[Advertisements⬇️]

YAR SHUGABA CHAPTER 30 - Bankinhausanovels
Tue. May 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAR SHUGABA 
CHAPTER 30
Sun fara shirye-shiryen biki ba kama hannun yaro, Musamman Ummi ta kira wata ‘yar Uwarsu daga Maiduguri tazo gyara Basma, an tsumata da turaruka sosai da dilka, dasu kayan k’arin ni’ima, Basma ta k’ara kyau sosai duk in da ta gifta k‘amshi ke tashi, in ko ta zauna a wuri sai yayi damshi, an gyara mata sumanta ya k’ara bak’i, silb’i da shek’i yayi kyau sosai. 
Ammi da Hajiya Murja sune suka tafi Dubai had’o kayan lefen Basma. Akwati dozin guda sha biyu tank’ame da kaya, Ango ma anyi masa nashi akwati biyar cike da kaya. Yaya Aryan yana ta shirye-shirye, Yaya Ahmad shima ba baya ba tare suke aiwatar da komai. Dady yasa an gyara gidan da Basma zata zauna, komai sabo aka sanya a gidan. Sweeping pool d’in an sauya ruwan ciki, lanbun gidan an gyara shi sai k’amshi ke tashi. ‘Biki saura kwana uku’ Gida ya gama cika da dangi, taron Mutane yafi ko wani taron biki da akayi a baya, Mutanan Kano, Kaduna, Gombe, Maiduguri duk sun hallara a gidan shugaban k’asa, ko wanne ya samu masauki. Hajiya Kaka da Inna suka sanya Basma a gaba suna mata Nasiha, Basma sai kuka take yi, Kaka tace “Basma, Aryan Yaro ne mai hak’uri dole sai kin ajiye rashin kunya da tsiwan ki in ba haka ba zaki rik’a shiga hakk’insa” Nan dai su kaita mata, tashi tayi ta mik‘e cikin shagob’a tace 
“Ni kun tasani a gaba sai mita kuke min, ai shima ya kamata ku kira shi kuyi masa fad’an, ni kunga tafiya ta” Kaka tace 
“kingaja’ira k0, saina sanya shi ya tsafala min ke mara kunya kawai tafi ki bamu wuri” Inna tace “Hajiya bar Yaran yauzu, wataran nan zata zo wurin ki niman tai mako” Basma tace “Allah ya kyauta” ta fice abinta tana dariya. ‘Ana Gobe Biki’ 
K’ayataccen walima suka had’a Maza da Mata a wani k’aton ha’l, aka kira wani Babban Malami yazo ya bada fatawa akan zamantakewar Aure. Matan ‘bankin hausa novels sun hallara, haka ma matan “Yar Shugaba Fan’s“ sun hallara, Wuri ya cika ya batse da mutane kowa ka ganshi yana cikin farin ciki, Amarya ta sanya wani material mai kyau da tsada ta d’aura alkebba a sama, haka ma Ango yasha farin yadi mai kyau ya sanya alkebba a sama
 Wuri d’aya suka zauna, wurin yasha decoration, Anci ansha taro yayi dad‘i da armashi. Sai misalin Sallan Magrib taron ya watse kowa ya koma gida. 
Amarya suna hanyar dawowa, zaune suke seat d’in Baya, Yaya Aryan ya matsa kusa da ita ya leka cikin fuskarta, runtse ido tayi alaman jin kunya, cikin murya mai dad’i yace “Insha Allah gobe In Allah ya kaimu, uwar haka kin zama tawa ni kad’ai”Murmushi tayi ta bud’e ido sai ya sauka akan nashi, ido d’aya ya kashe mata, sai ta rufe fuska da hannayenta tana dariya, k’unshin da aka mata a hannu ya kurawa ido kamarzai leshe su, dan sunyi masa matuk’ar kyau, cikin kasalan jiki ya kai hannunsa kan zanan, ya shiga binsu a hankali, nan takejikin Basma yayi sanyi kasala ya diran mata, cikin sauri ta cire hannun a fuskanta ta duk’un-k’une su cikin alkebbanta, murmushi yayi mai sauti.Kansa ne yaji yam masa nauyi runtse ido yayi ya bud’e idonsa sunyi ja,janyejikinsa yayi gefe ya d’aura bayansa jikin kujera, runtse idonsa yayi yana ambaton Allah a zuciyarsa, a hankali ya fara samun natsuwa, tunani ya shiga yi 
