[Advertisements⬇️]

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 15 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

NAYI GUDUN FARA

CHAPTER 15

A hankali take saukowa kasan, sanye take cikin atampha, sakar kasar england, me yarfin purple and black, dinkin riga da siket ne wanda akai mara shi daidai jikinta, dinkin ya kwanta luf ajikinta, ta kafa daurinta, wanda rabin gashin kanta duk awaje yake, fuskarta babu wata kwalliya sai gazal da man Iebe sai powder, wanda hakan ya fidda sihirtaccen kyawunta, dan ita bata fiya san cika kwalliya a fuska ba.Kafafuwanta sanye suke da flat shoe purple.
Tsit! falon, daman tasan hakan za ta iya kasancewa, abinka da namiji me amarya, ba lalle ta ga fitowar su yanzu ba, shi,isa itama bata damu da saita fito da wuri ba, yanzun ma yunwa ce ta sauko da ita.kitchen ta zarce ta dora musu abin kari, bata tsawwala wajen yin abu me wahala ba, sai tai madaidaici wanda zasu iya ci, ta ajje musu a dining,ta kai na maigadi kofar falo ta ajje, ta koma, dan ita bata san cewa ma amaryar bata gidan ba,nan ta dau nata tai hayewarta sama.
Cikin fargaba da kunci hade da tarrarrabi, hade da adduar Allah ya sanya mahaifiyarsa ta
ce ya maida ta, ta shiga gidan.babu kowa sai tayi sallamata taji shiru. Can sai ga wata mata nan ta fito da hijab ahannu dajaka, saboda nikab din dake fuskar laila ya sanya bata gane ta ba. nan tai mata sannu da zuwa, tace ta shiga ciki hajiyan za tazo. lta kuma ta fice.
Kutsa kai tayi cikin falon jikinta na rawa. Malale falon yake da cafet, ta zauna a gefe, bata dade ba saiga hajiyar Ramadan ta fito daga toilet na falon, Zama tai tace. “bakuwa wallahi kinga ina bandaki sannu da zuwa.” Yaye nikab din tayi,ta sunkwi da kai ido na neman kawo ruwa. Zare ido hajiyar tayi “Wa nake gani kamar amarya? kodai ba ita bace?.” “Nice.” Ta fada da kuka.
Hankalin hajiyar ya tashi “wani a bunne ya faru ‘yar nan? Ko ramadan din ne wani abun ya
same shi?.” Ta fada cikin fargaba. “Hajiya sakina ya yi, bansan hawa ba, ban san sauka ba. Daga wani kuskure ya hadamu.” Tafa hannuwa ta shiga yi. “Shi ramadan din Ta fada da mamaki. Nan ta shiga tafa hannuwa tana fadin innalillahi wainnna ilai rajuun, “anya! yaron anna na da hankali kuwa! Amma naga ma hankalinki, da kikai yo nan, yau da kinje gidanku, ina
muka ji da kunya, gaskiya yaron nan ya bani mamaki. “Ki gayan me ya faru?.”
Share hawaye tai “hajiya nima bansani ba, kawai daga ganin abinda bai gane ba, sai kawai ya sakeni.Ni kuma ina tsoron zuwa gida, sabida mahaifina,dan zai iya ballani,musamman idan ya gaya mai wani abun wanda ni ban sani ba, ga kuma sauran ‘yan bikin da ba su tafi ba.” “Kinyi hankali da kika yo nan, ai dana kowa ne, wallahi zai zo ya samenijrin wannan
danyen aikin ba anan ba, so yake asanyamu a bakin duniya ana cewa yasaki yarinya kwana daya.To wallahi sai ya komar dake ayau din nan.” Waya hajiyarta dauka ta kirawoshi, yana kwance kan gadonsa yana tunani, yaji wayarsa
na kara, nan ya d’auka, sunan hajiya ya gani sam! bai kawo nan taje ba. “Kazo yanzu ina son ganinka karka kuma bata lokaci,” ta kashe. Ya dade azaune, san nan ya mike ya shiga bathroom ya yi wanka, ya shirya ya fita falo, sai alokacin yaga breakfast din da ladifa tai, ko shaawarci bai ji ba.” Haryaje gidan hajiya na sababi, yana shiga idonsa ya sauka akan na Iaila. Wani takaici ya ji
ya kuma kamashi ‘wato wajen hajiyarsa ta kai shi.’ Nan hajiyarta umarci Iaila data shige dakinta can tai breakfast. Yana zama ta rufe shi da fada ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. “wallahi tallahi kaki yayeni Ramadan bansan hankalinka ragagge bane sai yau. To kaji da wai sai ka maida da ita, tunda saki daya ne, yanzu -yanzu kuma.” shiru yayi kana yace hajiya “dan Allah kiyi hakuri amma ni …””Dakata,” ta tsayar da shi dan bata bukatar abinda zai ce. “koma mai tayi maka, to yaci ace kafin ka yanke hukunci kayi tunani. hakuri akomai yana da riba, rimirimi kazo ka damu, dana hana, har da turo min Antynka, dan na yarda, amma yanzu kazo kai rashin hankali, kai zaka so a ce anyiwa kanwarka haka? Wanda ya sai rariya ai ya san za ta zubda ruwa, kuma tauntsun da ya ja ruwa ai shi ruwa kan doka.” Shiru ya yi ya shafa sumarsa.
