[Advertisements⬇️]

YAR SHUGABA CHAPTER 16 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAR SHUGABA 
CHAPTER 16
Yana isa d’akin ya shiga bugawa, kwance take bisa gadonta tana kallon tv, koda taji bugun k’ofan, ta d’auki kusan minti uku kafin ta mik‘e ta nufi k’ofar ta bud’e,tsaye ta ganshi yana k’are mata kallo, miyau ya had’iye da k’arfi, gaba d’aya hankalinsa ya tashi da ganin Basma cikin k’ananun kaya, hararansa tayi cikin tsiwa tace “Malam lafiya ko da matsala ne” guntun murmushi yayi bai ce komai ba, sai yabi gefenta ya kutsa kai cikin d’akin, zama yayi kan kujeran zaman Mutum d’aya, ya shiga k’arewa d‘akin kallo yana shakar kamshin d’akin, wanda ya saukar masa da kasala had’e da tsananin sha’awar Basma, ita kuma tura k’ofan tayi ta koma cikin d’akin ta zauna gefen gadonta ta cigaba da kallon tv, sun kai minti biyar a haka ba tare da wani yace wani abu ba, Yaya Shureym ne ya katse shurun yace “Basma meyasa bakya futowa falo ki zauna?” Cikin nuna ko in kula tayi banza dashi, yace “magana nake kinyi banza dani” Cikin yatsina fuska tace “naga cewa wannan ba matsalan ka bane, kaje ka cigaba da zama da karuwanka, don ni ban yarda aure ku kai ba, kyamarka nake ma, da zaka taimaka ka tashi ka fita da ka kyauta min” “Iya b’acin rai ransa ya baci, mik’ewa yayi da sauri zai isa inda ta zauna, ai da sauri itama ta mik’e tanaja da baya harta isa jikin bango, kankame jikinta tayi ta runtse ido domin yanda taga ransa ya b’aci ta sadakar zai duketa, gabda ita ya tsaya wanda hartanajin hucinsa, hannunta ya shiga b’amb’arewa a jikinta, a razane ta bud’e ido tana kallonsa, ba tayi aune ba ya rungumeta da k’arfi ya matseta a jikinshi, tirjiya ta shiga yi tana k’ok’arin kwatar 
kanta, ganin ya rik’eta gam yak’i sakinta, saita gantsara masa cizo a damtsan hannusa, da sauri ya saketa yana yarfe hannu, saita maza ta matsa a gun, yanajiyowa ya nima k’ara kamota, da sauri ta ruga, guje-guje suka fara a cikin d’akin,yana k’ok’arin kamata tana kaucewa. ‘ Safeena shiganta d’aki da tayi, tana tsammanin Shureym zai biyo bayan ta, sai taji shuru, ganin haka yasa ta lek’a falo sai taga wayam baya gun data barshi, cike da masifa ta fito ta nufi d’akin Basma, tana bud’e k’ofa sai ta cimmusu suna wannan wasan guje-guje, ai sakin baki tayi tana kallonsu, shiga ciki tayi rai b’ace, Shureym yana ganinta yayi sauri ya tsaya yana sosa k’eya, mugun kallo Safeena tabi shi dashi bata ce masa uffan ba, sai nuna masa hanyar waje da tayi alaman ya fita, sum-sum ya fita yana murmushi k’asa-k’asa, yana fita ta gyara tsayuwa tana kallon Basma tace “A hir d’inki da Mijina domin ba sa’anki bane, in kuma ke mayya ce to Mijina yafin k’arfnki, ki shiga taitayinki domin wlh inna kuma ganin haka zan d’auki tsastsauran mataki mafi muni a gareki” tsaki Basma tayi tace cikin fad‘a 
