NAYI GUDUN GARA CHAPTER 12

Advertisements

_____

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 12
Saida ya tsaya a hanya ya saima Ladifa  gasasshiyar kaza, sannan ya karasa. Tana kwance akan tree seater kanta akan dan tudun kujera,sanye da riga da siket na atampa kalar black&white, d’an kwalin kan ya d’an zame, fuskarta dauke da simple makeup. Tana latsa waya.jin motsin shigowa, sai ta tashi ta bud’e kofar shigowa falon, ya shigo yana raba idanuwa. sannu da zuwa tayi mai tana karbar jakarsa da ledar hannunsa. Ajje ledar tai akan dining, sannan ta tafl ta kai jakar sama ta dawo ta sameshi zaune yana jingine da kujerar, yana kallon wasan da ake hasakawa atashar tauraruwa da take kalla.”Ya dai naga yau kamar agajiye kake hala wani wajen kaje..? “Wallahi fa, na dan biya ta wurin hajiya ne,” ruwan da ta dauko mai d’an sanyi ta tsiyaya mai ya karb’a ya sha. Ta ce “abinci za ka fara ci ko wanka?.” “Ba ni abincin na debo yunwa, inna hau saman dukka nayi wankan duk agajiye nake. 
Ta shi tai ta shiga kitchen ta d’auko farantin me d’auke da kwanukan abincinsa ta dire agabansa, tare da ruwan wanke hannu, ya wanke ta d’auke, ta dawo ta zuba mai tuwon somovita da miyar kub’ewa bushashshiya, had’e da naman rago da man shanu.Masha Allah ya fad’a ya fara aikawa, domin yana da son tuwo a rayuwarsa. Rigarsa ya cire ya zauna daga shi sai vest. ‘ Littafin da take karantawa tun d’azu ta d’auka tana yi mai fifita.Duk da na’urar sanyin da ke kad’awa. “Ki bud’e ledar can sautin ki ne.” Nan ta mik’e ta bud’e tajuye a flate ta zauna suna hira,kad’an ta ci ta maida ragowar kitchen.Shi ma ya gama ci ta kwashe kayan.Zauji naga fa ka gaji, kalli yanda kake bin kushin.” “Zo kimin tausa kinji.Nan ta mike ta farai mai,ji ya ke kamarya yi bacci, don shine a idonsa, tana cikin tausar idonta ya sauka akan rigarsa agefe,inda ta yi gamo da shatin leb’an laila, zame hannunta ta yi ta janyo rigar. Ta k’urawa shatin ido. ‘Tabbas shacin leb’e ne,d’aga rigar ta yi, sai kamshi ya tashi, tabbas tasan turaren mijinta, wanda taji d’in nan kuwa ya bambanta da nasa. Kallonsa ta yi cikin kidima da mamaki. ldonsa a rufe duk bai ga abinda ke wakana ba. Nan fajikinta ya hau rawa, zuciyarta na raya mata cewa lalle akwai inda yaje,yayi shi,isa yake ta faman nuna gajiya. Bakinta ne ya shiga rawa tana san magana ta kasa,sai faman karanto addu’ar da duk ta zo bakinta.take cike da mamaki a zuciyarta. “Ki cigaba man, naji kin daina” Kuka ne ya kufce mata, ta buga mai harara tayi sama da sauri tana kunshe kukan da yazo mata. Sai ya yi saroro.Yana binta da kallo harta shige. Mamaki da al’ajabi ne sukai mai kawanya a kwanyarsa,tare da tunanin anya ladifa ba ta da aljanu. Rimi-rimi suke yanzu amma ta canja.Tsaki yayi kawai. Tana shiga dakin, ta sanya kuka mai karfl. “ashe! wurin wata ya je, ashe! Ya fara neman mata.” Ta fad’a tare da kuma sanya kuka. “lnnalilllahi wa’inna ilaihi raju’un! da me na ragi Ramadan ne? Yanzu har ta kai yaje yana kissing wata, wa yasan ma me sukai.” 
Sai ta runtse ido ta kwanta ruf da ciki, nan fa kyakkyawar zuciyarta ta gaggauta dakatar da ita ga munanan tunanin da ta fara, domin watakil zarginsa take’ ba zai haka ba.‘ Take zuciyoyinta sukai ta kawo mata farmaki, kan gaskiyane ko ba gaskiya ba. Runtse ido tayi hawayesuka ci gaba da zuba.Dan ta rasa na d’auka. 
