[Advertisements⬇️]

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 6
Washegari kuwa, rana bata fad’i ba, face sai da Ramadan yaje ya sayowa laila lphone 7 golden, aranar kuma ya kai mata. 
Ayayin da tai arba da ita, ta jinjinawa Ramadan, ta kuma dad’ajin dole ma ya zam nata. Bayan an kuma wayar gari. Laila na Zaune tana duba wayar, sai doka murmushi take, nan ta tashi ta d’auko dayar da tai k’aryarta fad’i ta kunnata, wata lamba ta latsa daga can aka d’auka. “Kana ina ne?.” Ya shaida mata yana sabon gari. 
Samu tai bakinta na shaida mai cewar, ya zo akwai wayar da za ta ba bashi. Nan ya yi mata alk’awarin kan zuwa anjima zai zo. 
K’arfe Ukun rana, sai ga lukman nan yazo ya shiga gidan.Tana zaune a d’aki taji maganarsa su na gaisawa da hajiyarsa, tana tambayarsa mutanen gudansu. Fitowa ta yi yace “ai na d’auka ba kya nan?.” Ta ce “ina kuwa zani?.” “Ai na san k’afarki k’afar yawo ce, kullum ina da biki.” “Kaji dai da shi  ta fad’a. “Zo muje soro akwai abinda zan gaya maka, ya tashi ya fita ta bishi, suna tsayuwa ta ce “ka san dai farashin sabuwar iPhone 7 k0? to ga wannan sabuwace a kwalinta.” Ta mik’a mai ya shiga juya ta. Ke yanzu saida ita zakiyi?.” “Ina da wata ne.” “Ya ce hmm! dan ya san halin Laila ciki da bai. “Wato saurayine ya baki ko zaki sayarne?.” “Lukman bana son sa‘ido, kawai muyi magana.” “Ina jinki ya fad’a yana dariya.” “So ina so ka saida mini da ita, ka kawon min kud’i cas! A hannu.” “Ke ma dai kinsan ba a aikin banza yanzu ko? in ta sayu mai zan samu?!‘ Ya fad’a yana mai duba wayar. 
Ka san dai kai mutumina ne ko, mai kake cine na baka na zuba? Ka san dai ba yau muka saba ba.” Nan ta mik’a mai kwalin wayar ya karb’a. Dariya ya sanya “laila laila, wato dai kink’i saduda ko?.” Tsaki tai. “Kai sai ana abin arzik’i kana sa ko zancen wani saduda, maina sama yaci ballan tana na k‘asa, Na sanka lukman banda zamiya dan na san hali.” Dariya yayi yace “na tafi kice da hajiya na tafl.” Lukman d’an k’anin babanta ne, yana harkar waya a fam center, kasuwar sai da wayoyi, tare suka taso da laila, ya bata shekara d’aya, da a gidansu yake, shi,isa sabo ya shiga tsakaninsu sosai. 
Tana komawa cikin gidan, babanta na Fitowa daga d’aki. Tsugunnawa tai ta kalleshi, “baba sannu da gida,” dan jikinta in banda rawa babu abinda ya ke, batai tsammanin yana nan ba, domin Allah ya zuba mata tsoron mahaifin nata, ba kad’an ba yake mata kwarjini. “Me kike ne? har yanzu baki wuce islamiyya ba?.” Shiru tai ta kasa motsawa. “Ba magana nake miki ba,kikai fik’i-flk’i da idanuwa?.” Ya fad’a da tsawa. “Da..ma… Da…ma.” Ta shiga magana da in‘ina. Daga can falo hajiyarta ta ce “ai gwanda dai kai magana, dan tun bayan da suka sauka ta daina zuwa, wai duk ba kamarta sai yara.” “Dan shashanci da za tace hakan! so nawa ina ganin yaran gidan alhaji sa’ad, duk ba sa’anninta ba ne, kuma suna zuwa? Da wannan gararambar, ai yaci tana zuwa, to daga yau karna k’ara ganinki a gida ba tare da kinje iskamiyya ba. In dai ba aure ki kai ba..” “To Abba,” ta fad’a tare da mikewa. “Ke tsaya,” ya kalleta, tare da k’ura mata ido. “Ni wai me yarinyar nan take shafawa a fatarta ne saratu?.” Jin tambayar da malam d’in yayi yawa ya sanya hajiya fltowa. “Ai gwanda dai da ka gani da idonka dai, yarinyar nan wallahi sam ban isa in gaya mata ba, bleaching ta ke karka ga mayukan da take shafawa, na yi fad’an na zubar,amma duk a banza ba ta ji.” Cikinta ne ya d’uri ruwa. Ta ce “Hajiya.” 