“ai ko wlh da kinga yanda zanyi k’asa-k’asa dake, ke d’in banza ke wacece da zaki zo ki nima shiga tsakanina da Mijina kuma d’an Uwana, kefa ba kowa bace face karuwa mara lasisi mara mutunci, ki gaugauta fita sabgata domin had’uwata dake bazai yi kyauba, kibar ganin ina miki shuru-shuru,jaka kawai” Ai tuni Safeena ta cika ta b’atse, magananun Basma sun tunzurata, bata san lokacin da tayi kukan kura ba ta nufi Basma gadan-dagan, Basma na ganin tayo kanta sai ta shige bayi da 
gudu tare da sanya key, tana maida numfashi, iya tsoro ta tsorata da Safeena, dan ta girmeta kuma ta Fita girman jiki, tace a flli ko banza nasha dakyar muguwa kawai” Safeena tana ganin ta shige bayi sai tayi kwafa, ta fita da sauri. Ta tadda Shureym a d’akinsa, ta shiga surfa masa masifa shi dai uffan bai ce ba, da ya gaji da jin haya niyarta sai ya shige toilet danyin wanka ya barta tsaye baki na kumfa, a ransa yace “Safeena akwai masifa,ta dage ta hakikance akan abin da yake halal d’ina, gaskiya bazan d’auki wannan sakarcin ba, domin ko ban son Basma ai ina feeling d’inta, balle ma ina sonta kawai kauda kai nake ina miki biyayya, saboda ina tsananin sonki, amma nasan hukuncin da zan d”auka” 
Basma sai da ta tabbatarta fita a d’akin saita fito da sauri ta rufe k’ofarta, ta haye gado tana kwasar dariya, ko ba komai ranta ya mata dad’i tunda ta bak’anta ran Safeena, Jakarta ta jawo na kayan gurinta, lollypop ta d’auko, ta bud’e sweet ta sanya a baki tare da lumshe ido dan dad’in ya fara ratsa ta, nan take ta tuna da sunanta Queen Basma ‘yar rawa, tashi tayi ta kunna radio tare da sakin sauti, ta shiga cashewa son ranta tare da tuno rayuwanta na makaranta cike da nishad’i.Yaya Shureym ya flto zai fita jin wakar da Basma ta sanya yasa shi girgiza kai, a flli ya furta “Basma dangin k‘uruciya” sai ya fice, Safeena ma fitowa tayi cikin shirin fita tabi bayansa da sauri ta taddashi harya kunna mota zai wuce, da sauri ta cimmasa ta bud’e gaba kusa dashi ta zauna, tana mai kallonsa cike da shagwab’a tace “haba baby shine zaka tafi ka barni” murmushi yayi yace 
“ai naga fushi kike dani shiyasa nayi shirin flta inje in wataya kona sarara” kamo hannunsa tayi tace”sorry Baby, d’azu raina ne ya b’aci bazan sake ba” gyad’a kai kawai yayi alaman ya gamsu, sai suka fice daga gidan. Washe gari’ Shureym ya tashi da sassafe yayi shirin office, haka ma Safeena tayi shirin fita, nan suka had’u suka flce a gidan. Basma tana jin k’aran fltan motansu, saita bud’e k’ofa ta fito, d’akin Shureym ta shiga ta gama kallon komai, yanda akayi decoration d’akin yayi mata kyau, kalan fentin coffee brown da milk color, haka ma kalan furniture d’in, d’akinsa ba kitchen sai dai akwai toilet babba wanda yafl nasu Basma. 