Acan falo kuwa, ya d’an dad’e a zaune, daga baya ya tashi yayi saman, bai duba inda take ba, sai kawai yayi nasa d’akin, yaje yayi wanka, sai da ya gama kimtsawa, sannan ya bita nata d’akin, shashshekar kukanta ne ya da ki kunnuwansa, ya karasa da dan hanzari. 
Sai ya tsaya ya k’ura mata ido, yana mamakin canjawarta na d’an lokacin nan, a hankali ya taka zuwa inda take ya zauna. “Lad’ifa.” Ba ta amsa ba, har sai da ya kuma kiranta, sannan ta amsa, duk da haka taki bari su had’a ido da shi. “Meye ya faru?.” 
Tunani ta shiga yi kan ta yi mai magana ko kuma ta kyale shi, tabbas barin kashi a ciki baya maganin yunwa, gwanda ta gaya mai, sosai taji kwarin gwiwa na shigarta. “Ina zuwa.” Ta mike ya bita da kallo, tare da mamakinta, duk ta canja, tsaki yayi ya tashi ya fita zai koma dakinsa , ita kuma za ta fito, d’auke da riga a hannu. “Meye wannan? Sannan ka kara rigar a hancinka, itama k’ashin wani kalar turaren mata take, domin tabbas na taba amfani da irinsa. Farkon zuwana gidan nan. Kalla ya yi yad’an zaro ido, tabbas shacin baki da jambaki ya ke gani,ga kuma kamshin turarenta. Tab’e baki tayi ta ajje rigar  tai wucewarta d’aki, hannunsa ya daka “rigima kenan, tabbas laila ce.” Sai ya bi bayanta, lad’ifa ta kalleshi “ni kawai ka rabu dani.” Ki Saurareni Lad’ifa,bansan ta yaya hakan ta faru ba. Wallahi tallahi babu wani abu da kike tunani.” Babu komai fa ya wuce, ni dai ina tunatarwa komai mutum ya ke Allah yana kallonsa.” “Me kike nufl wai? kina nufln ina bin mata ne?.” “Waya sani abin b’oye,” Tunda ga zahiri na gani,” ta fad’a idonta na taruwar hawaye. 
Duk abinda za ki, kiyi,kiyi tunda nake ban taba zina ba, idanma abinda kike tunani kenan, to kiyi gaggawar canja tunaninki, dan ni ma bansan ta yaya akai wannan abin ya shafl kayana ba, amma duk yanda zaki fassara ni, ki fassara, lokacinki ne.” yana gama fad’a yayi fucewarsa. Yana flta ta kuma fashewa da kuka. “Allahumma ajirni fll musibati wa aklifni khairan minha” Saida ta dad’e tana kwasar kuka, akarshe tai shirin bacci, wanda aranar kowanne a nasa d’akin ya kwan da tunanin daya dameshi. can Da safe da tunanin sanya ranarsa ya tashi, kobi ta kan Lad’ifa bai ba dake ta cike cike tana kumbura, tana gama had’a breakfast, yaci ya yi ficewarsa. Tarin bakin-cikine ya taru yayi mata fall arai, tunani kala -kala ke kaikawo akwanyarta game da mijinta, ba ta son zuciyarta ta ci gaba da zarginsa, amma kuma ai ta ga dahir, karshe ta tashi ta koma d’aki, dan ji tai duk gidan yayi mata zafi, da ace ta tambaye shi fita, da ta fita, kota samu sa’ida, amma ta kasa, sai kawai ta share, ta d’au wayarta ta shiga duniyar media, ko zuciyarta tayi taushi. Karfe goma wan babansa da kanin babansa, kanin mahaifiyarsa suka tafi gidansu laila, sunje akai musu tarba mai kyau, suka mika kokan bararsu tare da bada kud’in mun gani muna so, wanda suka hado da na sanya rana, inda aka sanya wata biyu. Da yake dama mahaifin laila ya yi bincike kan Ramadan tun farkon mika shi da laila ta yi, yasan cewa daga gidan mutunci yake, kuma shima babu laifi yana da shaida me kyau. Babu wani taro da sukai, sai ‘yan uwa najiki da aka sanarwa da sanya ranar karsu ji daga sama. 
Nan fa iyayin laila ya dada hauhawa, take ta fara wassafa yanda komai nata zai,ai a tsare, tare da tsara yanda za ta sallami duk wani saurayinta, sai waya suke da Ramadan bini -bini. 
