[Advertisements⬇️]

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 8 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

NAYI GUDUN GARA

CHAPTER 8

                     MONDAY
Ranar ta monday da farin-ciki ta tashi, ji take kamar an wanke mata zuciya, bata san me ya saba,ko dan adduoin da tai ta yine, kan Allah ya bata dangana,tabbas zata iya yarda da hakan, dan tun da suka samu sab’ani da Ramadan takejin ba dad’i a rayuwarta,tana jin koda mijin nata shine mai lefi, to sai ta kejin kamar awajen Allah tana cikin lefi,tun da mijinta na fushi da ita, shi,isa da suka shirya taji sauyi a ranta. Tana mamakin kanta sosai. Tun daya fita aiki sai ta tsiri gyare gyarenta, sanin cewa za tai bak’uwa sabuwar fuska, duk ta tanadar mata kayan tarba. Karfe goma-shabiyu Sallamar Salma ya karad’e falon. Ladifa da ke kitchen ta fito,murmushi ta sanya ta ce “bak’uwa mu kai?.” Salma tai murmushi, sanye take da bak’in lece mai yarfin fulawa green, ta yafa mayafi green,da bak’arjaka da takalmi,ta yi kyau sosai. Kallonta lad’ifa tace ga guri zauna..” Zama su kai suka gaisa. “Matar Abdallah ko?.” “Ni ce wallahi,” ta fad’a tana murmushi. “Shi ya kawo ni ya ma tafi.”
Masha Allah, “inai miki barka da zuwa,” nan tace mata tana zuwa, hanyar kitchen tai.
Salma tabi ta da kallo,tare da yaba  kirkinta azuciyarta. Da d’an faranti ta dawo, d’auke da lemo sai cincin da dambun nama, ta ajje mata, “gashi ‘yar uwa”Murmushi tai tare da yaba karamcin lad’ifar. Zama tai suka hau hira, kamar sun saba da juna. Lokacin sallahr azahar tai sukai sallah, suka ci lafiyayyen abinci, a lokacin an kawo wuta suka hau kallon wani film. Misalin  K’arfe Hudu ‘kawar ladifa mai suna Rahama tazo,suna kyalkyale dariya ita da Salma kan wani labari, taji sallamarta, rike baki tayi tace “wa zan gani kamar Rahma.” Rahma da ke shigowa falon, sanye cikin abaya bak’a, ta yane kanta da mayafin abayan, rik’e da jakarta. “Aini fushi nake da ke lad’ifa, kin manta da mu tunda kikai aure.” “Ni zance haka ko ke?.” Kallon mamaki Rahma kewa Lad’ifa, “lalle Lad‘ifa kinga wani irin kyau da kika k’ara! Kinyi fresh kin dad’aja abinki..” Dariya tai “har yanzu dai kina nan da surutun ki Rahma.” ” To me za a fasa,” ta fad’a tana mai maida kallonta kan salma,suka gaisa,nan ta zaro kati, ta ce to ga shi na bikina ne next week, saura kik’i zuwa.Tun da naga mijin naki kulle ya ke miki, babu bikin class mate namu da kika tab’a zuwa.” Dariya ta yi, amma naji dad‘i wallahi, insha Allahu zanzo.” Karma kizo waini ya naga fayau ne ba ciki haryanzu? Kodai har yanzu cin amarcin kuke ne.” Dariya salma tai da ita kanta Lad’ifarta ce.”Aa Allah ne bai kawo ba.” Mikewa ta yi tare da yi musu sallaama dan acewarta sauri take.Lad’ifa ta rakata ta tafl. Atare sukai girkin dare.Lafiyayyen girki sukai suka ajje. Suna gama girkin Lad’ifa taje ta feso wanka, ta sanya doguwar riga ta yadi yellow mai yarfln blue ajiki k’anana, d’inkin ya yi daidai da jikinta. ’ Fuskar nan daga powder sai man leb‘e sai kwalli da ta zizara a kyawawan idanuwanta, sai bulbula uban k’amshi take ta sauko k’asa, salma ta ce “kai ladifa wannan kyau haka, wallahi karki ga yanda kike min kyau, yanayin jikinki na birgeni, ga ki da kyau sosai. Irinku ne ko zakwi haihuwa nawa ba za a gane ba. Murmushi tai ta zauna kusa da ita,”kai salma kina kallon kanki kuwa, ke da kike da jikin kasaitattun mata, ke da jikinki ya ke komai masha Allah.Su mu kuwa hmm ba magana.” Hmmm! ladifa kenan, ba zaki gane bane, ki daina kushe kanki. Amma kinsan me? wallahi nan gaba kad’an zan k’ara k’iba, kuma muni zan, dan da can ina da kiba, daga baya ne na ragu sosai na dawo yanda kika ganni,, nina san da haka, yanzun ma dan baki ga yanda nake kaffa -kaffa ba, kar nasa jiki nai k’ibar, gashi Abdallahna bai san kib’a, wataran in yana
san tsokanata, yakan ce karna bari nai k’iba dan innai k’iba aure zai k’ara.”
