[Advertisements⬇️]

BAƘIN DARE CHAPTER 11 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BAƘN DARE 
CHAPTER 11
Hajiya Lubna da Naila dake zaune a Palo suna kallo wajen karfe goma sha daya na dare a firgice suka mike a lokacin da suka ga Alhaji Bala ya shigo kafa babu takalmi yabi ya fita daga hayyacinsa idon nan nasa yayi jazur 
Hajiya Lubna sallati kawai ta ringayi har Alhaji Bala ya zube akan kujera yana dafe da kansa 
Naila da Sauri ta matsa kusa dashi tana “Daddy mai ya sameka” 
Alhaji Bala dagowa yayi tare da cire hannunsa daga kansa a lokacin da ya kurawa Naila ido hawaye masu zafi suka hau zubo mishi wai princess dinsa daya kejinta tamkar ruhinsa ita zai kaiwa Na Maliya a lalata ta har na tsawon wata uku da ace yasan abinda Na Maliya zai nema kenan gwara ace Fatalwar Hajiya Nafeesa tayi ta bibiyarsa har ya mutu bazai taba iya kai Nailarsa wajen Na Maliya ba yayi duk abinda zai yi 
Naila hankali a tashe ta hau sharewa Alhaji Bala hawaye itama hawayen ya hau zubo mata tana “Daddy mai yasa kake kuka mai ya faru” 
Hajiya Lubna sakin baki tayi tana kallon ikon Allah Dan zata iya cewa this is the first time data ga hawaye a fuskar Alhaji Bala ko a lokutan baya da yake cikin tashin hankalin da bata San abinda ya haddasa masa shi bata ganin yana zubar da hawaye kamar yanzu 
Alhaji Bala hannayen Naila ya ruko yana “Angel insha Allahu indai ina rayye babu Wanda ya isa ya cutar dake I would protect you with all I have banida sama dake a rayuwata zan iya yin komai akanki babu wanda ya isa ya keta miki haddi sai dai idan bana numfashi 
Hajiya Lubna da sauri ta mike jikinta na rawa ta nufi wajen Alhaji Bala tana ” Alhaji wai mai yake faruwa ne waye zai taba Nailan”? 
Alhaji Bala mikewa yayi ba tare da ya kalli Hajiya Lubna ba ya nufi bangarensa 
Hajiya Lubna tayi sauri ta sha gabansa tana “Bala magana nake maka kayi min bayani waye zai cutar da Naila”? 
Alhaji Bala matsar da Hajiya Lubna yayi ya nufi dakinsa Dan a halin da yake ciki baya jin zai iya wani dogon magana 
Hajiya Lubna bin bayansa tayi da kallo har ya shige dakinsa Juyawa tayi ta kalli inda Naila ke zaune ta hada tagumi da hannu biyu hawaye nata zubo 
mata Dan Sam bata gane mai Alhaji Bala yake nufi ba 
Aranar Alhaji Bala ko runtsuwa bai yi ba yana saman gado a zaune yana ta tunanin yanda 
zai biyowa Na Maliya Dan Sam ba zai iya kai tilon ‘yarsa ba 
A takaice sai da Alhaji Bala ya zama tamkar wani zararre sabida fargaba da tsoro dan gani yake Tamkar Na Maliya zai iya zuwa ya dauke Naila ne Hajiya Lubna ta kasa gane kansa tambayar duniya tayi mishi akan ya gaya mata abinda ke faruwa yaki ya gaya mata 
Aranar da aka samu kwana uku da dawowarsa daga wajen Na Maliya yana zaune a dakinsa ya buga tagumi yana tunanin yanda rayuwa take juyawa dashi sai ayanzu yake daya sani bai kashe Mai gida ba Dan yasan mai Gida bazai taba masa haka ba yana ganin shima Kashe Na Maliya kawai zai yi ya huta inya so idan ya gama dashi sai ya San abun yi akan operation da yake fita babu Nassara Da wanan tunanin ya samu hankalinsa ya dan kwanta washegari ya dauki Hanyar sokoto da sassafe da zumar zuwa ya kashe Na Maliya,,, 
Bangarensu Akram kuwa sun gama shirya yanda zasu damke Alhaji Bala Dan sunga alamar ya fara dago Akram sabida mugun sa mishi ido da Alhaji Bala yayi Dan a ranar da zai tafi sai da yace mishi idan suka kuma fita wani operation din Akram bai tabuka abin arziki ba babu abinda zai hana ya kashe Akram 
Kwana biyu da tafiyar Alhaji Bala ogan Akram Abdullahi yayi arranging din motocin ‘yan sanda aka je akayi arresting dinsu Lion gabadaya 
Akram dake cikinsu a hankali ya fita daga tsakiyarsu yayi joining din yan sandan ya zaro ID card dinshi ya nuna musu yana Murmushi 
Mamaki ne ya hana su motsawa sakin baki kawai suka yi suna kallon Akram kamar wani sabon hallita 
Akram daya bayan daya ya bisu ya kwace wayoyin hannunsu da bindigogi aka tasa keyarsu aka yi waje dasu 
Killer kasa hakuri yayi sai da yace “Ak meyesa kayi mana haka Ashe shigowa kayi cikinmu Dan ka San sirrinmu you are not part of us why Akram ? 
