[Advertisements⬇️]

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 13 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 14
Bayan tafiyar abokansa, ya kullo dukkanin gidan, ya dawo falon. Ladifa na zaune suka hada ido da shi, sai yayi murmushi “uwargida ran gida.” “Hmmm tace ango kenan.” Ganin yanda yake ta zumudin shiga bangaren laila, ya sanya ta mike. “Ni dai nayi sama, agaida amarya.” Murmushi yayi, yace “ki jira zanzo muyi sallama.” “To,” ta ce mai tare dajin ruwan kuka na son saukowa,ta shige daki sai ta zauna ta dafe kumatu zuciyarta na rawa.Don ta san abinda yake mata duk shi zai bawa laila a daren yau. Runtse ido tayi taji hawaye masu dimi na saukowa, ga tsabar kishi dake cinta. Saita shiga ambaton Allah. Shi kuwa falon lailan ya shiga, direct can cikin dakin ya shiga shakar kashin dake tashi daga dakin yake, tana tsakiyar gado a kudundune tana kuka, jin shigowarsa ya sanya taji 
faduwar gaba. Zame babbar rigarsa yayi ya zauna kan gadon ya kalleta. Amaryata yau burinmu ya cika.” Sai ta sanya murmushi kasa-kasa Nan ya matsa kusa da ita jikinsu na gogar juna, hannunsa ya sanya ya zame mayafin dake kanta, suka hada ido sukai murmushi, saiya saki ajiyar zuciya, wani nannauyan numfashi ya sanya tare da ruko hannunta yana murzawa zuciyarsa na tsalle. Cikin zumudi irin na angwaye ya mike. “Amaryata ya kamata ki mike, kizo mu zauna muci musha.”Cikina a cike yake.” “Ba wani nan.” 
Ta shi yayi ya dauko leda mai dauke da kaza da kayan sanyi, wanda dai a al’ada ake yiwa 
amare. Saida ya tashi ya rungumota tana sinne kai yace “wai laila yau kunyata kikeji ne?.” Sai ta kalleshi ta sanya murmushi mai kayatarwa “Ai dole ne.” 
Zama yayi ya janyota jikinsa, ya fara ciyar dasu, da kyar take karba cike da yanga, tana taunawa a hankali, hakan sai ya ke birgeshi, ahaka har suka gama 
“Kiyi wanka da Alwala zamuyi sallahr nafila.” Dan daburcewa ta yi “habiby baccifa na keji. 
“Yau ranarmu ce, karki bata mana ita,” ya fada tare da janyota jikinsa ya shiga nanikarta yana goga hancinsu waje daya, ganin yana neman fita daga hayyacinsa ya sanya yace “please.” 
Sai ta kauda kai, haka kawai gabanta ke faduwa tana jin ba za ta,iya shiri agabansa ba, bata san yaya za ta kawar da sirrinta ba, wanda babu wanda ya taba sani. 
Ba tai aune ba taji yaja hannunta suka miki ya shigar da Ita bandaki Kallonsa tai tana murmushi Ya maida mata yace “kiyi kan na dawo. ” Ya fita ya shiga dayan dakin. Sam yama manta da lad’ifa, hankalinsa na wajen laila. 
Itako tsayuwa tai a toilet hankalinta a tashe, tasan dole ne sirrinta ya bayyana, nan tayo alwala, ta fito ta zauna, ta dade azaune, sai gashi ya dawo ya ce “laila tashi muyi sallah.” 