Rik‘e baki ladifa tai aranta ta ce Allah d’aya gari banbam. Kowanne mutum da kalarsa, ita nata mijin na san mace mai k’iba, ga wani shi kuma ba ya san ta. “Salma ta ce amma kinsan wani abu ne? ke kam ba za ki yi muni ba in kikai kib’a.” Dariya kawai ta sanya. Dirin motar Ramadan ce ta dawo dasu daga hirarsu, tun daga can waje, sukejin hargiwar mazan nasu,suna hira har suka shigo falon. Abdallah ne daga farko ya shiga yana barkwanci. “Amarya ina kike?.” Lad’ifa saita d’auko gyalenta ta yafa, tana murmushi, zama sukai a kujerun, lad’ifa suka gaisa da Abdallah, ya nai musu ya gida, salma ta gaida Ramadan. Alokacin akai kiran sallah suka flta, su kai yo sallah, lokacin da suka dawo matan sunjera komai a dining,direct can suka zarce. Lad’ifa da ke sunkuye cikin mayafi ta yi serving d’in su, suka hau ci su na santi. Bayan gama cin abincinsu, Lad’ifa taja salma, suka shige d’akin k’asa suka ci gaba da hira. Suna barin wajen Abdallah, ya bawa Ramadan hannu suka cafe. Masha Allah! wannan yarinyar kamar balarabiya haka, ina ka samota ne?.” “Kai zan tambaya ina ka samo taka flower.Ramadan ya fad’a yana dariya. Sai wajen k’arfe tara suka bar gidan, Ramadan nai musu alkawarin kai musu lad‘ifa. Bayan fitarsu ya kalli Lad’ifa, matata ya gidan? yau na san ansha hira ko?.”
Kallonsa tai da murmushi, “wallahi kuwa munsha hira, har Rahma ma tazo d’azu ta kawon katin bikinta.” K’awarki ko?.” Ta ce El “Allah ya kaimu,ya fad’a yana k’ok’arin hawa sama. Murmushi ta yi zuciyarta fes! har abada ba ta son ta ga suna samun sab’ani da shi.Amma ta tabbata samun sab’ani dolene, domin ko harshe da hak’ori na sab‘awa. Dole sai ana kai zuciya ne sa. Ita Allah’n da ya halicceta, ba ta san taga wani na fushi ma da ita balle mijinta. Haka nan ta ke tun fil’azal. Kuma za tace tarbiyyar mahaifiyarta ce. Zama laflya ai yafi zama d’an sarki.Ta ayyana a ranta.
Ta shi tai ta karkashe duk kayan kallon ta hau sama, ta san ba sakkowa zai k’ara yi ba.