Akram murmushi yayi yace ” am Never part of you guys nayi pretending Na zauna a cikinku Dan nasamu enough evidence akan Ku da Mai gidanku Alhaji Bala Alhamdulillah Na samu 
more than enough evidences” “Yaro take them away” 
Da sauri dan Sandan da aka kira da Yaro ya tasa keyarsu Killer suka shige motar Su Akram suka bisu a baya 
Alhaji Bala kuwa boye bindigarsa yayi a wandonsa gabansa Na faduwa ya nufl inda Na Maliya ke zama Dan ya yanke a ransa zai yaudari Na Maliya ne akan ya amince idan ya sakankance sai ya zuba mishi Harbi 
Tun kafin ya karasa Ya fara jiyo dariyar Na Maliya mai barazanar toshewa mutum kunne jiki na dan rawa Alhaji Bala ya karasa yana nan a zaune a saman ruwa sai yawo yake yi 
Zubewa yayi agabansa kamar zai yi mishi Sujadda Na Maliya kuwa ya cigaba da kyalkyala dariya ‘ Alhaji Bala ganin yaki ya mishi umarni daya dago ne yasa ya dago Dan Ya Kalleshi ga mamakinsa sai ganin bindigarsa daya boye a wandonsa yayi akan ruwa a gefen Na Maliya 
Da Sauri ya mike tare da kai hannunsa wajen daya boye bindigar yaga babu komai Na maliya kuwa ya cigaba da kyalkyala dariya 
Wani irin tsoro ne ya rufe Alhaji Bala Na maliya kuwa ya tsayar da dariyarda yake yi yace “ka bani tausayi ka dauka karfina dana mai gidanka daka kashe daya ne to idan kana tunanin zaka iya kasheni karyar ka ta sha karya domin a tafin hanuna kake duk wani motsin ka da shirin da kake yi ina kallonka ba zaka iya kasheni ba dan haka kajuya ka tafi ranakun Dana dibar ma idan sun cika baka kawo taba zanzo na dauketa da kaina idan kuma ka dauka da wasa nake karka kawo ta kagani karbi bindigar ka ka bace min da gani” 
Alhaji Bala ja da baya yayi da sauri jikinsa na mugun rawa a lokacin dayaji bindigar a wandonsa 
Zubewa yayi a kasa yana “ka rufa min asiri karka min haka ka fadi duk abinda kake so zan kawo maka cikakkun ‘yan mata guda goma zan kawo maka kudi amma Dan Allah ka rabu da ‘yata ba zan iya kaw0 maka ita ba Na Maliya Dariya ya kwashe dashi ruwan da yake kai yafara iyowa kan Alhaji Bala 
Alhaji Bala kuwa ya fara falfala gudu wufyaga anyi sama dashi an Nana shi da k’asa sai gashi agaban motarsa 
Aguje ya mike ya hau motarsa yabar wajen 
Ikon Allah ne kawai ya kawo shi gida Dan Sam ba’a hayyacinsa yake ba Na maliya ya masifar tsorata shi 
Yana isa gida bangaren Naila yayi a guje dan yaga k0 tana nan Dan gani yake kamar Har Na Maliya ya dauketa 
Naila dake kwance da wayarta a hannu tana buga game da sauri ta mike a lokacin data ga Alhaji Bala ya fado d’akin kamar Wanda aka hankado 
Alhaji Bala wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da dafe zuciyarsa a lokacin daya ga Naila Naila a tsorace tace “Daddy Lafiya kuwa”? Alhaji Bala girgiza mata kai kawai yayi ya juya yayi waje 
A tsakiyar dakinsa ya tsaya tare da dora hannunsa aka yana tunanin mafita dan Na Maliya yafi karfinsa ahaka ya raba dare yana tunani sai da wani tunani ya fado mishi ya saki wani murmushi cike da farinciki dan gani yake idan yayi haka shikenan Babu yanda za’ayi Na Maliya ya dauke mishi Naila da wanan tunanin ya samu bacci yayi awon gaba dashi rabon da yayi bacci cikin dadin rai irin wanan harya manta 
Bashi ya farka ba sai wajen Tara da rabi na safe yana kuwa tashi k0 sallah bai yi ba ya fice daga gidan dan yaje ya sama musu Visa shi da Naila dan barin kasar shi zai fiye mishi Alheri 
Bai dawo gidan ba sai wajen karfe hudu yana zuwa yacewa Hajiya Lubna ta fara hadawa 
Naila kayanta zasu bar kasan goben nan Mamaki ne ya rufe Hajiya Lubna da Naila zasu yi magana Alhaji Bala ya dakatar dasu ta hanyar daga musu hannu yace ” bana San tambayoyi ki had’a mata kayanta kawai gobe zamu tafi Dubai ke kuma zaki iya tafiya garinku idan na dawo zan biyo na dauke ki” 
