannan ta wuce, ta tafi xakinta, tana qwafa.
  *
  Zaman farfajiyar gidan Alhaji Jabir ya zamo mafi daxi ga Hari fiye da zama a ainihin cikin gidan, domin zamanta a cikin gidan tsanani yake zame mata, dukkanin giftawar minti a cikin tsangwama da takura take daga wurin Hajiya Silima da ‘ya’yanta.
  Zaune take a gefen fulawoyi ta yi tagumi. A cikin idanunta akwai qwalla, tana cikin damuwa matuqa.
  Idan ta zauna xin babban abin da take yi shi ne tunanin rayuwarta kaf a wurin Karime mai xanwake da irin gwagwarmayar rayuwar da ta sha, da wuya da wahala da quncin rayuwar da ta fuskanta a zaman shekaru sama da sha biyar da ta yi a wurin take yi.
  Sai dai ba wannan bane babban abin da a kullum kuma a koda yaushe ta fi tunawa, ta fi tuna rabuwarta da Karime xin. Abin da take da tabbacin ba za ta tava mantawa da shi ba. Ta tuno yadda suka yi.
  A kofar rumfar Karime mai danwake
  Hari a tsugunne, duk da ta kai minzalin budurtaka amma kayan jikinta wasu sashi a yage, ban da tana yin ‘yan dabaru, to kowa ma zai iya ganin wasu sassa mafi tsada na jikin nata. Ita kuwa Hari a kan kujera a zaune, cikin damuwa tana labartawa Hari labari mafi muni.
  “Kamar yadda ki ka ga alamu ba ni na haifeki ba to haka ne, mahaifiyarki mahaukaciya ce, ta mutu a ranar da ta haife ki, mahaifinki kuma ba mutum xaya ba ne, domin su uku suka haxu suka yiwa mahaifiyarki fyaxe aka haife ki…” Ta yi shiru tana huci.
  Hari kuka take yi, ta rasa me yake yi mata daxi, ta fi jin daxin irin wahalar da ta sha a yayin riqon da Karime ta yi mata fiye da wannan mummunan labari da take ba ta.
  Karime ta ci gaba, da cewa “Waxannan mutane waxanda a yanzu suka zama manyan Alhazai su ne mutanen da suka haxu suka yi wa mahaifiyarki fyaxe aka same ki, kin sansu, domin suna wucewa ta nan, idonsu idon mata, to sune iyayenki maza, Alhaji Jabir da Alhaji Tahir da Alhaji Nasir.”
  Ta xauko wani qunshin kaya, ta warware, ta xauko wata takarda ta miqa mata, “Duk wannan labarin da nake ba ki, mahaifiyarki ce ta ce in gaya miki ke kin san yadda za ki yi musamman dangane da su waxancan mutane uku. Sannan wannan takardar ita ta ce a ba ki, ban san me take qunshe da ita ba.” Ta  yi tari kafin ta ci gaba “Haka nan ta ce in ba ki labarin rayuwar ta a ainihin gidan iyayenta, amma ki yi min haquri domin na manta wallahi, na dai fi riqe wannan da na gaya miki.”
  Suka yi shiru, daman ita Hari ba ta iya yin magana sosai ba.
  “Yanzu ni dai na cika alqawari.” Cewar Karime, “Zan koma qauyenmu ne sai dai ki yafe ni, amma na san dole za mu rabu. Kin dai ji abin da mahaifiyarki ta faxa?”
  Hari ta kuma fashewa da kuka tana cewa “Iya ba ni da kowa sai dai ke, ke kaxai na sani, idan ki ka rabu da ni ya ya zan yi?”
  “Haquri za ki yi, ki rungumi yadda ki ka sami rayuwarki Hari, haka mahaifiyarki ta tsara miki, kuma a haka za ki rayu.” Cewar Karime.
  Hari tana ji tana gani, Karime ta rabu da ita, ta yi tafiyarta. A nan ta ci gaba da rayuwa, ta ci gaba da kwana a rumfar sayar da xanwaken Karime, duk wata wahala ta rayuwa ta fuskanceta tun a baya, don haka za ta iya jure wannan, kawai abin da ya fi damunta shi ne rabuwa da mace xaya da ta raineta, ta taso a tare da ita, ta sani wato Karime mai xanwake.
  Kwana huxu da tafiyar Karime, Alhaji Jabir ya tsinceta, ya kawo gidansa don ta zauna.
  Idan ta zo nan a tunaninta, sai ta ji wasu hawaye masu xumi sun gangaro daga cikin idanunta, ta ji zuciyarta ta yi zafi, ta yi quna.
  Tana nan zaune cikin hawaye a farfajiyar, bayan ta gama tunanin. Aka yi hon a babbar gate, cikin sauri maigadi ya je, ya buxe. Wani rantsattsen saurayi, matashi xan kimanin shekaru talatin zuwa talatin da ragowar motsi mai suna Munir tare da Zinatu suka shigo farfajiyar gidan a cikin motar. Munir xin ke jan motar, yayin da Zinatu ke zaune a gefensa, ta yi kwalliya sosai.
  Ya daidaita motar inda ya kamata, sannan ya yi fakin. Tun kafin su fito Munir yake kallon Hari da ke zaune. Da suka firfito, Munir ya tsaya yana kallon Hari, kallon baqunta?
  Zinatu ta kalle shi, sannan ta kalli wadda yake kallo, ta yi tsaki ta ce “Zo mu shiga mana.”
  Munir ya yi ajiyar zuciya, kana ya bi Zinatu suka nufi qofar shiga cikin gidan. Amma yana xan juyawa ya kalli Hari.
  Da suka je qofar shigar sai Munir ya tsaya, ya juya, ya  kuma kallon Hari.
  Ita kuwa Zinatu har ta shiga sai ta dawo, ta kalle shi. Sannan ta kuma kallon wurin da yake kallo.
  “Wata daqiqiyar ‘yar aiki aka kawo mana. Me ya sa ka ke kallonta?” Ta tambaye shi, tana kallon shi.
  Ya yi ajiyar zuciya, “Haka kawai na ji ina tausayinta.” Cewar Munir.
  Zinatu ta harare shi. “Mene ne abin tausayi ga ‘yar aiki wulaqantacciya? Ai kana vata tausayinka ne kawai.”
  “‘Yar aiki?” Munir ya maimaita a ransa, sannan ya yi murmushi ya tambayi Zinatu “Daga ina aka samota?”
  Zinatu ta yi dariyar mugunta ta ce “A titi Abbanmu ya tsintota, ya kwaso jaraba, ya kawo mana ita gida.”
  Ya dubi Zinatu sosai, sannan ya kuma kallon Hari da idanun tausayi, ya ce “Ban gane jaraba ba?”
  Ta kawar da kai, “Ba wannan ba ne ya kawo mu gidan nan ba mai sanyina. Ka zo mu shiga.” Ta yi masa fari da idanu, da murmushi a leventa.
  Munir ya yi ajiyar zuciya, ya bi bayanta. Har sun je za su shiga, sai ya juyo ya kuma kallon Hari.
  *
  A wannnan karon Hari tana zaune a jikin katangar farfajiyar gidan, kamar dai yadda abin ya zama mata  farilla. Shi kuma Munir yana tsugunne a gabanta. Hari ta kawar da kanta gefe guda cikin damuwa.
  “Ta ya ya kake tsammanin zan yarda da maganganunka? Ta ya ya kake zaton ban san yaudarata za ka yi ba ka cimma mummunar manufarka? Kamar yadda ire-irenku masu galihu suka saba yi ga ire-irenmu marasa galihu. Kar ka yi zaton ban san  cewa ungulu ba ta jewar banza ba? Sannan kuma ina roqonka don Allah ka daina zuwa wajena, domin hakan barazana ce a gareni matuqa ga mutanen gidan nan.”
  Munir ya yi murmushi ya ce “Ya kamata ki sani, ita kalmar nan ba a faxarta da qarya. Duk da na yi saurin faxa miki ita. To babu yadda za a yi a furta kana son mutum da gangan.”
  Hari ta kalle shi kawai, ta ce “Na sani, sai dai ana amfani da ita wajen yaudara. Kamar yadda ka zo da ita gareni. Ya kamata ka sani ban tava tunanin zuciyata za ta raunana har ka yaudareta da wannan kalma ba ka cimma manufarka, sai dai ka yi amfani da qarfi ko wani siddabarun.”
  Munir ya girgiza kai, ya ce “Ba zan tava yin haka ba. Wallahi, Billahillazi na faxa miki haka ne har ga Allah a zuciyata.”
  Hari ta kalle shi, ta kawar da kai tana hawaye. “Ba ka da wata hujja, ka fito kawai varo-varo ka ce ka ga banza za ka daka. Kuma in Allah ya yarda ba za ka yi nasara ba. Haka da gaggawa da sauri mutum ya faxa wa mace yana sonta, ai da walakin.”
  Munir ya ce “Ki yi haquri, ba yadda zan yi ne, kin san zuciya ba ta iya voye so, duk yadda mutum ya kai ga juriya ba zai iya voyewa ba, ni kaina na san na yi azarvavin furtawa.”
  Hari ta ce “Kai ya kamata in ba haquri. Idan da gaske kake, ka san ka fi qarfina nesa ba kusa ba. Zinatu ita ce sa’arka. Ba za ta tava yiwuwa ka haxa kanka da ni ba. Ni ba sa’arka ba ce, ka yi min nisa. Kawai dai abin da na faxa a baya ne dalilinka, ko ka qi ko ka so.”
  “So ba ya buqatar duk waxannan abubuwa da ki ke tunani Hari. Idan da yana buqata to da Zinatu ba ta ganni ta ce tana so ba, domin mahaifina ya zarci mahaifinta kuxi.”
  Hari ta kalle shi kawai, ba ta yi magana ba.
  Munir ya ci gaba “Ban tava cewa ina son wata ‘ya a duniyar nan ba, haka nan ban tava cewa ina son Zinatu ba, kuma ban tava jin ina sonta ba.”
  Hari ta tave baki, ta ce “Wannan kai ta shafa, ni ba ta shafeni ba.”
  Munir ya miqe tsaye ya xan yi shiru. Sannan ya ce “Ta shafeki mana, tunda ni ina sonki. Kuma ina so ki so ni.”
  Hari ta kalle shi cikin mamaki “Ana yin so dole ne?”
  “Ana yi mana.” Munir ya amsa mata.
  Ta yi dariyar takaici, “To ba zan so ka ba.”
  Shima ya yi dariyar takaicin, ya ce “Dole ki so ni.” Ya juya, ya fara tafiya don ya bar wurin.
  Hari ta bi shi da kallo tana hawaye.
  ENUGU
  Da yawan mutane suna mamakin yadda mace Bahaushiya ta zama ita Magajiyar karuwai a tsakiyar unguwannin qabilu a Enugun.
  Tun zuwan Barira Enugu wasu suke ganin ta zo da qafar dama, ita ba karuwa ba, amma yau da gobe sai ga shi ta zama jagora a gidan karuwan, har ma ta zama magajiyar su. Wani babban abin mamaki shi ne, yadda ba ta tava yin karuwancin ba, duk da zamowarta Magajiyar karuwai.
  Ita kam fes da ita, zuwanta cikin waxannan shekaru sai ga shi ta tara dukiya, ta zama mai kuxi, sunanta ya vace, sai dai a ce Hajiyarsu (wato karuwai). Babu abin da yake damunta face wani lokaci guda idan ta zauna tana wani tunani, tunanin da yake sa ta yin kuka, yake sa ta ta daxe tana zaune jugum.
  Ba karuwanci ko  neman kuxi ta zo yi Enugu ba, ta zo ne neman xanta Yusuf ne, ba ta gan shi ba, dalili ya yi zamanta a gidan karuwan, domin ta rasa wanda zai sauketa, sai wata karuwa Bahaushiya wadda ita kuma ‘yar asalin jihar Katsina ce, wannan dalili shi ya qaddara zaman Barira mahaifiyar Yusuf zama a gidan karuwai, saboda aminci da amanarta, yau da gobe sai ga shi ta zama jagorarsu.
  Tana samun kuxinta ne daga kyautuka da karuwai da Alhazan birni da kuma Ogogin Inyamurai da direbobi da suke ba ta.
  Har zuwa wannan lokacin tana tunanin za ta ga xanta, a baya an ce mata ana tunanin ko ya mutu, amma kuma tana ji a ranta xanta yana nan raye.
  Ta  share hawayenta, ta yi murmushi a ranta ta ce “Allah ya tsare min xana, ya nuna min shi kafin in bar duniya.”
  KANO
  Gwamnati ce ta gina lambun domin shaqatawar al’umma, an tsara shi gwargwadon yadda zai gamsar da wanda ya so ya gamsu xin. Akwai bencina don zama, da liluka don yin lilo, da ciyayi koraye shar don gamsar da mai fatan haka.
  Hari tana zaune a xaya daga cikin bencinan da ke lambun, da yake bencinan bibbiyu ne kowanne yana kallon xan uwansa, Munir ne shima a zaune a kan wanda yake kallon Harin, yana dubanta.
  Idan ka dubi Hari za ka tabbatar tana cikin damuwa. Haka shi ma Munir a cikin damuwar yake.
  “Na gaya maka akwai matsala. Kawai ka tashi ka maida ni gida.”
  “Babu wata matsala. Mutanen nan da ki ke tsoro ba damuwa suka yi da kasancewarki a gidansu ba, bare su duba su ga ba kya nan su neme ki. Nan kuma da muke ba kowa bare wani ya ganmu kamar yadda ki ke tsoro.” Munir ya faxa, sannan ya nisa. “Ni dai fatana ki sami nutsuwa ki furta min abin da nake son ji. Na yi miki alqawarin za ki sami sauyin rayuwa fiye da yadda ki ke zato.”
  Hari ta kalle shi kawai, sannan ta ce “Kana tunanin don kana ikirarin sani a daula shi ya sa zan so ka, har ka sami damar cimma burinka? To ka yi kuskure, ba zan tava cewa ina sonka ba, don ba na sonka, kuma bana jin zan tava sonka.”
