[Advertisements⬇️]

BAƘIN DARE CHAPTER 8 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BAKIN DARE 
CHAPTER 8
Wasa wasa sati biyu kenan da Alhaji Bala yaje wajen Mai gida abunda ake cewa kwanciyar hankali Sam Alhaji Bala bashi dashi dan Duk abinda Mai gida yace yayi yayi amma Kullum sai Hajiya Nafeesa tazo mishi a cikin mafarki k0 a zahiri yabi ya zama kamar mai karamin 
tabin hankali Dan ko yaya yaji motsi sai ya firgita ya zunduma lhu Hajiya Lubna da Naila kuwa hankalinsu yayi masifar tashi da halin da suka ga Alhaji Bala a ciki Dan tunda ya fara shafa wani magani mai Warin kashi a jiki ga jajayen candles da yake kunawa duk dare suka fara tsorata da lamarin Alhaji Bala Naila buya ma take a daki dan ta fara zargin Daddynta yafara samun tabin hankali kowane lokaci zai iya rufesu da duka dan abun nashi ya kai yanzu har da rana lhu yake shi kadai idan yana zaune a cikin Palo ya kuma ki gayawa Hajiya Lubna abinda ke faruwa idan ta matsa mishi da tambayoyi sai ya rufeta da fada tamkar zai daketa A haka suka zuba mishi ido suna mishi addu’a samun sauki Bangaren su Saiam kuwa Addu’a suke babu dare babu rana akan Allah yayi wa Hajiya Nafeesa Rahama ya kuma toni asirin Alhaji Bala har akayi sadakan bakwai bakinsu na dauke da azumi idan kagansu sai sun masifar baka tausayi dan kowacensu kalar idonta ya komaja sunyi shak’uwa da mahaifiyarsu fiye da tunanin mai tunani k0 abinci basa iya ci ballantana akai ga cikakken bacci ahaka nasu nafila ne akan Alhaji Nazifi tunda danginsu dake tayasu zaman makoki suna dan kwantar musu da hankali sabanin Alhaji Nazifi da ke wuni a d’aki baya fitowa ba um bare uhum uhum haka zai yi tagumi yana kallon Hoton Hajiya Nafeesa lokaci lokaci yana share hawayen dake zubo mishi duk Wanda yazo mishi gaisuwa sai dai ya hakura ya tafi dan Alhaji Nazifi baya ko motsawa daga inda yake kiran Sallah kawai ke sa ya tashi Sallar ma a daki yake yinta a k’arshen sujadarsa kuwa kuka yake fashewa dashi yayi ta yiwa Hajiya Nafeesa Addu’ar Rahamar Allah Sai da akayi Sati biyu da Rasuwar Hajiya Nafeesa Alhaji Nazifi ya dan fara dawo wa dai-dai a inda ya nemo wani babban Mallami mai tarin ilimi yace ya taya shi da addu’ar Allah ya tonawa azzalumin da ya kashe Hajiya Nafeesa Asiri shi da zaman lafiya har Abada 
Mallamin kuwa yace ya kawo kud’in Sadaka ya had’a kan Almajirai ya raba musu ayoyi da addu‘oi insha Allahu asirinsa na dab da tonuwa 
Makud’an kud’i Alhaji Nazifi ya bashi tare da yi mishi godiya 
A Daren ranar suna zaune a Palo gabad’aya kowanensu hannunsa d’auke da carbi yayan Hajiya Nafeesa Alhaji Musa da tun magriba yana gidan kallon Alhaji Nazifi yayi dayake Jan counter kansa a sunkuye yayi yace mishi yanzu sai dai a daga Auren Safna da Saiam idan Hajiya Nafeesa tayi Arba’in sai a d’aura musu Auren dan ba dan rasuwarta ba da gobene d’aurin Auren 
Saiam juyar da kanta tayi dan ita yanzu Sam Auren bama ya gabanta bata jin zata iya Aure ta rabu dasu Sahiba gwara ta zauna ta kula da kanenta tunda itace Babba 
Alhaji Nazif’l sai da yafara Sauke ajiyar zuciya kafin ya dago yace ” A goben za’a d’aura musu Aure insha Allahu babu abinda za’a fasa dan Nafeesa ta rasu bashi zai sa a daga daurin Auren ba dan k0 an daga ba dawowa zatayi ba ni nasan burinta bai wuce taga ranar daurin Auren Suba kuma insha Allahu zan cika mata wanan burin nata dazu na yiwa iyayen mazajen waya akan su Zoda shirinsu gobe karfe goma sha daya za’ayi Daurin Auren in yaso sa tare idan an kwana biyu” Tunda Ya fara magana Saiam da Safna suka d’ago arazane suna kallon shi kuka suka fashe dashi kamar had’in baki Saiam tace”Daddy dan Allah kar a d’aura mana Aure gobe mummy satinta biyu da rasuwa yau ya za’ayi a d’aura mana Aure gobe ni wlh na hakura da Auren zan zauna na kula da kannena idan mukayi Aure waye zai kula dasu Daddy Dan Allah mun fasa bama San Auren” Saiam ta karashe maganarta cikin matsanacin kuka Alhaji Nazifi Daji yake kamar shima ya fashe da kuka girgiza kai yayi ya mike daga kan kujera ya nufi inda suke a zaune 