Yauma sai kusan tara ya koma gida, dan sai da ya biya ta wajen gimbiya laila. Yana shigowa falon ya ganshi din dim! sai hasken tv da ke aiki, idonsa bai hasko masa inda lad’ifa ke ba. Hakan bai sanya ya damu daya wani gano inda taken ba, itako tana kujerar gefe ta yi lamo aciki, tana tunani zuciyarta na suya, duk da cewa zafin ya ragu, sai da yayi gyaran murya sannan ta ankara da shi. Sai ta mike jiki asanyaye, kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, ta yi mai sannu da zuwa tare da karb’ar kayan da ke hannunsa ta kai sama. Ta dawo ta gabatar mai da komai ta koma gefe, ya kalleta ya cire rigar samansa ya bar dagashi sai dogon wando da vest ya zauna yana kokarin cin abinci.Kallonta ya yi, yaga yanda ta kafawa tv ido sai ya yi d’an murmushi, dan ya san abinda ke damunta, shi ko ba zai zauna yana wani bata lokacinsa akan rarrashin ta ba, tana tumbotsai, akan shi abinda be san ya aikata ba.Sai da ya kammala komai, sannan ya kalleta ya ce “Lad’ifa” Ta juyo ta kalleshi fuska atamke, “ya dai?.” Wani karkataccen murmushi yayi, ya shafl gefen habarsa. “Ina son gaya miki yau an sanya mini rana, dan karki ji a wata duniyar, an sanya wata biyu. Gabanta ne ya fadi ras! ‘Ashe! dai auren nan sai yayi shi, duk da gani take ce, sai taji kamar an watsa wa kirjinta tafasasshen man zafi, wani irin zazzafan ruwan hawaye ne suka hau kwaranyowa daga idaniyarta kamar dama jira suke,, sai ta juya ta sunkwi da kai, dan bata so ya gani, amma ba 
ta san cewa ya gani ba. Kuka take bilhaqqi da gaskiya,tana sakin ajiyarzuciya akai kai, tausayinta ne ya kamashi, tabbas! ya san sonsa ne ya sanya ta ke kishi. Kuma dole tai kishi, Sai ya tashi tsam! yaje har inda take, ya tsugunna ya dago kanta, sorry lad’ifa, nayi laifl ko? Fizge kanta ta yi, “yanzu dama ashe! da gaske ne auren nan Ramadan? meya sanya za kai min hakane? aure shekara daya a sanya min damuwa.Dame na rage kane Ramadan?Duk wani abu da ya zama Hakkiinka ne ina kawar da shi, amma baka gani, yanzu ya dace kenan? dama ai na kula baka sona shi,isa yanzu zaka auro wacce kake so.” “Afuwan lad’ifa, wallahi Allah ne ya sanya hakan ya wakana, bayin kaina bane, kiyi hakuri, ko nayi auren nan aikece araina,wallahi ina sonki ladifa so matsananci ma kuwa.” Wani haushi ma ya bata, tun bayan aurensu sai ta kejin bai k’ara furta mata wata kalmar love ba, wai ya ce i love you, ai wannan tun yana neman aurenta. Amma shine sai zai mata kishiya yazo yana wani cewa haka,ji take kamar ta makure shi, hakan ya sanya ta mik’e. “Ni ka rabu dani kawai, ai dama haka kuke maza, da kun ci moriyar ganga sai ku yada kauronta, to wallahi ba zan yarda ba , ta fad’a tare da fashewa da kuka. 
Ta shi yayi ya riketa ya rungume ta tsam! Ajikinshi yana kokarin son lallashinta, sai ta hau fuzgewa. “Dan Allah ka kyaleni, bana son kana tabani.” 