  Munir ya girgiza kai cikin takaici “Ba nufina in sayeki da kuxi ko arziqin da Allah ya yi mana ba ne. Ina tausayawa rayuwarki ne kuma ina son in ganki cikin walwala da jin daxi da farin ciki kamar kowacce ‘ya. Kuma sona a gareki daban da taimaka wa rayuwarki da nake son yi. Ko da ba na sonki zan tallafawa rayuwarki.”
  Hari ta girgiza kai “Bari in sake maimaita maka, babu hanyar da daxin bakinka zai rinjaye ni Munir, ba zai yiwu ba.”
  Munir ya miqe tsaye, sannan ya durqusa a gabanta, ya marairace yana cewa “Ba daxin baki bane, ina roqo ne a gareki na san ba za ki qi yi min ba, ki tausaya min, har ga Allah nake sonki.” Ya yi shiru, ya fara hawaye. “Hari ban tava zubar wa da wata ‘ya mace hawaye ba. Na yarda da uzirinki da abin da ki ke gudu, amma ban yarda cewa ba kya sona ba, domin na ga soyayyata a idonki. Na yarda ki qi karvar soyayyar tawa a bisa wannan dalili naki, amma ki bar ni in taimaka miki. Sannan kuma ki sani lallai, idan ki ka qi karvar soyayyata, zan shiga mummunan halin da zai iya jefa rayuwata a halaka, kuma ke ce sanadi, sannan kuma laifinki ne.” Ya yi shiru yana hawaye, ya qura mata ido.
  Itama Hari hawayen take yi. Ta buxe baki kamar za ta yi magana sai ta kasa, ta sake buxewa a karo na biyu kawai ta ji mari a fuskarta. Kauuu!!!
  Cikin hanzari Munir da Hari suka miqe. Hari tana riqe da kuncinta, tana kallon Sunusi da ya mareta.
  Hajiya Silima da Sunusi da Zinatu ne a tsaye a kansu, duk ransu a vace.
  Zinatu tana kuka, ta ke cewa. “Munafuka, maciya amana, baqar halittar da ta zamewa iyalinmu bala’i.”
  Hajiya Silima ta kalli Zinatu, ta ce “Ki daina vata hawayenki a kan wannan jarababbiyar. Ni daman tun ranar da Alhaji ya shigo da ita gidan nan na san sai abin da hali ya yi, kuma ga shi muna gani.” Ta kalli Hari. “Wato shi ne har kin sami damar yaudarar yaron da an riga an gama yi musu magana da Zinatu. To ki sani waxanda suka fi ki ma sun yi kaxan bare ke.”
  Munir ya sunkuyar da kansa qasa yana takaici. Itama Hari kanta a sunkuye yake tana hawaye.
  Sunusi sai zare ido yake yana hararar Hari. Hajiya Silima ta kalli Sunusi, ta yi masa nuni da ido. Sannan ita da Zinatu suka juya a tare.
  “Yau xin nan za ki gane matsayinki, ki gane ko ke wace ce.” Sunusi ya sake zabga mata mari, ya finciki hannunta, ya ja ta da qarfi har tana faxuwa.
  Munir ya yi yunqurin bin sa, kawai sai ya ji ya kasa, ya buxe baki don yin magana, takaici ya hana shi, ya durqushe a wajen yana hawaye.
  A farfajiyar gidan Alhaji Jabir Sunusi ne yake ta dukan Hari, bai sassauta ba har sai da ya haxata da bango, kanta ya fashe ta faxi qasa sumammiya.
  *
  Falon ya yi tsit, babu abin da ke tashi sai qumajin faxan da Alhaji Jabir yake yi, duk ya haxa gumi hanci da goshi. Matuqar vacin rai, ransa ya vaci ba sai an faxa ba.
  Hajiya Silima da Zinatu zaune a gefe. A bakin qofar kuwa Sunusi ne a tsaye sai ciccije baki yake yi, yana cin magani.
  Alhaji Tahir ya ci gaba da faxan, yana cewa:
  “Babu wanda ya isa ya tsara min abin da nake so a gidana. Yarinyar nan ni na xaukota na kawota, kuma babu wanda ya isa ya fitar min da ita daga gida, don gida dai gidana ne, za ta yi rayuwa kamar ‘ya a gidan nan. Haka na tsara, ko an qi ko an so.” Ya kalli Sunusi. “Kai kuma wallahi idan ka qara sa hannu ka doketa ni da kaine, domin ranka zai yi matuqar vacin sai ka gwammace ba a haifeka ba.”
  Hajiya Silima ta muskuta cikin vacin rai, ta ce “Wai kai Alhaji ko son yarinyar nan kake yi ne, kake ta wata fuffuka? To wallahi ko ni ko ita a gidan nan, sai dai ka zavi xaya da za ta zauna.”
  Alhaji Jabir ya juyo a fusace cikin mamaki, sannan ya ce, “Na zaveta! Na zavi Hari.”
  Dukkansu suka kalle shi cikin mamaki da firgita. Kallon-kallo ya wadatu a xan lokacin, numfashi ya xan sarara, hankula suka tashi. Hakan bai dami Alhaji Jabir ba.
  “Kuma na yi shirin rabuwa da ke in har ba za ki bi abin da na tsara ba. Banzaye kawai ana tsara abu kuna vata wa mutane.” Ya yi waje cikin fushi.
  Suka bi shi, amma da kallo.
  *
  Falon gidan saukar baqin (guest house) mallakar Alhaji Jabir, ya ninka ainihin falukan gidan da iyalinsa suke tsaruwa da haxuwa.
  Can bisa xaya daga cikin kujeru da suka yi da’ira a falon, Hari ce zaune a takure. Sai kuma a tsaye a kusa da ita Alhaji Jabir ne yana kai gwauro ya kai mari, tsawon lokaci, sannan sai ya tsaya ya kalli Hari.
  “Na kawoki nan ne saboda lokacin kawoki ya yi. Zan mayar da ke mutum cikakkiya ta yadda duk wanda ya ganki sai ya kuma kallonki. Za ki tsere sa’a. Za ki keta tsara. Za ki zama babbar mace hakima kuma isasshiyar mace.”
  Ya yi taku gaba kaxan. Ya juya mata baya. “Hari za ki zama rantsattsiyar budurwa, kuma za ki zama budurwar danqo mallakarki sai wanda ya shirya, wadda Allah ya yiwa mafificiyar baiwa.”
  Ya je kan kujerar da ke kallon wadda take zaune, ya zauna yana kallonta yana murmushi.
  Hari ya xan yi tunani, ta tuna labarin da Karime mai xanwake ta ba ta, sannan ta tashi, ta je ta durqusa a gabansa, a nutse ta fara magana. “Me ya sa ka ke da duk waxannan burinka a kaina?”
  Murmushi kawai ya yi mata, yana kallonta sosai ido cikin ido.
  Hari ta ce “Ko abin da Hajiya ke faxa haka ne?”
  “Me take faxa?” Alhaji Jabir ya tambayeta.
  Hari ta miqe tsaye, ta koma kan kujerar da take ta zauna, sannan ta yi magana.
  “Cewa ta yi ko kana sona?”
  Alhaji Jabir ya yi murmushi, ya qura mata ido irin kallon soyayya. “Lokaci zai ba ki amsar wannan maganar ta ki.”
  Suka kalli juna.
  ENUGU
  Sale ya kurvi lemon, ya ajiye kofin, sannan ya dubi Yusuf, ya dubi yanayin falon Alhaji Yusuf xin, ya girgiza kai kawai, yana murmushi.
  “Ikon Allah kenan, wasu shekaru kamar goma sha huxu kenan ko sha biyar ne? Na dai manta, ka ke cewa kai ba za ka iya rayuwa a nan jihar qabilu ba, yau ga shi da alama har ka fi ni son rayuwa a Enugu.”
  Alhaji Yusuf ya girgiza kai, ya ce “Bari kai dai rayuwar ce ta juya, wai kwaxo ya faxa ruwan zafi…” Ya yi shiru, ya xaga kansa sama yana tunani.
  Sale ya kalle shi sosai, ya ce “Babbar matsalata da kai wannan tunanin da kake yawan yi…”
  “Ba zan iya daina wannan tunanin ba Sale, abubuwan da suka faru a gareni kowaye ba zai iya manta su ba. Zai rinqa yin tunani kamar yadda nake yi, ba mamaki ma ya fi ni.”
  Ya durqusar da kansa, sannan ya xauki ruwa a kofi ya kurva, ya yi ajiyar zuciya.
  “Mahaifina ya rasu, ba na tare da shi, mahaifiyata ta vata a yayin nemana, ba mamaki a yanzu ta mutu.” Ya xan yi shiru cikin damuwa, kafin ya ci gaba “Na rasa Harira, ta mutu itama….na rasa iyayen Helen….na rasa abubuwa da yawa Sale.”
  “Amma ka sami abubuwa da yawa Yusuf. Ka yi kuxi a tsawon shekarun nan, ka je Saudiyya ka zama Alhaji, ka mallaki kamfanunnuka da shagunan sayar da kayan lantarki, Helen ko in ce Halima wadda ka sauyawa suna, ta zama xiya a gareka, ka zama Alhaji, ka…..ka sami abubuwa da yawa Alhaji Yusuf…”
  Yusuf ya girgiza kai, ya ce “Dukkanin waxannan abubuwan da ka zayyana ba su kai abu xaya daga cikin abubuwa da na rasa ba Sale.”
  Sale ya yi nishi ya ce “Haka ne, kuma haka rayuwar take…”
  Shigowar da Halima (Helen) ta yi tare da sallama, shi ya katsewa Sale maganar da yake yi. Yarinya ta zama budurwa, kuma kyakkyawa da ita. Tsawon rayuwar da ta yi a hannun Yusuf ya zame mata uwa ya zame mata uba, ta sami iliminta na addinin Musulunci da na boko, ta yi saukar karatun Alqur’ani, da sauran littattafan Hadisai da Fiqhu da Sira da lugga da sauransu, sannan a vangaren boko musamman da yake ta samu tsallaken shekaru biyu a yayin karatunta na firamare da sakandire, yanzu tana shekara ta xaya a jami’a inda take karantar ilimin sanin halittu, wato Biology.
  Ilimin Halima da tarbiyyar da ta samu a wurin Yusuf ya taimaka mata wajen zama mai kyakkyawar tarbiyya da kyakkyawan hali. Kullum qara qaunar mahaifinta Yusuf take yi, yayin da shi ma yake qaunar xiyarsa, kuma take shiga ransa.
  Cikin kyakkyawar suttura wadda ta yi matuqar yi mata kyau take, daman ita ba ta yarda da sanya wulaqantattun kaya ba. A hannunsa yana riqe da takarda, ta iso ta durqusa har qasa ta miqa wa Yusuf tana cewa “Ga shi Daddy.”
  Yusuf ya yi saurin karva cikin sakin fuska, yana murmushi “Yawwa my daughter, na gode.”
  Ba ta tashi ba, tana tsugunnen, tana wasa da ‘yan yatsun hannunta, da alama akwai wani abu da take son cewa.
  Yusuf ya kalleta, ya yi murmushi “My daughter me ya faru ne?”
  Cikin ladabi ta ce “Daman game da littattafan nan ne da….”
  “Oh sorry!” Ya katse ta, “Wallahi na siyo miki na manta su a cikin mota ne.” Ya xauki makullin motar ya miqa mata, “Je ki xauko.”
  Ta sa hannu biyu  ta karva, sannan ta tashi, ta fita tana taku a hankali cikin nutsuwa.
  “Allah mai iko.” Sale ya faxa lokacin da Halima ta fita daga falon.
  Yusuf ya kalle shi.
  “Gani na yi ‘yar Ibo ta zama ‘yar Hausa. Allah ya taimaki rayuwar Halima, ta taso cikin hasken Musulunci, da alama wannan ne dalilin da ya sa Allahn ya haddasa muqaddarin zamanta ya dawo gareka.” Ya yi shiru. Yusuf ya nisa.
  “Lokaci ya zo da zan nemi mahaifin Halima da danginta. Lokaci ya yi da zan tonawa Igwe asiri, komai zai faru sai dai ya faru, cin amanar da ya yiwa iyayenta ya zo qarshe.”
  Sale ya girgiza kai, “Haka ne, amma akwai matsala.”
  “Wacce irin matsala?” Yusuf ya buqata.
  “Na san mahaifin Helen idan har yana da rai zai ci gaba da neman ‘yarsa, idan ya ganta kuwa zai karveta, koma ya ya suka yi da Igwe to zai so xiyarsa ta dawo gare shi, idan ta koma gare shi me kake tsammanin zai faru?”
  “Sai ka faxa.” Yusuf ya ce da Sale.
  Sale ya ce “Halima za ta koma addinin mahaifinta. Sannan rayuwarta za ta sauya, ta juya baibai dama ta koma hagu.”
  Yusuf ya girgiza kai, “Haka ba za ta tava yiwuwa ba.”
  “Ta ya ya ka san hakan ba za ta yiwu ba?” Sale ya buqata.
  “Sanin hali. Sanin Halima da na yi sosai shi ya sa.”
  “Uhm. Bari kai dai rabu da wannan rayuwar.” Cewar Sale.
  “Na daxe da rabuwa da ita Sale.” Cewar Yusuf.
  Suka yi shiru suna numfashi a xaixaiku, suna kuma tunani da nazarin rayuwar.
  KANO
  Fish Park, xan qaramin wurin cin abinci ne, wanda an fara shi ne da sayar da kifi, daga baya da masu wurin suka fahimci akwai ilhama suka fara sayar da sauran kayan ciye-ciye da shaye-shaye, kamar su naman kaji, naman salwa, farfesu da sauransu. Haka nan a vangaren kayan shaye-shaye, ban da na kwali da gwangwanaye har da haxin gargajiya masu qara lafiya.
  Wurin an tsara shi ta yadda babu ruwan na wancan teburin da na wannan teburin, kuma babu hayaniya, ga tsafta, ga qamshi da yake tashi. Zai yi wuya wani ya san wani ya zo wurin.
  Teburin da ke can gefen gabas na wurin cin abincin cike yake da kayan shaye-shaye da ciye-ciye kamar farfesun kifi da na salwa da kaji da su tufa da lemon kwali iri-iri da sauransu.
