[Advertisements⬇️]

BAƘIN DARE CHAPTER 15 - Bankinhausanovels
Tue. May 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BAƘIN DARE 


CHAPTER 15Da Madaukakln mamaki Alhaji Bale ya zubawa Akram Ido dake wani irin Murmushl 
Akram kuwa yace “Kana mamaki ne Alhaji Bala yau dubunka ya cika asirinka ya tonu yau mutane zasu San wanene kai yau duniya zata San irin mugayen abubuwan da kake aikatawa yau za’a San irin sana‘ar da kake yi har kake taimakawa mutane ake maka kallon mutumin kirki nan kuwa babu Wanda ya kai ka zalunci a d’oron k’asa am not who you think am not one of you nashiga cikinku ne Dan na kara Sanin kai waye Alhaji Bala despite abinda ya faru da ya kamata ya zame maka ishara na fyaden da aka yiwa ‘yar ka har ya kai ta ga rasa ranta wannan bai sa ka saduda ba kayi nadamar abinda kayi kasan cewa abinda kake yiwa yaran wasu ne ya juya kanka amma me a madadin kayi nadama a lokacin ka kara shan Alwashin yanda zaka cigaba da farautar dukiyoyin jama’a kana ketawa ‘ya’yansu 
haddi not any more Alhaji bala
Wani mahaukacin Dariya Alhaji Bala ya fashe dashi yace “kayi kuskure Akram da kayi tunanin wannan soki burutsun da kake yi zai tsoratani I thought as much kai ba Alheri bane 
awajena and ayau zanyi finishing dinka Lion Black before counting of 3 Ku bude mishi wuta” 
Alhaji Bala yace yana buga kafarsa da kasa tare da rike hannun Akram dake rike da 
bindiga Su Lion ajiye bindigogin hannunsu sukayi amadadin su bi umarninsa 
Alhaji Bala ya saki baki yana kallonsu cikin tsananin mamaki Akram kuwa ya saki murmushi yana girgiza kai 
A tsawace Alhaji Bala yace “kanku d’aya kuwa ko Baku ji mai nace bane shoot this fool before counting of 2” 
Lion a hankali ya girgiza kansa yana “oga bazamu iya ba” Alhaji Bala jikinsa ne ya fara rawa for the first time yaji gabansa ya fadi 
Shammatar Akram yayi ya dauki bindigarsa daya ajiye a k’asa. 
A tare sukayi pointing juna da bindigar 
Alhaji Bala kyalkyalewa yayi da dariya yace “Akram you are such a big fool wlh babu abinda zai hana yau na kasheka Sai a yau nake dana sani Dana taimake ka Mai gida ya yaudareni da ya bari na jawo ka jikina tayaya mutane zasu San abunda nake aikatawa 
tayaya dubuna ya cika Do u have any prove against me no u don’t have now drop your gun or I else 
“Or else what Alhaji Bala wat can you do”? Yaji an fadi daga bakin k’ofa Da sauri ya waiga Dan yaga Wanda yake magana Abdullahi ne ya shigo ‘yan sanda suna take mishi baya tare da pointing dinshi da bindiga 
Alhaji Bala ido ya waro sosai a lokacin da ‘yan sanda suka zagaye shi ‘yan jarida da video 
coverage suma suka hau haska su da cemarorinsu 
Bindigar Hannun Alhaji Bala  subucewa yayi daga hannunsa cikin tashin hankali yafara 
binsu da kallo daya bayan d’aya jikinsa na rawa 
Akram kuwa ya kara sakin murmushi yace ” yadai oga y are u speechless daka gansu I 
thought ai zaka bude musu wuta ne da suka shigo” 
Juyawa yayi ya kalli masu video coverage da hotuna yace “Ku dan Matso kadan kuga Wanda ke mana wannan aika aika kuga Wanda ke farautar dukiyoyin jama’a da yiwa yaran mutane fyad’e” 
Da sauri suka matsa kusa da Akram Dan burin kowa yaga shi ya fara d’aukan wanan mugun Dan fashi da ya addabi jama’a 
Alhaji Balajikinsa in banda rawa babu abinda yake yi gani yake kamar mafarki yake yi wai shi yau ‘yan sanda suka zagaye da ‘yan jaridu ‘ 
Akram kuwa a hankali ya matsa kusa da Alhaji Bala ‘yan sanda kuwa suka kara saita shi da bindigoginsu in case in zai yi gardama 
Akram da murmushi ya kai hannunsa fuskar Alhaji Bala dan ya Ciro mask din fuskarsa 
Alhaji Bala yayi sauri ya rike mishi hannu yana “Akram Dan Allah karka min haka ka rufa min asiri kar ka kunyatani” 
Wani irin murmushi Akram yayi ta gefen baki yace “kunya kuma Alhaji Bala kunya fa kace al babu batun kumajin kunya a yau babu batun rufin asiri ayau a yanzu zan cire wannan Mask din fuskar taka kowa yasan kai waye” 
Alhaji Ghali da sauri yaje ya tsaya a gefensu Akram dan ya matsu yaga waye 
Alhaji Bala runtse idonsa yayi da karfi jikinsa na masifar rawa a lokacin da Akram yafara kokarin cire Mask din fuskarsa 
”Alhaji Balaaaaaaaaaaaa” Alhaji Ghali yace cikin shock tare da nuna shi da hannu 
Wayanda kuwa basu San Alhaji Bala ke wannan ta’asar ba suma jikinsu ya hau rawa suka kura mishi ido har da masu kara Murza idonsu dan su tabbatar da shine ko bashi bane. 
Alhaji Bala kuwa runtse idonsa yayi gam yaki ya bude idonsa dan nashi din camerori ke haska shi ko ta ina 