“Dole ka zauna da yarinyar nan duk yanda take,duk da bansan abinda ya faru ba, kuma ba na fatanji, ba irin yanda ban maka ba, kan ka hakura da auren nan, sai nan gaba kayi, amma ka nace, ai duk wanda baiji maganar manyansa ba, to yana tare da danasani, to wallahi yanzu ni zan murza kambu na, atoh! kuma wallahi makamancin hakan naji ya sake faruwa, zaka gamu da mummunan bacin raina. Duk abinda kaga ya rikita maka lissafi kazo ka sanar dani, idan sulhu ne sai ayi, idan kuma mataki ne ad’auka, amma sam! ban yarda da dabi’ar saki ba.” “Shi ke nan, na maida ita,” ya fada tare da mikewa. “Tsaya ka jirata, ka jira ta gama breakfast saiku tafi nan ya zauna fuska atamke ya sha alwashin, wallahi sai ya nunawa lalla kurenta, sai ya sanya tai danasanin sanya acuci maza. Dan duk wahalar data ba shi. Sai ya fanshe.Haka hajiyarta kuma hadasu tai musu nasiha sosai, musamman lailan. Sai wajen sha daya da rabi suka fita, yana gaba tana gefe, fuskarsa atamke, kamar kurame haka suka zauna, dan shafa fuskarta tayi ta kalleshi tace “Am so sorry ramadan wallahi ba yaudararka nayi ba. Wallahi gani ganin da kawaye na kemin ne. sanya na tsiri sanya wa.”
Wani banzan kallo ya watsa mata. “Na tambayeki ne? Me ya sanya baki tafi gudanku ba? shine za ki je gidanmu. dan tsabar rashin zuciya.”
Shiru tai tana tunani a ranta dole ta lallabashi a yanzu, kafin komai ya daidaita, a lokacin za ta nuna mai bata daukar rashin mutuncin da namji. Dan bata san cewa Ramadan
kwallo ba ne sai tsakanin jiya iyau. “Kuma ki bude kunne ki saurareni, karki bari na sake ido biyu da kayan cikonki, if not
wallahi sai na baki mamaki.”
Ta gefe ta harareshi sai kuma ta saki kukan munafurci. “Ai tun ajiya na san cewa ramadan baka da kirki, dan nasan cewa baka sona, jikina kake so, kome ma zaka iya yi mini, amma wallahi ba zan yarda da cin kashi ba. Ta fada tare daci gaba da kuka.
Kallonta yayi bai ce komai ba, don zai iya tsayawa ya narketa a titin nan, domin iya wuya ta kaishi, ya kula bata da kunya. baisan cewa haka take ba sai ijiya da yau. Kwafa yayi yana ayyana irin gurzarta da zai yi, domin sai taji duk wani haushi da radadi data sanya shi yayi. Haka zalika yayi maganin me tsinin baki. Har suka karasa zuwa gidan babu wanda ya kara magana, Suna zuwa ya kallonta, yayi yace “get out.“
Tsaki ta saki a ciki-ciki tai waje, tana tunanin aranta dole ta saita shi, sai ta rama duk wulakancin da yayi mata. Dan ita ba sakaryar mace bace.‘ Dakinta ta shige direct, shi kuwa ya dade a zaune cikin motar sannan ya flto.
ldon maigadi kirrr yana ta tunanin mai ya sanya suka fita da wurwuri haka. Suda suke sabon aure. Girgiza kai yayi. ‘Allah ya sanya ba aika ~aika yayi ba, akaje asibiti’ sai daya gama tunanin gulmarsa ya juya yayi bayan gidan. A hankali ya taka, kafafuwansa falon, zuciyarsa nata san ganin ladlfa, dan tun jiya bai
kara sanya ta a idonsa ba, saman ya haye. Ko zai dan samu haushin dake ransa ya huce. D’akin ya shiga, kamshi ya bugeshi, tana kwance tana bacci, ga flate da cup da ta karya a gefen tebur, dankwalin ya zame, gashinta dake tsefe ya baje a kan fulon, sai kyalli yake, wani irin kewarta ne ya kamashi, gashi daman duk a takure yake, karfln hali kawai ya yi a jiyan nan. Gadon ya hau ya zauna, ya kurawa bayan ta ido, matsawa ya yi kusa-kusa da ita ya shiga shafar gashin kanta yana shinshina kamshin da gashin keyi, sai lumshe ido yake.