Tuesday at 1am A Yau baban laila ya kuma kiranta kan batun Aure, yana zaune tana durk’ushe a gefe. Yace”Wato na gaya miki ki fitarda miji kinki ko? To karna k’ara ganin kowanne k’ato yazo nan k’ofar gidan, kuma na baki zuwa gobe, ki sanarda duk wanda kike so yazo ina son ganinsa, inba haka ba wallahi da d’an lami zan had’aku, daman ai ya nace yana k‘aunarki.” Tasan babanta duk abinda ya fad’a zai aikata shi kuwa, magana d’aya ya ke kat! “Kayi hak‘uri baba, insha Allahu zanyi abinda kace.” “Ta shi ki ban waje, ya fad’a cike da fad’a~fad’a. Nan ta mik’ejiki a sanyaye. Tana shiga d’aki ta yada hijab gefe. Wayar Ramadan ta buga ba a d’auka ba, nan ta k’yale na wasu mintuna. Yana office ya ga miss call d’inta, duk da aikin da sukai mai yawa sai da ya tsaya ya buga mata.
“Ya dai lalilata abar sona.” “Murmushi ta yi. Allah ko ramadan, to ya aikin?.” Ya amsa da lafiya. “Akwai tambayar da kake yawan yi min, amma kwana 2 na ga tayi nisan kiwo‘ “Zolaya kikeji dai babyna, ba kisan cewa duk sanda na ji muryarki ba, sai na ji kamar na d’aukeki na maida ki ciki na ba.”
Lumshe ido tayi.Don abin da ta ke san ji kenan a yau. “Ki ce wani abu man habibty, yaushe zaki bani dama ne?.” Anzo wajen ta fa’da azuciyarta tana mai sakin wani gutun murmushi. “Da ace kana da lokaci, ai da ko yau zaka iya zuwa baba ya ganka, domin yana san ganin fitaccen jarumina.”
Babu wata magana mai dad’in saurara, da na tab’a ji a wajenki habibty sai wannan, gobe insha Allahu zan zo wajen abban na ki, don na k’agu na ganki a gidana.”Murmushi tai mai d’an sauti, bari na barka haka mijin laila, karna raunata ayyukanka.” Nan suka rabu, yana maijin kamar anyi mai albishir da gidan aljanna.
Tun wajen k’arfe uku na yanma kanta ke ciwo, ga wani irin murd’awa da mararta ke yi, tana kwance ta kasa koda d’aga k’afafuwanta. Sai runtse ido kawai take tana bud’ewa . Saboda azaba.
Ko yanzu ta san waya na da muhimmnci, da ta naimi Ramadan. A kansa ta d’ora lefin Runtse ido ta kuma, yi jin kanta na cigaba da ciwo. da k’yar ta samu taje ta d’auko panadol tasha, ba ta dad’e da shaba, bacci ya flgeta, cikin baccin taji wani irin murd’awar mara,kamar za ta shek’a barzahu, kuka ta fara tana bubbuga gefen cikinta, da k’yar ta sauko daga benen, lokacin har biyar da rabi. Lek’awa ta yi waje, ta ga mai gadi baya wajen, saita koma falon tana dawowa, durk’ushewa ta kuma yi tana numfarfashi,tunda take bata tab’ajin irin ciwon ba,jini taga yana bin k’afafuwanta, nan hankalinta ya kuma tashi. Jiri ne ta ji yana kwasarta, tun tana iya gane kalolin komai da ke falon, har ta suma. K’arfe shida Ramadan ya faka motarsa, a harabar gidan ya shiga, ya sabajin k’amshi ya dokeshi,yau da ya bud’e falon ya ji sab’anin hakan. Kiran sunanta ya ke,yaji shiru, hanyar sama ya yi, ya ganta zube ba numfashi. Ai da sauri ya k’arasa ya ga jini duk k’afarta, da sauri ya deb’o ruwa, agigice ya yayyafa mata ruwa, amma ko motsi ba tai ba,in hankalinsa ya yi dubu ya tashi, da sauri ya sureta, hankali tashe sukai asibiti. Sunje aka karb‘eta da gaggawa, aka fara duba ta.”
