TAGWAYE CHAPTER 1

TAGWAYE 
CHAPTER 1
Gida ne kantameme mai daukan ido, kace ba’a ‘kasar nan tamu Nigeria aka ginataba. Kana shiga wani iska mai matukar gamsanNa zakaji ajikinka sabida yawan Flawowi dakuma ruwa wanda turawa suke ‘kira Swimming pool acikin gidan akwai dabbobi irinsu 
‘Dawisu, Karnuka da tsuntsaye gwanin ban sha’awa tamkarwurin shakatawa ta Gwamnati. 
nan. Mota ce baki wuluk ‘kirar Cross Tower ta gangaro kofar gidan tana Horn babu sassautawa sekace daga sama tafado. Mai gadi tun baigama uzurinda takaishi bayan gidaba yafiche aguje yana hada gumi sabida kuncewarda cikinsa yayi tunda safe yaketa zirga zirga cikin bayan gida. Sanin halin Madam din tasu yasa Malam Habu yafice aguje yadanna remote dake makale a saman gate din sannan tawangale. Kamar ko ya sani mai gidan ce MA’ISHA tashigo babu alaman sassauci tattare da tukinta 
Fitowa tayi “Hadeddiyar yarinya mai kimanin shekara ashirin” tana taku daya daya tamkar babu jini ajikinta, Bakar gilashin dake makale a idanuwarta ne tacire cikin bacin rai tave’Habubakar na tsallameka, kafara tattara kayanka tunda wuri sabida banson ka qara koda awa guda anan gidan ka fahimta’. Ma’isha tafada batareda juyowaba. Hajiya kimin afuwa, na’san nayi kuskure amma dalilinda yasa banfito nabude mikiba, Hajiya wallaahi tunda safe naketa gudawa cikina ba lafiya. 
Wannan kuma kai kajiyo sabida banice nadaura maka ciwon cikinba, And beside nasan tsiyan talaka daman ku bakwa rabuwa da ciwon ciki se kuyita fama domin ni Ma’isha Tilon Yar Alhaji Sambo Maidugu nafl Qarfin wulakanci wallahi. 
Tana fadan haka tajuya a fusace tayi cikin gida, Tana bude kofan Parlourn fuskarta ya chanza wanda ya bayyana murmushi mai kwantar da hankali; Baby Sorry nabarka kai kadai a gida kuma nasan kayita jirana koh? 
Wani dan saurayine ya amsa mata Babu komai beb kinfi karfin haka, ke ai agogoma dakanta wataran se’tajiraki. 
Fashewa da dariya Ma’isha tayi ‘Amma Faruq bakada dama wallahi haka kace koh. Ehh mana Ma’isha Ammafa kinajin dadinki Yar Alhaji Sambo Maidugu yanzu ke kadai kike rayuwa cikin Wannan kataparen gida? 
Ma’isha tana shiryamusu abinci a dining yayinda take amsa mishi; Uhmm ni kadai nake rayuwa anan kuma wallah rayuwata anan din tafimin rayuwa achan gidan so Dari. Domin ni bazan iya rayuwa da wannan Ya data kwacemin dukkan farin ciki a rayuwata ba na tsaneta. 
Faruq yamike cikin daurin kai yaje yakamata suka zauna akujera yana bata abinci a baki ‘Baby wallahi nima ina tayaki kishi, yanzu da’ace ke kadei ce Yar Alhaji Sambo Maidugu wallahi ina mai tabbacin cewa kina chan kasashen waje tareda Abbanki kuna kasuwanci amma yanzu wannan Twin sister’n naki mai farar kafa… 
Twin What? Ma’isha tamike cikin bacin rai ta tsinke shi da mari a fuska ‘Faruq tashi kabarmin gida bana ‘kaunarka kuma daga yau se yau karka sake kashigomin gida dasunan kazo muyi zance na tsaneka sabida duk mai hadanida MA’INA makiyi nane. 
Mikewa Faruq yayi wuf yarungumota yana hawaye ‘l’m Sorry love kiyi hakuri. 
Waye kuma wannan Ma’isha? Irin firgitar da Ma’isha tayi dakuma tsoron daya bayyana a idanuwarta yasa zakasan cewa wannan Dattijon dayayi magana mahaifinta ne Alhaji Sambo Maidugu. Dattijo ne mai farar fata. shi da Ma’isha de kamar an tsaga Kara kamaninsu take, Kamar yedda Ma’isha da Yar uwarta Ma’ina sukeda mugun kamanni wanda ko iyayensu basa banbantasu se wajen sutura da dabi’u sabida anan kam sunyi hanun Riga. Faruq koh bai tseya wata wataba dirkowa yayi ta window ya haye katanga yaceci ransa sabida kowa yasan halin Alhaji Sambo Maidugu yakan iya daure mutum akan Tagwayen nan nasa Ma’isha dakuma Ma’ina. ‘Abba kayi hakuri Saurayi nane sunansa Faruq’ Tafada cikin sanyin murya. 
