[Advertisements⬇️]

BAƘIN DARE CHAPTER 4 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BƘIN DARE 
CHAPTER 4
lhu Saiam keyi sosai ta kankame kan Hajiya Nafeesa akan kar atasheta bacci take ba mutuwa tayi ba 
Dak’yar matan suka banbare hannunta daga kan gawan Hajiya Nafeesa Saiam kuwa ta hau birgima a kasa gwanin ban tausayi 
Matar Alhaji Nazir makocinsu Alhaji Nazifi ce tafara ankara da halin da Samha take ciki dan kirjinta sama yake sosai 
Salatin da tayi da karfi ne yasa suka juya suka kalli inda Samha ke kwance cikin mawuyacin hali Sahiba hannu ta dora aka tana ta shiga ta uku ta lalace Da sauri ‘yan sandan suka umarci matan da a saka Samha a mota itama tana bukatar taimakon gaggawa 
Mata biyune suka kinkimi Samha sukayi waje da ita inda daya daga cikin ‘yan sandan ya dauko wani zani daya gani akan kofa ya rufe Hajiya Nafeesa Kafin ya maida hankalinsa kan Safna da Suhaima dake zaune a kusa da gawan Hajiya Nafeesa sai shesheka suke suna jiyo muryar Saiam da aka kulle a dressing room tana su bude mata ita mummynta bata mutu ba 
Da kyar Suhaima ta iya basu labarin duk abinda yafaru daya dan sandan yana recording dayan kuma yana rubuta statement din bayanan ta 
Karfe takwas dai-dai yan uwa da abokanan arziki suka ringa tururuwa cikin gidan suna koke koke familyn Hajiya Nafeesa gabadaya sai da suka zo ciki kuwa har da mahaifinta da mahaifiyarta 
Suna shigowa su Suhaima suka fashe da mugun kuka Safna ta mike da gudu taje ta rungume hajiyar su Nafeesa Dan tamkar an tsaga kara sabida kamaninsu da Hajiya Nafeesa banbanci kawai ita hajiyar su Nafeesa ta tsufa Agaban gawan Hajiya Nafeesa ta tsugunna ahankali ta yaye zanin da aka rufe mata fuska dashi 
Runtse idonta tayi da karfl data ga yanda jini ya wanke fuskarta Fuskarta ta kumbura tayi suntum Girgiza kai kawai take hawaye na gudu a fuskarta ahankali ta maida Zanin ta rufe 
Ta fara magana cikin wani irin yanayi tana “Nafeesa bazan taba yafe wa Wanda ya kasheki ba amatsayina na mahaifiyarki zanta addu’a Allah ya tarwatsa rayuwar Wanda ya kashe ki shi da kwanciyar hankali a duniya sai dai alahira“ Kuka take sosai Wanda yasa duk wayanda ke palon kuka 
Mahaifin Hajiya Nafeesa kuwa yana daga nesa ya kurawa Gawan Hajiya Nafeesa ido jikinsa sai rawa yake yana tuno shekaranjiya da tazo gida tana ta abubuwa haka kamar na bankwana sau uku tana fita ta dawo idan suka tambayeta mai ta dawo yi sai tayi murmushi tace ta dawo ne tayi musu Sallama Ashe sallamar karshe take musu Ashe tafiyar da ba’a dawowa zatayi Alhaji Mamman fashewa yayi da kuka yana “Ya Allah ka tonawa wadanan azzuluman asiri Allah ka hanasu zaman lafiya a gidan duniya Allah ka wulakantasu Allah ka dai-daitasu” 
Kuka Alhaji mamman keyi sosai 
Ahankali mazan suka fara mikewa suna Barin palon dan za’ayiwa Hajiya Nafeesa wanka a suturceta akai ta gidanta na gaskiya Ciki kuwa Saiam gajiya tayi da buga kofar ta sulale kasa tana “Mummy ki tashi kice baki mutu ba baccine ya daukeki“ 
Ahaka tayi ta sumbatu tana kuka akarshe ta koma tana sauke ajiyar zuciya ahankali wani irin bacci ne yayi awon gaba da ita ko minti biyar batayi da bacci ba tayi mafarki yanda take kwance Hajiya Nafeesa ta bude kofar dakin ta shigo fuskarta dauke da wani irin murmushi exactly kayan data sane ajikinta har da hular net din Zumbur Saiam ta mike tana nunata da hannu tare da cewa “Mummy dama baki mutu ba ni nasan mafarki nake yi ba mutuwa kikayi ba” 
Murmushin da Hajiya Nafeesa ke yine yajuye zuwa bacin rai tafara magana tana “Haba Saiam Akan me zaki ringa Min kuka alkawarin da kika daukar min kenan kada ki sake ki kara zubar min da hawaye mutuwa Riga ce a Wuyan kowa idan lokacin kafiyarka yayi babu makawa sai ka tafi Dan haka nima lokacin tafiyata ne yayi addu’arku kawai nake bukata 
Haba Saiam kada ki manta kece babba keya kamata ki ringa kwantarwa da kanenki hankali ki zame musu tamkar uwa Daddynku na cikin wani hali kiringa kwantar masa da hankali ki zama jajirtacciya Dan Allah Saiam idan kun tuna ni kuyimin addu’a kawai karku 
manta azumin danace Ku rama min” Saiam da sauri tace “to mummy wai yaushe zaki dawo muna bukatarki mummy” 
Wani murmushi Hajiya Nafeesa tayi daya sata masifar kyau da haske tace “Saiam da kunsan inda zanje ayanzu da baki ce na dawo ba da Baku wahalarda kanku kun zubarda hawayenku ba inda zanje yafiye min inda na Bari sau dubu dan haka kucigaba da min addu’a Saiam kina so inyi fushi dake”ne? 
