[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
YAR SHUGABA
CHAPTER 33
‘Bayan Mako D’aya’
Aryan da Basma sun murmure sunyi kyau sun fara kumari, kwance suke bisa gado Aryan yace
“My Queen nan da Mako guda Insha Allah zamu je Makkah muyi Umara tare da Honey Moon, amma fa nayin Ibada, sannan Gobe Insha Allah zamuje Asibitoci domin in cika miki alkwarinki”
Kallonsa take cike da So da K’auna tace “Myn Godiya nake Allah ya k’ara maka Budi na Alkhairi yasa kafi haka” “Ameen My Pretty” sai ya rungumeta tare tayi mata sumba a goshinta. Daga nan kuma suka yi Addu’an barci, cikin minti goma Basma barci ya d’auketa. Shima ba dad’ewa barci ya kwashe shi. Saura kwana Uku su tafi Makkah, suka zagaye dangi tare da yi musu Sallama, har Kano sunje sun kwana d’aya, suka je Kaduna ma suka kwana washe gari suka dawo Abuja, a gidan Abba suka yini kowa na farin ciki da sauyawan su, sunyi kyau da k’iba gwanin sha’awa, sai dare suka koma Gida. Ranarda zasu tafl, harda su Momy suka yi musu rakiya, Basma har kuka tayi saboda kewar ‘Yan uwanta. A cikin Jirgi Aryan ya rungumeta ajikinsa yana lalla shinta har barci ya d’auketa.
‘MAKKAH’
Sun samu masauki a hotel d’in kusa da Harami, suka yi wanka a tare sannan suka ci Abinci, Basma ta shirya cikin jallabiya Brown mai ratsin fari a jiki babu kwalliya fuskarta amma tayi kyau, sannan ta shirya Aryan cikin doguwar jallabiya fara da farar hula, ta sanya masa turare, tana murmushi tace “My Aryan ina kishi ka fita domin gaskiya Mata karsu kallen min kai, dan ba k’aramin kyau kayi ba” Murmushi ya sakar mata yace “ai kema kinyi kyau sosai,ji yadda Jallabiyar ta amshi jikinki, nima gaskiya ina kishi dan haka Nik’af zaki sanya” Dariya ta sanya tace “Nik’af? bazan iya numfashi a ciki ba Allah kuwa, ban tab’a d’aurawa ba, Ni koda nayi Islamiyya bana sanyawa sai dai ina sanya Hijab har k’asa da safa, amma bana iya sanya Nik’af, kuma ai fuskata ba kwalliya” Dariya shima yayi yace “Ai fuskarki k0 ba kwalliya kyanki na nan, amma naji baza ki saka ba, sai dai zaki rik’a d’aure fuska kina bonewa” Dariya ta kyalkyale da shi ta fad’a jikinsa, rungumeta yayi kamar bazai sake ta ba sai da suka yi minti biyu a haka kana suka saki ajiyar zuciya a tare yace “kin ga tashi mu wuce masallaci” Ba musu ta mik’e suka wuce masallaci. Sun duk’ufa wajen yin Ibada da yiwa Allah Godiya bisa Ni’imomin da ya basu, sannan kuma
da Addu’an Allah ya k’ara musu zaman lafiya acikin zamansu ya barsu tare har a Aljanna, ya saka wa iyayensu da gidansu Aljanna. Sun rokawa dukka nin Al’umma Musulmi da kuma samuwar zaman laflya a K’asar mu Nigeria da dukkan Duniya gaba d’aya. Nima dai na taya su da “Ameen Ya Rabbi” ‘Bayan Mako Guda‘
Suka wuce ‘MADINAH‘ dan ziyaran Masallaci Monzon Allah S.A.W. Basma ta kira Hajiya Kaltum ta sanar mata da zuwansu, cikin farin ciki tace su tawo gidan ta. Anan suka samu masauki da kyakkyawan tarba. Bayan sun natsa, Basma ta kwashe labarinta tas ta bata Hajiya Kaltum, ba k‘aramin mamaki tayi ba da labarinta, tace
“Ashe Basma ke ‘YAR SHUGABA’ Ce, lallai rauyuwa kenan, da ace da farko na rik’e ki da wulakanci da baza ki Ni meni ba, Naji dad’i sosai kuma Nagode“ Nan dai suka cigaba da hira. A masallaci suke kwana danyin Ibada. Satin su biyu a Madinah suka shirya dawowa Makkah, Basma Check d’in kud’i ta rubutawa Hajiya Kaltum masu yawa wanda ni kaina ban san yawansu ba, ta bata ta ciresu a bank, dan cigaba da kasuwancin ta, Hajiya Kaltum tayi mata Godiya harda kuka, kaya ta had’a ma Basma na gyaran jiki, ta kuma had’a mata da guzirin wasu kayan. Cikin farin ciki da kewarjuna suka baro Madinah, shima Aryan ya yaba sosai da Mutuncin Hajiya Kaltum.
’MAKKAH’
Sati guda suka k’ara a Makkah suka shirya dawowa k’asarmu Nigeria, Watan su guda kenan a K’asa Mai Tsarki, Basma sunyi lbada sosai sunyi kuma Honey moon cikin Soyayya da K’aunar Juna. Haka suka tarkato zuwa K’asarmu Nigeria. ‘Nace “Allah yasa Basma ta kwaso guziri mai Albarka a Makkah”! Lol.
‘NIGERIA‘
Jirginsu k’arfe Biyar na yamma ya sauka, su Yaya Ahmad, Yaya Naufal, Meena, Deeja, Na’ima da Anwar sune suka je tarbansu. Gidan Abba suka wuce gaba d’aya da kayansu, gida ya hautsine da murnan dawowarsu, a falon Abba duk suka zaune, Abba ya sauko suka gaishe shi, yayi musu barka da dawowa. Nan hira ta b’arke a tsakaninnsu sai gab da Sallan Magrib kowa ya watse, su Basma suka
shiga d’aya daga cikin d’akin dake Falon Abba suka yi wanka suka sauya kaya. Bayan Sallan Isha‘i a part d’in Abba suka ci Abinci duka mutanan gidan, Yaya Ahmad yace “In kun kimtsa zan mai daku gida”
Yaya Aryan yace”Ai ni na kammala, dan na gaji ina buk’atarin kwanta da wuri”
Yaya Ahmad yace “Basma ke fa?”
Itama tace “Na gama” Yaya Aryan yace
“Kayan tsaraban nan a barsu anan washe bari zamu zo, kowa a bashi tsarabansa”.
Sun shiga Mota sai suka fita gate, Yaya Ahmad ya wuce dasu k’ofar wani Gida dake kusa da gidan Abba, Aryan yajuyo da sauri yace “ina zaka kaimu kuma? Don Allah ka kaimu gida mana, muna buk’atar mu huta, ka bari Gobe in Allah ya kaimu in munzo sai mu shiga nan d’in” Dariya Yaya Ahmad yayi yace “mai kake ci na baka na zub, Ni dai ku zuba min ido kurum” Basma da Aryan suka had’a ido sai basu ce komai ba. Hon yayi Mai Gadi ya bud’e wangameman Gate, shiga yayi tare d’ayin kwana ya d’anyi tafiya kad’an, Manyan flat guda Uku ne a cikin Gidan, k0 wanne da tazara a tsakanin su, da kuma k’ofar shiga. Parking yayi a flat na tsakiya ya fito, key ya ciro a aljuhunsa ya bud’e k’ofar da zai sa dasu da cikin gidan yace ‘ “Ku fito mu shiga mana” Ba musu suka shiga, tafiya suka yi kad’an ya sadasu da k’ofar babban falon,ya bud’e k’ofar da key kamshin turaren wuta mai dad’i ya daki hancinsu, Yaya Ahmad ya shiga suma suka bishi a baya, kujerun Falon su na wancen gidan suka yi arba dashi, cikin mamaki Yaya Aryan yace Ya naga kayanmu a nan kuma?” Yaya Ahmad ya zauna yana murmushi yace “nan kuka dawo, gaba d’aya kayanku dake wancen gidan mun dawo muku dashi nan, muma nan muka dawo, flat na farko na Naufal ne, na biyu naku ne, na uku kuma nawa ne, munk’i tarewa munce sai kun dawo kun fara shiga kafln mu dawo, Abba ya gida mana shi”