Tsinketa da mari yayi zuciyarsa natafasa da bakin ciki dakuma danasanin barin Ma’isha dayayi tazauna a Irin wannan babban gidan ita kadai har natsahon shekara goma, domin tunda take karama shekaranta goma tadawo nan gidan tana rayuwa ita kadai se masu kula da ita dakuma masu aiki. 
“Ki tattara kayanki yanzun nan ba se anjuma ba kizo mutafi gida domin daga yau na yanke shawara zamanki a wannan gidan takare”. Alhaji Sambo yafada ransa a bace yakira layin securities dinsa awaya inda yagayyatosu gidan Ma’isha domin azo atattara kayan Ma’isha akai Alhaji Sambo’s residence dake unguwan Maitama Abuja. Ma’isha kuwa kuka take sosai, idanuwanta suna zuba tamkar ambaliya. Yana furta zancen barin gida hawayen suka tsaya chak Nan take tamanta da marinda yayi mata ta rude 
tamkar ankawo mata sakon mutuwa ‘Abba bazan iya rayuwa awanchan gidan ba kayimin afuwa’ tafada guiwowinta a kasa tana hawaye ‘Abba I’m sorry bazan iyaba. 
Ma’isha yau in mutuwa zakiyi sedei kimutu amma zakibar gidan nan kuma idan kasheki Ma’ina zatayi gwara kawai kifara salati domin ayau zaki koma gida daya da Y’ar uwarki Ma’ina sannan kisani kam inbar Nigeria tsena deideita tsakaninku, Sabida matsalar ma 
daga gareki take wanda tun kina ‘kankanuwa kika daura mata kiyayyarda ko a tarihi babu wanda yatabajin hakan…. ‘ Azuciya Ma’isha ke tunanin hanyarda zatabi abarwannan zancen nakomawa gidan Alhaji Sambo Maidugu domin abayyane yake kuma kowa yasan cewa bazata taba hada gida tareda Ma’ina ba, Abba ma dei tasuniyar gizo da kokinsa kawai yakeyi…. 
Beefpie, sausage, Fried brown rice, chicken sos, coconut juice, Almond, rice berries, fish pie, fresh fruit drink dakuma traditional Maiduguri Amala. ‘Finally mun kamalla girke girkenda muketa famanyi tunda safe Alhmdulillah 
 Ma’ina tafada cikin farin ciki 
yayinda tayi tsalle sukayi tapi da Stephine (ma’aikaciyar gidan) Madam munyi kokarifa yau idan Oga yadawo dole seya bamu Maki Dari bisa Dari a wannan girkin tamu. Washe hakori Ma’ina tayi “Sosai ma,aiko yau Daddy seya bamu maki 100+ kan wannan girkin. Wata mata ce fada kalar larabawa tashige kitchen din ta samesu ‘Ma’ina dear zoki shirya Abbanki zai iso nanda minti goma. ‘Momy minti goma kuma? shi da yace tun karfe sha biyu dedei zai sauka daga jirgi’ Ta amsa cikin shagwaba. Murmusawa umma tayi sannan takama hannun ta suka wuce Daki,Yayinda ma’aikatan gidan masu uniform suka tattara abincin Abba duk aka shiryamasa a babbar Parlourn sa dake Sama. 
Gida ne kantameme cikeda kayan zamani dakuma kayan more rayuwa iri daban daban, Inda Hajiya Safeenah Sambo tareda Yarta Ma’ina Sambo Maidugu kadei suke rayuwa aciki, Sunada ma,aikata bila adadin yawansu. Kuma duk shigarsu iri daya wanda kan nuna cewa ma’aikata ne nagidan Alhaji Sambo Maidugu. 
Kasancewar zaman kad’eicinda Ma’ina keyi yasa tasaba sosai da ma’aikatan, duk suka hadu suka zama abokan juna, Ako yaushe Burinta shine Suhada kai ita da Yar uwarta MA’ISHA suzauna gida daya kuma suyi rayuwa lrin yadda kowa keyin rayuwa da Yan uwansa a gida gwanin sha’awa. Sedei tanada tabaccin cewa hakan bazata taba faruwaba domin koda mafarki tayi,Asubahin farko zata tashi tayi Sadaqa… a 
Alhaji Sambo Maidugu dakuma Alhaji Saminu Maidugu Tagwaye ne wajen Malam Isma’il da Hajiya Fadimah… Sambo da Saminu sun taso su kad’ei Malam Isma’il ya mallaka domin aranarda sukazo 
duniya ranar mahaifiyarsu tabar Duniya. Sun tashi cikin talauci da yunwa ….. 

About Ismail

Check Also

TAGWAYE CHAPTER 35

TAGWAYE CHAPTER 35 Tukin awa guda ce takai Miemah gida, afusace taflto cikin gaggawa tanemi …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *