[Advertisements⬇️]

YAR SHUGABA CHAPTER 24 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAR SHUGABA
CHAPTER 24
Bayan sun kaishi asibiti likita ya duba shi, ya tabbatar musu da damuwa ce ta haifar masa da suma “amma yanzu ya farfad’o, nayi masa alluran barci domin kwakwalwansa ya huta, zuwa anjima inya farka, komai zaiyi dai-dai insha Allah” 
Bayanin da likita yayiwa su Yaya Ahmad kenan sai ya wuce, zama suka yi suna ta zancen zuci, Yaya Ahmad, Yaya Naufal, da kuma Yaya Jamal sune suka kawo shi asibiti. A can gidan kuma sun k’ara shiga damuwa fiye da damuwar rashin Basma, Dadsy ya shiga tunanin ina yasan Aryan, lallai fuskansa tayi masa kama da wanda ya sani da dad’ewa, amma ya kasa tuna komai, matsantawan da yayi ma kansa da tunani ne ya haifar masa da ciwon kai, dole ya yakice abin a ransa dan gudun matsala. Awa biyu Yaya Aryan ya farka, sai dai bai iya furta koda kalma d’aya ba, idanun sa sun masa nauyi da kyaryake iya bud’esu a hankali ya rufe, hawaye mai zafi ya gangaro masa a kefen idonsa, Yaya Ahmad ya matsa kusa da gadon cikin sanyin murya da tausasa zuciya yace, 
“Aryan kayi hak’uri duk kan tsanani yana tare da sauk’i, dan Allah ka sanyawa zuciyanka salama, insha Allah komai zaiyi dai-dai, ka rik’a Addu’a a zuciyanka zaka samu sassauci, yawan damuwa baida amfani domin zai rik’a cutar da lafiyanka” 
A hankali ya bud’e idonsa, ya bud’e baki zai yi magana amma ya kasa, Yaya Ahmad ne ya dakatar dashi ya d’aga masa hannu yace “karka furta komai, ni dai kayi amfani da shawaran dana baka”. Haka suka cigaba da zama a Asibiti sai yamma lis likita ya sallame su. Suka wuce dashi gida tare da magungunansa, suka gaisheda Umma, kana suka yi musu sallama. 
Umma ta kawo masa abinci faten Irish da naman kaza a ciki, da kyaryaci kad’an kana ta zauna kusa dashi ta dafa kafad’ansa tace ”Aryan ya kake abu kamar ba tsatson musulmai ba, banji dad’in yanda kake nuna rashin tawakkalin da kake yi, koda nasan zuciya ba tada k’ashi, daman dalilin dawowarka kenan kazo kaga abin bak’in ciki, amma haka Allah ya rubuta, ni dai ina k’arajan kunnenka ka cire Basma a ranka, kayi tawakkali da lamarin Al|ah yanda yazo maka, Basma dai da auren wani akanta dan haka ka cireta a rayuwanka, in dai baso kake ka sanyawa kanka wani ciwon ba, a kullun ina maka Addu’a Allah ya baka mata tagari mai tsoron Allah” Aryan rungume Umma yayi ya soma kuka wiwi, yace Umma ina k’ok’arin cireta a rayuwata, abinda naji ne ya d’aga min hankali, yanda Shureym ya azabtar min da Basma, yayi mata mugun rik’o, Umma ba zan samu natsuwa ba har sai Basma ta dawo cikin koshin lafiya ta cigaba da rayuwan farin ciki kamar yaddah kowa yake yi, dan Allah ki yafemin Umma na, son Basma ajini na yake, cireta a zuciyata abu ne mai wahala, sai dai na miki alkawarin kiyayewa akan haka”. Umma ta kwantar da Kansa bisa cinyarta, ta shiga lallashinsa har saida yayi shuru yana ajiyar zuciya. 