Ta shi tai ta daura zani.Duk bakinta taji ya mutu, ta dauko hijab sukai naflla, yayi mata 
tambayoyi akan addini ta amsa daidai, da yake Allah ya sanya da ilminta.Da kansa ya zaro rigar baccinda yake da bukatar ta sanya,ita kanta saida taji kunya , ganin rigarda kadan ta dara cinyarta. Da kyar ta karba ta shige bandaki. Ta dade aciki, wanda shi harya kagu, sai gata ta fito daga bandaki sanye da hijabin.Bata taba zatan zata shiga rudu irin na yau ba, dan tasan zumudin Da Ramadan keyi, addua take kawai Allah ya sanya karya ce wani abun. Tashi yayi ya kashe wuta, ya bar ta bed lamp kawai, a hankali ya cire hijab din jikinta, idonsa arufe yajan gota jikinsa,ya shiga nuna mata salo kala»kala, wanda tun tana nokewa har ta saki jiki bata san sanda taji ta a gado ba. lnda yake wa kwadayi tun fara had’uwa da ita, ya shiga romancing dinta. Amma sai yaji wayam! baiji tudu ba,sai daya kuma dumfara sosai, sannan ya ankare, nan ya shiga rudani da kokonto, anya kuwa lailarsa ce, ina suke? Ya tambayi kansa. Wani irin zabura yayi ya tashi ya kara hasken fitilar. Ita ko tasan tata ta kare yau. Nan Jikinta ya hau rawa, kura mata ido yayi, yace “laila ya haka? anya kece kuwa”Ni ce wallahi meye ne.” Ta fada irin bata gane ba. “Dama kayan alatun ba naki bane? ashe! abinda ake fada na cewar wasu matan na cuko dagaske ne! Tabbas yau na gasgata, dan ga shi yazo kaina.” Filo ya damka cike da wani tarin haushinta. Ya kalleta da jajayen ido “ni zaki yaudara, wannan shine nayi gudun gara na tadda zago, wallahi na shaida gwanda garar,jibi fa.” Saiya dafe kai. “Dan Allah kai hakuri habiby, wallahi ina da dalili na.” “Wani wawan mari ya bata, dalilin me? ni zaki yaudara da manyan boobs babban hips, ashe! duk cuko kike.” “dama….dama dansu kake sona?.” Shut up!, wallahi sai na nuna miki ni waye, afusace ya kunna fitila haske ya gauraye dakin. Tana zaune tai tsirbi tsirbi, ta kare jikinta tana kuka. Sai ya dafe kai cikin bakin-ciki “ni zaki yaudara laila, me nai miki?.” 
Ba tace komai ba, sai kukan da take rusga, kalllon agogo yayi ya ga har kusan sha biyu da rabi. Sai ya saki tsaki. Ya sha burin shan budurinsa da ita. Yayi doki har ya gaji sai ya kuma sakin tsaki. “Tashi ki debomin duk abinda kike cikon dasu.” Jajayen idonta ta daga ta kallleshi da suka rine saboda kuka. “ba zan dauko ba, ka bani mamaki, ashe dama jikina kake so? yau da son gaskiya ne ai ba zaka damu da duk yanda ka ganni ba.” “ki tashi nace” “Ba zan tashi ba Ramadan” ta fad’a tana mai shashshekar kuka. “Karki ta shi.” Ganin yanda yake huci ya sanya ta zumbula hijab, ta mike tai toilet himilin kaya ne ta fito 
dasu, a hannu sai ya saki baki. 
“Oya zauna ki wassafa mini , ni nama kasa gane ta yaya nake ganinki gaba daya ko ina tsaf Hararsa tai “tunda na Fito maka dasu sai ka sarara min.” Don tazo iya wuya kan abinda yake mata. ‘ Cikin taku ya mike, yace “kinji na rantse ma saikin sanya na ga yanda kike aika aika da yaudarar maza, domin wallahi yau sai kin gane ni ramadan banda mutunci.” Mikewa tai tana hawaye ta daura zani dan ta tsuke, aiko  Bra ce guda biyu, daya mara hannu me 5050 ajiki, d’aya kuma babu, amma tafi mara hannun girma, nan ta sanya mara hannun sai kirjin ya dada girma da cika, ta dauko dayar push up ce ta sanya ta jata, sosai sai ga kirjin yayo sama ya dago sosai sun bullo ta sama. Tsaki yayi yace “amma bakiyiba laila.” Wani mugun kallo tai mai ta juya yace “oya su wadannan fa?.” 
Nan ta d’auki wani gajeran jins me kauri sosai ta sanya, ta d’auko wani abu mai kamar roba brown yana da laushi kamar danko, shape d’in botton din mace ne da shi, shima daidai iya cinya, sai gashi yayi daidai ya dameta ya fitar mata da shape, nan ta dauko under wear ta sanya, ta zira siket ta sanya jigida daga kugun dan jigidar ta kara taimakawa wajen fidda shape din, sai gashi nan ta fito das! Sannan ta dau tommy belt, wanda zai rage girman tumbinta, dan tana da tumbi, ta sanya ta balle, sai ga cikin ya koma, ta zira riga sai ga shi ta dawo lailar da ta yaudareshi. 
Murmushin takaici yayi yace mata “amma wallahi ba zan lamunci tsiyar nan ba, keko kunya ma ba kyaji? kin hada kaya ajiki, laila dole ki gane baki da wayo, wallahi gobe zaki barmin gida,dan bazan lya zama da ke ba, dan da zalar na kalleki zanji takaicin abinda kikamin kuka ta sanya “Ramadan karka yi min haka, wallahi nayi nadama.” 