cikin farin ciki Basma ta mik’e ta shiga bin d’aku nan tana kallo, murna fal cikinta dan tsarin gidan yayi mata, katon falo ne sosai mai d’auke da d’akuna guda hud’u, ko wanne da toilet a ciki, an kuma sanya Furnitures a ciki, ga katon kitchen a falon da extra toilet. Daga cikin kitchen d’in akwai wani d’aki shine store d’insu, shak’e yake da kayan abinci da masarufl. A takaice gida ya tsaru yayi kyau sosai dan yaji kayan Alatu da more rayuwa. Yaya Aryan ya soma Godiya, Yaya Ahmad yace “Ka rik’e Godiyan ka, in ka had’u da Abba kayi masa” ya mik’e yana Dariya, Yaya Aryan yayi masa rakiya, suna gabda barin falon Yaya Ahmad ya juyo yace “Basma akwai swimming pool ta baya, akwai kuma Lanbu in kin za gaya ta bayan gidan, za kiga k’aramar k’ofa da zai sadaki da lanbun” Yana gama fad‘a baijira mai zata ce ba ya fita. ‘Washe Gari’ Sun had’u gaba d’aya a gidan Abba, suka yi masa Godiya da gidan da ya sauya musu tare dayi masa Addu’a sosai, sun raba tsaraba gaba d’aya, harda na Mutanan Kano da Kaduna
sun ware musu. A ranar su Yaya Ahmad da Yaya Naufal suma suka tare a Gida jensu.
‘Da dare’
Basma da Yaya Aryan suna zaune a falo, Basma tayi pillow da cinyansa yace mata “My Queen akwai wani shawara dana yanke, nasan kema zai miki dad’i in kika ji”
Basma ta tattaro natauwarta tace “lnajinka Myn” “Yauwa Babyna, dama so nake ki had’u dasu Meena ku bud’e wata organization na taimakon Al’umma, Nak’asassu, Almajirai, masu k’ara min k’arfl, marasa lafiya da dai tallafawa Talakan K’asarmu baki d‘aya, ta wannan hanyar ne za muyi amfani da dukiyar da Allah ya bamu domin mu nima Lahiranmu da shi, kinga Ni dasu Yaya Ahmad sai mu rik’a jagorantar ku akan abin, amma me kika gani?” Wani farin ciki ne ya rufe ta, sai ta mik’e ta zauna tare da sumbatarshi a kumatu ta gyara zama tace “Yaya Aryan ka sani farin ciki sosai Wallahi, na dad’e ina tunanin wani hanya zanbi dan taimakon Al’umma A matsayina na “YAR SHUGABA’ dan haka wannan shawaran naka yayi, Gobe Insha Allah zan tattauna dasu Meena”. ” Masha Allah da kika amshi shawara ta, yanzu ki bari kar kiyi magana dasu, zan shirya Meeting a tsakaninmu gaba d’aya, sai mu had’u a anan don mu tattauna, amma kan lokacin zanyi magana da Yaya Ahmad, kuma sunan organization d’in ‘_QUEEN BASMA (‘YAR SHUGABA) FOUNDAT|0N_‘. tsalle tayi ta fad’a jikinsa ta fara sumbatarshi ta ko ina, nan ta rikita shi gaba d’aya, d‘aukarta yayi tana wutsil-wutsil da k’afa tare da kyalkyata Dariya, suka shiga cikin bed room d’in su.
Ni ganin karna wuce gona da iri yasa nayi musu fatan Alkhairi, sai na nufi gidan Yaya Ahmad don naga wainar da suke toyawa._
Hmmm
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]