[Advertisements⬇️]

YAR SHUGABA CHAPTER 28 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAR SHUGABA 
CHAPTER 28
Mai Martaba yayi sallama, duk suka amsa, ya cigaba da cewa “Godiya ya tabba ga Allah ubangijin talik’ai, mai kowa mai komai, wanda ya halicci sammai da k’assa’, yayi mu maban banta jinsi, mungode wa Allah wanda yayomu a cikin Musulunci, wannan Al’amarin da ya faru babu abinda za muyi sai yiwa Allah Godiya, a yau Allah ya sada Alhaji Ibrahim da Iyayensa” Abba ya amsa da kwarai kuwa, Ummana yau ina so ki bada labarin yanda a kayi kuka tsinci Ibrahim keda Abbana lokacin ina k’asar waje karatu” Kaka Ma’u ta share kwallan daya zubo mata, nan ta shiga basu labarin faruwar lamarin tun daga farko har k’arshe, kukan su Meena ne ya k’aru a felon, Malam ya nisa yace “lokacin da Ameena ta aiki Khalil kasuwa, har yamma bai dawo ba” daganan ya cigaba da basu labarin yaruwansu gaba d’aya bayan ba Khalil, Umma ta d’aura itama da irin rayuwar da suka yi da Abban su Aryan, har zuwa had’uwar su da Basma da irin taimakon da tayi musu, har Auren su Deeja da Ahmad babu abinda ta rage hatta soyayyan Basma da Aryan ta bada labari, tana gama labarin ta cigaba da kuka. Falon ne yayi shuru na tsayin minti, Umma ta taso wa Basma da mikin rabuwa da Aryan, ta mik’e ta isa wurin Umma ta d’aura kanta bisa cinyarta, ta cigaba kuka mai kashe zuciya. Abba yace “Alhamdulillah, Basma kece silan komai, sanadin ki gashi dangi mun had’u, Allah ya muku Albarka gaba d’aya” duk suka amsa da “Amin”.Abba ya gabatar da duk Familynsa masu Malam Faffa, sai suka sanyawa zuri’a Albarka. nan dai suka cigaba da hira, yara suka fita zuwa farfajiyar gidan, suka baje kolinsu a acan, Aryan dai yana tare da Ahmad suna hira, su kuma su Yaya Naufal b’angaren hiransu daban dasu Yaya Shureym, matan kuma duk suna tare, harda Safeena yanzu ta zama ‘yar gida. ‘Da Yamma’ 
Mai Martaba da Abba, Dady da Malam duk suna hira gaba d’aya, Mai Martaba ya kalli Abba yace “Alhaji Muktar nifa naga iri ina so in za’a bani” Abba ya kalle shi cikin rashin fahimta yace “ban fahimce ka ba” Mai Martaba yayi murmushi yace”K’anuwar Ibrahim nake bara ko zaku bani aurenta” cike da farin ciki Dady ya kalli Abba yace ‘ “kasan me yake nufi kuwa? Aishatu Mahaifiyar su Aryan yake magana fa” Abba yace “Alhamdulillahi, abu yayi kyau, ai ga malam nan a kusa sai muyi magana” cikin kawaici na Manya Malam yace “wannan ai maganarku ne, Aishatu k’anwarku ce ku zaku yanke hukunci, ni nawa sai dai nasa Albarka” farin ciki ne ya rufe su dajin kalaman Malam, nan suka yanke hukunci hatta sadaki suka yanke, suka sanya rana mako mai zuwa in an sakko sallan Juma’a a masallaci, Abba yace Zuwa gobe in Allah ya kaimu, sai mu kirata mu tattauna da ita dan ta sani, nasan ba zata k’i amimcewa ba”. ‘Washe gari’ Haka duk suka had’u suka ci abincin safe, da yake su Umma sun kwana gidan president, bayan sun kammala, Abba ya kira Umma yana so suyi magana, ba musu Umma tabi yansa, suka zauna a falonsa na sama, Umma na k’asa gefen, Abba na zaune bisa kujera, Dady ne ya shigo shima ya zauna, ta kuma gaishesu,Abba ya nisa yace “wata magana ce zan sanar miki ban sani ba ko zai miki dad’i, mun yanke shawara ba tare da saninki ba, Mai Martaba yazo mana da wata magana akan yana son ya aureki” Da sauri Umma ta d’ago kai tare da dafe kirjinta tace “Ni kuma?” Dady yayi dariya yace “meye abin firgita, ke d’in fa, kuma mun amince har ya bada sadaki, mun yanke Juma’a mai zuwa zamu d’aura auren ku bayan an sakko Sallan Juma’a” sun kuyar da kai tayi cike da jimami dajin kunya tace “shikenan Allah ya tabbatar mana da Alkhairinsa” Abba da Dady suka had’a ido tare da sakar ma juna murmushi suka ce “Ameen” Abba yace 
tunda kin amince, mungode Allah ya miki Albarka, zaki iya tafiya“ mik’ewa tayi jiki a sanyaye ta musu godiya ta fito. Da misalin k’arfe biyu na rana, Dady suka shirya tafiya, yace lallai dasu Malam zai tafl, haka suka shirya hard’asu Umma dasu Aryan, duk suka tafi Kaduna, Deeja banda ita da Meena saboda suna jego, harda kuka lokacin da zasu tafi suka yi, Leema tabi Mijinta Yaya Jamal, Kaka Ma’u ma ta bisu don ta samu K’awa Inna, tace ba zata zauna Abuja ba. Mai martaba ma ya tafl da iyalinsa, domin yin shirye-shiryen bikinsu da Umma, Yaya Shureym ma ya tafi da Safeena Kano. ‘ Gidan kowa ya watse, sai su Ammi da Yaransu. Washe gari Abba ya wuce Germany domin halarta wani taro a k’asar. Basma ta koma part d’in Ammi, hankalin kowa yanzu a kwance yake, Yaya Ahmad ya cigaba da zuwa aikinsa,Yaya Naufal ma haka, Meena kuwa anata jego. 