Zama yayi agabansu ya tank’washe kafafunsa ya kira sunan Saiam da Safna yace “Karku manta ni ina raye ban mutu ba ni zan kula dasu har zuwa lokacin da suma zan Aurar dasu burin Mahaifiyarku Kullum bai wuce taga ranar Aurenku ba kuma ni nasan a yanzu idan aka d’aga d’aurin Auren nan sabida ita bazata ji dadi ba gwara in cika mata burinta duk da bata Raye idan ta kannenku ne insha Allahu ni zan kula dasu ba wai ana d’aura Auren gobe a goben zaku tare ba sai an d’an kwana biyu haka mun d’an k’ara samun nutsuwa mun 
karasa sauran shirin namu sai Ku tare” A takaice da kyar Alhaji Nazifin da Alhaji Musa
suka shawo kansu Saiam suka yarda za‘a d’aura musu Aure a gobe Su Suhaima kuwa tausayin Kansu ne ya k’ara lullubesu dan ahaka da suke d’an ganin juna hankalinsu ke kwanciya ayanzu kuma idan Saiam da Safna suka yi Aure gidan girma zai kara yi musu 
Bangaren Akram kuwa suna nan suna shirye shiryen yanda zasu kama Alhaji Bala cikin Sauki shi da yaransa inda Akram ke kiran su Lion da suka Dade da komawa gidansu dake Daji dan cika Umarnin Alhaji Bala ‘ 
Akram kuwa karya ya ringa musu da Mahaifiyarshi ce ba lafiya shi yasa bai dawo ba amma kafin ogansu ya dawo zai dawo Akram ganin anyi sati Biyu Alhaji Bala bai kira shi ba yasa yafara shan jinin jikinsa yana tunanin ko dai Alhaji Bala ya gano cewa shi Ss ne Lambar Alhaji Bala ya gwada kira bai d’aga ba sai da ya mishi miss call biyar bai d’aga ba take hankalin Akram ya tashi oganshi ya kwantar masa da hankali yace ya kira su Killer ya bugi cikinsu yaji idan kuwa suma basu d’aga ba to tabbas sun gano shi 
Yana kiran Killer ya d’aga wayar Akram yace mishi a cikinsu akwai Wanda sukayi waya da oga kuwa dan yana ta kira bai d’auka ba 
Mamaki ne ya rufe Killer yace mishi suma tunjiya suke kiranshi baya dauka yanzu nan ma fire ya gama kiranshi bai dauka ba Hankalin Akram ne ya kwanta da yaji abinda yace sai yace mishi to bari zai cigaba da kiran shi watakila yana hutawa ne da haka suka yi Sallama Oganshi yace ya kwantar da hankalinsa tamkar Alhaji Bala ya gama zuwa hannu ne 
Bangaren Alhaji Bala kuwa ayau yafi kowace rana shiga tashin hankali dan Hajiya Nafeesa bata bacewa idan ta zo mishi a yanayi na ban tsoro take zuwar mishi sosai Hajiya Lubna sallati kawai take yi dan ita bata ganin abinda yake firgita shi yake ihu yana zagaye d’akin abinda Alhaji Bala ya kwana yana yi kenan Naila kuwa kuka kawai take tana tunanin ko aljanu ne suka sako Alhaji bala agaba Sai da aka fara kiraye kirayen Salla Alhaji Bala ya daina ganin Hajiya Nafeesa A guje ya fito daga d’akinsa duk yabi ya Firgice kamar bashi ba daga shi sai dogon bak’in jallabiya babu ko dogon wando a ciki yaje ya hau motarsa ya bar gidan Rabonsa da yaji shi cikin kwanciyar hankali tun kafin yaje gidansu Hajiya Nafeesa haka ya ringa fisgar motarsa ikon Allah kawai ne ya kai shi mai duguri wajen mai gida 
Yana parking yasa hannu abayan seat d’in motarsa ya zaro karamar bindigarsa yasaka a Aljihunsu fuskar nan tashi a turbune 
Sai da mai gida ya gama uzurinsa kafin ya fito daga cikin gidansa Ya zauna akan buzunsa yana kallon Alhaji Bala daya kafe shi da ido ya tsaya tamkar wani soja Murmushi mai gida yayi yace “kura ya dai k0 dai fatalwar ce duk ta firgita ka haka dama na gaya maka wanan zabin farkon shi zaka bi ka ta rabu dakai idan ba haka ba wlh sai ta zarar dakai” 
Alhaji Bala wani irin kallo yayi wa mai gida yace “mai Matar ai babu dan ta zarrar Dani duk inda nayi sai na ganta yanzu mai gida kana so kace min babu abinda zaka iya yi wanan matarta rabu dani”? Mai gida wani kallo ya watsa mishi yace “idan da akwai zan tsaya b’ata wa kaina lokacine babu abinda zan iya yi akai zabin nan dai nafarko shi zaka bi ta rabu dakai” Dariyar mugunta Alhaji Bala ya kwashe dashi yace ” yanzu dai kana so kace min Fatalwa tafi karfinka kana so kace min duk abubuwan nan daka rataya da aljanun da suke maka aiki bazasu iya min maganin matar nan ba”? 