Ramadan ya kasa tsugun! baisan cewa haka ya damu da Lad’ifa ba sai yau, idonsa ya yi jajawur. Doctor ne ya flto, ya bishi a baya nan ya ke sanar mai ta yi miscarriage ne na cikin wata uku, mamaki k’arara ne suka wanzu a fuskar Ramdan. “Ciki kuma?.” “Ka yi mamaki ne? Doc d’in ya tambaye shi. “Sasai ma kuwa na yi mamaki, saboda da ni da ita babu wanda ya sani, ba ta irin laulayin masu ciki, sannan kuma tana period.” “Ba wani abu bane wannan, akan samu hakan daga wasu matan, ka ga suna period yayinda suka d’au ciki, yanzu dai duk mun mata abinda ya dace. Yanzu magunguna zan
rubuta maka a siyo mata.Mun mata Allura, zuwa gobe insha Allahu za mu sallameta.”
Ya ji bak’incikin zubewar cikin, tashi yayi ya tafl d’akin da ta ke kwance, duk ta d‘ashe ta rame, sai duk ta bashi tausayi, ashe! tana d’auke da gudan jiinsa. Hannunta ya rik’e yana kallonta. Nan ya bugawa hajiyarsa waya, ya gaya mata, itama cikin jimami ta ce zata zo,ya kuma buga gidansu ya sanar. Zuwa yamma duk sun zo sun duba ta, har salma da abdallah. Washegari aka sallameta. Suna zaune kan kujera. Sai sannu ya ke mata,tana mamakin ganin yanda ya ke nan, nan da ita, ko dan ba tada lafiyane? ta fad’a aranta. Zama ya yi a gefenta ya kamo hannuwanta yana matsawa.Sannu lad’ifa, ya kikejin jikin?.” Ta ce masa “Alhamdlh.”
Amma yakamata ace da kikaji ciwon tun farko ki sanar mini, da ace da wuri kika sanar, da nasan baki galabaita da yawa ba.” Da mamaki ta kalleshi. ‘Ko dai ya manta ba ta da waya ne.’ Ta fad’a azuci. “Hmm! ta ce,”zauji ka manta banda waya.” Tana fad’a sai yace.”Kai shaf! Na manta.” Wani kallo tai mai a kaikaice, wanda sai da yaji duk ya muzanta. “Zan siyo insha Allah.”
Ba ta ce mai ce komai ba, sai rufe ido da ta yi. Ita kanta tai mamakin ashe! ciki gareta, taji ba dad’i na zubewarsa, nan ta yi adduar Allah ya bata mafl Alheri.Kwana biyun da ta kasance ko girki hana ta yayi, sai dai ya sayo musu abinci daga waje, wannan rashin lafIyar ce ta sanya baije gidansu laila ba. D’an lokutan ta samu kulawa daga maigidan nata,kuma ta godewa Allah bisa hakan Sai da ta dawo garau, sannan ya maida hankalinsa kan wasu lamuran.
Bayan kwana biyu.
Ana yi gobe bikin Rahma, ta dinga tunanin ya ya za tai ta tambayeshi zuwa. Sai da ta bari ya dawo da daddare. Lokacin kwanciyarsu ya yi, sannan ta yi shirinta Cikin wanka ta yi d’akinsa. Yana zaune yana danna laptop ta shiga, ya kalleta bai ce komai ba, har ta samu wuri ta zauna daga can gefen katifar, kusa da laptop d’in nasa, shiru tai tana kallon yanayinsa.Ganin kamar da sassauci a yanayin nasa, ya sanya sai ta ce zauji gobe ne fa bikin Rahma. Ka ga yau akai lunch banje ba, gobe yini.” Kallonta yayi yace.” Ke da baki dad’e da farkowa daga rashin lafiya ba, wani irin biki haka? ya fad’a yana kallonta duk da ya san cewa Rahmar k’awarta ce sosai, dan ya san rawar da ta taka a bikin ita Lad’ifar. Wasa take da zoben hannunta. Ta ce ya dai ci ace naje.” Bai ce komai ba. ya ci gaba da danne dannensa. Harta k‘osa da zaman, sai ta zame ta kwanta daga gefe. “Babu damuwa gobe sai ki je.”