Da sauri Saiam ta girgiza kanta 
Hajiya Nafeesa tace ” to karki kara zubar da hawayenki karki kara bari kannenki suyi kuka ko daddynku maza tashi ki tafi d’
akinku kije kiyimin addu’a kafin akaini makwancina” 
Duk mafarkin da Saiam tayi baifi cikin minti biyu ba da sallati ta mike zumbur tana bin ko ina na dakin da kallo gani take kamar ma ido biyu Hajiya Nafeesa tazo mata ba mafarki take ba maganganun da Hajiya Nafeesa tayi mata sai amsa kuwaa yake a kunenta 
Adai-dai lokacin da aka gama yiwa Hajiya Nafeesa sutura aka sata a tsakiyar dakin Ganin bugun kofarda Saiam take yayi yawa ne yasa 
Akaje aka bude mata kofar da sauri ta fito daga dakin har tana tuntube Cak ‘ta tsaya ta kurawa makarardake tsakiyar dakin ido an lullube Hajiya Nafeesa da faron likkafani 
Ahankali ta ringa tafiya har sai data karaso gaban makarar ta tsuguna ahankali wasu siraran hawaye suka zubo mata 
Da sauri ta dauke hawayen da bayan hannunta ta runtse idonta cikin dakewa da karyayar zuciya tafara karanta suratul Rahman cikin wani irin rawar murya mai dauke da kuka aya goma kawai ta iya karantawa tafara jero addu’oi tana yiwa Hajiya Nafeesa Addu’a ‘yan dakin kuwa sai ameen suke cewa Ganin maza sun fara shigowa zasu zo su dauki gawar Hajiya Nafeesa ne yasa hajiyar su Nafeesa zuwa ta janye Saiam Aikuwa kamarta zuga su Saiam dasu Safna tuni suka fashe da wani irin kuka suna kallon makarar Hajiya Nafeesa da akayi sama dashi kuka suke sosai suna shikenan mummyta tafi Duk inda ka kai da taurin zuciya sai ka zubar da hawaye Saiam kamar daukewar ruwan Sama tayi sauri ta tsayar da kukan da taketa kamo hannun su Safna gabadaya tayi ta tafara goge musu hawaye tana “mummy tace karmu sake mu zubar mata da hawaye idan baso muke tayi fushi damu ba tace muringa mata addu’a kawai” 
Tausayin Saiam neya k’ara rufe duk wayanda ke dakin dan sun dauka duk zafin mutuwar 
Hajiya Nafeesa yasa Saiam ta fita hayyacinta bata San mai take cewa ba 
Fadar mutanen da suka sallaci gawan Hajiya Nafeesa bata bakine dan sai da aka kashe hanyar da motoci suke wucewa dan inda makabartar yake da dan tazara sosai daga gidansu Hajiya Nafeesa ahaka aka kai Hajiya Nafeesa dubanin mutane na yabon hallayenta na gari banda kananan yara da har dasu akaje binneta suna ta kuka Hajiya mai raba musu alewa duk ranarjuma’a ta mutu 
ldan ka kalli yanda su Saiam suke zaune waje d’aya suna Jan carbi hawaye da majina na zubo musu lokacin da zaka fara hawaye ba sani zakayi ba 
Bama sa iya amsa gaisuwar da ake musu ciki kuwa har da saurayin Saiam da Safna da zasu Aura suna ganin halin da su Saiam suke ciki sai gashi hawaye ya hau zubo musu sabida adaren da Hajiya Nafeesa zata rasu da suka zo zance suka je suka gaisheta haka kawai ta hau yi musu wa’azi da nasiha tana kan kujera sanye da hijabi da fararen hakoran makkanta sai murmushi take she is very social and civilized dan har ga Allah har suka je gida suna yabon halayenta ashe mutuwa na nan tafe 
Saiam cikin dakushashiyar muryarta ta kalli Suhaima tana tambayarta inda Samha take da Daddy dan duk abinda akayi basani tayi ba Ta hau tambayarta ina zata je 
Cikin muryarta da bata fita tace zata je asibitin ta gano halin da suke ciki dan tamkar yanzu Hajiya Nafeesa kece mata ta kwantarwa da Daddynsu Hankali da kanenta 
Fawazz Saurayinta da sauri ya mike yace zai kaita asibitin Saiam k0 kallonsa bata yi ba tayi waje kamar iska zai dauketa  

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]