“Wallahi yanda kika sanya ni a kunci ,sai kema kin shiga,” ya fada tare da zama ya dafe kai, idonsa harda da taruwar hawaye , sai ya tuno da ladifa, dukda bata da girman boobs nata ma yafi na laila girma a hakan.Kuma surar jikinta tafi kyau. 
Runtse ido yayi shi baisan ya zan kwatanta laila ba, adan ganin da yayi mata bata da wani suffa ta mata, ashe! Ciko ne ke fito da surarta. Laila bata da wani shape, bata da wani fasali, kamar namiji, atsaye take kamar doya, tana da cikar fuska ne kawai zuwa wuya sai damtsen hannunta dake da lukuti, sai uban tumbi, kwata-kwata shi,isa idan tai cikon da take ake ganin kibarta, sannan cikon na taimakawa wajen fidda mata da shape sosai saboda yanayin gayunta da ya sanya ba zaka taba ganewa ba. Dan dama dama ma tana da kyan fuska da kalar fata me kyau. Sai gashin da 
take dashi, wanda bai ma kai tsawon na lad’ifa ba da tsawonsa. 
Kuka kawai take, tana son Ramadan sosai, ayau tayi danasanin sanya cikon nan. Data sani ta barshi ya santa ayanda take, ko ba komai zata samu mesonta duk yanda take. Ayau ta dada tabbatar da wasu mazan dan irin hakan suke son wasu matan. 
Bangaren lad’ifa kuwa, ganin har 10 ba labarinsa, ya sanya ta saki kuka mai cin rai, ganin hakan ba mafita bace, sai kawai tayo alwala taita jera sallah har bacci ya kwasheta.Ramadan saboda tsabar takaici duk tarin sha’awar lailar da yakeji, sai yajin duk babu, sai ya bar dakin ya koma sama,ya shiga nasa dakin ya kwanta, harda su hawayen bakin-ciki, domin ta sammace shi ainun! ya gwammace ma yayi asarar komai daya kashe mata, daya zauna da ita, tashi yayi ya rubuta mata takarda saki daya ya ninke ya ajje ya kwanta. Laila kuwa ihun kuka tasha sosai! a haka tai bacci. 
Da asubahin fari. Ramadan ya shiga d’akin, tana zaune ta idar da sallah, fuska atamke ya mik’a mata takarda. “Ki koma inda kika fito, kici gaba da yaudara, wallahi inna barki kallonki takaici zai dinga janyo min.” Ya fada tare da juyawa. Kuka ta fasa, ta sunkwi da kai, ko kallonta baiba ya fice. 
Kalubale ga wasu matan dake ciko, wallahi wannan masalar ya faru agaske kamar daiyanda kuka ga komaiya wakana, wanda aranar da aka kaita mijin ya saketa, saboda a ganinsa ta yaudare shi, wannan ishara ce babba, duk me yi ya hankalta, saboda bakowanne namji bane zai iya controlling b’acin ransa. Me yayizafi ne. Duk dan a samu miji ne wasu ke hakan keko kuma ayaudari wasu mazan ko, to wallahi kika bar yanda Allah ya tsaro ki sai kinfi daraja.Kuma in kikai karatun ta nutsu ma sai kinga kinfi kyau ayanda Allah ya barkin. Yau mai gariya waya wa laila. Kina zaune a yanda kike wani shi kuma irinki yake so, ba sai kinyi ciko ba k0 canja halitta irinsu bleacing, karin gashi, da sauransu zaki samu miji ba, wasu ba dan masu samu miji 
bane, kawai dan ace ai wance ta hadu, duk inda suka shiga ana yabawa, wallahi duk macen duniya inhar Allah yasa
Bata mutu ba har sai tayi aure, to da mijinta aduniya. Komai rashin kyanki wallahi sai ya aureki, kuma yaji ba kamarke musamman in kikai katari da nagari. Sai dai in kin hadu da irinsu Ramadan ne marasa godiyar Allah kamar yanda yake wa ladifa. Wanda gashi nan shi ma yaga hukuncin Allah. Ai Allah daya gari bambam. Abincin wani gubar wani.Ba sai kin cika ba zaki zama kasaitacciyar mace. Allahn daya yi maka halitta kana ganin bai maka ba, har sai kaje kayi wani ciko dan kayi yanda kake so, to Allah aiyana madakata yana kallon kowa. Allah kuma ya shirya masu yi su gane Allah ya kyauta 
Gari na haskowa wajen 7 Ramadan ya koma ya taradda laila kife na kuka, nan kuma ya daka mata tsawa, a salibe ta mike ta tashi ta fita. “Dan Allah kai min rai, wallahi in naje gida bansan me zance ba, baba zai iya karya ni, bantaba jin an saki mace a ranar daren farkonta ba, sai akaina.” 