  Alhaji Tahir da Alhaji Nasir da Alhaji Jabir ne a zaune. Suna ci suna hira, suna nishaxi suna dariya.
  Alhaji Nasir ya kalli Alhaji Jabir da ya ga ya yi shiru, ya yi gyaran murya. “Uhm’uhm. Alhaji ko a kawo abar ne?”
  Alhaji Jabir ya yi dariya, ya ce “Me kenan?”
  Alhaji Nasir ya kalli Alhaji Tahir shima yana dariya. “Ka ji wai ya manta abar?”
  “Ai sai ka tuna masa ka ce masa ruwan kwavi ko kuma Ruwan Bagaja.” Cewar Alhaji Tahir.
  Alhaji Nasir da Alhaji Jabir suka haxa baki, suka ce “Arna na bakin tafki ba. Kamru uwar haddasa a sha ki, don alhaki ba aikin lada ba.”
  Suka yi dariya gaba xayansu, sannan suka tafa.
  Wata zuqeqiyar budurwa, sanye da qananan kaya ta shigo wurin don ta siyi abinci.
  Gaba xayansu, suka bi ta da kallo. A daidai lokacin Alhaji Tahir yana tsiyaya lemo a kofi bai san lokacin da ya rinqa tsiyayawa a kan plate xin farfesun kifi ba.
  Alhaji Nasir ya kai masa duka, yana faxin “Girma! Girma dai Alhaji.”
  Alhaji Jabir ya karva yana cewa “Kima da mutunci dai xan Audu.”
  Suka sake qyalqyale wa da dariya gaba xayansu.
  Alhaji Jabir ya nisa yana cewa “Wannan abu ya tuna min da ranar bakwai ga watan bakwai a kusa da rumfar Karime mai xanwake.”
  Suka yi shiru suna tunani, jim kaxan sai kuma suka tuna, suka nisa.
  Alhaji Tahir ya yi dariya ya ce “Ranar buge aiki kenan?”
  Suka yi dariya, cikin nishaxi.
  Alhaji Jabir ya ce “Bana mantawa da wannan ranar. Yarinya xanya, ai ni tun da nake a rayuwata ban tava hawa gulbin da ya kai wannan daxi ba.”
  Alhaji Nasir ya ce “Ba wanda zai manta da wannan ranar. Kun san fa ni na fara kwashe mata aiki.”
  “Ai wannan rana tana cikin karatun mafarkina. Abin mamaki, babu wanda bai gamsu ba.” In ji Alhaji Tahir. Suka ci gaba da shan lemo suna nishaxi.
  *
  Hari ce kaxai a cikin faffaxan kuma qayataccen falon a gaban madubi (mirror), tana kwalliya.
  Sanye take da baqar riga shirt, da baqin wando irin na nigogin yanzu wato fensil, da baqar safa. Kanta babu xankwali, ta xaure gashinta. Sannu a hankali tana shafa, tana goga hoda da sauran mayuka, har ta  gama.
  Ta xauko baqin takalmi ta sa, ta xauko baqar riga kwat qarama ta xora a kan shirt xin. Ta xauko hula malafa baqa ta xora a kanta. Sannan ta xauko baqin gilas.
  Tana kai gilas xin fuskarta ta juye, kyawunta ya bayyana sosai. Sannan ta xauko wasu hotuna guda uku, ta kalle su xaya bayan xaya, ta girgiza kai, ta maidasu cikin dirowar da ta xauko su. Ta xauko jan baki ta sake goga wa a leve, ta shafa eye-shadow ta kuma shafa man fuska, kwalliya kamar ba za ta daina ba. Sannan ta juya a gaban madubin ta ga, ta yi kyau sosai, ta gamsu da hakan, sannan ta nufi qofa don fita, tana takun qasaita.
  Ita kanta Hari ta san jiya ba yau ba, rayuwarta ta sauya daga xan lokacin baya, zuwa na yanzu da Alhaji Jabir ya xaukota daga cikin iyalinsa, ya wareta, yake yi mata hidima.
  Sannu a hankali Hari ta isa farfajiyar gidan. Akwai motoci rantsattsu a ajijjiye. Ta zaro mukullin mota matrix daga aljihunta, ta danna key-remote xin motar da za ta shiga, motar ta yi qara.
  Tana isa ta buxe murfin qofar motar ta shiga. Ta tasheta. Kafin ta fara tafiya ta saki wani kixa mai nauyi, sannan ta ja motar ta tafi.
  *
  A rayuwar Alhaji Jabir yana son hutawa a inda shuke-shuke suke, ko wuri da yake lambu ne. Yanzu haka shi ne zaune a gaban wani tebur mai xauke da kayan marmari da madara da lemo a kai, a kusa da shuke-shuke masu kyau, yana shan madara, ga jarida a hannunsa yana karantawa.
  Hari ta qaraso a mota daf da shi ta yi fakin ta fito, ta gyara gilas xin dake fuskarta, tana kallon yanayin wurin, sannan ta rufe motar. A hankali ta nufi inda Alhaji Jabir ke zaune.
  Alhaji Jabir ya ankara da zuwanta a daidai lokacin da yake shan madara, yana kallonta. Bai san lokacin da ya rinqa tsiyaya wa kansa madarar ba.
  Hari ta qarasa wajen tana faxin “Haba my gentleman, aje-waya mana, kana vata rigarka fa.”
  Alhaji Jabir ya yi saurin dubawa, ya yi dariya, “Au, uhm.” Ya ajiye robar madarar. “Ai dole in vata rigata ba. Kullum a sabuwar Hurul’aini ki ke zuwar min. Hari ke kyakkyawa ce.”
  Hari ta yi murmushi. “Na ji, sai ka yi sauri ka tashi mu tafi, ka canza rigarka a can. Ka ga mutane sun fara kallon ka.” Ta kalli wani da ya wuce yana kallonsu. “Yi haquri, na barka kana ta jirana ko?”
  Alhaji Jabir ya ce “No, ba komai.” Ya tashi, yana kicin-kicin xin save babbar riga, yana kallonta har ya yi tuntuve da teburin da yake kai bai lura ba.
  Suka nufi mota.
  A cikin motar, Hari tana jan motar, tana yi tana juyawa ta kalli Alhaji Jabir. Shi kuma yana ta kici-kicin cire babbar rigar, har ya cire, ya jefata bayan motar.
  “Kana ban mamaki my gentleman.” Cewar Hari.
  “Kin ga, kin cancanta ne, kin yi iya yi, komai ya ji, don haka ba abin mamaki ba ne don mutum ya rikice saboda ke.”
  Hari ta yi dariya.
  Alhaji Jabir ya ci gaba da cewa “Wannan dalilin ne fa ya sa na ke taka-tsantsan da ke. Kuma na qi yin gaggawar mayar da ke gidana tsawon lokacin nan da ki ka yi a guest house.”
  Hari ta ce “Ni na fi jin daxin zamana a nan guest house xin ma.” Ta xan vata rai.
  “Duk da haka, nima na sani amma dole zan kai ki in gabatar da ke garesu.”
  Hari ta yi masa hararar tafiyar da zuciya ta ce, “Wacce irin gabatarwa kuma ban da ta farko?”
  Ya yi qwafa “Waccan daban, wannan daban. Kar ki manta waccan gabatarwar an yi miki ne a matsayin tsintacciya, kuma wadda ba ta wayewa ba, amma wannan a matsayin haxaxxiyar mace za a yi shi, idan a can an raina miki, a wannan lokacin sai dai a sara miki.”
  Suka yi shiru.
  Hari ta kalle shi da gefen idanu. “Haka ma ka ce za ka gabatar da ni ga abokinka, amma shiru.”
  “Haka ne. Amma wai ke me ke damunki ne, kin manta yadda duk wanda ya ganki yake neman liqe miki kamar danqo. Wannan ja’irin yaron ma fa Munir yana can wai shi sai ke. Dubi yadda Alhaji Nalado daga ganinki sau xaya ya nace a kan in haxa shi da ke, haka wannan xan iskan likita Dr. Ken daga ya baki magani ya duba lafiyarki sai dogon Turanci wai wani Hey I love this pretty beautiful girl.” Ya maqe murya na tsokana. “Ka ji tsinanne.”
  Suka yi dariya.
  “Kin san sunan da ya dace da ke kuwa?”
  Hari ta kalle shi tana murmushi. “A’a sai ka faxa.”
  “Budurwar danqo ki ke, mai lakato wanda ya ganki.”
  Suka fashe da dariya.
  *
  Falon ya haxu, gwargwadon haxuwa, kuma an tsara shi yadda ya kamata, komai a muhallinsa. Idan ka xauke fankar da ke juyawa, yanzu falon ya yi tsit, kamar babu halittu a ciki.
  Alhaji Tahir ne tsaye ya juya wa xansa Munir baya. Shi kuma Munir xin yana zaune a kan kujera. Dukkansu suna cikin damuwa, Munir ya yi tagumi.
  Idan ka ga Alhaji Tahir ba sai an kuma yi maka wani bayani ba, ka san cewa uba ne ga Munir, yanayi da siffa.
  Jim kaxan Alhaji Tahir xin ya yi gyaran murya, sannan ya juyo, ya kalle shi. “Ka san me kake tunanin aiwatarwa kuwa? Ko ka san tun muna yara muke tare da mahaifin wannan yarinya, Alhaji Jabir. Kawai yanzu za ka zo min da wata magana. Muna murna, muna farin ciki, zamu haxaku, mu qara danqon zumunci shi ne za ka zo ka nemi bijirewa mutane.” Ya yi shiru. “Wai shin ma me ya sa ka ce yanzu ka fasa, ai ba a yin abu sai da dalili. Me ta yi maka, ko me wani ya yi maka?”
  Munir ya miqe tsaye a hankali, ya xan rissina a gefen mahaifin nasa, sannan ya ce. “Abba babu abin da aka yi min. Kuma ba cewa na yi na fasa auren Zinatu ba. Kawai dai a yanzu na samu wadda zuciyata take so ne, ba ita wadda aka haxamu ba. Kuma duk wani qoqari da zan yi in voye abin ya gagara, ba ni da abinda zan yi sai dai in amincewa zuciyar tawa, domin rashin yin hakan na iya sa in rasa kaina gaba xaya. Ita kuma Zinatu abin da na yi qudiri a raina shi ne, idan na auri ita wadda nake son sai kuma in dawo gareta, in aureta…”
  Alhaji Tahir ya kalle shi a fusace. “Wace ce wannan, ‘yar waye da ta janye hankalinka daga abin da iyayenka suka tsara kuma suka zava maka?”
  Munir ya xauko wayarsa, ya daddana, hoton Hari ya bayyana, amma a lokacin ba ta yi haxuwar yanzu ba, tsohon hoto ne. Ya ajiye wayar a kan teburin da ke gabansu.
  “Ga ta nan.” Ya juya, ya fita daga falon.
  Alhaji Tahir ya kalli wayar cikin fushi, yana tunanin wane irin rainin wayo ne na ‘yan zamani a yanzu. Ya yi jim. Sannan ya matsa a hankali, ya xauki wayar ya kalla. Nan da nan yanayinsa ya sauya, ya xaga gira ya fara murmushi. Sannan ya gyaxa kai, ya zaro wayarsa ya fara daddanawa yana kallon wayar xan nasa. Ya buxe bluetooth xin wayarsa, ya tura hoton Hari zuwa cikin wayarsa.
  Ya kammala yana murmushi, sannan kuma yana girgiza kai
  *
  Tsaye suke a cikin farfajiyar gidan sun yi cirko-cirko suna kallon juna, a yanzu idanun Zinatu ya fara tara qwalla, ita da Munir xin duk a cikin damuwa suke.
  Cikin vacin rai take magana “Amma Munir ka ba ni mamaki wallahi, kuma ka sire min. A ce ka rasa wadda za ka juya min baya sai domin ‘yar shegiya, mara iyaye, mara asali. Ai wannan ci baya ne, kuma wulaqanta kaine. Babban abin kunya ne mutane su ji cewa saurayina yana son wannan wulaqantacciyar yarinyar.”
  Munir ya zuba mata idanu a fusace, “Zinatu ba zuwa na yi ki gaya min maganar banza ba. Zuwa na yi ki gaya min inda Hari take.”
  Zinatu ta yi matuqar firgita da jin wannan magana ta Munir. Ta kalle shi, qwallar da ta taru a idanunta ta fara fitowa, ta dafe qirjinta ta ce “Munir!” Ta girgiza kai cikin takaici. “Yanzu Munir abin da za ka gaya min kenan?”
  “Ba gaya miki na yi ba, tambayar ki nake. Ki ba ni amsa, ko in matsa gaba in tambaya.” Ya nuna cikin gidansu.
  Zinatu ta fashe da kuka mai qarfi. Ta ruga cikin gida.
  Bin ta da kallo ya fara yi, sannan ya yi tsaki, shima ya bi ta cikin gidan da sauri.
  *
  Alhaji Tahir ne a cikin motar yana tuqawa a nutse, a hankali. Sannan yana waya.
  “…Ina fatan da manajan Gizo Computers nake magana…”
  Ya xan yi shiru, bayan da ya ji abin da aka faxa masa daga can vangaren na wayar, sai ya xora da faxin
  “….To wani hoto ne a cikin memory card xin wayata nake son a fitar min da shi a matsayin hoton kati.”
  Ya kuma yin shiru, sannan.
  “……yanzu ma ina kan hanya, zan qaraso nan da mintuna ashirin da biyar, daman na kira ka ne don in tabbatar kana nan kafin in zo…..To shi kenan.”
  Ya kashe wayar, yana murmushi. Ya ci gaba da tuqinsa, har ya sha wata kwana.
  *
  Gefe guda na lambun Munir ne zaune da Hari, sun yi kwalliya dukkaninsu, sun sa tabur a tsakiya suna duban juna.
  Munir ya qura wa Hari ido cikin tsantsar qauna. Ita kuma tana yankar tuffa tana ci, ta sunkuyar da kanta qasa saboda kunya da kissa irin ta mace. Har dai ta damu da kallon qurillar da yake yi mata, ta xago kai ta kalle shi tana murmushi.