Daga sama ta ji maganar sai ta yi murmushi. Godiya nake.” Ta fad’a tare dajuyawa d’ayan b‘angaren. Ta dad’e tana tunanin rayuwa har bacci ya kwashe ta.
Washe gari Ranar saturday K’arfe uku daidai ta gama shirinta, cikin lace d’inta brown, mai manya -mayan fulawas
kalar copee da manyan stones, d’inkin riga da zani ne rigar cip cip da ita, da ya
ke lace d‘in nada kauri sosai, hakan ya sanya ya d’an cika Lad’ifar, sai ta yi kyau sosai, ta kafa d’aurin da ya flto da shape d‘in kyakkyawar fuskarwa sosai, tare da sanya sark’ar daya da ce da shigarta, haka mayafinta brown mai stone birjik ajiki, ya dace da shigarta sosai. K’arshe ta d’auko jaka da takalmi kalar copee ta sanya ta yi kyau iya kyau sosai.Saukowa k‘asa tai ta fita can, ta kira maigadi tace dan Allah ya taimaka ya nemo mata adaidaita sahu.
Ta koma, direct tai kitchen, irin kayanta wanda ba ta bud’e ba, ta d‘auko wani babban jug na tangaran mai saitin cups shida acikin kwalinsa, ta sanya a babbar leda wanda shine zata ba ta gudun mawa. Maigadi ya dawo ya sanar da ita ya samo, nan ta kulle ko’ina ta fita tai mai sallama.
Shi kan mamaki ke cika maigadi, aduk sa’ilin da zai ga ta fitarta unguwa, to sai dai taje titi, ta nemi adaidaita bacin ga mijinta da babbar mota amma ba ya kaita. Anya ko yana kishinta!.’ Ya fad’a cikin mamaki, domin in akai duba da kalar kyan da Allah ya zuba mata. Dole za kaji tsoron a taya ta ko a kalleta Jinjina kai maigadin ya kumayi
“Ai koni nan aradun Allah. Da ina da mota, ba zan bar matata ta fita titi unguwa ba, alhalin ina da mota, matata ma da take bata kai had’uwa da kyan wannan ba, irin matar alhaji nan ba a barinsu suna yin titi saboda tsaro, dan sai a iya tsaidata, ya fad’a yana mai komawa d’akinsa. ‘
Har k’ofar gidan bikin mai babur ya ajjeta ta sauka, ta shiga gidan aka nuna mata inda amaryar suke da k’awayenta. Tana shiga aka yi cahhh! ana kallonta, wanda suka santa na cewa. “Lad’ifa kin ganki kuwa.” Dariya kawai ta ke in aka ce hakan, domin ita dai ba ta ganin wani canji. Amarya ta ce” ai na yi fushi, sai yau.” “Hmm! kawai ke dai bari, banji dad’i bane kwana biyu.” Tai mata yaya jiki suka gaisa, aka kawo abin motsa baki na biki.
Wata k’awar amarya ce zaune daga can gefe da alama tana da aure. Suna hira da k‘awarta.Wanda tun kafin shigar Lad’ifa su ke zantawa. “Ai hajjo in gaya miki, wallahi a zamanin nan ha a ragawa namji, ai maza sai wuta, da kinyi sakosako sai a maida ki Shara.” Dariya suka sanya. Allah ko tawan, aiko wallahi ko ni bana ragi, idan ka gayan kule zance casl, shi’isa gamu nan,mu haura mu yi sama mu dawo k’asa. Kuma dole ace da mijin iya baba. Wallahi ni har sha yina ake, dan an san ni ba irin sakarkarun mata bane.Bana d’aukan rainin d’a namiji.