D’akin Safeena ma yanayin d’akin Basma ne, sai dai itama ba Kitchen sai toilet kamar na Basma, kalan fentin d’akin ash da pink ne hakama furniture d’inta, fitowa tayi ta shiga cikin babban kitchen na falo, nan ma ya tsaru sosai, kuku guda biyu ta gani a ciki, cikin ladabi suka gaisheta tare da tambayarta abinda take buk‘ata, da murmushi tace bata buk’atar komai” shiga tayi store d’in ta shiga diban abinda ba tada shi ta kai kitchen d’akinta, kana ta flce farfajiyan gidan, baya ta nufa inda shukoki na furanni suke, ta shak’i iskan wurin sai taji dad’i a ranta, nan take ta tuno da wurin shak’atawan da suke zuwa ita da Yaya Aryan, idonta ya ciko da kwalla, zama tayi kan wani kujera na katako mai lilo, runtse idonta tayi ta shiga duniyan tunanin Aryan, ta kai kusan rabin awa agun kana ta bud’e ido, ta shiga rera kuka, istigfari tayi ta nima yafiyan Allah akan tunanin da tayi na Aryan Alhalin tanada auren wani akanta, tashi tayi ta nufi d’akinta ta fad’a bayi dan watsa 
ruwa, kojikinta zai mata dad’i. Yaya Shureym yana office amma ya kasa aiwatar da komai, gaba d’aya tunanin Basma ya cika masa kai, burinsa bai wuce ya samu Basma ba, agogan hannunsa ya duba yaga k’arfe 11am na safe, mik’ewa yayi da sauri ya d’auki wayansa,jakansa da key d’in mota ya wuce gida. Basma ta flto wanka d’aure da towel a k’irjinta, tana zaune gefen gado cike da damuwa a ranta, tunanin iyayenta da family d’inta takeyi, tunawa tayi da tun ranar da suka sauka ta kashe wayarta bata kuma waiwayan sa ba, murmushi ne ya sub’uce mata data tuna dasu Meena, tunanin ya sukaci amarci ne ya fad’o mata, tace a “guys nayi missing d’inku sosai, anjima zan bud’e waya muyi chart” Tana gama fad’an haka taje kusa da dressing mirror ta soma Shafa mai,jin motsin k’ofa tayi sai tajuya da sauri, dan shaf ta manta bata rufe ba d’azun, Yaya Shureym ne tsaye yana jefo mata mayen kallo, gabanta ne ya shiga fad’uwa sam bataji k’ugin motansa ba, takowa ya fara yi yana mata wani shu’umin murmushi, Jada baya ta shiga yi, k’ok’arin isa Waldrop d’inta tayi da nufin d’auko hijabi dan ta sanya, da sassarfa ya cimmata a gurin,jikinta ne ya soma b’ari, hannu ya kai saman k’irjinta inda ta d’aura towel d’in, ta rik’e gam ta shiga kuka tana cewa “meye haka Yaya Shureym dan Allan ka flta” 
Murmushi kawai yayi ya sanya k’arfinsa ya fisge towel d’in, da sauri ta tsugunna k’asa ta shiga kuka da k’arfl, d’aukarta yayi ya jefata kan gado, zanin gadon ta jawo ta rufejikinta dashi, cire kayansa ya shiga yi, vest da gajeran wandon kawai ya rage ajikinsa, sai ya hau kan gadon, Basma ganin haka ta kuma rushewa da kuka, bai hanashi fasa k’udirinsa ba, zanin gadon ya shiga yayewa amma Basma ta cukukuyejikinta da shi, wani wawan mari ya sakar mata, sai ta tsandara uban ihu, duk da haka baisa ta saki ba, cikin fushi yace wlh ko ki so ko kar kiso yau saina karb’i hakk’i na” Wani marin ya kuma sakar mata, duk da haka tak’i saki, da k’arfl ya finciko zanin gadon, sai ta k’ank’ame hannunta a k’irjinta, kuka take kamar ranta zai fita, magiya ta shiga yi masa cikin kuka 
“Yaya Shureym dan Allah ka kyaleni karka kasheni, me nayi maka ne da zaka yi min 
mugunta” Bige mata baki yayi, bakin ya fashe saijini, abinda yake son aiwatarwa bai fasa ba, Basma kuwa gunjin kuka take yi, a wannan lokacin tariga ta sadak‘ar, cizo ta ganna masa a kunne sai ya saketa ya kai mata naushi a baki, ya shiga dukanta ta k0 ina Basma wani wahalanlan ihu ta saki wanda yayi dai-dai da shugawar Safeena falon, dama ta shigo falon da mamaki, saboda ganin motan Shureym da tayi a gida, da sauri ta nufi inda takejin kukan, harta isa d’akin Basma, ta tsaya a bakin k’ofar, dai-dai lokacin Shureym yana k’ok’arin kai ga cika k’udurinsa Basma ta saki wani wawan k’ara, ai da k’arfl Safeena 
ta tura k’ofan ta buga garam, ta fad’a d’akin ta tuna huci…. 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

One thought on “YAR SHUGABA CHAPTER 16”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]