  “Kai kallon ya yi yawa fa.”
  Ya yi saurin yin ajiyar zuciya, ya kawar da kai. Jim kaxan ya sake xora idanunsa gareta yana kallonta yana murmushi.
  “Kin wahalar da ni, kin wahalar da zuciyata Hari. Me ya sa ki ka guje ni tsawon wannan lokacin?”
  Ba ta yi magana ba, ta ci gaba da cin tuffarta.
  “Ke fa nake tambaya?” Cewar Munir.
  Ta yi murmushi “To yanzu ba gani na dawo gareka ba. Sai me kuma?”
  Ya yi ajiyar zuciya. “Hari ki sanar da ni abin da ki ka qi sanar dani tun a baya, in har abin da idanunki suka gaya min gaske ne.”
  Hari ta kalle shi cikin mamaki. “Me idanun nawa suka gaya maka?”
  “Sun nuna min kina sona, kuma sun tabbatar min da haka. Saura kawai ki furta min da bakinki, in dai ba so ki ke zuciyata ta fashe ba.” Munir ya faxa cikin marairaicewa.
  Ta yi dariya, “Idan na gaya maka, ka ga ka sami amsa biyu kenan, ai sai gatan ya yi maka yawa, ko ba haka ba?”
  “Ba haka ba ne.” Ya ce kamar zai yi kuka.
  Ganin yana neman fashe mata da kuka, Hari ta yi sauri ta ce “To ina sonka.”
  Cikin hanzari ya miqe tsaye, yana shafa Fatiha. “Alhamdulillahi, masha Allahu. Kai amma…”
  Hari ta katse shi, “Amma da sharaxi.”
  Ya yi saurin kallonta, har yanzu yana murmushin jin daxi. Ya zauna. “Mene ne sharaxin, wanda ya riga ya zama cikakke tun kafin ki faxa min?”
  Ta yi murmushi saboda jin abin da ya ce, ta buxe baki don yin magana, wayarta da ke cikin jaka, ta yi qara alamun an kira ta. Ta xauko wayar daga cikin jaka, ta danna wajen karvar kira, ta sa a kunne. Ba ta yi magana ba, kawai sai yanayin fuskarta ya sauya zuwa vacin rai, sannan ta ce.
  “To gani nan.” Ta yi saurin tashi, ta juya ko magana ba ta yiwa Munir ba, ta fara tafiya.
  Munir ya bi ta da kallo cikin mamaki, fuskarsa ta sauya zuwa vacin rai.
  *
  A falon gidan saukar baqi na Alhaji Jabir, Hari ce a tsaye, ko jakar da ta baro wurin Munir da ita ba ta ajiye ba, shi ma Alhaji Jabir xin da suke tare, yana tsaye, yana dubanta.
  “Ko kaxan ba na son wannan yawon. Kin san yadda mutane suke ta zurutun bibiyarki, suna cewa suna sonki, me ya sa ba za ki rage fita ba?”
  Hari ta xan sassauta murya ta ce “Zan rage my gentleman, I am sorry. Bana so kana vata ranka, don’t worry please.”
  Suka yi xif, babu mai yin magana sai numfashi tsawon xan lokaci, har Alhaji Jabir xin ya sauko daga fushin da ya yi, zuciyarsa ta yi sanyi. Ya yi murmushi.
  “Ai ke ce kin kasa gane baiwa da ni’imar da Allah ya yi miki, kina nema ki xebo mana yuyar mutane.” Ya xan tsahirta. “Sannan kuma ina son in mayar da ke gidana wajen iyalina. Ya ki ka gani? Don lokaci ya yi.”
  Hari ta marairaice cikin shagwava, “Duk yadda ka yi daidai ne.”
  Alhaji Jabir ya ji daxi sosai, ya ce “Duk da haka, zan so ki gaya min, kamar zuwa yaushe ki ke ganin ya kamata in mayar da ke xin?”
  Ta nisa, ta ce “Gaskiya ne. To ka qara min ko sati biyu ne, ina son in gama karance wani littafina a tsanake, don bana son karatun ya shiga hayaniya.”
  Ya yi dariya, “To ‘yar boko. Hari ke dai ‘yar baiwa ce, komai karvarki yake. Kyau ya amshe ki, kwalliya ta karve ki, murmushi ya amshe ki, boko ma da ba ki fara shi ba tun farko, ya karve ki.”
  Suka yi dariya.
  *
  Ita dai Hari tana son zaman gaban madubi, ko don yin kwalliya, ko kuma don yin tunani, ko haka kawai ka ga ta zauna tana qurawa kanta idanu, kamar mai tunanin wata rana za ta rikixe ta zama wata halittar.
  Ta yi shiru tana kallon kanta a jiki. Wani hoto ne a gabanta a kife. Ta sa hannu a hankali ta xauki hoton ta duba shi, hoton Alhaji Tahir ne, mahaifi ga xan matashin saurayinta Munir.
  *
  A can nasa gidan, a tsaye a tsakar xakin barcinsa, Alhaji Tahir ne yana ta safa da marwa hoton Hari ne a hannunsa, idan ya kai safa sai ya kalli hoton haka idan ya kai marwa ma. Yana yi, yana murmushi tsawon lokaci, kafin daga bisani ya je ya zauna a kan kujera, ya qurawa hoton idanu.
  *
  Har yanzu Hari tana zaune a gaban madubin, sai ta xan nisa, ta xauki hoton Alhaji Tahir xin da ke gabanta, ta miqe tsaye, ta qurawa hoton ido. Kana ta ajiye hoton a kan gaban madubin tana kallo lokaci guda kuma tana qoqarin xauko jakarta da ke gefe itama ajiye.
  *
  A can nasa vangaren, Alhaji Tahir ya jingina hoton Hari a qirjinsa, yadda dai ‘yan soyayya suke yi, xan lokaci, sannan ya ajiye shi a gaba yana kallo yana murmushi.
  *
  A inda take a tsaye Hari ta xauko jakar tata, ta lalubo farar takardar da Karime ta ba ta, daga mahaifiyarta, ta warwareta, ta karanta rubutun da ke ciki, sannan ta kuma kallon hoton Alhaji Tahir xin, ranta ya qara vaci. Ta cije, baki, ta xauko hoton, ta kifa shi.
  *
  Alhaji Tahir ya sumbaci hoton Hari da ke hannunsa, sannan ya qyalqyale da dariya, kamar mahaukaci.


  BABI NA SHIDA
  A
  gogon da ke falon gidan Alhaji Tahir kamar sauran agogunan duniya da aka saita su daidai, ya nuna qarfe goma sha biyu da rabi da minti uku (12:33) na dare. Falon babu kowa, sai yanzu da Alhaji Tahir ya fito daga xakinsa yana tafe a hankali sanye da kayan barci, ya shigo falon.
  Ransa a vace yake, ya xaga kai ya kalli agogon, sannan ya je ya zauna a kan kujera, ya yi ajiyar zuciya.
  Yana nan zaune cikin tunani, kamar ya tuno wani abu, sai ya xaga kai ya kalli hoton su na iyali, hoton da ke xauke da shi da matarsa  Hajiya Feenah da xansa Munir, hoton ya yi kyau.
  Tsawon lokaci ya xebe yana kallon hoton, bai san lokacin da ya yi tagumi ba.
  Yana cikin wannan hali, ya zura hannu a cikin aljihun rigar barcinsa, ya xauko hoton Hari, ya kalla, sannan ya mayar da shi cikin aljihu. Ya miqe a hankali, ya nufi xakinsa zai shiga. Sai ya ji kamar an turo qofa a bayansa, hakan ya sa shi tsayawa, sannan ya juyo.
  Hajiya Feenah ta shigo falon babu sallama, ta yi kwalliya sosai, yanayinta yana xauke da yanayin maye, duk da ta yi ‘yan dabaru, amma babu wanda zai kalleta, ya kasa gane ta sha giya.
  Alhaji Tahir da Hajiya Feenah suka tsaya suna kallon juna, har zuwa lokacin da Alhaji Tahir ya yi ajiyar zuciya, ya kuma kallon agogo, sannan ya kalli matar tasa cikin fushi.
  “Wato yawace-yawacen naki ya wuce iya rana har da dare ma? Iskancin naki a yanzu ya qara havaka ko? Wai ke me ki ka xauki matsayin auren da yake kanki ne, me ki ka mayar da ni ne a matsayin mijin ki?”
  “Shashasha mana! Shashasha na mayar da kai.” Ta faxa cikin maye, tana yi masa wani irin kallo.
  Ya zazzaro idanu da ximbin mamaki, “Ni ki ke kira shashasha?”
  Hajiya Feenah ta gyaxa kai. “E mana. Ka manta ran nan, kai ka nemi in kiraka da wannan sunan na xaga maka qafa? To yanzu shashancin ka yi shi ya sa na kira ka da sunan. In ban da shashasha ma, ta ya ya ina dawowa sai ka ce wata qaramar yarinya ka hau yi min faxa, ai wannan ma iskanci ne da shashanci….”
  Bai san lokacin da ya qarasa gareta ba a zuciye, ya kwasheta da mari har sau biyu.
  “Duk giya ko qwayar da ki ka shawo ni ba za ta hanani ladabtar da ke ba, idan kuma ki ka sake, ki ka ci gaba da waxannan kalaman naki a gareni, to za ki yabawa aya zaqinta yanzun nan.”
  Hajiya Feenah ta fusata, ta fara magana cikin maye. “Ba ka isa ka hanani buxa baki in yi magana ba, kuma wallahi wannan marin kamar a bakin rayuwarka ka yi shi.”
  Ta wuce xakinta tana tangaxi.
  Alhaji Tahir ya bi ta da kallo cikin mamaki, sannan ya juya don ya shiga nasa xakin, a nan suka haxa ido da Munir wanda yake tsaye a bakin qofar shigowa falon daga cikin gida, yana hawaye saboda halin da iyayensa suke ciki, da abubuwan da ya ji a tare da su.
  *
  Munir ya taho a hankali zuwa inda motarsa ke ajiye, yana riqe da jaka (briefcase) a hannunsa. Yana zuwa wajen motar, ya buxe qofar gaba, ya ajiye jakar, sannan ya rufe, ya xauko wayarsa daga aljihu ya daddana lambobi, sannan ya kara a kunne.
  A can bakin mudubi na guest house, Hari ce a zaune tana yin kwalliya. Wayarta dake gefe a ajiye, ta yi qara, sai ta xauka ta duba fuskar wayar, ta ga mai kiran an rubuta M. Ta yi murmushi sanin cewa Munir ne ya kira, ta danna abin karvar kira, ta kara a kunne.
  “Hello…”
  Munir yana tsaye a bakin motarsa, yana murmushi, har zuwa lokacin da ya ji daga nata vangaren Hari ta xaga wayar.
  “Assalamu alaikum mai haifar da murmushin kan fuskata.Ya ki ke?”
  “Kamar yadda ka ke cikin qoshin lafiya. Kai nake yiwa kwalliya ma a yanzu.”
  “Ma sha Allahu.” Ya xan yi shiru cikin jin daxi, kana ya xora da cewa “Wallahi nima ina ta shirye-shiryen wannan haxuwa tamu, sai ga shi kuma Dad xina ya yi min wani aike wai yanzu-yanzun nan zan wuce China.”
  Hari ta zare idanu cikin mamaki, ta ce “China?”
  “Wallahi kuwa. Amma ba zan tafi ba sai gobe, duk da shi mun rabu dashi a matsayin na tafi xin. Don haka zan je otel ne in zauna har sai na ganki zuwa gobe sai in wuce.”
  Hari ta yi dariya kaxan ta ce “Ka je mana idan ka dawo ai ma haxun, ko za ka daxe ne a can xin?”
  “Haba dai, ba zan iya tafiya ba tare da mun tattauna ba, maganar ce ai kin san tana da muhimmanci sosai. Gara in tsaya mu yi ta, sai in tafi zuwa gobe.” Cewar Munir.
  “Ba matsala ina jiranka.” Ta amsa masa.
  “Da zarar na nutsu za ki ji ni  zuwa an jima, yanzu ma otel xin zan je.” Ya kashe wayar, ya zagaya, ya buxe motar ya shiga, ya tasheta, ya tuqa ya tafi, yana murmushi. Kai tsaye Royal Hotel ya nufa.
  *
  Rashin haxuwarta da Munir a wannan lokacin ya sa Hari ta yi tunanin amsa kiran da Alhaji Tahir ya yi mata, tun jiya ya matsa mata da kira a waya gami da saqonnin waya, wai yana son su haxu.
  Ta xan yi jim tana tunani, sannan ta xauko waya ta kira Alhaji Tahir xin, cikin zumuxi ta ji yana amsa mata. Kawai cewa ta yi.
  “A ina zamu haxu?”
  Ya amsa mata, ya yi mata kwatancen wurin da za su haxu, wani ofis xinsa da ke keve a unguwar Qwarori. Ta ce masa kawai, gani nan tafe.
  ‘Yan mintuna ne da ba su wuce talatin da biyar ba, suka sada Hari da inda Alhaji Tahir ya ce su haxu, kuma cikin wannan lokaci, shima tuni ya sa an tanadar mata abubuwan motsa baki iri-iri, an jibge a kan tebur.
  Tun shigarta yake buxe bakin murmushi, bai rufe ba, ya ba ta kujera ta zauna, shima ya zauna, ya yi mata tayin cin abin sha da ciye-ciyen da ya tanadar mata, kamar yadda bai disashe a murmushinsa ba, haka bai daina kallonta ba, shigarta ta yi masa kyau, komai nata ya  yi masa kyau, fatansa Allah ya kai damo ga harawa, jinsa yake yi a cikin wani hali kamar a qololuwar sararin samaniya.
  Da Hari ta ji shirun ya yi yawa, sai ta miqe a hankali, ta xan yi taku tana duban yanayin ofis xin, tana kuma nazarin kayayyakin alatun da aka zuba a ciki, sannan jim kaxan ta juyo, ta kalli Alhaji Tahir.
  “Alhaji na fa san kai ne mahaifin Munir. Ko ka xauka ban sani ba?”
