[Advertisements⬇️]

BAƘIN DARE CHAPTER 14 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BAƘN DARE 
CHAPTER 14
Bangaren su Samha kuwa rigima ake sosai da Alhaji Nazifo dan dangi sun sako shi agaba akan ya Auri cousin dinsa Nazifa sabida bai dace ya zauna babu mata ba kuma su Samha suna bukatar masu kula dasu 
Fir Alhaji Nazifi yace bai San wannan zancen ba babu macen da zai iya zama da ita zai iya kula da ‘ya’yansa ba sai yayi Aure ba 
Babu yanda dangi basu yi dashi ba har Mahaifiyarsa yace Sam ba zai yi wani Aure ba shi da Aure sai dai A Iahira akan dole suka hakura suka zuba mishi ido Nazifa kuwa ta tattara inata inata ta tafi
Daga Alhaji Nazifl sai su Samha da suka rage 
Alhaji Nazifl yana iya kokarinsa wajen kula dasu baya bari su zauna su kadai ballantana suyi tunani tsakiyarsu yake shiga yayi ta jansu da hira shi yake kai su makaranta kasancewar Saheeba da Suhaima makarantar gaba da secondary suke yi a university of abuja department dinsu ma daya suna level 2 suna karantar mass communication 
Samha ce kawai ke final year a secondary school babu abinda suka fasa game da abubuwan da Hajiya Nafeesa keyi na bangaren sadaka duk ranarjummaa da takewa Almajirai 
Samha haka kawai fuskar Akram ya kasa bacewa a idonta indai ta zauna ita kadai sai tunaninsa ya fado mata ta ringa jin wani iri a zuciyarta Wanda ta ringa alkanta haka da kiyayyar da take musu Dan babu wayanda ta tsana kuma bazata manta dasu ba sama dasu Alhaji Bala har gobe tana hango fuskokinsu a idonta Wanda Akram yafi tsaya mata a zuciya ta kuma rasa dalilin haka babu ranar da zata dungura goshinta a kasa batayi addu’a akan Allah ya tona musu asiri ba 
Su Saiam kuwa suma tuni suka fara warwarewa Dan mazajensu na iya bakin kokarinsu wajen debe musu kewa kullum a cikin waya suke dasu Saheeba addu’a suke sosai Akan Allah yayiwa Mahaifiyarsu Rahama duk da wani zubin su kanyi mafarki da ita a cikin kyakyawan yanayi 
Bangaren su Akram kuwa tuni sukayi arranging din yanda zasu damke Alhaji Bala aranar da zaije operation gidan Alhaji Ghali inda suka jawa su killer kunne sosai akan su basu hadin kai kar Alhaji Bala ya gane wani Abu har suyi arresting dinshi 
Tuni su Akram suka nufi Dajin da suke zama Dan sujira Alhaji Bala 
lnda ‘yan sanda kuwa suka yi surrounding din gidan Alhaji Ghali ba tare da saninsa ba har da masu video coverage da hotuna 
Alhaji Bala kuwa a no mercy dinsa ya nufi Abuja da mugun nufi a zuciyarsa dan tunda Naila ta rasu yaji bai ki duk Wanda yayi tozali dashi ya mutu ba most especially mata Sa’annin Naila Dan aransa ma ya kuduri idan Akram yau ya bijirewa Umarninsa babu abinda zai hana ya harbe shi 
Karfe goma sha d’aya ya isa Dajin fuskar nan tashi a daure yana shiga kantamemen palon dukansu suka mike tsaye alamar girmamawa dan dama haka suke gaishe shi 
Akram kuwa haka kawai gabansa ya yanke ya fadi da suka hada ido da Alhaji Bala take ya hau Jan addu’oi aransa akan Allah ya basu Nassara har su damke Alhaji Bala batare da wani failure ba 
Daya bayan daya Alhaji Bala ya ringa binsu da kallo wanda da ace da wadatar haske awajen babu abinda zai hana yaga yanda su killer suka fita daga Hayyacinsu gaban Akram kuwa sai faduwa yake 
A hankali ya sauke idonsa akan Akram dan shine a karshe gabansa yaje ya tsaya ya damko kafadarsa yace ” Akram a yau inaso kasani babu tausayi babu imani a cikin al,amarina kayi taka tsan tsan karka bijirewa umarni na dan wlh yau slide mistake idan kayi sai ka tafi lahira na d’au alwashin sai na d’au fansar Kisan da aka yiwa ‘yata Naila wlh babu Wanda zan ragawa yau Dan haka u guys should be very carefull“ 
Killer ji yake kamar ya fito yayi magana yace wa Alhaji Bala Akram pretending yake ayau za’a kama shi dan ayanda yakeji aransa gwara a kashe Akram inyaso a kamasu gabad’aya take yayi amana da shawara daya yanke 
Ya bude Baki yace “Oga inada Magana” Gaban Akram ne yayi wani irin Yankewa ya fadi ya zubawa Killer ido 
Killer kuwa ya d’auke kai ya kalli Alhaji Bala ya bude baki zai yi magana bude bakinsa keda wuya yaji an dauke shi da wani bahagon mari daya sa ya kusa kurmancewa 
Dafe kumatunsa yayi da hannu biyu ya waiga da sauri Dan yaga Wanda ya zuba mishi 
wannan Marin 
Hajiya Nafeesa ya gani a gefensa ta gwallo ldO tana kallonsa Sai huci take Wani razannan ihu yasa ya kankame Black yana nuna hajiya Nafeesa da Hannu Su Alhaji Bala kuwa suka bi inda yake nunawa da kallo basu ga komai ba 
Wani ihun ya kara sawa A lokacin da Hajiya Nafeesa ta ringa doso shi yaje ya kankame Alhaji Bala yana kokarin magana 
Amma ina amadadin yayi magana sai gwaranci yake yi kamar mai koyon magana 
A zuciye Alhaji Bala ya ture shi daga jikinsa ya dauke shi da mari yana “wanan wane irin iskanci ne zaka ishe mu da ihu menene yake tsorata ka wani sabon iskancin ne haka”? 