“Wannan ya zama izina ga masu hali irinki. Sai ki gaya musu gaskiya, domin duk wanda yaji yasan kin cuceni, a aure babu yaudara, saboda me zaki yaudareni?.” “Ashe! dama ba sona kake ba! dan surata kake so 
na.” “Shut up ina surartake ajikinki? surar cikon? ki tashi nan ta na rage miki hanya.” Nan ta mik’e da takarda ahannu suka fita, maigadi na cewa “oga amaryar ba lafiya ne?.” “Eh kawai ya fada suka fice, fuska atamke yaja. ‘ Adaidai titin da zai sada ka da unguwarsu ya ajjeta. “Fice kiban waje. Allah ya isa tsakanina dake.” Ko kallonsa ba tai ba, tayi gaba shi kuma yabar wajen.Ta saki nikab Allah yaso ta tawo dashi. 
Duk arude take ta rasa ta yaya za ta doshi gidansu, tana tunanin intaje, me za ta 
ce? amatsayinta na amarya da aka kai jiya, wandda tasan ‘yan biki ma basu gama wucewa ba, kuka ta sanya ta dinga risga, dana sani na baibayeta. Wani tunanine ya fado mata arai, sai ta juya da sauri ta tari adaidaita, tayi gidansu ramadan, ba zata taba bari Ramadan ya kubce mata ba, domin tasan dole indai uwarsa nada kirki dole ta sanya ya maida ta.Kuma da wuya ta taradda mutane a gidan. “
Ni laila zata yaudara?” Ya fada yana share hawaye. “Naso yarinyar nan, ba hidimar da ban sha akanta ba, dubu hamsin na bata sati daya baya tace zata biki maiduguri, wanda awajen musa mai tirela na amso, dama yana bina bashin dubu d’ari, yanzu bashin dubu d’ari da hamsin ne akaina, kuma wallahi duk agunta suka tafi. Kullum musa mai tirela sai yayi mini magana. Ajiya sai da yayi min kashedin in ban kai ba sai ya sa an rufe ni amma ace duk a banza.” 
Kallon katin daurin aurenta dake hannunsa yayi, wanda haladu ya kawo mai. “Kin cuce ni laila, kin yaudareni kinyi aure, ba tare da sanarwa ba, kin tafi gidanki, ni kin barni cikin ba shi.” Ya fada da kunarzuci. Haladu yace “atoh! tun yaushe nake gaya maka ka rabu da ita, ba tsararka bace, yaudararka take, amma ka nace, saboda kana ganin babu wanda ke da big girl irinka. Wallahi ni ina ganin idonta, nasan za tai tsiya. ai ga shi nan ka gani. Saika kori gaba. “ldan a naiwa kowa iskanci yayi hakuri, wallahi banda ni murabus, wallahi ba zan  hakura ba, wallahi saina rama, wallahi sai ta gane shayi ruwane. So nawa nake cewa mahaifiyata ban da kudi, duk dan na tara na faranta ranta, kai kanwata ko kud’in anko bana bata sai ta sha mita. Duk kuma kudina, a sayan credit d’in laila ke tafiya. Wallah zata 
san da murabus tayi. Me za kai? kawai kai hakuri, kaima ai da lefinka wallahi, ba kai ma mahaifiyarka da kanwarka abu ba, wanda kasan inkai ma mahaiyarka zaka samu lada, amma ka bige da yiwa budurwar da yadararka ma kawai take ba aurenka za tai ba. Yau da ace aurenka za tai shine in kai mata baka fadi ba, amma kaki ganewa, ai gashi nan, alhakin mama ne, daman ance in ba ai sharar masallaci ba a yi ta kasuwa.”Wallahi da zuciya d’aya na so laila, amma ni taiwa haka, na rantse yanzu haka zuciyata 
kukan rashinta take, amma wallahi sai na kunsa mata bakin ciki nima.” “Hakuri yana da riba, shi dai za kai kawai, saboda baka san waye mijinta ba, karka saka 
kanka a masifa.” Bai kuma magana ba sai kawai yayi gaba yana maijin haushi. 
Hhhhhhhhhhhhh! nasha dariyar laila da ramadan. Sai nace alhakin ladifa ne ya kama ramadan  K0ya zata. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]