  Alhaji Tahir ya yi dariya, ya ce “Ko ba ki sani ba ma ni zan sanar da ke da kaina domin hakan shi ne mataki na farko na cimma burina na samun soyayyarki Hari.
  “Abu na farko da ya kamata in nusar da ke shi ne, matsayinki ya wuce yara, ki fi qarfin vata lokaci da yin soyayya da su, yaron nan da ya ganki ya yi azarvavin cewa yana so, kin girmi tattalin arziqinsa, kin girmi ajinsa, kin yiwa matsayinsa fintinkau, kin shallake tunaninsa kakaf. To me ya sa za ki tsaya vata lokacinki a banza a kan mafi qanqantar matsayi a kanki?”
  Ya yi shiru yana kallonta. Ita kuwa murmushi take yi.
  “Abu ne na zahiri da ba sai an tsaya ana yi miki tambihi a kansa ba, ke budurwa ce ta danqo wadda kin fi qarfin kai hannun yaro. Don haka ina mai hanzarta shawartarki, ki zare tunanin wani xan qaramin arne a lokacin da ake maganar su Ci-wake. Ni na shirya wa xaga darajar rayuwarki na cillata can qololuwar sararin samaniya, in zubata a zubin da ba a tava zuba rayuwar wata ‘ya budurwa ba…”
  Wannan lamari yana baiwa Hari mamaki, mutanen da ta sa a gaba, suma sun sa ta a gaba, mutanen da take neman tsinkawa igiyar rayuwa, su kuma suna neman xinke mata igiyar rayuwa, mutanen da take neman ganin bayansu, su kuma suna neman ganin ci gabanta. Sai dai duk da haka ta san suna da wata manufa a tare da ita, manufarsu iri xaya ce da manufar da suka cimma a kan mahaifiyarta, suka kai rayuwarta qarshe, suka mayar da ita daban a sauran halittu.
  Hari ta juyo a hankali, ta dubi Alhaji Tahir ta ce. “Kana so ne in watsar da soyayyar xanka Munir in karvi taka kenan?”
  Alhaji Tahir ya gyaxa kai ya ce “Abin da nake nufi kenan Hari.”
  Suka kalli juna cikin wani yanayi, kowanne da yanayin da yake ciki.
  “Za mu je Royal Hotel mu ci abinci.” Ya ce da ita.
  *
  A daidai wannan lokacin Munir ya fito daga cikin Royal Hotel, ya nufi qofar daga waje otel xin domin siyo katin waya, yana tafe ya xauko wayarsa yana daddana lambobi, ya yi kira, sannan ya kara a kunne, ya jira domin ya ji an xauka.
  Kiran ya yi daidai da lokacin da su Hari da Alhaji Tahir ke tafe a mota don zuwa Royal Hotel, inda za su ci abinci.
  Hari ba ta xauki kiran Munir ba, don haka ya qara danna kira, ya kara a kunne a karo na biyu, zuwa yanzu ya isa xan kiost xin sayar da katunan wayar da ke wajen otel xin, har ma ya miqa kuxi a bashi katin. Aka miqo masa, ya juya don komawa cikin otel xin. Wannan ya yi daidai da isowar motar mahaifinsa Alhaji Tahir wajen, kai tsaye motar cikin otel xin ta nufa.
  Cikin hanzari a razane Munir ya voye a bayan kiost xin, yana kallon motar har ta shiga cikin otel xin, saboda gigicewar da ya yi, ya hana shi ganin waxanda suke cikin motar, da a nutse yake da ya ga wadda yake ta yiwa waya ta qi xauka, wato Hari a cikin motar.
  Bayan da motar ta gama shigewa, Munir ya yi ajiyar zuciya, ya ci gaba da danna kiran Hari, sannan ya kara a kunne.
  Alhaji Tahir ya yi fakin a wurin da ya dace, shi da Hari suka fito kusan a tare cikin nishaxi. Yana rufe motarsa, juyawar da zai yi sai ya hango motar Munir a ajiye a layin motoci, ya tsaya yana kallonta cikin mamaki.
  Wayar Hari ta yi qara, kamar yadda ta yi ta yi a cikin mota, ba ta xauka ba, wannan lokacin ta xauko, ta san ko wane ne don haka ko dubawa ba ta yi ba, ta kalli Alhaji Tahir, sannan ta xauki kiran, ta kara a kunne, ta koma gefe, ta  ce “Hello.”
  A wajen otal xin, Munir riqe da waya a kunne kamar mara gaskiya, ya yi sauri ya ce.
  “Tun xazu nake buga wayarki ina son sanar da ke ina tafe zan zo wurinki.”
  Hari ta ce a cikin waya, “Matsalar network ce. Kuma gashi Alhaji ya aikeni, sai dai nan da mintuna arba’in mu haxu….” ta xan yin shiru, kafin ta ce “Ya na ji kamar muryarka tana rawa?”
  “E wallahi, a otal xin da nake ne na ga Dad xina ya shigo, shi ne na tsorata nake fatan Allah ya sa kar ya ga motata, domin idan ya gani asirina ya tonu kenan.” Cewar Munir a waya.
  Hari ta yi ‘yar dariya, ta ce “To Allah ya kiyaye.”
  Ta yi sauri, ta kashe wayar, ta bi bayan Alhaji Tahir, tana yi tana juyawa, tana ‘yan kalle-kalle, kamar mai son ganin wani abu, har suka shiga reception xin otal xin.
  *
  Kamar mintuna ashirin da biyu zuwa da uku da shigar Alhaji Tahir da Hari cikin xaki mai lamba 7 na otal xin Royal, sai ga Harin ta fito, yanayinta ya sha bamban da yanayin da ta shiga xakin a xazu. Duk ta bircike, ba ta san lokacin da ta ci karo da wani ma’aikacin otal xin ba da ya zo wucewa.
  Ya dubeta sosai, ya ce “Hajiya akwai wata matsala ne?”
  Gaban Hari ya faxi, bakinta ya fara rawa, ta girgiza kai alamun ba komai. Da sauri-sauri ta wuce, ta bar ma’aikacin nan tsaye yana kallonta, har ta vace.
  Ta ratsa cikin reception tana yiwa masu hidima da wajen wani irin kallo na gefen idanu, ta wuce, ta fita daga ciki, ta iso farfajiyar otal xin, gabanta ya ninku wajen faxuwa, a lokacin da ta yi kicivis da Munir, wanda ya nufo inda take don shiga reception.
  Ta fuskanci bai ganta ba, sai ta yi hanzari ta zame, ta voye a bayan wata mota. Munir xin ya zo ya wuce ta kusa da ita bai ganta ba.
  Yana wucewa kuwa, ta yi sauri ta fito ta ci gaba da tafiya zuwa qofar fita daga otal xin. Har ta je daidai qofar fita, sai ta ji muryar Munir yana kiranta. Ji ta yi kamar an sare mata rabin kai, ta tsaya nan a razane, sannan ta juyo a hankali suka haxa ido da shi.
  Da farko ran Munir a vace yake, sai kuma ya yi mata murmushi. Itama ta yi sauri ta qaqaro wani makararren murmushi ta jefa masa. Ta haxiyi yawu, ta ce.
  “Ai da tafiya zan yi, ka sa na zo wuri ina ta yawo ban ganka ba.”
  Munir ya faxaxa murmushin shi, ya ce “Am sorry, ai da na gaya miki inda nake ban yi zaton zuwa za ki yi ba.”
  “To gashi na zo kuma.” Ta xan yi shiru. “Sai dai ba a nan ya kamata mu zauna mu tattauna ba.”
  “Qwarai kuwa, ai daman ba a nan ya kamata mu zauna ba. Bari in yi sauri in xauko motata, in zo mu tafi.” Munir ya faxa, sannan ya nufi wajen motarsa, yana kallon motar mahaifinsa.
  Allah-Allah yake yi, kar ya samu matsala, ya ji daxi, har ya xauko motar tasa, ya zo ya xauki Hari, bai ga mahaifinsa ya fito ba.
  Sai da suka xauki hanya, sannan hankalin Munir ya kwanta, haka itama Hari. Don haka suka fara hira. Munir ya kalli Hari cikin farin ciki, yana murmushi.
  “Tun da na haxu da ke wasu abubuwa nawa da dama suka qaru, wasu da dama kuma suka ragu. Na sami daxin farin ciki da walwala, na daxa samun kwanciyar hankali, na daxa samun nutsuwa, arziqina ya havaka, na sami qwarin gwiwa daga wurin mahaifina. Na rage hayaniya, raina ya daina vaci sosai musamman a kan soyayya. Uhm, ai ke alkairi ce a gare ni Hari.”
  Hari ta yi dariya ciki-ciki ta ce, “Kamar yadda kake alkairi a wurina kenan.”
  Ya ji daxin abin da ta ce, ya ce “Zan zama alkairi sosai a wurinki musamman a lokacin da na aureki, za ki tabbatar da ni a mafi alkairin mutum Hari.”
  Suka yi dariya. Da ace Munir ya nutsu sosai zai ga cewar Hari a cikin wani hali take na damuwa, amma farin cikin kasancewa da ita ya rufe masa ido.
  Kafin xaya daga cikinsu ya yi magana, wayar Munir ta  yi qara, ya xaukota daga aljihu, ya duba, baquwar lamba ce, ya danna karvar kira, sannan ya kara a kunne, ya fara magana.
  “E…. ni ne” Ya faxa sannan ya yi shiru yana sauraro, “E xansa ne…..” Ya nutsu, yanayinsa ya sauya.
  Haka itama Hari hankalinta ya daxa tashi. Munir ya yi fakin da mota, ya sauke wayar daga kunnensa, bayan da ya ji an kashe daga can xin, ya yi huci, tuni gumi ya fara tsattsafo masa.
  Da qyar Hari ta iya juya wa ta kalle shi, sannan ta yi qarfin halin cewa “Me ya faru?”
  Bai kalleta ba ya ba ta amsa, “Hari babu lafiya, mahaifina ne ya…..” Ya yi shiru, sannan ya kuma cewa “Bari in kai ki gida sai in je wajen.”
  Hari ta girgiza kai, “A’a bari in sauka a nan ka yi sauri ka je…” Ba ta jira abin da zai ce ba, ta yi sauri ta buxe motar ta fita, ko leqawa motar ba ta yi, ta ce masa wani abu ba, ta fara sauri, ta bar wajen.
  *
  A yanzu gawar Alhaji Tahir tana lillive da farin qyalle a cikin xakin, qofar xakin a buxe, jami’an tsaro suna shige da fice, waxanda suke ciki kuwa suna ta dube-dube irin nasu na aiki, wani yana xaukar hotuna, wani yana bincike a gado da qarqashin gadon da cikin dirowar xakin.
  A harabar xakin daga gefe, Munir ne a zaune a kan wata kujera stool, fuskarsa sharkaf da hawaye, sannan sai Inspector Daniel Musa, wanda ake taqaita sunan a ce masa Dani, da yake zaune shima a gefensa, suna fuskantar juna. Akwai wasu jami’ai guda biyu da ke xan nesa kaxan da su.
  Babu mai wucewa ta harabar xakin, saboda su samu damar aiwatar da ayyukansu.
  Munir ya dubi Inspector Dani, ya ce “Na rasa me Dad ya yi wa wani a wannan duniyar?”
  “Shi ne abin da muke aiki a kai.” Cewar Insp. Dani. Wani jami’i mai siffar mutan da, sunansa Aliko Kuxa, ya iso ga Insp. Dani, ya miqa masa wasu takardu guda biyu da ke cike da rubutu cikin girmamawa, sannan ya dube shi.
  “Wayarsa ta vace, sannan kuma akwai finger-prints na hannun mace a wasu sassa da dama na xakin….”
  Munir ya yi sauri ya dube shi.
  Kallon da Munir ya yi masa, bai dami Aliko Kuxa ba, ya ci gaba da jawabinsa, musamman da yake shi aikinsa yake yi.
  “Xaya daga cikin ma’aikacin otal xin nan, ya sanar damu ya ga wata yarinya budurwa ta fito daga cikin xakin kafin a san abin da ya faru, kuma ya ganta cikin wani hali har ya tambayeta, a yanzu haka yana can yana bayar da fasali da yanayinta ga S.B. Akwai kuma takarda (evidanceda muka gani.” Ya miqa masa, Insp. Dani ya karva ya duba. Ita ba rubutu sosai.
  Aliko ya ci gaba da bayani, “Tana bayyana cewar su uku ne ake son kashewa (on target), saura abokansa guda biyu.”
  Munir ya dubi Aliko, a ransa ya tuno Alhaji Nasir da Alhaji Jabir abokan mahaifansa.
  Insp. Dani ya dubi Munir, sannan ya dubi Aliko, “Ya yi kyau. Ya batun vangaren motarsa, da kuma bin kira daga kamfani…”
  “Duk ana kan wannan aiki. Mintuna ashirin masu zuwa komai zai kammala. Ni zan wuce can farfajiya.”
  “Okay. Ina sauraronka.” Ya kuma duban Munir. Ya ci gaba da kwantar masa da hankali, yana ba shi haquri, tare da tabbacin zai binciko wanda ya aikata laifin.
  Kafin su bar wurin, ma’aikacin nan ya yi bayanin yadda ya ga Hari, ya kuma fasaltata gwargwadon yadda ya kalleta, Munir ya yi tsai da hankalinsa, a qarshe ya girgiza kai, a ransa ya ce.
  “Ko kaxan ba Hari ba ce. Ba Hari ba ce.” Ya tabbatar wa da kansa Hari ba za ta aikata wannan aiki ba, duk da irin fasaltata da aka yi, fasalin ya nuna kaso mafi yawa Hari ce kamar yadda ya santa, to amma zuciyarsa ta rufe ba zai tava yarda cewa ita xin ba ce.
  Da aka fasalta, fasalinta ne ya faxo a ransa, amma ya qi yarda ita ce ta aikata wannan aikin, ya ma nisantata matuqar nisa da wannan lamari. Kawai ya xauka ne saboda soyayyar da yake yi, kuma saboda ba su daxe da rabuwa ba, shi ya sa ya kawota a rai.