‘Da dare’ Yaya Ahmad yana zaune da Basma suna cin abinci a plet d’aya, ya kalleta yace “Basma wannan irin santi ‘ haka, ashe Deejana ta iya girki sosai?” 
Murmushi tayi tace “wallahi Yaya Ahmad ta iya sosai, kuma kasan haka Umma ta iya girki fa, fried rice d’in nan yamin dad’i, yau zan cika cikina sosai” “ki dai ci a hankali kar kici ki kasa tashi da yin numfashi, kin san ance ana so a kasa ciki kashi uku ne, kashi na farko na abinci, kashi na biyu na ruwa, kashi na uku kuma na numfashi” murmushi tayi tace “hakane kuwa Yaya Ahmad, nima wasa nake maka dana ce haka” nan suka cigaba da cin abincin har suka kammala. Yaya Ahmad yace “Queen Basma” da sauri ta d’ago ta kalleshi tana murmushi tace “ya a kayi ne Yayana” yace “kawai naji kiran sunanki ne, ina so ki gayamin yaushe zaki koma gidan Shureym“ a razane ta mik’e tace “komawa gidan ya Shureym kuma?” yace 
“yes, mako guda aka baku, ku sasanta kanku, kuma week d’in ya kusa k’arewa, ina tunanin kun gama sasantawa ai” 
Hawaye ne ya sauka a kuncinta, ta koma ta zauna bakin gadonta tace “Yayana wallahi bana son zama dashi, amma in har abinda iyayenmu suke so kenan, zan koma in dai ransu zai yi musu dad’i” Yaya Ahmad ya nisa yace “zanyi wani abu akai” da sauri ta d’ago kai tana girgiza kai tace “a’a Yaya Ahmad kar kayi komai akai, haka Allah ya tsaramin rayuwata, kuma ni yanzu bana son Yaya Aryan ma” sai ta k’arasa maganar tana kuka. Murmushi yayi yace “me Aryan ya miki da harzaki daina Sonsa lokaci d’aya?” Cikin kuka ta bashi labarin abinda yayi mata, dariya Yaya Ahmad yayi sosai yace “Basma har yanzu ke Yarinya ce” b’ata fuska tayi tace “Dariya ma kake min k0?” ta k’arasa maganar cike da shagwab’a, toshe bakinsa yayi yace 
“nayi shuru, na daina dariyan yi hak’uri yar k‘anwata, kinga bari naje na kwanta dare yayi, da safe kisa masu aiki su kawo mana tire d’in abincin nan” “to Yaya Ahmad Allah ya bamu alkhairi” ya amsa da “Ameen” ya wuce. ‘RanarJuma’a” An d’aura auren Sarki Abdallah da Aisha (Umma) bisa sadaki dubu Hamsin, sun dawo gida, an yi walima da ciye-ciye, kowa ka ganshi yana cikin farin ciki, Hajiya Sa’a tak’i zuwa saboda bak’in kishi, Hajiya Murja kuwa da ita aka zo Abuja dan shagalin Biki, gidan Umma cike yake da ‘yan Uwansu na Gombe, ko da suka ji labarin ganin Dady sunyi murna sosai. ‘Washe gari‘ Yaya Ahmad ya samu Mai Martaba a side d’in da President ya ware masa, ya zauna ya gaishe yace”Baffa nazo wurin ka ne muyi wata magana” Mai Martaba ya gyara zama yace “ina jinka Ahmad” Yaya Ahmad ya risina kansa k’asa yace “Abba akan batun auren Basma da Shureym ne, a gaskiya Abba Basma bata son zama da Shureym saboda tana da wanda take so, tun farko Abba ya matsa mata akan sai ta auri Shureym, to ni ina niman Alfarma dan Allah Baffa kayi wani Abu a kai, domin itama ta samu farin ciki a rayuwarta kamar yanda kowa yake rayuwan farin ciki, nasan Basma ba zata tab’a cewa a raba auren nan ba, saboda yin biyayya a gareku, amma kuma Baffa wallahi tana cikin damuwa” ya k’arasa maganan cikin fuskan tausayi. Mai Martaba yajinjina lamarin yace “ai dama munce suje su sasanta kansu, gashi mako gudan ya cika, kaje karka damu zanyi wani abu akai“ Yaya Ahmad ya risina yayi masa godiya kana ya fita. A ranar aka wuce da Umma kano gidan Mai Martaba Sarki, gaba d’aya Matan gidan suka tafl Kano, Mazan ne kawai suka bari, Dady ya koma Kaduna, president ya cigaba da gudanar da ayyukan sa. 
Umma ta samu tarba sosai wajen dangin su Ammi, anyi taro an watse mutanan Kaduna sun koma, na Abuja ma haka, Aryan dole ya dawo Abuja, Abba ya bashi wani part da zai zauna saboda gidansu ba kowa a ciki sai masu gadi, Malam da Inna suna kaduna, Umma kuma ta koma Kano. Aryan baiso dawowa gidan ba, saboda yasan Basma tana nan. 
Hmm kome zai faru?
Muje dai zuwa

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]