“Yi min shiru, ko k’arya na fad’a?.” “Ta shi kije ki d’ebo min mayukan.” Ya fad’a da sauti me girma. “In banda lalacewa ta zamani saratu, har me zai sanya yarinya tana kod’ar da jikinta? bayan ga yanda Allah ya yita.” “To dai kaima malam ka fad‘a” Tsayuwa tai agaban mudubi tana kunkuni “ni wallahi.” “Ba za ki kawo ba?.” Ya fad’a da fad’a. Jiki na rawa ta d’iba ta je ta ajje, ya ce ta zuba a leda, nan ta zuba, ya ce “to daga yau, kar na k‘ara ganin kin canja halitta wajen yin bleaching. 
Kuma kiji da wai, zaman ki haka ya fara isata, tunda kin gama HND ya ci ace ki tsaida miji .” “Kaima dai Alhaji. Yo in banda zamani ma har yarinya budurwa ace ita za ta tsaida miji.? Ta fad’a da muryar takaici. 
“Kin san saratu zamani ayanda ya canja, yaran yanzu ba su kai biyayyar nada ba, kuma auren dole ba fa’ida bane, dole abi abu a sannu, ko ta fidda mijin ai saina tantance shi, ko kin manta yaron nan haladu da na ce yazo su gana da juna,ta bud’amai toka afuska.” “Na tuna,” ta fad’a tana jinjina kai. Ita ko laila na sunkuye sai kumbura take kamarta fasa ihu. Nan ya maida kallonsa ga laila da tai tsuru tsuru. ” ki tabbatar kin tsaida d’aya a samarin da ke zuwar miki, idan ba haka ba, wallahi sai dai kiji na d’aura aurenki. Shashashar banza da wofl, kuma ki gaggauta fita kije karatu.” Ya fita yana sababi. Zumbura baki tai tace “ni wallahi hajiya bana san zuwa makarantar nan, na fayi sauka da komai.” 
“Hmm! ido waka raina ko laila? shi ba ki mai ba saini ko? to karda Allah ya sa ki je, ki ga yanda zamu kwashe,” ta fad’a tare da mikewa ta bar wajen. 
D’aki laila ta shige tana k‘unk’uni, ” ni kam gaskiya anfara takuramin,” ta fad’a tana mai sanya hijab dan tafiya. 
Laila itace ‘ya ta biyar a gidan nasu, wanda suka kasance duk mata ne, itace auta, duk 
yayunta mata ne su 4 sunyi aure sai ita kad‘ai. Mahaifinta malam bala, malamin makarantar boko ne secondry, sai mahafiyarta saratu mace ce mai san addini, tana da ilmin addinin islama da yawa akanta. Tana sana’ar saida atamfofi wanda ita ke dad’a bawa maigidan na ta gudunmawa. Wanda laila itama take tab’a bussness d’in atamfar saboda ta samu mafaka. Duk yaran gidan babu wacce batai sauka na Qur‘ani ba da wasu littafan. Wanda mahaifan nata suke ida jajircewa da inganta samuwar ilmin nasu. 