  *
  Ba a cikin rana suke ba, asalima a cikin ofis xin akwai fanka amma Alhaji Nasir ya haxa gumi, yana tsaye yana duban Alhaji Jabir da ke zaune, sai nishi yake yi.
  “Kai ka fiye ruxewa da sauri.” Alhaji Jabir ya kori shirun.
  Mamaki ya kama Alhaji Nasir, “Haba Alhaji, ruxewa fa ka ce, ko ba ka ji abin da na gaya maka ba ne, ba ka ji sun ce sun tsinci takarda mai nuni da cewar saura mu ba, ko kana tunanin Alhaji Tahir yana da wasu abokai a duk duniyar nan bayanmu? Mu kaxai ne abokansa, mu muka taso da shi tun muna qanana, har muka girma…to ya kake tunanin ba zan damu ba, hankalina ba zai tashi ba?”
  Alhaji Jabir ya xan yi qwafa ya ce “Ai tashin hankalin naka ne ya yi yawa.”
  Alhaji Nasir ya girgiza kai, ya juya baya yana tsaki, ya ce “Na rasa me muka yiwa wani, arziqi ko dukiyar da Allah ya bamu shi ya tsonewa wasu idanu suke neman hallakamu? Me muka yi, mun rayu muna harkokinmu na arziqi, ba mu shiga harkar wani ba, ba mu hanawa wani ba, ba mu toshewa wani komai ba, ba mu cutar da wani ba. Rayuwa mai kyau, amma ake neman cutar da mu…”
  Alhaji Jabir ya yi murmushi, “Haka ne, amma kuma me muka yi a rayuwar can ta baya?”
  Da sauri Alhaji Nasir ya juyo, ya qurawa Alhaji Jabir idanu, ya buxe baki kamar zai yi magana, sai kuma ya kasa, ya cije baki.
  “Ba cije baki za ka yi ba, tsayawa za mu yi, mu yi tunani, ko a yanzu bamu shiga haqqin wani ba, balle ya shiga namu, a da fa, mene ne ba mu yi ba, shin anya kuwa? Mu tuna ni da kai da muka rage, mun tava tunanin mu tuba kuwa. Ba sai na tsaya lissafo munanan ayyukan da muka yi ba, domin duk ka sansu, mu tuna bayan mun yi su, Allah ya qyalemu da rayukanmu, me muka yi tunanin yi domin daidaita lamuranmu da Allah ta hanyar tuba?”
  Waxannan zantuka na gaskiya da Alhaji Jabir yake yi, Alhaji Nasir jinsu yake yi kamar ana caccaka masa tsinin mashi a qahon zuciya, da ya ji ya yi shiru, sai ya harare shi, ya ce.
  “To yanzu me kake nufi?”
  Alhaji Jabir ya girgiza kai, “Abin da nake nufi? Ai na riga na faxa a abin da na ce a baya, ko ba ka ji ne yanzu don kana ruxe?”
  Suka yi shiru, fanka tana kaxawa, Alhaji Nasir yana kuma yin gumi.
  Alhaji Nasir ya kori shiru, “Na ji, Allah na tuba. To yanzu me ka yanke game da abin da jami’an tsaro suka ce?”
  “Me suka ce, maimaita min?” Alhaji Jabir ya buqata, ba wai ya manta ba ne.
  Alhaji Nasir ya yi tsaki, “Cewa suka yi mu nemi wurin da zamu voye, mu yi gudun hijira zuwa lokacin da zasu binciko wanda ya kashe Alhaji Tahir.”
  Alhaji Jabir ya yi dariya, “Na tuno.”
  “To yanzu ka amince zamu tafi can gidan gonar nawa mu zauna zuwa lokacin. Ka san wurin dai babu wanda ya san shi, bare ya kawo tunanin muna can.” Cewar Alhaji Nasir.
  “Haka ne, zamu je zuwa wani xan lokaci, amma ni tunanina ya daxe da sauyawa…”
  Alhaji Nasir ya katse shi, “Wannan wani abu ne daga baya ka yi min bayanin sauyawar, amma yanzu bana buqata, idan ka shirya mu haxu sha xaya da rabi na dare.”
  Ya juya ya fita.
  ENUGU
  Alhaji Yusuf da ke tsaye ransa a vace yake, Halima da qawarta mai suna Blessing Obinna, ‘yar qabilar Ibo a tsugunne a gabansa. Yadda halin Halima yake, haka halin Blessing yake, tana da kirki da girmama na gaba da ita, da biyayya, ba ta iya sanya ballagazazzun sutturu irin na sauran qawayenta ba, sau tari ma ta fi so ta yi koyi da Halima.
  Daman Hausawa a cikin hikimar zancensu sukan ce, sai hali ya zo ake abota.
  “Ke na tambaya, wa ya tava min ke. Kar ki xauka ba zan san a halin da ki ke ciki ba, akwai abin da ya faru da ake, shi nake son ki gaya min.”
  Yadda ya tsani mutuwarsa, haka ya tsani a tava masa Halima, kullum yarinyar shiga ransa take. Ita kuma Halima ba ta son duk wani vacin rai ko aka vata mata rai ta gaya masa, domin ba ta son ransa ya vaci.
  Sai dai ita kuma Blessing ba ta voye-voye, don haka ta zayyane wa Alhaji Yusuf komai.
  “Mun zo wucewa ne wata karuwa ta yi shaye-shaye kawai ta ce wai mun sa mata ido, muna kallonta, shi ne ta hau mu da duka, amma ta fi dukan Halima…”
  “A ina take?” Ya katseta cikin fushi, bai ma tsaya ta bashi amsa ba, ya juya, yana cewa “Ku taso mu je.” Ya zari mukullin motarsa, ya yi waje, suka rufa masa baya.
  Yana qoqarin yin fakin a qofar gidan karuwan da motarsa, Halima da Blessing a bayan mota, wayarsa ta yi qara. Kafin ya baro gida ya sanar da jami’an ‘yansanda halin da ake ciki, ya gaya musu su haxu a qofar gidan karuwai na Hajiyarsu.
  Ya xaga wayar, sannan ya ce “E, na iso qofar gidan…to sai kun qaraso.”
  Tun kafin su fito daga cikin motar, Blessing ta nuna wa Alhaji Yusuf karuwar da ta doke su xin. Tana tsaye a qofar gidan cikin wata mummunar shiga, tana zuqar sigari abinta, zuqa irin ta qwarewa.
  Ba su fi mintuna biyar da zuwa ba, ‘yansanda suka qaraso a cikin motarsu hilux, su huxu ne, direba xaya. Na baya su biyu suka diro, na cikin motar mutum xaya ya fito.
  Shima Yusuf a lokacin ya fito, ya qarasa wurinsu, suka yi magana, ya nuna musu ita.
  Ganin motar ‘yansanda wasu daga cikin karuwan nan suka fara zazzamewa, samari da qedarai da ogogi da suke zuwa suma suka tsaya kallo, musamman masu qwarin wuya, waxanda zuwa kamen ‘yansanda bai cika tada musu hankali ba.
  Jim kaxan sai ga wurin ya tara mutane, biyu daga cikin ‘yansandan masu qananun muqami suka nufi wurin wannan karuwa, har suka qarasa gareta.
  “Zamu tafi da ke ofis ana son ganinki.” Xaya ya ce da ita.
  Ta yi musu kallon wawaye ne ku, ta watsar ba ta yi magana ba, ta ci gaba da zuqar tabar tana busa musu hayaqi.
  Ba zato bare tsammani sai ji ta yi xaya ya sheqa mata mari, ya daqumi qugunta, yana zagi, yana kuma qoqarin fincikarta.
  Kan ka ce mene ne wannan, wurin ya cika, sauran karuwan dake wurin suka zagayesu suka hana a tafi da ita. Suna ta faxa da zagi.
  Suma ‘yansandan suna mayar musu da martani, wasu karuwai guda biyu suka ratso wurin suna tsayar da ‘yansandan. “Hajiyarsu ta ce a tsaya gata nan fitowa.”
  Yusuf da xaya xansandan da suke tsaye, suka ratsa cikin taron suna dubansu. Yusuf yana faxa, yana cewa “Babu wadda ta isa ta ce a tsaya, kuma babu ‘yar iskar da za ta hana a tafi da ita, don yau sai ta gane ita ‘yar iskar qarya ce tun da ta tava min Halima, daga yau ba za ta kuma sha’awar dukan wata xiya ta mutunci ba…”
  “Itama za ta zama xiyar mutuncin, don Allah ne ya ke shiryawa…”
  Wannan maganar ta katse Yusuf, muryar mai maganar ita ta tafi damunsa, ba kurari ko wani abu, duk da ba cikin kurarin ta yi maganar ba face cikin salama.
  Muryar ita ce murya ta farko da Yusuf ya fara ji a rayuwarsa, ita ce muryar da yake fatan ya kuma ji a ranar da zai qarar da rayuwarsa, muryar mahaifiyarsa Barira.
  A qame ya juyo, shi da Hajiya Barirar suka sandare cikin wani yanayi, da gudu bai yi tunanin da qafafunsa yake tafe ba, Yusuf ya isa wurin mahaifiyarsa ya rungumeta, tuni idanunsa suka wadata da hawaye, bakinsa yana rawa, amma duk da haka faxi yake “Umma….Ummata, ashe zan kuma ganinki.” Gashi babban mutum amma yadda yake maganar, ya baiwa mutanen da ke wajen tausayi, musamman waxanda suka san darajar iyaye.
  Hatta tsigalalliyar karuwar da ta doki Halima sai da ta tsaya tana kallo, kuma nan da nan sai ga hawaye a idanunta, domin yadda Yusuf yake magana cikin sambatu da tsananin qauna ga mahaifiyar tasa, abin yana da karyar da zuciya, ya tuno mata da nata iyayen, da yadda aka rabata da su, aka mayar da ita karuwar qarfi da yaji.
  Yusuf ya saki Hajiya Barira, yana kallonta, yadda yake kuka da hawaye haka itama take yi, shi ya iya yin magana, amma ita kasa buxe baki ta yi, bare ta ce komai.
  Ya kama hannunta, “Zo mu tafi Ummata, zo mu je…Alhamdulillahi.” sam ya manta da abin da ke faruwa, ya manta da wata yuyar jama’a da suka taru saboda shi, ya je ya buxe gaban motar, ya sa mahaifiyarsa, sannan ya zagaya, ya shiga, ya tada motar, ya ja suka tafi, ya manta da su Halima ma da suke zaune a bayan motar, sai da suka fara tafiya, sannan ya gano Haliman ta madubin motar tana hawaye. Ya girgiza kai, ya dubi mahaifiyarsa, ya dubi Halima, qauna a kan qauna ta dira a cikin zuciyarsa.
  *
  Dukkanin mutanen da ke faffaxan falon Alhaji Yusuf xin sun yi tsit, tun daga kan Halima, Sale da Yusuf sun yi shiru. Hajiya Barira ce take magana.
  “Rayuwata a gidan karuwan nan ta fi kowacce rayuwa da na yi a baya muhimmanci. Domin a zamana a gidan ne, na yi aikin da ya kamata duk wata mace tagari ta yi, wato qoqarin xora ‘yanmata kan hanya musamman namu na Hausawa ko Musulmai da suke baro gidajensu, su baro garuruwansu su taho ire-iren waxannan gidajen da suke da tabbacin ba su da takura.
  “Lokacin da na shigo garin nan na rasa wanda zai sauke ni, kun san yadda yanzu lamarin ya zama, zai yi wuya ka ga ainihin masu neman taimako don Allah, sai ‘yan bogi, su kuma masu taimakawar sun yi qaranci, yanzu idan kana son a taimaka maka sau tari sai a wurin masu aikata wasu laifuka, suna yin haka ne domin qoqarin rage raxaxin aikata laifukan da suke yi. Da na zauna a gidan, sai na ga akwai gudunmawar da zan iya bayarwa wajen wayar wa da matasan matan nan kai domin su fuskanci wannan harkar da suke aikatawa ba ita ce mafita ga abin da ya jefasu a ciki ba.
  “Na samu ‘yanmata irin namu kusan goma sha biyu sun haqura da wannan harkar a tsawon zamana a gidan, hatta ita wannan yarinyar da ta doki Haliman tana gab da barin harkar, domin kullum da ka ganta a nan tana tuna mahaifanta ne, tana kuma qara yin nadamar halin da take ciki, duk da jefata aka yi.”
  Ta yi shiru. Sai tashin numfashi a falon, kafin ta ci gaba.
  “Da yawa daga cikin ‘yanmatan da Allah ya taimaka suka shiriya a cikin wannan lokacin sun yi qoqarin su rabani da wannan gidan, na nuna musu cewar kamar yadda suke da wani givi a rayuwarsu, nima ina da shi, domin na rasa gudan jinina, wanda shi ne dalilin tahowata Enugu, kuma ina sa ran ganin shi. Sannan zamana a gidan, yana taimaka min yin aikin alkairi.”
  Ta yi shiru tana maida numfashi. Kana daga bisani ta kalli Halima, kafin ta dubi Yusuf. “Yadda ka riqe wannan yarinya, Allah zai saka maka da alkairi, sai dai ka san za ta so ta san ainihin iyayeta.”
  Yusuf ya tashi, ya je gaban mahaifiyarsa ya durqusa ya ce “Babu abin da ban gaya mata ba, amma ita ta ce ba ta san kowa ba sai ni a matsayin uwa da uba gareta.”
  Hajiya Barira ta kalleta cikin tausaya, ita kuma Halima ta sunkuyar da kai tana hawaye.
  Yusuf ya ci gaba da cewa “Sai dai, da yake na sa a yi min bincike a Kano, an gano mahaifinta, a nan unguwar Sabongari yake yana sayar da kayan lantarki, kuma an ba ni adireshinsa, idan muka koma Kano zamu neme shi.” Ya kalli abokinsa Sale. “Na gayawa abokina ni can Kano zan koma da harkokin kasuwanci na.”
  “Nima na fi son haka.” Cewar Hajiya Barira.
  KANO
  Kamar yadda Haule take ta kuka, haka shima Alhaji Idi yake yin kukan kamar wani yaro, yana durqushe a gabanta yana ba ta haquri, ita tana kukan famin ciwon rashin xiyarta da ya yi shekara da shekaru, shi kuma yana kukan rashin Harira gaba xaya.