Cikin barcinta taji alamun ana tab’
a ta sai ta bude ido tai karo da shi, yana mata wani irin kallo, wanda kana ganinsa kasan yana cikin mayen sonta.Ya ke. Mikewa tai ta zauna, cikin sanyayyar murya mai zaki, hade alamun barcin daya fara d’aukanta tace “barka da warhaka zaujina angon amarya.” Mikewa tai cikin wani irin yanayin ta kalleshi, kallon da ta san dole yaji ajikinsa tace. “Sai
yanzu aka tuna da ladifa.” Ta shi ya yi tsam! Yace”zonan.“ Bata karasa ba, sai ma gefen mudubi da ta tsaya tana yin komai cikin sanyi. Tsam! Taji ya rungumeta ya lumshe ido. Cikin sanyin murya tace “ya haka? Mutum me amarya harya ke nanukar uwargida
haba! wannna ba lokacin ladifa ba ne.” Ta fada ta matsa daga inda yake. “Haramun ne?.” “Ni dai bance ba,” ta fada da dan murmushi, ta daura dan kwali a kanta tare da sunkuyawa za ta dau flate ta kai kitchen. Sai taji ya janyota ta fada jikinsa. da sauri ta kalleshi da manyan idanuwanta. Shaukin sonta ne ya debeshi wanda ya kejinsa ajikinsa a kuma yanzu, nan da nan ya shiga yamutsa ta.Yana shafata sosai yana wani lumshe ido. Jin yana neman rikice mata, ya sanya ta mike da sauri. Cikin kasalalliyar murya tace “Bai kamata ba, bai dace ba, lokacin amarya kake fa, meye naka na zuwa guna? haba! Karka ban kunya man, mutum mai dakakkiyar amarya, har zai wani damu da tsohon hannu, nidai gaskiya ka koma karmu shiga hakkinta.” Ta fada cikin
shagwaba. Dariya yayi “Wacece tsohon hannun?.” Wani salon kallo tai mai tace “shafa kaji, ta fice da sauri.” Murmushi yayi shi ma ya futa yayi dakinsa.
Laila kuwa tana shiga daki ta cire hijab ta kwanta tana tunani, ta dade azaune daga karshe ta tashi tayi wanka ta kwanta sai bacci. Bayan mintuna. Gidan ya yi tsit! duk da alama bacci kowannensu ya koma, sai wajen biyu ladifa ta tashi tai sallah, ta sauko ta dan gyagygyara falo, ta sanya mai kamshi,ta shige kitchen, ta gyara ta dora girki, dan yau ba tai da wuri ba, nan ta dawo falo ta zauna, so take taga amarayar ramadan, ammma shiru.” Bata dade da zama ba, sai ga ramadan ya sakko kasan, cikin wando tree quaterda armless, ya zauna. “kawo min ruwa baby?!‘ ya fada tare da duban ladifa. Bayan ta kawo mai ya sha. Tace “Amaryar taka hala mai tsada ce, naga haryanzu bata fitoba.”Kallonta yayi yace”bacci ta ke.” Bata kara magana ba, sai ta maida idonta kan tv tana maganar zuci, ita sai ta ga yafi zumudi kafin ai auren, amma a yau dukta ganshi ya zama wani iri, duk rawarjikin nan babu. Anya! babu wata a kasa kuwa, saitai sauri ta kawarda tunanin.
Laila bata da niyyar fita public dan koda ta tashi tai wanka ta shirya cikin wani lace,ta tsara kwalliya, sai ta zauna a falonta, tanajira Ramadan ya shigo. Ragowar kazar jiya ta dumama kawai taci tasha lemo ta dau waya tana chating.
Sai wajen karfe shida na yamma lokacin an kusa kiran sallah ta fita public falo, shima so take taga mai ke gudana. Lokacin Ramadan ya fita daga can zai zarce masallaci.
Idonta ne ya sauka akan ladifa da ke zaune, sanye cikin doguwar rigar abaya pink mai stone green. Ta daura dan kwalin abayar. Shock Iaila tayi, sakamakon arba da tai da ladifa, sam! bata zaci haka take ba, duk sai taji ta dan raina kanta . Amma kuma sai ta basar, saboda tasan itama ba mummuna bace. Zama adaya daga cikin kujerun tayi. Bata da alamar kula ladifa sai ma wani yauki da take wai ita amarya. Sai ita ladlfarce ta kalleta. “Amarya sannu ya bakunta. Tun dazu nake tambayarki.” Kallonta tai ta dan canja fuska. “Allah ko? tona gode.” Ta fada tajuyar da kai. Ba a dade ba akai kiran sallah ta koma shashenta. Haka ladifa sukai sallah. Ramadan bai dawo ba sai wajen isha’i. Mamaki ke cika ladifa ganin yanda ramadan baya wani zumudin Laila kamar da.