Makkah’ 
Basma ta sauka lafiya ta kama d’aki a hotel dake kusa da harami, wanka tayi ta kwanta domin ta huta, tunanin rayuwarta takeyi, hakanan taji gabanta na fad’uwa, Aryan ne ya fad’o mata a rai, hoton fuskansa ke mata yawo a cikin kwayar idonta, hawaye ne ya soma zarya a idonta, bata hanasu zuba ba domin hakan ne zaisa taji sanyi a ranta. Takai kusan rabin awa a cikin wannan yanayin daga bisani ta mik’e tayi shirin fita ta wuce cikin masallaci. 
‘Nigeria’ 
An samu bayanai akan Basma ta shiga jirgin k’asar Etopia, sakamakon binciken da akayi a airport, haka Abba ya tura wasu domin dubata a can k’asar na Etopia, Abba ya sanya an sakaye Shureym a cikin wani d’aki dake cikin gidansa, za’a bashi abinci da komai na buk’ata, Fita ne kawai bazai yi ba dan har masu tsaronsa aka aje, har sai anga basma. Safeena duniya tayi mata k’unci, kuma gaba d’aya dangin su Shureym sunk’i amincewa da 
ita, dole yasa tayi d’amaran komawa gidansu Adamawa, da tsohon cikinta gunin tausayi. Dady da Abba sun shawo kan mai martaba da kyar, akan ya maida aurensa da Mami, ba dan yaso ba ya maidata d’akinta, duk sun koma gida, an cigaba da Addu’a Allah ya bayyana Basma. 
Masu bincike sunyi iya k’ok’arinsu wajen bincika Basma, amma babu nasara, k’arshe hak’ura suka yi suna dawo Nigeria, hankalin su Momy ya kuma tashi, lamarin ya k’ara dagule musu, Addu’a suke kawai da sadaka domin Allah ya bayyana ta. Bayan wata guda’ 
Safeena ta haihu ‘ya mace, babu abinda ta samu daga dangin mijinta, iyayenta su suka yi komai, koda ta kira Shureym ta sanar masa, yayi murna sosai sai dai ba halin zuwa, ya kira Maminsa ya gaya mata amma ba halin zuwa itama, saboda tana bisa hukuncin Mai Martaba. Ranarsuna Yarinya yaci sunan Kausar. Kowa ya cigaba da harkokinsa, sai dai damuwa yana k’arkashin zuciyansu na rashin sanin inda Basma take, Yaya Ahmad yayi iya k’ok’arinsa ganin an samu labarin gajinta amma abu yaci tura, Momy ciwo riris ya kamata duk tayi bak’i ta lalace, ta b’angaren Shureym kuwa ya zama tamkar zautacce, ba shida magana saina Basma, shi dai burinsa ta dawo ya nima gafaranta su cigaba da zaman aurensu. 
‘Makkah’ 
Basma ta murmure ta k’ara kyau, ta samu natsuwa sosai, sai dai zuciyarta yak‘i karaya da takoma gida, gani take har zuwa lokacin su Abba basu saduda ba, tausayin Momy take da kuma Yaya Ahmad, sai Yaya Aryan tasan tabbas sune wanda sukaf’l kowa damuwa akan rashin ta, kayanta ta had’a ta nuf‘l Madina, ta had’u da wata mata yar k’asar Nigeria tana aure anan madina da mijinta, Hajiya Kaltum itace ta bata masauki a gidanta, kullun a masallacin fiyayyen halitta s.a.w take yini, sai dare take komawa makwancinta, tana ibada sosai kuma zuciyarta ta samu kyakkywan natsuwa. Wani lokacin sai taji kamar ta dawo 
Nigeria, wani b’angare na zuciyarta ke gargad’inta akan ta k’ara hak’uri da sauran lokaci. 
‘Bayan wata guda’ 
‘K’asar Monaco’ 
Yaya Aryan ya koma ya cigaba da karatunsa, saura masa wata guda ya dawo gaba d’aya, hankalinsa yana Nigeria kullun cikin tambaya yake ko anga Basma, amsa dai d’aya ne ba’a ganta ba. Jidda ta matsawa Yaya Aryan amma duk da haka bata samu yanda take so ba, k’arshe tayi fushi ta daina kula shi. 
“Nigeria“ 
Khadija ta sillib’o d’anta Namiji kyakkyawa mai kama da Yaya Ahmad, gida ya cika da yan barka, wannan haihuwarsai ya rage musu rad’ad‘in rashin ganin Basma. 
Kwana biyu da haihuwar Khadija Leema itama ta haihu, sun samu d’iya Mace, nan hidima ya k’aru, Leema gaba d’aya aka d’aukota sai Abuja, Kaka Ma’u itace mai yi musu wanka itada da Deeja, farin ciki baya misaltuwa a wannan family, yanzu Meena ce tayi saura, had’a taron suna suka yi, suka k’ara kwana biyu na sunan Deeja aka had’a da Leema, yaron Yaya Ahmad yaci sunan Abba Mukhtar, suna kiransa da Walid, sai YarinyarYaya Jamal sunan Ummi taci Sadiya, suna kiranta da Walida, anyi taron suna an watse cikin farin ciki. 
‘Madina’ 
Basma tana madina tayi sabo sosai da Hajiya Kaltum, Hajiya Kaltum ‘yar maiduguri ce kasuwanci mijinta ya dawo dasu Madina, yaransu biyu Nana da Amir. Basma ta fara shirye shiryen komawa Makka, Hajiya Kaltum ta shiga gyara Basma sosai, dilka dasu gyaran jiki tayi mata, Basma ta k’ara kyau sosai, duk tunanin Hajiya kaltum Basma komawa Nigeria zata yi, shiyasa take gyarata saboda ta sanar mata tanada Aure. Ranar da zata tafi ta bata sauran had’in Magani, harda tsaraba, sannan suka amshi number juna, suka yi sallama cike da kewar juna. 
Basma ta koma jiddah, hankalinta ya koma gida, zullumi da fargaba ya cikata akan son sanin ya makomar aurenta yake, da haka tace bari ta k’ara kwana ki ta cike wata uku, kafin ta koma Nigeria. Bayan wata guda’ 
Meena ta haihu ‘ya Mace kyakkyawa mai kama da ita, farin ciki ba’a magana a gun su, yan barka sunata zuwa, su Leema da Deeja kuma anata wankan jego, gidan ya k’ara cika da mutane, Meena, Leema, Deeja suna zaune suna hira Meena tace “Allah sarki Queen Basma, wlh inna tuna life d’in da muka yi a baya har kuka nake saboda missing Basma da nayi, gashi yanzu duk mun haihu ita ko nata auren bata ji dad’insa ba, kuma duk taf’lmu kamun kai, amma Allah saiya jarabceta, ga gata da komai amma bai mata maganin matsalanta ba” Leema tace 
“bari kawai Besty, ai missing ma ba’a magana, naso ace duk wannan shagalin tana nan a kayi, wlh Yaya Shureym ba k‘aramin azzalumi bane, bana fatan Basma ta cigaba da zaman aure dashi” 
Deeja tace “gaskiya ne, amma ni kam ina ganin son Basma a idon Shureym fa, kawai yayi rashin hankali ne a kan lamari, kuma Basma tana da sauk’in kai, muzguna mata da yayi ne yasa tayi masa haka”  Leema tace “kunga dai Yaya Shureym d’an Uwana ne Ubanmu d’aya dashi, Amma wlh koda yana son Basma, ni sai na zugata karta koma gidansa, dan basu dace ba” nan dai suka cigaba da tattaunawa. Yaya Aryan ya sauka ajirgi direct ya wuce gida, ya samu Umma ta yi masa barka da zuwa, abinci yaci kana ya wuce ya watsa ruwa, k‘ananun kaya ya sanya, ya fito yace ma Umma ya tafl gidan Abba, zaije yaga yaron Deeja, Umma tace “a dawo lafiya, ka gaida mutanan gidan”. Yana isa ya wuce part d’in Abba suka gaisa, kana ya je part d’in Ammi nan ya samu Momy duk suka gaisa, sai ya wuce part d’in Deeja yaga Walid sun gaisa sosai na zumumci, Deeja sai murna take da ganin Yaya Aryan, nan ta rakashi part d’in Yaya Naufal yaga Baby, daga nan ya wuce part d’in Kaka Ma’u yaga Baby Walida yarinyar Leema. Suka gaisa saiya musu sallama ya wuce. 