  Haule ta sassauta kukan nata, “Ai ba qaramin ganganci ba ne, mutum ya haifi xa amma ya nuna ko in kula a kansa, gashi nan Allah ya jarrabeka da matuqar sonta.”
  Sama da shekaru tara da suka wuce, Alhaji Idi ya sami kansa a cikin wani yanayi na matuqar qaunar xiyarsa Harira, babu irin neman da bai yi mata ba, amma ya rasata, Allah ya zuba masa jarrabar sonta, kullum yana tare da hotonta, kullum yana mafarkin zai kuma ganinta, kuma kullum yana baiwa matarsa Haule haqurin abin da ya aikata musu a baya. Tun bata damuwa da halin da yake ciki, har ta dawo tana tausaya masa.
  “Rakiya ce ta cuce ni, Allah ya tsinewa Rakiya, Allah ya isa tsakanina da Rakiya.” Haka yake ta faxa yana kumfar baki, yana zare idanu. Ya xaga hannunsa sama, yana addu’a “Allah ya sa in ganki xiyata Harira…”
  “Ba za ka tava ganin Harira ba.” Ya ji an katse shi. Shi da Haule suka juya, suka kalli mai maganar. Karime mai xanwake ce, tana takowa a hankali tare da dogara sanda, tana xingishi. Ta zo ta tsaya a daf da su.
  “Na yi sallama, ba ku ji ba. Na ji addu’ar da kake yi, Allah ya amshi addu’arka ne ya kawoni, amma ba don ka ga wadda kake son gani ba, sai don in gaya maka halin da take ciki.”
  Suka yi jugum suna sauraronta.
  “Bayan da ka kori ‘yar taka, mun haxu da ita, ta zauna tsawon lokaci a inda nake, da ace ka nemeta tun a lokacin, tun kafin abu ya lalace da ka sameta, sai dai ba ka nemeta ba har ta ci duniyar rayuwarta a wulaqance, aka yi mata fyaxe, ta haukace, a qarshe ta mutu a ranar da ta haifar maka jika ta wannan halin.”
  Ta juya za ta tafi. Alhaji Idi ya tashi a guje ya sha gabanta yana cewa, “Harira ta mutu? Ina jikar tawa da ta haifar min, tana ina? Kawo min ita in ganta.”
  “Ba za ka ganta yanzu ba, sai dai nan gaba idan Allah zai haxaku, sunanta Hari kamar yadda uwarta ta raxa mata, itama ta mutu tana qaunarta, duk da ga a halin da ta sameta.”
  Faxuwa Alhaji Idi ya yi a wurin, Haule kuwa sai gunjin kuka take yi. Karime ta girgiza kai, ta fice ta bar su.
  *
  Hari ta fito daga cikin xakin tana duba wasu takardu a hannunta, Alhaji Jabir ne ya ba ta ajiyar su, yau ne kuma ya ce ta tuna masa ya ba ta ajiya, domin yau xin ne zai yi amfani da su, baya son ya manta.
  Vangaren Alhajin ta nufa, tana tafe, sai ta ji an tsayar da ita da kalmar “Ke!” Ta san muryar mai maganar, don haka ta yi saurin juyowa. Hajiya Silima ce.
  Yadda take kumbura kamar ta ci babu, yadda take zare idanu kamar damisa, ta nufo wajen Hari, ta fizge takardun da ke hannunta ta duba, sannan ta girgiza kai ta ce “Wai ke don ubanki wa ya dawo da ke gidan nan, kin manta kin zame mana jaraba, kin lalata komai, kuma kina nema ki kawo komai qarshe a wannan gidan, da sauran gidajen abokan maigidan? To wallahi ba za ki bar gidan nan ba sai na haxaki da ‘yansanda sun kamaki.”
  Ta mari Hari xin, ta kuma yi mata varin makauniya. Hari ta yi zafin nama ta rama, tana cewa “Ba ki ji abin da maigidan ya ce ba kenan?”
  Marin da Hari ta yiwa Hajiya Silima ya faxo a kan idon Sunusi da ya shigo a lokacin, da gudu ya nufo Hari yana hargagi rai a vace, ya yi tsalle da qafafunsa yana qoqarin buga mata a qirji, ta yi saurin kaucewa, tsautsayi ya gifta, Sunusi ya doki ginin da ke wurin, qafarsa ta karye.
  Ya faxi yana gunjin kuka, saboda tsananin zafi, Hajiya Silima ta yi kansa tana ihun neman taimako.
  Hari ta yi waje da gudu, ta bar gidan tana gudu. Har sai da ta xan yi nisa da gidan, sannan ta fara tafiya da sassarfa, a lokacin ta ji wayarta tana qara, ta zarota daga cikin qugun zaninta. Alhaji Jabir ne, ta xauki kiran tana qoqarin daidaita nutsuwarta.
  Daga can vangaren, yana tsaye a falon voyayyen gidan Alhaji Nasir, yana murmushi, ya ce “Hello…”
  “Hello my gentleman ina ka shiga ne?” Hari tana magana da sauri-sauri.
  “Afuwan Hari, na xan yi wani balaguro ne, daman yanzu ma kiranki na yi in ji muryarki…”
  “Amma fa akwai matsala my gentleman. Kana ina ne?” Ta yi saurin cewa da shi.
  Hankalin Alhaji Jabir ya tashi, “Matsala, kamar ya ya?”
  “Maganar ba za ta yiwu a waya ba, kana ina.”
  Ya kwatanta mata gidan gonar. “Sai dai ina son idan ki ka kusa zuwa ki kirani….”
  Ya yi sauri ya sauke wayar, saboda jin shigowar Alhaji Nasir da ya yi, ya kasa juyawa, sai da ya ji Alhaji Nasir xin ya yi magana.
  “Da wa kake waya?”
  Alhaji Jabir ya juyo, ya dubi Alhaji Nasir da yake yi masa wani irin kallo, ya ce “Wace irin tambaya ce wannan?”
  “Ka manta an ce mu haqura da buga waya, mu kasheta amma yanzu kake waya. Shin da wa kake waya?”
  Alhaji Jabir ya yi tsaki, ya ce “Iyalina na kirawo, domin ni ba zan iya zama tsawon wannan lokacin ban kira su na ji halin da suke ciki ba.”
  “Iyalinka fa ka ce? Ka fi ni iyalin ne, amma ni na haqura.”
  “Ni ba zan iya haqura ba na ce maka.”
  Alhaji Nasir ya cije baki “Ka ga Alhaji, iyalin fa da kake faxa, ba wani damuwa ka yi dasu ba, ni kaina da na fi ka damuwa da iyali, zan iya haqura da su a cikin wannan halin, idan har zan sami nawa ran…”
  Alhaji Jabir ya katse shi “Kai ke nan.” Ya xan yi shiru, kafin ya xora da cewa “Kai bari fa in gaya maka wani abu a wannan harkar, abu ne da idan ka shuka dole sai ka girba ko ba daxe ko ba jima, kana da alhakin rayuka a kanka, domin ka sha yin fyaxe, ta wannan hanyar kawai na san za a iya rasa rai, ko na wadda ka yiwa, ko kuma na wanda za a samu a sanadin haka…”
  Ya kama hannunsa, ya zaunar da shi, sannan shima ya zauna ya qura masa ido, “Bari in gaya maka wani abu da ba ka sani ba, wanda ake tunani ya kashe Alhaji Tahir ba wani bane, ko ba wata ba ce face….”
  Qarar wayarsa ta katse masa magana, ya yi saurin dubawa, ya ga Hari ce, ya tashi, ya juyawa Alhaji Nasir baya, sannan ya xaga, “Hello, kin iso?”
  A can vangaren Hari ta amsa da “E.”
  “To ki biyo ta bayan gidan mai shuxin fenti akwai qofa.”
  Jikin Alhaji Nasir ya fara karkarwa.
  *
  Hari ta tsaya tana kallon gawarwakin Alhaji Jabir da Alhaji Nasir da ke gabanta a cikin falon voyayyen gidan Alhaji Nasir xin, ba za ka iya fassara yanayin da take ciki ba. Amma dai wani irin kallo da take yiwa gawarwakin abin tambaya ne, kamar tana qoqarin gano wani abu.
  Ta motsa kaxan, domin xaukar wata jarida ta gani a ajiye a kan teburin wurin, sai kuma ta tsaya cak, saboda jiyo qara motoci da ta yi suna yin fakin a wajen gidan.
  Ta yi sauri, ta je ta leqa, motocin ‘yansanda ta gani guda biyu, sun tsattsaya, suna diddirowa, ga mamakinta, daga bayansu kuma sai ta ga motar Munir shima ya yi fakin, a ranta ta fara tunanin ko daman Munir xansanda ne?
  Kafin ta fara tunanin inda za ta lalubi amsar nan, ta yi sauri ta nufi qofar fita daga gidan ta inda ta biyo. Ta taki sa’a, yayin da take fita ta bayan gidan, su kuma ‘yansandan ta gaban gidan suka shigo.
  Cikin lura da kulawa, ta bi ta inda ya kamata, ta ratsa ta gefen motocin ‘yansandan tana kakkauda kanta, da sauri-sauri, a lokacin hankalin Munir ya yi kanta, amma bai mayar da hankalin sosai ba, domin hankalin nasa ya fi tafiya vangaren gidan, ita kuwa Hari tuni ta bar wurin.
  Sai kuma ya fara tunanin yadda aka yi ‘yansanda suka sami labarin inda abokan babansa suka voye, da kuma tunanin wani abu zai faru. Nan da nan ya dawo cikin hayyacinsa, ya yi sauri ya juya, ya kalli yarinyar da ya gani kamar a mafarki ta fito daga sashen gidan, ta wuce.
  Yana qoqarin komawa cikin motarsa, biyu daga cikin ‘yansandan da suka shiga gidan suka fito, suna sanar da waxanda suke wajen.
  “An kashe su, su duka biyun. Irin kisan da aka yiwa Alhaji Tahir.” Xaya ya ce.
  Wanda ake gayawa xin ya girgiza kai ya ce, “Ba mu san aikinmu ba.”
  Munir ya fasa shiga motar, ya nufo inda suke. Ya ja wanda ya yi magana ta qarshe gefe, ya yi masa wani xan jawabi, nan da nan yanayinsa ya sauya, ya dubi xaya daga cikin ‘yansandan ya yi masa inkiya.
  Hari tana tafiya cikin sauri, kawai sai ta ga motar ‘yansanda a gabanta, ta yi saurin juyawa don bin wata hanya, sai ganin motar Munir ta yi a gefen, ya buxe mata qofar motar, alamun ta shiga.
  Ta qi shiga, tana juyawa, ‘yansandan suka kewayeta. Ta juya, ta kalli Munir, ya girgiza mata kai.
  *
  A unguwar Sabongari ta jihar Kano, gida mai lamba 88 dake Church Road, shi ne gidan Azubuike mahaifin Helen, wato Halima a yanzu.
  Tsaye a qofar gidan Yusuf ne da mahaifiyarsa Hajiya Barira da ‘yarsa Halima suna tsumayin iso daga gare shi.
  Lahadi ce, don haka unguwar babu hayaniya sosai, sannan da yawa daga cikin magidanta suna zaune a gidajensu, domin hutun qarshen sati.
  Wata yarinya ce matsakaiciya, wadda ta doshi shekaru goma sha xaya, ta fito ta riskesu, da yaren Ibo take gaya musu su shigo. Ta juya, su kuma suka bi bayanta. Suka ratsa harabar gidan, zuwa wani falo da ke rufe da qofa, yarinyar ta tura qofar, ta buxeta, ta ba su izinin shiga, tana sanar da su cewar yana ciki.
  Lokacin da suka shiga yana zaune, dattijon Ibo ne yana zaune cikin kamala, yanayinsa da alamun amintaka a tare da shi.
  Falon a shirye yake, sannan kuma an wadata shi da kayayyakin alatu da qawa, babbar talabijin plasma a kunne, tashar NTA ce a kunne ana labarai.
  Yana ganin sun shigo, ya miqe domin tarbar su, yana nuna musu wurin zama. Sai dai tun da idanunsa, suka kalli Halima, ya daina kallon kowa sai ita, yanayinsa ya sauya, tunaninsa ya karkata gareta.
  Suka zazzauna, sannan suka gaggaisa, yana matuqar jin Hausa, wannan yarinyar da ta shigo da su, ita ta kuma dawowa xauke da lemukan kwali da na kwalba, ta ajiye a gaban su Yusuf da Hajiya Barira da Halima, sannan ta juya, ta koma inda ta fito.
  Jim kaxan da fitarta, mace ‘yar kimanin shekaru talatin ko fiye, mai suna Mercy ta shigo cikin murmushi, ta zo kusa da mijinta Azubuike, ta zauna, suka gaisa da su Yusuf cikin girmama, itama ta kafawa Halima idanu.
  Abin da yake baiwa su Yusuf mamaki, yadda yanayin tarbiyyar gidan Azubuike ta bambanta da yadda suka tsammaceta, suna da kyakkyawar tarbiyya, hatta sutturun dake sanye a jikinsu, ba irin waxanda za ka gani a jikkunan yawancin ‘yan qabilar Ibo ba ne.
  Azubuike ne ya kawar da shirun yana cewa, “Ku sha lemo mana.”
  Yusuf ne kawai ya xauki lemu, ya buxe yana sha, Halima da Hajiya Barira suka ce Alhamdulillahi.
  “Abubuwan da suka faru a gareni da iyalina sun faru ne kamar yadda aka so su faru, hatsarin da ya faru da su ko in ce da ku,” Ya nuna Yusuf “Ya faru bisa qaddara, amma ko da bai faru ba, ana shirin daman a ga bayansu waxanda suka mutu xin, har da ita Helen.” Ya dubi Halima.
  “Igwe Onyebuchi da Mamansa, su suka shirya kashemu su mallake dukiyata gaba xaya, kafin ni su suka yi sanadiyyar hallaka mahaifiyata, don haka duk wani shiri sun yi. Hatta zuwan da matata Ndidi ta yi qauye, su suka nemi ta je, sun yo mata tsafi idan ta zo komai na iya faruwa da ni da ita. Kafin ta zo xin hatsarin ya afku.