D’aya daga cikin ‘yan sandan ne ya matsa kusa dashi ya kamo hannayensa ya saka mishi 
ankwa 
Alhaji Bala da sauri ya bude idonsa sakamakon wani mahaukacin dariya dayaji a gefensa Na Maliya ya hango akan ruwa sai yawo yake asaman ruwa yana kyakyata dariya Alhaji Bala kuwa hawaye ya hau zubo mishi a idonsa 
Na Maliya yace “Alhaji Bala mai akayi da maza ai baka ga komai ba tukuna sai na taso maka wayanda zasu na debe maka kewa a kurkuku sai ka roki mutuwa ta dauke ka da rayuwar tashin hankalin da zaka ringa yi” 
Wani Mahaukacin dariyar ya kara kecewa dashi ya bace 
Alhaji Bala hawaye kawai yake a lokacin da ‘yan sanda biyu suka fara tura keyarsa suna 
nufar waje dashi Su Lion ma tuni aka saka musu ankwa a hannu akayi waje dasu 
Alhaji Ghali dake daskare awaje daya dan tsabar mamaki binsu yayi da sauri Wani dan 
sanda ya dakatar dashi akan kar ya bisu Masu hotuna da video coverage sai turereniya suke wajen d’aukan Alhaji Bala har aka dasu 
 Black  suka fara tafiya babu abinda kakeji saijiniya 
Masu video coverage da hotuna tuni suka koma kan Akram dake Rike da Mask din Alhaji 
Bala suka fara daukansa ‘yan jarida kuwa suka fara jera mishi tambayoyi 
Akram kuwa dakyar ya ratsa su ya shige cikin mota sai hamdala yake a zuciyarsa da Allah 
ya cika mishi burinsa na damke Alhaji Bala 
Sai da suka koma cikin gidan Alhaji Bala dake Cikin daji suka d’auko Killer dake huge huge yana zabga ihu shi kad’ai dan Yanzu kuma ba iya Hajiya Nafeesa yake gani ba har da wasu daya kashe da hannunsa ahaka aka kwashe shi aka sa a mota suka nufi: headquarters 
d’insu da ake ajiye manya manya masu laifuka 
Alhaji Bala kuwa kansa a sunkuye sai addu’a yake Allah yasa Mafarki yake bayajin zai iya jurewa idan mutane suka gano shine yake aikata wannan ta’asa da wane ido zai kalli mutanen garinsu da wane ido zai kalli Mahaifiyarsa da kannensa da wane ido zai kalli mutanen da yake taimakawa a matsayinsa na mutumin kirki mai tausayin Talakawa lallai Akram ya shamace shi daya san cewa Akram dan bincike ne da ya Dade da kashe shi 
Kafln kace me labarin Alhaji Bala shahararren mai kudi mai taimakawa talakawa ya karade gari da jIhohi gabad’aya akan shine shahararren dan fashi da makami mai farautar dukiyoyin jama’a da yiwa yara fyad’e duk gidan radio ko television daka kuna labaran kawai ake yi hotonsa aka hada da Wanda yasaka mask da ainihin hotonsa da mutane suka San shi dashi Alhaji Bala 
Jama‘a gari kuwa sai mamaki suke manyan masu kud’i da suka San shi ta hanyar taimako suka hau bugawa junansu waya wasu ma basu yarda ba sai da suka ringa bugawa shugaban ‘yan sanda waya dan su tabbatar da abinda sukeji wayanda kuwa sukayi falling Victim kuwa tuni suka hau sujadda suna godewa Allah wasu kuwa suka ringa shirin zuwa ganin shi 
Akram kuwa kansa ya dau zafi ‘yan jarida sun cika bakin office din shi sunajiran ya fito ya 
musu Karin bayani akan yanda yayi nassarar cafke Alhaji Bala da yanda akayi ya gano Alhaji 
Bala dan fashine 
Sai da Akram yayi wanka ya shirya a toilet dinsa dake cikin office dinsa ya daura alwala yazo ya ringa jera namfilfili na godiya da Allah daya bashi nassara akan Alhaji Bala bai samu 
fitowa ya saurari ‘yan jaridar ba sai wajen 10am na safe 
Farin suit ne a jikinsa da bakin nectie yayi masifar kyau ai yana fitowa camera ta hau haska shi ‘yan Jarida sukayi dafifi suka hau yi mishi tambayoyi har suna turereniya 
Akram kuwa sai da ya gyara tsayuwarsa yayi godiya ga Allah tare da addu’a kafin ya fara 
magana cikin hadadden turancinsa inda gidan talabijin na AIT suke haskawa live tare da raba screen d’in gida biyu Akram a daya bangaren yana kwarara jawabi daya b’angaren kuma hoton Alhaji Bala ne dan fashi da hoton Alhaji Bala da mutane suka sani a matsayin 
mai taimakon Talakawa 
A dai-dai lokacin iyalan Alhaji Nazifi na zaune a palon gidan suna karyawa Samha mayyar kallon Indian series tana aikin nata na kallo ganin sun tafi talla ne yasa ta fara kokarin canza tasha inda kuwa ta kamo tashar AIT adai dai lokacin da aka hasko Akram yana kwarara bayani agefe ga hoton Alhaji Bala mikewa sukayi gabadaya dan bazasu taba manta fuskar Alhaji Bala ba Kofin shayin dake hannun Samha ya subuce daga hannunta ya fadi kasa gabanta na 
mugun faduwa kurawa Akram ido kawai tayi 
Adai dai lokacin da Saiam itama take kallon labaran ta latso lambar Alhaji Nazifi dan tace su kamo tashar AlT 
Wayar na ringing amma Alhaji Nazifi ya kasa dagawa dan mutuwar zaunen da yayi ……. 

Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]