Haka nan yau yaji nishad’in son zuwa wurin shak”atawa, yana tafiya a mota a hankali sanyin AC na ratsa shi, wak’ar sudan ya sanya, sautin na duka a hankali. A haka harya isa wurin. 
Basma ta sauka a jirgi da misalin k’arfe Biyar na yamma, iska mai sanyi yashiga ratsata, gaba d’aya zuciyarta ta cika da tunanin Yaya Aryan, burinta bai wuce tayi tozali dashi ba, taxi ta d’auka drop ta sanya kayanta a ciki, ta shiga ta zauna, lumshe ido tayi taji tana buk’atar zuwa wurin shak’atawa kafin ta isa gida, har sun d’auki haryan da zai sadata da gida, saita sanya mai motan ya sauya akalan motan, da ya fara kaita wurin shak’atawa. Suna kaiwa tace wa mai mota, dan Allah kad’an jirani ina zuwa” yace “to hajia sai kin fito” ta shiga cikin wurin a natse, har saida ta kai inda suka saba zama da Yaya Aryan ta samu guri ta zauna, runtse ido tayi ta shak’i iskan dake gurin, nan take taji k’amshin turaren da ba zata tab’a mantawa ba, waige-waige ta soma yi, amma babu 
alamansa. Ta b’angaren Aryan yana zaune ta bayan in da Basma ke zaune nesa da ita, ya d‘aga kansa sama ya rufe idonsa, da alama ya shiga yin tunani mai zurfl, Basma tashi tayi tana bin inda k’amshin turaren ke fitowa harta hango Aryan zaune agun, murza idonta tayi sosai ta bud’e ta kafa masa ido, ta tabbatar Yaya Aryan d’in ta ne, murmushi ta saki saita gyara tsayuwa, 
ta b’oye a bayan wata bishiya tana kallonsa, kamar ance ya farka daga dogon tunanin da yake ciki, haka ya farka yana waige‘waige, jikinsa ya bashi ana kallonsa, amma sai ya mik’e ya danyi taflya kad’an saiya dawo ya zauna, iska ke kad‘awa sosai a gun, iskan ya gauraye k’amshin turaren su ya bayar da wani k’amshi mai dad’i, lumshe ido Yaya Aryan yayi ya 
bud’e, Basma sai murmushi take yi zuciyarta ya wanke tas ba sauran damuwa. Yaya Aryan ya kurawa wurin bishiyar ido, yana nazarin tanan ne ake kallonsa, “to waye a gun” ya shiga tambayan kansa, mik’ewa yayi ya doshi bishiyar, Basma na ganin ya tunkaro wurin, saita juya da sauri ta b’oye a bayan wasu fulawawi, koda yazo gurin wayam ba kowa, mamaki ya kamashi yace a ransa 
“ko dai Basma kemin gizo kamar yanda ta saba min” murmushi yayi sai ya juya zai tafi, da sauri Basma ta fito daga mab’oyarta, Aryan yaji ance Yaya Aryan” 
A razane ya tsaya cak ya kasa koda motsi mai k’arfi balle ya iya juyawa, ya shiga tambayan kansa “mafarki nake ko gaske ne” domin yaji muryan da ba zan tab’a iya mantawa da ita ba ya daki kunnensa… 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]