Laila ta taso mai son kwalliya da san ta yi saurayi mai kudi. Tun bayan shigarta higher institution’s ta falle, musamman da samari ko ta’ina ke dannowa, saboda Allah ya sanya akwaita da farin-jini sosai, ba wani fitaccen kyau gareta ba, amma ba za ka sakata sahun jerin munana ba, tana da haske kad’an ba za a sakata acikin layin farare ba, kuma ba za ka sanya ta acikin bak’ak’e ba, sai dai ta fi kusa da bak’ak’en, tana da yalwar gashin gira, manyan ido da dogon hanci mai d’an fad’i da madaidaicin baki, tana da k’iba, amma ba can ba, acike take dai ko’ina, wanda k’ibar tata bai b’oye shape d’in ta ba da dirintaba. Tana da yawan fara’a, wanda hakan ke dad’a flddo da kyanta, da yawa yanayin skin nata 
kwalliyarta, zuwa yanayin zubin fuskarta da yangarta ke rud’arsu. Laila akwai iya d’aukan wanka, wanda class mate nata ke kiranta da komai daidai ko ‘yar kwalisa. 
Yanda ta ke shiga kuwa kamar d’iyarwani mai kud’in. Ganin yanda samari ke farauta akanta, saboda tana da structure mai fusgar maza, ya sanya duk inda ta shiga sai ta yi samari kuma masu kud’i. 
Ta kuma had’u da wayayyin mata masu irin hallinta, suka dad’a nuna mata yanda ake waftar kud’i awurin samari, wanda tun da ta fara har ma ta zarce . Duk saurayin da zai ce yana sonta, har idan ta san akwai dala, to saita karb’i tayinsa.Sai dai ita ba ta yarda namiji ya rab’ivjikinta. 
Ranar da ta fara gane cewar samarin fa ba wai dukkansu ne na gari ba, ta gane da dama dan jikinta su ke sonta, ba ta gano ba, sai ranar da ta had’u da wani mahfuz. 
Tana tsaye abakin titi, bayan sun gama luctures, sanye ta ke da wani yadija mai ratsin bak’i a jiki, ta d’ora bak’in mayafl, bak’arjaka, da red din takalmi fuskar nan tamkar alokacin tai kwalliya, ta matse iya matsewa, ko’ina
Tunda ya doso amotarsa idonsa na kanta. 
Parking ya samu yayi a daidai inda take , nan ya fito kallo daya tai mai ta d’auke kai, ‘ba laifi,’ ta fad’a aranta. “Yammata.” 
Ya fad’a yana mai tsare ta da ido, nan dai ya yi mata duk dabarar da saida ta hau motarsa dan ya sauke ta agida, bayan ya karb’i lambarta, nan ya sauketa a bayan layinsu. Nan sukai salama ta flta, tun daga ranarsuka fara soyayya, sakar mata kudi kawai ya ke. Sanin da taiwa mahfus, shi ya dad’a bud’e idonta da kud’i, da duk wani kalar wayewa. Ranarda ya fara kaita shopping kuwa, a ranar ya fito mata da maganar data soma hargitsata, ta d‘auka zai mata zancen Fitowa aurenta,ne sai ta ji yana mata zancen cewa, yaushe za ta bashi kanta,kuma babu wata kunya atattare da shi yayinda ya fad’a, bata gane 
mai yake cewa da farko ba, har sai da ya fahimtar da ita. Kicinkicin ta yi da fuska ta ce. Ba na irin harkar nan.” “Saboda me?” ya tambayeta. “Kawai ba halina bane, idan har da gaske ka ke sona ka ke, to ka aure ni mana, koma meye ayi acan.” Shiru ya yi, “to shikenan, dama gwadaki dai kawai nake, amma yaci ace ko d’an..” “Ko me?.” 