Hajiya Lubna wani mamakin ne ya kara rufeta tace “mai Naila zataje tayi a Dubai Al halin basuyi hutun makaranta ba wai nikam Alhaji mai ke faruwane da kake boye min wlh idan baka fadamin ba babu inda za’a kai min ‘ya dan Sam bana gane maka kwana biyu idan wani abun ne zai samu Naila ka fadamin mana” 
Wani mugun tsaki Alhaji Bala yaja yace “kindai San bazan cutarda ‘yata ba koko ke baki isa ki hada kanki dani ba awajen kaunar Naila gobe zan kai ta Dubai idan an kwana biyu zan dawo da ita idan kinga dama ki had’a mata kayanta idan baki ga dama ba ki barshi idan munje can na siya mata sabbi” 
Daga haka Alhaji Bala ya shige dakinsa Hajiya Lubna zaman dirshan tayi akan kujera tana tunanin mai Alhaji Bala ke nufi da kai Naila Dubai definately akwai abinda ke faruwa da yake boye musu” 
Naila kuwa tsoron Alhaji bala ne yafara rufeta dan bai tab’a cewa zai kai ta waje ita kadai batare da mahaifiyarta ba 
A takaice haka su ukun sukayi jungum jungum ko abincin dare babu Wanda yaci acikinsu 
Alhaji Bala kwance akan gadonsa shi kadai sai sakin munshari yake alamar yanajin dadin baccin da yake yi 
Hajiya Lubna kuwa tana kwance ita da Naila dan tare suke kwana 
Kamar a Mafarki Hajiya Lubna taji anaja mata kafa bude idon da zata yi sai tayi tozali da wani dirkakken mutum a tsaye hannunsa rike da wani dogon bindiga sallati tayi cikin faduwar gaba ta bude idonta sosai anan taga su wajen shidda ne duk sun dora kafa akan gadon da suke a kwance kai ko baka fada ba kana ganinsu kasan Arna ne dan dukansu wuyansu sanye yake da cross gasu murtuka murtuka 
Naila itama juyawa tayi da zumar ta gyara kwanciyarta kamar cewa akayi ta bude idonta tayi tozali da samudawan da suka zagaye gadon da suke kwance babu alamar imani Sam a 
tattare dasu dan bama su San shi ba tunda arna ne 
Jikin Hajiya Lubna rawa kawai yake bakinta ma haka 
Da hannu daya murjejen dake gabanta ya damkota daga kan gadon ya wurgarda ita k’asa dayan ma ya cakumo Naila da hannu daya sukayi waje 
A babban palon gidan suka zubar dasu 
Anan ma wasu hudun ne a zaune akan kujera sun ma fi wayanda suka shiga dakin Girma da tsayi 
Tuni hantar cikin Hajiya Lubna ya kada Naila kuwa tafara shivering Cikin Command Wanda ke zaune akan One seater yace “go and fetch me the boss” 
Da sauri biyu a cikinsu suka nufi bangaren Alhaji Bala 
Alhaji Bala kuwa hancinsa a sake sai sharara munshari yake bai ma San abinda ke faruwa ba Wani wawan duka John ya sakarwa Alhaji Bala a cinya ‘ Alhaji Bala ya mike a firgice 
Hantar cikinsa ne ya kada a lokacin da yayi tozali da wayanda ke tsaye akansa kafin ya kai ga tunanin wani Abu 
John ya capko hannunsa yaja shi daga kan gadon 
Alhaji Bala ji yayi kamar da rodi John ya rikeshi ahaka suka hankada keyar Alhaji Bala sai gasu agaban Steven ogansu gabadaya 
Steven kuwa kalle kalle kawai yake yana pito sai wasa yake da bindigar hannunsa 
Alhaji Bala kuwa tuni yajike da gumi cikinsa na murda mishi dan wadannan sunfi karfinsa nesa ba kusa ba addu‘a kawai yake aransa Allah yasa iya kudi suka zo dauka 
Steven cikin kakausar murya yace “Mr man you know wetin bring us so no waste our time if u mess up i go scatter your head” 
Alhaji Bala jiki na rawa yace “okey sir if it is money u would have it but pls don‘t harm us” 
Wani Mahaukacin Dariya suka kwashe dashi gabadaya Steven yace “go bring money jare na only money we go chop and this girl we get tiny tiny breast” Steven yace yana kai hannu kirjin Naila dake rawar Dari 
Alhaji Bala cikin tashin hankali da kaduwa ya daka tsalle yaje ya tsaya agaban Steven gabansa na mugun fad’uwa ………. 
Hmm anzowajen 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]