Wata daga can gefe ta sanya baki a hirar tasu, ai kunyi mini daidai, ni fa ina ganin bekyan matan da ke barin namiji na wulak’antasu, ai wallahi nai aure ba zan jure ba.Dan ina ganin irin wahalar da antyna ke sha, amma kamar wacce zuciyarta ta mutu, kullum cikin binsa
take, dan kuwa baki ganta ba duk ta kojale. “D’ayar ta ce yo ina dalili..” Amarya tace kudai kubi a sannu, yanzu hud’ubarku kuke so na d’auka?.” Wadda aka ce da hajjo ta ce. “Ahh Rahma bamu ce ba, hirarmu muke.Ba muce ki d’auka ba. Abinda kawai zamu gaya miki shine karki bari atauye hak’k’inki . Sannan kuma ta manya da ke cewa aita hak’uri. Amma k0 hak’urin ma kisan yanda za kiyi shi, kar kiyi na cutuwa, wataran in abu ya yi tsamari ma,jefar da hak’urin gefe. Ku raba gari.” Dariya suka sanya. Amarya ta tashi ta flta tana cewa: “ba da niba, da raba gari.”
Lad’ifa da kejinsu tai tsai! tana tunani.
Tabi Bayan mar Amarya. Hajjo Ta ci gaba da cewa, “ai wallahi kika nunawa namiji wai ke biyayya tsantsa, wallahi sai ya maidaki shara tama fiki daraja hmm.”
Da ya ke duk sunyi school da su saide ba wani harka suke sosai da Lad’ifa ba, saboda ko a classs d’insu, group d’insu hajjo basu da kunya sosai. Ta kallesu.
“Ni kuwa, sai nake ga, kamar bai dace ba, a matsayinka na wanda kake k’asan mutum, yaci da kai ya sha da kai, kuma ace ka zauna kana yimai abu kamar ba kasan waye shi a gareka ba, sai nake ga shi miji ai abin girmamawane, saboda tarin nisan dake tsakaninsa da matar sa wanda dole shine asamanta, Kuma sai nake ga, abinda hak’uri bai baka ba, ai rashinsa ma ba zai baka ba. Banga abin burga ba ga macen da za ta maida miji kamar wani abokin gabanta.ba” Cab! Lad’ifa! dama kina nan da sanyin nan naki?.” Dariya hansa’u ta sanya,ta ce irinsu Lad’ifa ne miji zai wanke su da mari su hau bashi.haquri” Dariya su ka fasa dukkansu. Hajjo tace “wallahi ka mareni,kan ka sauke na maida hannuna.”
Kan fuskarka”Ashha! to mai zai kaiki har kiyi abinda zai da keki, ai idan ka san halin mutum sai ka ci maganin zama da shi.”
Lalle ma Lad’ifar nan, irinku ne ‘yan dad’i miji k0? wallahi sai randa ya narko miki kishiya za ki gane namiji ba d‘an goyo bane, mazan yanzu ai ba a d’aura alkawari da su, ki nuna mai cewa kefa kwanyarki tas take! Kar kike kallonsa, sai ku zauna lafiya” “Ga ya mata dai.”
Lad’ifa ta ce, kishiya kuma, “ai lallamin miji ko akasinsa ba shi zai sanya ya kasa k’aro
amarya ba.” Wata da ta shigo ta ji hirar ta su “tace kai kai! dama har yanzu akwai irinsu wannan.” ta nuna Lad’ifa “Yo ni mijina nace yayi min abu, ya k’i  ai wallahi ya tasamma rashin zama lafiya.” lta dai shiru ta yi dan duk babu abinda taji ya burgetaa game da hirarsu. “Amma dai yakamata kafin ka fad’i komai ka duba girman Allah, domin shi ya ce mubi su, domin aljannarmu na tafin k’afarsu, sai idan miji ya yarda dake Allah zai yarda da ke,biyayyar miji ita za ta kaika ga duk hanyar zama lafiya, koda ace kana biyyayr kuma wahala kake sha awurinsa, to romon ladan biyayyar naga Allah, sai kaje lahira zaka riska, idan kuma aduniya kina ganin kin haye, idan kuma kaje lahira fa alokacin da Allah ke azabtar da ke kan rashin biyayya ga miji ki ce me? A yayinda za ki komai ki duba girman Allah. Komi za ki ki yi ma mijinki ki yi dan Allah, domin shi ya ce ki bi mijinki, Annabi muhd s.a.w. ya ce da za a umarci wani yayi wa wani sujjada, to da ance mace taiwa mijinta, saboda tsananin girman da yake da shi a gareta.