Ta kalleshi rai a b’ace. Ka ga malam, idan ka san akwai abinda ke ranka game da ni,just leave me a lone, kowa ya kama gabansa.” ‘Kin d’auka zan kashe miki kud’i abanza ne?.’ Ya fad’a a zuciyarsa yana mai shafa gemunsa. Ganin tana k’ok’arin ficewa ya sanya ya ce “sorry madam,” yana wani killer smile, nan ya ja motar, tun daga ranar tajanye masa, kuma ta canja salon duk yanda ta ke sakewa da samarin. 
Akwai wata rana da ake bikin k’awarta, shine duk ya yi jigilar kaita, ranar da ta kasance dinner shine ranar da ya so cimma burinsa a kanta, inda bayan gama dinner d‘in, ya d’auketa k’arfe goma dan kaita gida. Suna cikin tafiya ya tsaida motar, ya kalleta cikin ido. Itama ta kalleshi “ya dai mu tafi mana, ta fad’a da d’an tsoro afuskarta, da yake da duhu lokacin, ya sanya ba ta san lokacin da ya rarumeta ba, ya hau kissing nata sosai kota’ina, da k’yar ta k’waci kanta. Ta d’au wani abin ado agaban motar ta rafka mai, ta b’alle motar, ko tsikareren takalminta ba ta d’auka ba, Ta fita da gudu tana haki. 
Allah ya taimaka mata, kafln ya k’araso ta tari d’an adaidaita ya barwajen da ita, nan ya kaita gidan bikin, da ya ke bikin aminiyar ta ne ya sanya ta ke gidan Tun daga nan suka rabu. Ada tana nuna san kud’insu muraran, amma tun bayan wannan abin da ya faru tsakaninta da mahfus, ya sanya ta canja salo, dan ta kula da yawansu abinda ke kawo su wajenta kenan, babu wanda zai zo mata dan aure,masu santa da auren kad’an ne, ita kuma ba irinsu take da muradin aura ba. 
Ramadan na acikin ma su kud’in samarinta, shine kad’ai ya furta mata zai aureta, shi,isa ta ke tunanin ta samu mijin aure.
                Sunday 12:pm
 Ramadan na tafe acikin mota yana jin k’ira‘ar sudais. Yana Kan hanayarsa ta dawowa daga gidansu hajiyarsa. 
Sun tsaya ajuction yaji ana tab’a glass d’in motar, nan ya juyar da idonsa,wa zai gani idan ba abokinsa ba. “Kai! Kai! Abdallah.” ya fada da mamaki fal fuskarsa yana kallonsa, suka saki dariya, nan aka ba da hannu, sai suka samu bakin titi suka tsaya, da yake Abdallah a mashin yake, ya sanya ya kashe mashin d’in ya shiga gaban motar Ramadan suka chafke. “Amma gayen nan fa, kaji jiki, zumunci ka yanke.” Ramadan ya ce”kaji ka, yanzu ni za ace na yanke zumunci ko kai?.” “To dai duk mun yanke,” abdallah ya fad’a suka sa ke gaisawa. Ramadan ke tambayar sa iyali, ya ke gaya mai ai watansa d’aya da aure, tafawa su kai. Ramadan ya ce “ashe ka shigo layinmu.” Abdallah ya ce “kaifa, yaushe ka yi ne?wajen fa shekaru biyu bamu ga juna ba, tun bayan rasuwar inna..” 
“Wallahi ni ma dai baifi wata goma da aurena ba.” “Kai dan Allah. 
Allah ya sanya alheri, amma Ramdan ya kamata yanzu mu je gidana, kaga amaryata, ka ga next time, sai mu je na ka gidan, ni da madam. Shafa gemu ya yi, “anya, gida nake san komawa da wuri.” 