Sai da yaje yayi wanka sannan ya dawo falon. Yana zama sai ga Iaila ta fito, cikin doguwar rigar wani yadi mai mannewa ajiki, sai girgiza take. Yana kallonta yasan ta makala kayan cikonta. Dariyace taso ta kufce mai sai ya dake.
Duk dan ta nuna wa lad’ifa, ya sanya ta zauna kusa da Ramadan dake danna waya, har ga Allah tana son ramadan ji take kamarta maida shi ciki, so take kawai tai abinda zai huce.Tun data ga ya watsar da ita, ba rawar jikin da ango ke akan amarya.
Cike da budewar ido tai murmushi “angona, I miss you, tun dazu nake dakonka, nan ya kalleta suka kalli cikin idanuwanjuna. Sai ya dauke kai. “ai naga kina bacci.” “Baki ga my beautiful ladifa ba.”
Wani dam Laila taji ta kalli gefen ladifa dake danna waya. mun gaisa fa tun kan ka shigo, yanzu ma ban kula bane,duk ka dauken hankali dearna.” Tashi tai “Zauji bari na kawo abinci.” “Okey ya ce. Laila ta bita da kallo ta tabe ba ki. Azuciyana ta saki tsaki. ‘Ji iyayi wai zaujl.’ A fili kuma tai dan murmushl. Adaidai lokacin ladifa ta fito ta ajje warmers na shinkafa da miya da flate,hade da cokula. Ta kalli Ramadan “zauji bisimillah.” Nan ya mike dan dama yinwa ke sasukarsa. Mikewa tai ta bishi a baya tana wani yarfa ido. Duk dan ladifa ta ji haushi. Ita ko Iskar data kwaso ta ma lad’ifa ba ta kalla ba, dan ta san duk abinda take. lta ta riga ta wuce gun. Sarving dinsu tayi ta zauna tafara cin nata. Laila sai wasu badalu take yi. Shi kuma yana biye mata, dan dukya kawar wa da lad’ifa tunani akan canjinsa.
Bayan sun gama cin abincin. Suka koma kan kujera. Kallon laila kawai yake yanajin haushita, dan ya san tabbas! Ya san ta kuma sanya acuci mazan nan, runtse ido yayi lelle zai koya mata hankali. Sun dad’e suna kallo, da hira jefl jefe, wanda duk ya maida hankalinsa kan ladifa. Can ya Mlke . Ya kalleta laila, yace tashi ki biyo ni.” Ya kalli ladifa yace”Sai da safe babyna.” Murmushi tai tace “sweat dreams darling.” Wani tsaki laila tai ta kalli ladifa ta tabe baki. Nan ta mike tabi bayansa tana karairaya da kayan ciko, direct a bangarenta ya tsaya a falo.
Tana karasawa ya kalleta ya ce “wallahi wallahi, laila kinji na rantse miki this is the last warning da zan miki, akan kuma saka kayan acuci mutane din nan, wallahi zaki fuskanci bacin raina mara musaltuwa.”Jijjiga jiki ta shiga yi. “Wallahi Ramadan bansan haka aurenka zai zame mun ba, da tun farko ban fara ba.” Wani takaici ne ya kuma shigarsa. ” kin manta na sallameki,kika nace na dawo da ke, to har idan kina son Zama da ni dole ki yi abinda na umarceki, dole kibi umarnina, saboda nine mijinki ba kece ba.” “Wallahi ni fa ba za a takuran ba, haba! nifa bantaba ganin irin wannan ba, ciko da nake yi ai ni naga zan iya, tun fa jiya kake ke min masifa, sam! baka nuna wani abu da zai nuna cewar ni amarya bace.”
“Shut up, fool girl kawai, wallahi ba dan hajiya ba, yanda kika yaudareni, wallahi da bazaki dawo min ba.”Oho! dole ace da mijin iya baba,yaudara da kake ta ambata, kai kaso, dan ban janyoka kazo ka soni ba, kai kaji ka gani, dan haka ka sarara min hakanan, ta fada tai shigewarta cikin dakinta.
Dafe kansa yayi, abinda ladifa ba tai mai kenan yana fada tana fada. Tsaki yayi dole ya nuna mazantaka akanta yanzu kuwa, Dan taga ya rabu da ita, dole yau ta gane bata da wayo dan sai ya fanshe duk jalalar da ta sanya shi. Kurna ba daga kafa,
Nan ya kullo kofar falon ya bita dakin afusace.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Hmm nanfa akeyinta

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]