“me yasa nakejin irin hakan kwana biyun nan?” basarwa yayi ya jawo wayansa ya nima wayar Yaya Ahamd suka fara magana akan hidimar biki. Basma ko ta mak’ure gefe d’aya, Allah-Allah take su isa gida ta fita a motan, gaba d’aya hankalinta a tashe yake, abinda Yaya Aryan ya mata duk ta susuce. “lallai akwai aiki a kaina, bazan k’ara shan wani Magani ba” Zancen zucin da take yi kenan. ‘Washe Gari”_Ranar D’aurin Aure_‘ Ya kama ranar Asabar Weekend, da misalin k’arfe (10am) na safe, Babban Masallacin Juma’an dake Abuja ya cika da Jama’a, Manyan Mutane ke wurin, hatta daga k’asashen waje Abokan President sunzo d’aura auren su Basma. Unguwar ya cika da motoci da Mutane, Ni kaina na kasa yanda zanyi na shiga Masallacin d’auko muku rahoto, Yaya Ahmad na hango dasu Yaya Naufal d’auke da sink’in goro suna k’ok’arin shiga ciki, da k’arfin na bud’e murya na kira Yaya Ahmad, da sauri ya juyo, mik’awa Yaya Jamal sink’in goron yayi suka shiga ciki, yazo guna da sassarfa yace  hala Mutane sun hana shiga d’auko abinda ke wakana a cikin Masallacin?” Murmushi nayi masa nace “kwarai kuwa, taron Mutanan ne suka min yawa kamar an sauko Sallan idi, yanzu dai bari nabi bayanka k0 zan samu hanyar shiga” Dariya yayi yace “Ai dole a baki hanya dan in bakya wurin nan d’aurin auren bazai yuwu ba, domin kece jagoran komai, dan haka biyoni a baya”. Haka nabi shi a baya, Mutane na darewa suna bani hanya sai gaisheni suke tamkar sun ga Sarauniya. lol Muna shiga waliyyan Ango da Amarya suka fara shiga, nan take aka d’aura auren ‘Aryan Aliyu da Basma Mukhtar Bukar‘ Bisa sadaki dubu d’ari lakadan ba ajalan ba, nan a kaita sanarwa aka soma raban goro da Sweet da dai duk abin da ya shafi Al’adan bahaushe. A can gida kuwa Yaya Ahamd ya kira Deeja ya shaida mata an d’aura, da sauri ta fita ta shaidawa Mutanan gidan nan fa Mata suka fara sakin gud’a. Amarya na k’urya d’akin Ammi su Meena na tare da ita, ta sha kwalliya tayi kyau har ta gaji, leshi ta sanya Marron da kwalliyan fari, anyi mata d’auri na Amare na head, sarkan gold da dan kunne ta sanya tare da abun hannu sai kyalli suke, k’amshi ke tashi ajikinta, duk inda tajuya sai an kalleta, black beauty yayi fa, nan take suka dinga d’aukarta photo suna turawa a WhatsApp groups groups harda su Instagram. Fitowa suka yi da ita ‘Yan Uwa suka mai mayeta sunata gud’a, masu d’aukarta photo nayi, Basma tunda taji an d’aura Auren wani sanyi ya ratsa zuciyarta, hawaye ne ya sauka kuncinta tana murmushi, Leema ce ta goge mata tace “Meye haka kuma karki b’ata kwalliyanki” Mana Murmushi tayi tace 
“ko na b’ata za’a sake min wata, ku barni nayi kukan farin ciki na samu cikar burkina” Juyawa suka ga tayi ta nufl cikin falo, haka suka rufa mata baya, d’aki ta koma ta cire head d’in ta d‘auko sallaya ta shifid’a ta kuma sanya hijab, dama tana da Alwala sai ta kabbarta Sallan Nafila na Walha, raka’a biyu tayi, ta jima a sujuda na k’arshe tana Addu’a, bayannan ta d’ago tayi lamuzi tare da sallama. Tajima a zaune tana yiwa Allah kirari, Addu’a kuwa tayi 
su da yawa. Bayan ta idar ta Shafa a’ddu‘an tare da goge hawayan da ya sauka kuncinta, farin ciki ya gama rufeta ta mik’e ta maida sallayan da hijab mazaunin su, wasu kayan ta sauya, mai kwalliya ta gyara mata fuska aka kuma d’aura mata wani head d’in, wannan karan shadda ta sanya doguwar riga tasha aiki har k’asa, tayi matuk’ar kyau, su Deeja sai kallonta suke cike da burgewa. B’angarden Ango kuwa suna can sunata hada-hada da Mutane,Yaya Shureym shima ba’a barshi a baya ba ya mance komai ya kama Matarsa Safeena, dashi aketa hidimar bikin, Ango yana tare da Abokai da ‘yan Uwa sunata hira. ‘_Da k’arfe takwas na dare_‘ 
Kowa ya gama shirin zuwa Dinner, Amarya ta sanya wani leshi mai matuk‘ar kyau da tsada, mai kalan pink da fari sai rashin bak’i ajiki, da kalmi da pos bak’i, head fari ta sanya, Ango yasha shadda fari anyi mata aiki da bak’in zare yayi kyau sosai, hula bak’ar dara da takalmi bak’i ya sanya. 