Abdallah ya ce “saifa ka je,” ya fad’a yana kallon Ramadan. “Amma fa kana damawa 
Ramadan, duk ka zama wani big alhaji.” Dariya ya yi yace “zolaya ko?.” Nan abdallah ya fita ya hau mashin, ya ce ya biyo shi a baya, hakan kuwa su kai. Ramadan da Abdallah abokai ne, tun na yarinta tare su kai kai makaranta har zuwa secondry, suka kuma d’ora da university atare, gamawarsu da shekara biyu ne mahaifiyar Abdallah ta rasu, inda adaidai lokacinne kuma akai wa babansu Abdallah canjin wurin aiki zuwa ibadan, da ya ke soja ne.” Tun daga nan zumuncinsu ya yanke, daga nan kuma kowa ya fuskanci tasa rayuwar. Adaidai madaidaicin k’ofar gidan Abdallah suka tsaya, Ramadan ya fito suka shiga gidan, wadda ya ke k‘aramar kofa ce za ka shiga gidan na daidai mai rufun asiri, tsakar gidan suka 
shiga in da k’ofar falo ke kallon ka. 
shiga su kai falon gidan gwanin sha’awa, duk da cewar komai bai kai na gidan Ramdan kyau da tsaruwa ba, amma shi ma komai daidai. Abdallah ya k’wala mata,kira tana d’aki adaidai lokacin tana shiryawa, wanda ba ta dad’e da fitowa daga wanka ba. “Naaam,ta fad’a tana saurin d’aura d’an kwali. Gadar, gadar,ta fito da d’an sauri tazo ta rungume Abdallah, tana cewa “wlcm nawan.” 
Ya ce “ya gidan Amaryata?.” Ta amsa “k’alau,” tana sakar mai fari. Sam! Tama manta ya ce mata da bak’o yake. 
Sai da ya yi mata rad’a a kunne “da bak’o fa nake tafe, ki ka fito haka k‘yandau-k’yandau, kije ki d’auko hijab .” Kunya ce ta d’an kamata ta d‘ago, sai a lokacin ta kula da Ramadan dake zaune yana murmushi, ganin sun manta ma dashi. Murmushi ta yi ta gaida Ramadan ya saci kallonta.Wani rawa zuciyarsa tayi ganin zunzurutun kyanda ya gano atattare da ita, a kallo d’ayan da ya samu ya yi mata, nan ta juya, ya bita da kallo a fakaice. Macace ce doguwa ba can ba, irin matan nan ne da ake kira da masu k’irar kalangu, tana da faffad’an k’ugu mai girma sosai, da tudun baya shi ma irin sosai d’in nan, ga cikar k’irji tubarkallah, fuskarta round face ce mai d’an cika, da dogon hanci. K’alubale gareku matan dake fitowa sakayau gurin abokan miji babu mayafi k0 hijab, wai hakan wayewa k0? wannan ba wayewa bace sai yad’a fasadi, Dan wani namijin baya raina abin kallo. Adai dinga kula Chafewa su kai bayan shigewarta, Ramadan yace ” aboki ashe! flower ce agida nan naka, amma ka iya zab’e fa.” Dariya Abdallah yayi yace “kaji shegen sama da sa ido.” Dariya suka sanya su biyun. Adaidai lokacin ta fito sanye da hijab, nan ta kawo musu abubuwan motsa baki, wanda sai da Ramadan yaci ya sha agidan, sannan ya tafi inda Abdallah ke sanar mai zasu zo shi da madam d’insa. 
Yana tafe a hanya, sai tunanin yanda yaga matar Abdallah ya ke, nan zuciyarsa ya ji yana dad’a burin mallakar laila saboda aganinsa ga Abdallah nan da bai kai shi komai najin dad‘in rayuwa ba, ya mallaki matar gaban mota. Tabbas! Laila ce ta dace da gidansa. Yana jin ita ce macen da zai bugi k’irji ya ce yana da mace agida. Hello guys gamu nan fa,ya kuka ga chapter d ‘in nan?  mai me zaku ce da Ramadan ne wai? Haka mai zakuce da laila.?
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]