An san cewa dole miji yayi miki abinda ba za ki ji dad’i ba,balllantana auren yanzu da rabinsa hak’uri ne, to sai kice zaki hura, karki zak’e domin tafi ,,,,, zafl, ko fa kaurara murya ba a san mace tai wa mijinta, wanda muryarta harta d’ara tasa k’ara.Amma wallahi akwai matan da miji sai dai ya fita yabar musu gida saboda tsabar masifa da jaraba Wallahi abinda hak’uri bai baka ba, rashinsa ma ba zai baka ba. Idan yayi miki abu kika ga babu ta yanda za ai ya gane kurensa, sai ki barshi da Allah, to wallahi Allah sai ya saka miki, ko ba dad’e ko ba jima. Idan ka
ga fa baka ci ribar hak’uri ba to hak’urin bai yawa ba, rayuwar ma nawa ce.: Numfashi Hajjo taja ta ce: “Ke kam da alama ana tauye hak’k‘inki ladifa, wannna irin rai-rai haka, kamar wata alarammiya Duk abinda kika fad’a mun sani, kawai ba zamu d’au raini bane.” Dariya ladifa tai tace “dama fa ni bance ku d’auka ba, kawai ga ya muku nake, kamar yanda nima ba zan d’au na ku ba.” “Anyi 1-1 kenan.” Cewar hajjo tana gatsine fuska. Wata dattijuwa da tun fara maganar Lad’ifa ta shiga falon tana cin abinci, ta kalli lad’ifa tace “amma ko ke ‘yar nan Allah ya yi miki albarka, na dad‘e baji yarinya mai hangen nesa irinki ba azamanin nan, yarinya k’arama kamarki na da irin wannan tunanin. Ai mijinki ya yi dacen mace ta gari.lrinku ne ake dad’ewa ana kukan rashin ku. Kin burgeni wallahi, dan Ta kallesu, “to wallahi abinda ta fad‘a gaskiya ne.Mu alokacin mu ka isa miji na magana kana maidawa, ai shi’isa aure ya ke da kark’o awancen lokacin, amma yanzu saboda rashin sanin darajar aure daga mazan har matan shi’isa ba ya kark’o. To ba a d’au auren a ibada Ba
Ko ada akwai tantiran maza, amma indai kinsan ilmin zaman aure, ki ka rik’i hak’uri kuma, ki ka san yanda za ki zauna ai ba aji kanku ba.Ku dai Allah ya sa ku gane kunji,” Ta fad‘a tana kallonsu hajjo. Ta maida kallonta ga lad’ifa “Ke kuma ki ci gaba da yanda kike.Wallahi da ina da jika dana had’aku k‘awance, ta koyi irin halayenki.”
Tab’e baki hajjo tai tace ciki -ciki,ji tsohuwar nan, ai da, da yanzu ba d’aya bane da da kai yake cikin tukwane. Yanzu ko mun samu freedom.” Tana fad’a tana mai turo d’auri gaba. Haka dai aka gudanar da komai. Lad’ifa tai hotuna da amarya ta bata, gudunmawa, k’arfe shida ta tafl gida.
Ba a nan na so tsayawa ba,amma ganin typin din ya d’au tsawo,ga shi ana ta dakon labarin, ya sanya na dakata.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Aci gaba da bibiya akwai darasu dadama a a’ciki.Domin a akwai mata irin Lad’ifa sosai dake da matsalara zamantakewar aure,in kaji ta wasu ma ta Lad’ifa nafila ce acikin  nata 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]