Ango yana bayan seat aka flto da Amarya aka sanya ta a kusa da Yaya Aryan, Yaya Ahmad shine ke mazaunin driver sai Deeja a gefensa, Walid ta barshi wurin Momy. Suka kama hanyarWajen Dinner. Tunda Basma ta shigo Motan, gaban Yaya Aryan ke bugawa ya nima natsuwansa ya rasa, 
kansa ne ya soma sarawa nan da nan idanunsa yayi ja, Basma kuwa farin ciki ya cika ta matsawa kusa da shi tayi ta kamo hannunsa, da sauri ya runtsa idonsa saboda azabar da kansa yake masa, Basma ta matsa da bakinta kusa da kunnensa tace “myn yau ba magana k0?” Murmushi yayi yajuyo ya kalleta suka had’a ido, a razane tace “Yaya Aryan meya samu idonka yayi ja haka?” Murmushi ya mata yace “Missing d’inki ne yasa haka” 
Kunya ne ya kama ta saita janyejikinta ta koma gefe, ajiyan zuciya ya saki a hankali, ambaton Allah ya shiga yi a hankali ya soma dawowa hayyacinsa, lamarin ya fara damunsa tsakanin jiya da yau, kuma hakan bai damunsa sai Basma na tare dashi. A ransa yace “Me yake shirin faruwa dani ne?” babu amsa, dole ya kauda tunanin a ransa. Sun isa wurin dinner. Wurin ya tsaru sosai, mutane sun hallara zuwan Amarya da Ango ya rage, haka suka fito ya sakala hannunsa cikin nata nan take ciwon kai ya dawo, d’aurewa yayi har suka isa mazaunin su kana ya zare hannunsa a nata. Taro ya kayatar kuma and an sha anyi hotuna, anyi rawa an zubda Naira. Matan ‘bankin hausa novels “ sai rarraba ido suke yi, haka ma matan ‘Yar Shugaba  Fan’s  suma sun cashe sosai. Haka aka gama taro kowa ya koma gida cike da farin ciki. Washe gari‘ Da misalin k’arfe Hudu na yamma gaba d’aya iyayen suka had’u a falon Abba, Basma na gefe kusa da Kaka Ma‘u, Aryan yana gefen Kaka Malam, nasiha sosai iyayen suka yi musu akan zamantakewar Aure, Basma kuka take yi mara sauti, shi kuma Aryan jikinsa ne yayi sanyi sosai, bayan sun gama Abba yace “Hajiya Fatima ina so da ganan ku wuce da Basma gidanta” Ammi tace “to Yallab’ai” Nan ta kama hannunsa Basma su Ummi na biye dasu suka wuce wurin motocin gidan, Momy dai part d’inta ta wuce ko waiwaye batayi ba, hawayen farin ciki ke Fita a idonta, saboda Basma ta auri wanda take so tasan tabbas zata samu natsuwa. Umma ma bata bisu ba tabi bayan Momy. Basma kuka take da kyar suka sanyata a mota kamar wannan ne aurenta na farko, gaba d’aya motocin gidan suka kwashe su aka wuce kai Basma gidanta. Suna kaiwa dama gate d‘in abud’e yake haka su kaita parking suna fitowa, falon suka shiga sun tadda su Deeja, Meena, Leema, Safeena, Munayah Matar Yaya Adam, sun kintsa komai na gidan, sun zauna suna jiran zuwan Amarya, Ammi ta wuce da ita d’akinta, ta ajeta kan gado, wani k’aramin kofi ta dank’a mata a hannu tace mata a kunne, “bayan sallan Magrib ki tabbatar kin sha wannan, Allah ya baku zaman lafiya” Basma ta k’ara fashewa da kuka tace “Ammi karki tafi dan Allah” Dariya tayi Tace”A’a Basma, aiko tafiya ya zama dole kuma ai wannan ba shine aurenki na farko ba balle kice baki saba ba, nan da kwana biyu zamu dawo” 
Sai tajanye jikinta daga na Basma ta wuce tana share hawaye, haka suka tafi suka bar su Deeja, sai dare insu Yaya Ahmad sun kawo Ango sannan zasu taf’l tare dasu. 
‘Wai Yaya Aryan yadai?’. Muje dai mu gani

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]