  “Sun hana ni aiwatar da komai a kai, sun ce an kai musu gawar Amaka da Helen sun binne, sannan ma sun hanani zuwa qauyen kwata-kwata ta hanyar tsafi.”
  Ya yi shiru, yanzu kowa a cikin damuwa yake saboda tausaya masa.
  “Dukkanin saqonka da bayanin abubuwan da suka faru na samesu, kuma na yarda, na yi bincike har a asibitin da aka kwantar da kai da Helen da kuma ofishin ‘yansandan da suka karvi lamarin, suka turaku Enugu, duk na sami labarin komai, kuma an yi haka ne kamar yadda aka tsara musu. Yaran Igwe da suke nan Kano suke tafiyar da tsarin da ya tsara musu.”
  Ya yi tsaki, sannan ya ce “Sai dai da yake ramin qarya qurarre ne, dukkanin qullinsu gareni bai yi tasiri ba, yanzu zaman da ake Igwe Onyebuchi da mahaifiyarsa sun daxe da mutuwa, saboda tsafin da suka yi min ya juya ya koma kansu, ba su ci dukiyar tawa ba, kamar yadda suka so, kuma ta dawo gareni.”
  Ya kalli Mercy, “Wannan ita ce matar da na aura daga baya, tana da matuqar kirki fiye ma da Amaka, ta yaye min baqin ciki da yawa, ta taimaka min wajen havakar dukiyata da arziqina a wannan jiha. Ina gode mata, itama ta haifa min xiya xaya, Chidinma, ita ce wadda ta shigo da ku nan.”
  Suka yi shiru gaba xaya, a yanzu Yusuf ya tsaya da shan lemon, yayin da Hajiya Barira ta xauko na kwali ta buxe ta fara sha, tana cike da tausayin Azubuike. Ita kuwa Halima sai kallonsa take yi, da yanayinsa, tabbas sun yi matuqar kama, tana jinsa a ranta, tana jin cewa suna da matuqar alaqa, ko da ba a faxa mata ba.
  Sai yanzu Yusuf ya yi nishi ya yi magana, “Allah mai iko.” Haka kawai ya ce.
  Azubuike ya kalli Halima, sannan ya kalli Yusuf ya ce “Na san ka zo kawo min ‘yata ne ko?”
  Yusuf girgiza kai kawai ya yi.
  “Ko ba ni ba, duk wanda ya kalleta ya san ‘yata ce.” Yana duban Halima, “Kuma na karveta a matsayin ‘ya, sai dai na dawo maka da ita ka ci gaba da riqe min ita har qarshen rayuwarmu gaba xaya.”
  Suka kalle shi cikin mamaki. Bai damu ba, ya ci gaba da magana, “Ba qin karvarta na yi ba, zan fi kowa jin daxi idan na karveta, sai dai barinta a hannunka kuma ya fi komai muhimmanci da girma, domin idan ka dubeta sosai, yanzu Helen, ko da yake bari in ce Halima, ta zama kai, yanayinta, tsarinta, al’adunta, addininta duk irin naka ne kuma sune mutum ko ba haka ba?” Ya tambaya.
  “Yusuf ya gyaxa kai.”
  “Uwa uba ka tarbiyyarta da ita tarbiyya mai kyau, ka tarbiyyar da ita halayenka, don haka kai ne ka fi kowa cancantar riqeta, ba ni ba, ni dai na fi kowa son ta zauna a wurina, amma zamanta a wurinka shi ma kwanciyar hankalina ne, kar ka damu.” Ya kalli Mercy, “Sannan kuma duk dukiyar da na karva tawa ta qauye, mallakinta ne, zan turo maka ita gareka.”
  Suka kuma yin shiru gaba xayansu, idan ka xauke shi Azubuike dukkaninsu hawaye suke yi, har Hajiya Barira har Yusuf xin saboda tausayi.
  “Ba kuka za ku yi ba, godewa Allah za mu yi gaba xaya, sannan mu tsara yadda rayuwa za ta kasance mana, domin a yanzu kun zamo ‘yan uwa a garemu.”
  Hajiya Barira ce ta yunqura ta ce “Tabbas wannan abu da ya faru, ya faru ne bisa wani tsari na Ubangiji da ya tsara domin ya haxamu mu zama ‘yan uwan juna, kuma mun zama xin, sannan kai xin ka zama mutum mai kima da girma da na haxu da shi, wanda ban yi zaton haka ba. Haqiqa Allah ba zai tava barin wani ya cutar da kai ba, kamar yadda ba ka da nufin cutar da wani, idan har wanin ya cutar da kai, to sai don dai Allah ya jarrabeka da wannan cuta.”
  Azubuike ya dubeta, ya ce “Kina nufin Allah zai iya kareni ina matsayin da nake ciki?”
  “Allah yana kare dukkanin halittunsa, Kiristoci, Yahudawa, Musulmai kai ko a wane irin addini kake, ko ma a ce ba ka addini, domin wannan ne yake nuna shi xin shi ne Allah, kuma shi ne mahaliccin dukkanin wata halitta, yana sane da dukkanin halittu na ko’ina, waxanda suka rigaya da waxanda za su so nan gaba, ba shi da buqata ga kowa da komai.”
  Azubuike ya kalli matarsa Mercy, cikin gamsuwa da maganar Hajiya Barira.
  Halima dai kuka take, sannan kuma lokaci-lokaci takan xaga kai ta kalli mahaifinta, da ta ji an yi shiru, sai ta tashi, ta je gaban Azubuike, ta durqusa har qasa, tana faxin “Dad ina qaunarka, ina sonka.”
  Azubuike ya rungume ‘yarsa yana faxin “Halima ina qaunarki, rabon da in ji xumin jikinki tun kina jaririya shekarun da yawa….” Muryarsa ta karye, sai yanzu hawaye suka zubo masa.
  Suka tausaya masa, matuqar tausayawa.
  Tsawon lokaci suna cikin wannan hali, sannan suka mimmiqe, domin su Yusuf za su tafi, a wannan lokacin aka nuno hoton Hari tangameme a akwatin talabijin xin falon, hankalin Yusuf ne ya fara yin wajen, kafin su ma su dube shi, su kuma dubi abin da yake kallo.
  A labaran ana bayanin yadda zaman farko na kotu ya kasance ga shari’ar Hari da ake zarginta na kashe su Alhaji Jabir.
  Hankalin Yusuf ya tashi, ya matsa kusa da talabijin xin, sannan ya juyo, ya kalli mahaifiyarsa yana cewa “Umma Harira ce.”
  Hajiya Barira ta girgiza kai ta ce “Wannan ba Harira ba ce, amma dai suna da alaqa, idanunka sun rufe ka kasa ganewa.”
  Suka yi shiru lokacin da suka ji mai labaran yana faxin ranar da za a yi zama na biyu, wato sati biyu masu zuwa.
  BAYAN SATI BIYU
  Kotun ta wadatu da jama’a, waxanda aka kawo qara da waxanda suka kawo, sannan kuma sai ‘yan kallo, da suka yi dafifi.
  A cikin kotun akwai Alhaji Idi da Haule da Yusuf da Hajiya Barira da Halima har da Munir da Hajiya Silima da Zinatu.
  Wasu sun je saboda ci gaba da shari’ar Hari wasu kuma saboda wasu shari’o’i da za a yi. Waxanda suka je saboda shari’ar Hari, wasunsu sun je domin su ga an hukunta Hari bisa mummunan laifin da ta aikata, musamman vangaren su Hajiya Silima, wasu kuma sun je suna Allah-Allah ace ba ita ta aikata laifin ba, idan kuma ita ta aikata a yi mata sassauci a yayin shari’a.
  Bayan zaman alqali, ya bayar da umarni mai karaton qara ya karanto. Cikin ikon Allah, qarar Hari ya fara karantowa, ya bayyana inda aka tsaya, da jawaban lauyan vangaren mamatan su Alhaji Jabir da abokansa, sai kuma jawaban mai shari’a a wancan zaman.
  Bayan ya gama ne, mai shari’a ya dubi Hari da ke tsaye a cikin akwakun waxanda ake tuhuma, masu laifi ko marasa laifi, ya ce.
  “Kin ji abin da ake tuhumarki ko?”
  Hari ta gyaxa kai ta ce “Na ji.”
  Alqali ya ce “To ko kina da wani abu da za ki ce?”
  Hari ta dubi mutanen da ke zaune a cikin kotun, suka haxa ido da Munir, wanda yake ta qwalla, sannan ta juyo da kanta ta dubi mai shari’a ta ce “Babu abin da zan iya cewa.”
  Alqali ya ce “Kamar ya ya babu abin da za ki iya cewa, wannan yana nuna cewar kin aikata kisan gilla ga mutane ba su ji ba, ba su gani ba.”
  Kafin kowa ya yi magana, sai ganin hannun wata mata aka yi a sama, tana neman izinin yin magana. Dukkanin mutanen da ke wurin sai da suka dubi inda take, Hari cikin mamaki ta ce a fili “Karime!”
  Alqali ya ba Karime mai xanwake izinin ta taso, ta fito inda ya dace. Bayan ta fito xin, Alqali ya ba ta damar ta faxi abin da za ta faxa xin.
  “Mutanen da ake zargi wannan yarinya Hari ta kashe sune iyayenta.” Karime ta fara magana.
  Kowa da ke kotun sai da ya yi mamaki, kuma aka kalleta, amma ban da Hari.
  “Sannan kuma ba ita ta kashe su ba, ni na kashe su.”
  Alqali ya cire gilashinsa, ya kalleta sosai, akwai alamun mamaki a tare da ita. Ta ci gaba da magana.
  “Ni na kashesu, ma’ana ni na sa a kashe su xaya bayan xaya, kuma Alhamdulillahi burina ya cika. Na gode Allah da ya nuna min lokacin da na cimma burina.”
  ‘Yan surutai da ake a kotun ya sa ta xan yi shiru, daga bisani alqali ya ba da umarnin a tsahirta, bayan an tsahirta, ya kuma ba ta damar ta ci gaba, ta ci gaba xin.
  “’Yata guda xaya tal Jamila da Allah ya ba ni na haifa da mahaifinta kafin Allah ya yi masa rasuwa, sune suka yi sanadiyyar mutuwarta ta hanyar yi mata fyaxe, wani mummunan abu a kan hakan shi ne, a gaban idanuna suka yi mata, domin sun xaureni ne hannu da baki. Kamar yadda suka aikata ga xiyata, haka suka aikata ga Harira mahaifiyar wannan yarinyar Hari.” Ta nunata, a yanzu kuka take yi.
  “Zuciyata ta gaza qyale wannan abu, ba za ta tava mantawa da wannan cin mutunci da keta haddi ba, kuma gani ba ni da ‘yancin da zan yi qara a saurareni, shi ne dalilin da ya sa na sha alwashin ganin bayansu, domin kawo qarshen zaluncinsu ga masu rauni, wato mata, in kawo qarshen cin mutuncinsu da keta haddi, Allah ya taimake ni na cimma burina, Alhamdulillahi.”
  Babu wanda bai tausaya mata ba, a cikin kotun, ba mamaki sai dai ko alqali. Tsawon lokaci tana yi, kuma kowa ya yi shiru, akwai waxanda suka yi qwalla a cikin kotun, ita kam Haule da ke zaune sai kuka take yi itama, hatta Alhaji Idi shima hawaye yake yi, haka Yusuf.
  Bayan an xan nutsu, alqali ya fara rubuce-rubuce a wani littafi da ke gabansa, sannan ya xago ya kalli Hari, kana ya kalli Karime, ya kuma xauko wani littafin ya yi rubutu, sannan ya ce.
  “A bisa abubuwan da kotu ta saurara a yanzu, da kuma kalaman kotu ta ji, kotu tana buqatar ji daga vangaren lauyan masu qara.”
  Lauyan ya miqe, sai da ya kalli Hari sosai, sannan ya koma ga Karime, kamar zai yi magana, sai ya fasa ya dubi alqali ya ce “Mai girma mai shari’a, a matsayina na lauyan masu qara, mun gamsu da maganganun da Karime ta yi, kuma bisa rashin cikakken dalili na cewar Hari ce ta yi kisan, da kuma wasu shaidu da muka samu daga jami’an tsaro da ya tabbatar mana ba ita ba ce ta yi kisan face tana tare da Alhajin lokacin da aka yi kisan, sannan sai kisa na biyu, babu wata shaida da ta nuna cewar tana wurin, face kira da aka samu nata a cikin wayar Alhaji Jabir.”
  Ya yi shiru yana duban Karime, “Babu wata alama da ta nuna Hari za ta iya kisa ko ta sa a yi. Bisa waxannan dalilai a vangaren masu qara sun janye daga qarar Hari, za su shirya takardun tuhuma ga Karime, duk da ita da kanta ta amsa laifukan da ta aikata.” Ya je, ya zauna.
  Alqali ya yi rubuce-rubucensa, sannan ya xago ya dubi Hari da lauya, ya ce “Bisa la’akari da abubuwan da suka wakana, kotu ta wanke Hari daga wannan laifi da ake zarginta, kuma ta ba da belinta. Sannan kotu ta xaga sauraron qara har zuwa ashirin ga wata.”
  Alqali ya baiwa mai karanto qara domin ya karanto qarar gaba.
  *
  Bayan kwana biyu, bayan an samu nutsuwa, Alhaji Idi ya so ya karvi Hari, amma ta qi amincewa, ta zavi zama a hannun Alhaji Yusuf.
  Halima ta shawarci Yusuf ya auri Hari. Ya nuna mata zai duba, ya tuna cewa Azubuike, ya yi masa tayin ya auri Halimar, ya zai yi kenan.
  A cikin wannan hali kuma sai ga saqo daga Insp. Kayode, kuxin da Yusuf ya tsinta tun farkon zuwansa Enugu ba a sami mai su ba, don haka an mallakawa Yusuf su.
  QARSHE
  Mu haxu a, Kushewar Baxi da ‘Ya’yanmu

About Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *