[Advertisements⬇️]

BAƘIN DARE CHAPTER 3 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BAƘIN DARE
CHAPTER 3
Da Sauri su lion suka fice daga gidan suka hau mota suka bar Layin aguje da mota biyu suka je tafiya sukayi mai Nisan gaske kafin su yanki wani daji sukayi ta kutsawa ciki babu gidaje ko d’aya sai bishiyu suke ta wucewa sai da suka kusa minti 20 kafin su isa wani katon gida dake tsakiyar dajin Cikin zafin nama black da fire suka fito suka bude gate din gidan Suka shige da motarsu tunda suka taho babu Wanda yayi magana acikinsu in banda ogansu Dake ta zuba tsaki akai akai Akram kuwa yana daga bayan motar kansa sai Sara mishi yake haryanzu yana jin ihu da kukansu Samha a kunensa tundazu da suka taho yake hango hajiya Nafeesa a idonsa Matar da ta tsaya tsayin daka Dan kar wani Abu ya sami ‘ya’yanta matar data sadaukar da rayuwarta sabida ‘ya’yanta take ya ringa hango yanda taringa tsalle tana dambe dasu lion da iya karfinta akan kar a ketawa ‘ya’yanta haddi sai gashi nan a cikin mintuna da basu wuce Ashirin ba sai gata a kwance a cikin jini rai yayi halinsa lailai duniya ba matabbata bace rai ba’a bakin komai yake ba tabbas lokaci yayi daya kamata dubun Alhaji Bala ya cika Lokaci yayi da mutane ya kamata su San irin sana’ar da yake yi insha Allahu bazai bari ya kuma fita wani operation din batare da asirinsa ya Tonu ba da wanan tunanin suka k’araso gidan bayan anyi parking ya fito daga cikin motar bayan dukansu sun shige ciki A katon Palon da babu komai sai rug carpet da one seater guda d’aya suka zazzauna inda ogansu shi kuma ya zauna akan kujerar yana wani muzurai yana karkada kafa koba a fad’a ba kasan ransa a mutukar b’ace yake Akram ya zubawa ido a lokacin da yake shigowa shima fuskarsa a daure shima waje ya samu ya zauna kusa da fire dukansu suka sunkuyar dakai 
Ogansu girgiza Kansa yayi ya dauko wayarsa daga cikin Aljihu yayi dailing wani number yasaka a handsfree sai da yayi ringing ya kai sau biyar kafin a d’aga wayar cikin wani irin kakkausar murya yace “Kura ya akayi kake kirana da asubar nan”? Ogansu rusuna kansa yayi tamkar yana gabansa yace ” Yi hakuri mai gida wani Abu mai mahimmaci yasa na kiraka yanzu Dan na Gaza hakuri” Daga daya bangaren Wanda yacewa Mai gida ya kara cewa “ina jinka” 
“Mai Gida agaskiya nagaji da fita operation da Akram babu abinda yake tsinana min sai bacin rai sau hudu kenan muna fita dashi bai taba yin komai ba sai dai ya tsaya ya kallemu ayau shine har da hanani cika manufata agaskiya mai gida ni zan hakura dashi haka zan harbeshi sabida gudun tonuwar Asirina” Mai gida da sauri yace “kana haukana Ashe Baka da hankali kasan kuwa rashin wanan Akram din acikinku shine zai sa asirinku ya tonu da wurwuri Dan ban yarda ma ka karb’e Akram din acikinku shine zai sa asirinku ya tonu da wurwuri Dan ban yarda ma ka karb’e shi ba sai danayi aiki mai karfi akansa tauraransa na da kyau na duba nagani shigowarsa cikinku ba karamin Alheri bane kuma ta silarsa akwai alherai da yawa da yake tunkaro Ku kamar yanda na fada maka kuyi hakuri da halinsa kuringa fita dashi operation karku sake Ku matsa mishi akan abinda bayaso tauraranka Dana shi nada kyau da haske Dan haka ka cigaba da hakuri nan da sati biyu kazo ka sameni akwai abubuwan da zan Baku da kai da yaranka kuyi amfani dashi har shi kansa Akram din” Wani mugun harara ogansu ya wurgawa Akram daya sunkuyar dakai yana jin duk abinda suke cewa aransa yana “nafi karfinku wlh da Allah na dogara haka Allah zai cigaba da boye muku manufata akanku” Muryar ogansu ne ya katse masa zancen zucin da yake “To shikenan mai gida ngd sai na kara kiranka babu laifin aikinmu na yau ya Dan yi kyau sai dai abincin da banci”ba Mai gida wani mugun dariya yayi yace “gwara da baka ci abincin nan ba Dan zai iya zame maka guba” Daga haka ya kashe wayarsa 
Ogansu zaro ido yayi yabi wayar da kallo yana girgiza kai daga baya ya ajiye wayar hannunsa Yasa hannu biyu ya dora a fuskarsa tare da zaro Mask mai fatar fuskar mutum daga fuskarsa ainihin fuskarsa ya bayyana Adai-dai lokacin Akram ya dago ya zuba mishi ido a ransa yana cewa “this is Alhaji Bala mai kudi known as kura insha Allahu asirinka zai tonu soon mutane zasu San true color dinka” Ni kaina sakin baki nayi ina kallonsa Dan ogansu fuska ya saka ayanzu da yacire mask din 
Fuskarsa ba baki bane wuluk kamar yanda mask din yake yana da Dan haske da bajajjen 
hanci Brief case din ya jawo da kudin suke ciki ya ringa zaro wrappers din kudin yana ajiyewa a cinyarsa har sai da ya kwashe tas daga cikin brief case din inda a lissafin da yayi brief case din million biyar ne a ciki Mai da kudin yayi cikin brief case din ya ringa zaro wrappers uku uku yana cillawa su lion duk Wanda ya cillawa sai ya chape tare da godiya Akram ya wullawa akarshe tare da zuba 
masa harara Akram kuwa ya saki murmushi yana “thank you boss” adai-dai lokacin daya chafe kudin Ogansu kara daure fuska yayi adai-dai lokacin daya daga hannunsa yana nuna Akram yace “Ak this should be  First and last da zaka min abinda kayi min yau u are just lucky mai Gida yace na bika ahankali if not wlh da am done with you since idan fa muka fita ba wani Abu kake iya tsinana mana ba raka mu kawai kake wai kuma ahaka u are part of us idan muka samo harda kai za‘a raba so dan haka babu ruwanka da yanda zamu na operation dinmu idan zamu kashe dubu muyi raping dubu is non of your business ka zuba ido kawai” Akram murmushi yayi yace “am sorry boss insha Allahu bazan kara ba wanan ma na maka magana ne sabida naga time na tafiya kar gari ya waye azo a kama mu” Wani mahaukacin dariya ogansu yayi yace “waye zai kama mu kai kasan Rabin ‘yan sandan nan ina hulda dasu koda zan fita operation ina gaya musu shi yasa wani zubin ma idan aka kirasu suke jinkirtawa basu zuwa da wuri sai sun dai dai ci na kusan barin gurin danaje operation ina barin gurin zaka ga sun iso suma ina basu nasu kason hahahahahhaha” 
With much interest Akram yace “haba no wonder shi yasa Ashe ba’a taba kama mu ba Ashe suma sun daure mana gindi boss su wa dawa waye a cikin ‘yan sandan”? Akram ya tambayeshi Dan yasan sunayen ‘yan sandan da ake hada baki dasu suna wanan ta’asar Ogansu kuwa wani dariyar ya kara kyalk’yalewa dashi ya hau zayyano mishi sunayen manyan ‘yan sandan masu daukeda babban rank inda Akram jikinsa ya dau rawa Dan not even in his dream daya taba tunanin zasu iya haka amma azahiri kuwa nunawa ogansu murna yake ahaka suka shantake suna hira su lion kuwa suna ta busa sigari sai da gari ya waye wajen 7 ogansu yayi hamma yace zaije ya kwanta Killer yaje ya dauko masa linder yaci kamar wata abinci suma suje suyi enjoying Kansu anjima zai wuce port
Harcourt wajen iyalinsa sai ya kuma jin labarin wani mai kudin da haka kowa ya watse ya kama gabansa inda Akram ya kwanta a tsakiyar carpet yana tunano halin dasu Samha suke ciki yasan by now suna can suna ta kuka 
Wai ni kam waye wannan Alhaji Balan ne sai dai kun biyoni xamuji k0 wanene 
Bangarensu Saiam kuwa Akram na ficewa Samha ta duro daga kan gado itama tazo kusa da gawar Hajiya Nafeesa tana ta kuka tana “mummy meyesa kika tafi kika barmu ya kikeso muyi rayuwa babu ke mummy kin manta hirarda mu kai dake jiya kince insha Allahu sai kin Goya ‘ya’yana mummy amma tun su Aunty Saiam basuyi Aure ba kika tafi mummy why? Kuka suka kara fashews dashi kamar ta zuga su banda Saiam data rungume kan Hajiya Nafeesa tun dazu ta kura wa jinin dake ta zuba ido ko kifta ido bata yi Suhaima ce ta fara ankara da Alhaji Nazifi dake kwance kamar matacce da sauri ta mike tayi wajensa tana ” Daddy Daddy Daddy” ko motsi Alhaji Nazifi baiyi ba wani mugun ihu Suhaima ta fasa tana “shikenan mun zama cikakkun marayu Daddy shima ya mutu” Safna da sabida tashin hankali bama tasan babu kaya ajikinta ba da gudu ta tashi tana “AAA Daddy bai mutu ba Suhaima daddy bazai tafi ya barmu ba ” Aguje ta nufi bandaki ta debo ruwa ta watsawa Alhaji Nazif Alhaji Nazifl kuwa yaja wani dogon ajiyar zuciya still bai farka ba wani ruwan Safna ta kara watsa mishi ahankali ya kara Jan wani numfashin kafin ya bude idonsa ahankali ya 
zubawa Suhaima da Safna ido kamar Wanda bai sansu ba 
Take maganar Hajiya Nafeesa ya hau amsa kuwa a kunensa “Alhaji idan wani Abu ya samu yarana wlh bazan taba yafe maka ba” Mikewa yayi zumbur yana “Nafeesa” tare da nufar wajen da take kwance da gudu inda su Suhaima suka bishi abaya aguje 
Zube wa yayi akan gawar yana kallon jinin dake ta zuba akan tiles Sahba na kwance a k’afar Hajiya Nafeesa Saiam kuma ta rungume kan Hajiya Nafeesa gam ta kurawa waje daya ido Samha kuwa ta rike hannun Hajiya Nafeesa tana wani irin kuka kamar ranta zai fita majina sai futowa yake a hancinta Alhaji Nazifi hawaye ne ya hau gudu a fuskarsa yana ” Nafeeeesa karki min haka karki tafi ki barni” 
Samha hadiye kukanta tayi tana wa Alhaji Nazifi wani irin kallo tana “Daddy kana ina lokacin da barayi suka harbi mummy?Daddy kana ina lokacin da mummy take fadin ka tashi akan ka hana a keta mana haddi? Daddy wane kokari kayi Dan kar ayi mana fyade? Daddy wane kokari kayi Dan kar su kashe mummy? Daddy mummy lost her life because of us she sacrifice her life because of us Daddy kana ina hakan duk ya faru? Daddy ayanzu zaka zo kace kar ta tafi ta barka? Daddy ayanzu kake da bakin magana? Daddy agaban idonka aka ringa kokarin yi mana fyade Daddy agaban idonka aka harbi mommy sau uku Daddy sai yanzu zaka zo bayan sun tafi ? Sai yanzu zaka yi kuka Daddy? 
Duk maganar nan da take yi kuka take sosai Alhaji kuwa zuciyarsa ya ringa bugawa da sauri da sauri kansa na juyawa ahankali yakai hannunsa ya ruko daya hannun Hajiya Nafeesa yana “ki yafemin Nafeesa bazan iya rayuwa babu keba Nima biyoki zanyi” daga haka ya rike zuciyarsa ahankali ya sulale kasa Wani mugun ihu Suhaima ta fasa daya tilastawa makota yar rige rigen shigowa Suna sallati Dan tun dazu suke so su shigo so suke barayin suyi nisa adai-dai lokacin da ‘yan sanda suka kara so gidan su Samha kuwa numfashinta ya ringa fita da sauri da sauri Saiam kuwa tamkar dutse tana nan a kankame da kan Hajiya Nafeesa ta zubawa waje daya ido Sallati mata hudun da suka shigo da mazajensu suke tayi suna kiran Hajiya Nafeesa sai a lokacin Safna ta Ankara ba kaya ajikinta Dan hada ido tayi da mijin wani makocinsu yana mata kallon kurilla da sauri ta janyo hijabi tasaka A adai-dai lokacin da ‘yan sanda uku suka shigo da mace daya 
Da kyaryan sandan ya tilasta wa matan suyi shiru dasu Suhaima Dansu tambayesu duk 
yanda akayi Alhaji Nazir dake gefen gidansu Alhaji Nazifi ne yafara cewa bari akai Alhaji Nazifi asibiti Dan yana numfashi kadan kadan da sauri suka kinkimeshi sukayi waje 
‘Yan sandan kuwa suka tsugunna a kusa da gawar Hajiya Nafeesa macen ta ringa daukar gawan hoto da wajen da dajinin ke zuba akan tiles din kuka yaran suke kamar ransu zai fita Ahankali macen ta matsa kusa da Saiam Dan tace mata ta sausauta rikon da tayi wa Hajiya Nafeesa haka sabida ta dauki fuskarta hoto 
Kukansu ne ya dauke gabadaya a lokacin da Saiam ta aza daya hannun ta abakin ta alamar suyi shiru ssshshhssh tace cikin whisper kamar bata San aji’ mai take cewa “kuyi shiru karku tashi mummy daga bacci bacci take yi ba mutuwa tayi ba uban waye yace mummy ta mutu to duk Wanda yake wa mummy fatan mutuwa shi zai mutu ba mummy ba dan haka Ku matsa karku tasheta 
Mummy ai baki mutu ba ko? ni nasan bacci kike yi ba gobe kika ce zamuje gidan Aunty 
khadija ba Ni nasan bazaki mutu ba lah mummy kinga wai kuka suke kin mutu” 
Wani mugun ihu Safna ta fasa tana tashiga uku ta lalace Aunty Saiam ta haukace su Sahiba kuwa jikinsu ya dauki rawa suka zubawa Saiam ido dake kwantar da gashin Hajiya Nafeesa’Yan sandan kuwa hankalinsu ne ya tashi suka hau yimata video still lokacin tana surutu ita kadai Samha kuwa zubewa tayi akasa Dan kokawa take da numfashinta 
Ahankali aka fara rarrashin Saiam data kara rungume kan Hajiya Nafeesa kamar wacce za’a kwace ta sai surutu take ita kadai tana yiwa Hajiya Nafeesa rada a kunne ganin bama tasan suna yi ba yasa suka fara kokarin banbare hannun Saiam daga kan Hajiya Nafeesa data rungume 
Wani mugun ihu ta ringa yi tana karsu tashi mummynta bacci take ba mutuwa tayi ba su rabu da ita kar su tasar mata mummynta ……….
 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]