Killer zaro ido kawai yake yana gwaranci yana nuna Hajiya Nafeesa da hannu sai kokarin kankame Alhaji Bala yake 
Ihu kawai yake yana zagaya wajen yana gwaranci Dan Hajiya Nafeesa tsorata shi take sosai 
Akram kuwa mamaki ya ringa yi na abinda yake tsorata killer haka har maganarsa ta koma ta yara 
Alhaji Bala a zuciye ya damko killer ya wulashi daki ya kulle ya dawo cikin palon ya kalli agogon hannunsa yaga karfe sha biyu da minti ashirin 
Bakaken kayansa ya d’auko yasa ya dauko mask dinsa ya saka a fuskar shi with Command yace su wuce time yayi
Da sauri suka ringa ficewa jikinsu na dan rawa Alhaji Bala ya ringa mamakin yanda akayi basu da kuzari kwata kwata sai da ya koma dakin daya sa killer ya saka seletep ya rufe mishi baki sabida ihun da ya ringa yi Dan har fitsari ya saki a wando 
Sannan ya fito suka d’auki hanyar gidan Alhaji Ghali yana ta sake saken irin muguntar da zai yi 
Basu sha wahalar shiga cikin gidan ba dan Alhaji Bala sai da ya shirya sosai kafin su taho mai gadi ma gindin bindiga ya buga mishi ya zube awajen a sume 
Da zuwansu da shigarsu cikin gidan ‘yan sandan dake kewaye da gidan duk suna Sane tuni suka kara gyara tsayuwarsu suna jiran abasu Umarni banda masu video coverage da hotuna da suma suka zama ready suna jiran su fara aikinsu dukda wasu sun fara daukansu video a lokacin da suka shigo 
Alhaji Bala kafa daya akan d’aya ya dora a centertable d’in dake cikin palon yana girgiza k’afa a lokacin da su Black suka raba Kansu suna fito da mutanen dake cikin gidan ciki kuwa har da Akram da wani irin farinciki yake ratsa shi na cikar burinsa finally Alhaji Bala yau asirinsa zai tonu 
Alhaji Bala kuwa wani irin dariyar mugunta yake a lokacin da yaga ana hankado keyar 
‘ya’yan Alhaji Ghali Dan dukansu sun zo Hutu su wajen Uku hadaddun yan mata kyawawa dasu 
Alhaji Bala sai Lashe lebb’e yake yana matsa cinya yana hararo yanda zai musu fata fata har sai sun koma ga mahallicinsu 
Alhaji Ghali kuwa da matansa biyu jikinsu rawa kawai yake 
Sai da ya gama karewa ‘yan matan kallo ya maida kallonsa kan Alhaji Ghali yace “kasan abunda ya kawo mu ba sai ka bata mana lokaci ba” 
Alhaji Ghali jiki na rawa ya shiga gyada masa kai 
Alhaji Bala kuwa ya kalli Lion da black sukayi sauri suka tisa keyar Alhaji Ghali suka shiga ciki suka hau fito da kudadde a brief case suka hau ajiyewa agaban Alhaji Balan daya tsurawa ‘ya’yan Alhaji Ghali ido da suka cure waje daya jikinsu na rawa 
Sai da suka gama ajiye kudin agabansa ya kalli Alhaji Ghali da jikinsa ke rawa yace “Ka tabbata duk kudin dake cikin gidanan kenan”? 
Girgiza masa kai Alhaji Ghali kawai yayi dan yama kasa magana kwata kwata 
Alhaji Bala murmushi yayi ya mike ya nufi wajen ‘yan matan yana wani lashe lebb’e 
Alhaji Ghali kuwa yayi sauri yasha gabansa cikin rawar murya yace ” bawan Allah Dan Allah dan annabi karka taba min yarana idan kud’i kake so zan kara maka” 
Alhaji Bala wani Mahaukacin dariya ya kwashe dashi yace “k0 duk kudin duniyan nan zaka bani wlh babu abinda zai hana ni yaga yaran can” 
Gaban Alhaji Ghali ne yayi wani irin faduwa ya durkusa akan gwiwarsa yace “bawan Allah ka rufamin asiri dan Allah karka taba min yarana” 
Alhaji Bala wani dariyarya kara kecewa dashi yace “ai ba iya yaranka zan taba ba harda wadancan guzumayen” 
Akram kallonsu kawai yake yana murmushi 
A lokacin da ‘yan matan suka fashe da kuka suna kara kankame juna 
Alhaji Bala ture Alhaji Ghali yayi daga gabanshi ya nufi wajensu yana wani dariya 
Alhaji Ghali kuwa yabi bayansa da Sauri yana rokon shi 
Fuska a d’aure Alhaji Bala ya juyo ya kalli Akram da still murmushi yake shimfide a fuskar shi yace “take care of this fool” 
Akram cikin takun kasaita ya nufesu yana wani irin murmushi adai~dai lokacin da Alhaji 
Bala ya finciko dayarsu ta Saki wani wawan Ihu 
Wani bahagon Mari Alhaji Bala ya shimfida mata a fuska ya jawo rigarta zai raba gida biyu yaji an dora mishi bindiga a keya yaji ana fadin ” thousand days for the thiefs one day for the 
owner Alhaji Bala your cups is full” 
Alhaji Bala a hankali ya juyo dan ya gaskata muryar Wanda yaji ………… 
Hmm su Alhaji bala anzo hannu

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]