Mai gida zuba mishi ido yayi yana kallonsa a dai dai lokacin da zoben daya saka a hannun shi ya fara mishi zafi
Take Mai gida ya mik’e hankalinsa a tashe yana kallon Alhaji Bala dan yasan ba alheri ne ya kawo shi wajensa ba kafin ya kai ga wani tunani 
Alhaji Bala ya zaro bindigarsa daga Alhajinsu ya nuna shi dashi yana “Mai gida banga amfaninka a doron kasa ba tunda bazaka iya magance min matsala taba idan dai kasar da kake bugawa ta gaske ce bai kamata ace da ka buga bai gaya maka gidan matar nan da zamuje zai zame min masifa ba dan haka gwara na kasheka tunda yanzu ba amfani kake min ba kafin mai gida yayi wani yunkuri Alhaji Bala ya sakar mishi bullet hud’u Mai gida take ya zube a kasajini na ambaliya wajen yafara dan girgiza Alhaji Bala dake huci yayi tsaki yajuya ya nufl wajen motarsa 
Alhaji Bala sai daya bar wajen mai gida yafara tunanin wajen wa zai nemi taimako wane mallami zai samu ya iya mishi aiki Hajiya Nafeesa ta rabu dashi yana cikin wanan tunanin wani tsohon Mallaminsa Mallam na maliya ya fad’o masa arai shima wani hatsabibin Mallami ne dan shi akan ruwa yake zama a dalilin Mai gida ya watsar dashi Bai tsaya wani dogon tunani ba ya d’auki hanyar Sokoto bashi ya isa kungurmin dajin ba sai Tara na dare Sai daya sha bakar wahala ya iya gane wajen Tunda ga nesa ya farojiyo muryar Mallam na Maliya na mishi maraba tun bai karasa ba ya 
hau fada mishi abubuwan dake tafe dashi Alhaji Bala kuwa da hanzarinsa ya karasa wajen da yaji muryarsa na fitowa 
Sai da yayi kamar zai yi mishi sujadda kafin ya dago ya kalli Mallam Na Maliya dake ta juyi 
asaman ruwa a zaune shi ba a kasa ba shi ba a sama ba 
Sai daya fara kwashewa da wani mahaukacin dariya yace “Kurwar matar nan daka kashe tana da karfi rabaku sai an sha wahala amma awajena Abu mai sauki ne zan baka wani ruwa ayanzu kayi wanka da shi zaka daina ganinta na ‘yan kwanaki kafin ta cigaba da zuwar maka kafin lokacin kasan yanda zakaje kabarinta ka haka rami agefen kabarin nata kasa wanan wukar da layan ka binne idan dai kayi haka ta rabu dakai kenan har abada” Jikin Alhaji Bala ne ya hau rawa yace “Na Maliya ai bansan a inda aka binneta ba” “Wanan yafi komai Sauki kaje unguwarsu idan kaje ka samu wani Mara karfi kace ya raka ka makabarta zakaje kayiwa mammata addu’a daga nan zaka iya bugar cikinsa kaji a inda aka binneta tunda sunan mijinta ba boyayye bane kana cewa Ashe matar Alhaji wane ta rasu ni kuwa ina kabarinta yake da haka zaka bugi cikinsa bayan kayi mishi alheri ni nasan zai nuna maka daga nan sai ka aiwatar da kudurinka indai ka samu ka binne ni nasan zata rabu dakai har Abada” Wani nanauyan ajiyar zuciya Alhaji Bala ya sauke Dan gani yake abin da kamar wuya kansa ya kara sadawa k’asa kamar zai mishi sujadda kafin yace “Godiya nake Na Maliya menene ladan aikina” 
Wani Mahaukacin dariya Na Maliya ya kwashe dashi kafin yace ” kai ma kasan bana fad’a sai komai ya kammalla kuma duk abinda nace ayimin idan ba’ayi min ba kasan mai zai biyo baya dan ba iya fatalwar matar zan sa ya ringa bibiyarka ba har da sauran mutanen daka kashe” ‘ 
Alhaji Bala girgiza kansa yayi yace angama indai Hajiya Nafeesa zata daina bibiyarsa da haka yayi mishi sallama da zumar sai ya dawo ya mike a gajiye yaje ya hau motarsa ya kuma daukar hanya ……. 
Hmmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]