Sai ya rabu da ita,ta zauna gefen kujera ta cigaba da kuka kasa-kasa, bai k’ara tanka mata ba, har saida ta gaji dan kanta, sa’ilinsa taji zuciyarta ta danyi sanyi, sai kuma ta shiga sakin ajiyar zuciya. Anan kuma tunaninta ya dawo, ta shiga kundin aiki da hankali. Ganin kamar salama ta sauka afuskarta, ya sanya yace “kiyi hakuri lad’ifata, Insha Allahu ba zaki dana -sani ba.Wannan kukan duk ba zai fishshe ki ba, domin auren nan babu fashi,gwanda ki sanya ranki a inuwa, ki rungumi kaddara.Harara ta watsamai. “Da ran nawa a rana yake? ai ba sai ka fad’a ba, wallahi da ban rungumi kaddara ba, da yanda kaci amanata da tuni na bar maka gidanka, amma kawai ina duba abubuwa da yawa ne wallahi, dan haka ina yi maka fatan alkairi, ya baka  jumurin iya rike mata biyu,da kuma kwantanta adalci.” Tana gama fad’ar hakan ta mike ta koma sama, tana jin kamar tabar masa gidansa, kaiji take sam! ba ta san ko ganinsa, gani ta ke kawai baya sonta, sai taji dukwani rin yanayi mara dad’na shigarta.Ashe! Haka matan da ake wa kishiya keji, lalle ta jinjinawa mata masu, kokarin hadiye kishinsu, shi,isa ake so a yayinda miji ya bijiro da batun kishiya, ake san aiki da hankali, da hakuri dajuriya. Dan wasu kishi kamar mahaukata ya ke maidasu, sabida tarin yanda sukejin zujiyarsu na yi, idan ba suyi aiki da hankali ba, sai aga suna ta aikata aikin baban giwa, tabbas me rike kishi sai jajjirtacciyar mace mai hakuri, nan tayi tajan addua tana kokarin saita zuciyarta, dan al’amarin yana neman fin karfinta, rarrashi kawai take so, tana so kawai taji muryar hajiyarta ko taji sanyi. 
Shi kuwa sanin cewa ma zuwa wajenta kamar dad’a wani tunzura ta zai yi, sai kawai ya zarce d’akinsa, yayi wanka tare da gabatar da duk wasu abinda ya saba aiwatarwa kan ya kwanta ya yi su, ya baje akan lallausan gadonsa ya shiga bacci da munshari. 
Haka ta kasance wajen laila ma, haka tai ta bugawa kawaye da abokan arziki tana sanar musu sanya aurenta, dan aranarji take kamar duk wani burinta ya gama cika, haka itama ta kwanta cikin farinciki. AYayinda Lad’ifa kuwa, baccin ma yaki zuwa, in banda kuka ba abinda take yi, ta dad’e tana yi, sai wajen 12 sannan gajiya ta saukar mata, ba ta kwanta ba, sai da ta gabatar da nafiloli ta dora da salati, had’e da istigfari da hailala, da rok’on Allah ya sassauta zuciyarta wajen kishi, ya basu zaman latiya, ya sanya matar ta gari ce. Ta dade tana kaiwa Allah kukanta k’arshe bacci ya d’auketa akan sallayar. 
Da safe akasalance ta mike sabida rashin samun wadataccen bacci, haka tai musu breakfast ta ajje, ta san in be tai ba, zuwa zai ya hau ta da fada, nan ta koma d’akinta taci gaba da bacci, ba ta san sadda ya fice ma daga gidan ba. 
Sai wajen goma ta mik’e tai wanka ta flta ta sha black tea kawai, danji take ma bata san saka komai a bakinta. Bayan gama sha sai ta koma d’akinta ta d’au wayarta ta kira hajiyarta,tana jin muryarta hajiyar sai zuciyarta takarye ta fara hawaye tace “hajiya.” Cikin tashin hankali hajiyar ta ce “meye ne auta? na ji muryarki na rawa, alamar kina kuka.” 
Kukan ta kuma sanyawa, “hajiya wai ni Ramadan zai wa kishiya, har an saka rana wata biyu,” ta fada da shashshek’Ita kanta hajiyar abin ya doketa,tana tuno yanayin ‘yartata mai hak’uri da sanyi, sai take tunanin tabbas! Za,a kwareta. Nan ta shiga kallashinta”Kiyi hakuri kinji auta, duk macen da Allah ya tsarawa mijinta zai kara aure to tabbas! sai ta shi ga zullumi, wasu ma har su kauce hanya duk saboda kishi, amma muddin kika mik’awa Allah lamuranki sai kiga komai yazo da sauki, ba nason ki tashi hankalinki, ki sanya aranki cewar Allah ne yace suyi, ki cire komai aranki ki tarbi amarya da zuciya d’aya kinji, ban da kauce hanya ,da bin hudubar shaidan . Sannan ban da kauracewa miji da maida kai gefe, kar kishi ya sanya ki hofartar da lamurraku da shi, kici gaba da abinda duk ki ke mai. Sannan adan lokutan nan da zafin kishi ke cinki, to ki iya sarrafa harshe banda fito da kowacce irin magana gatsal kinji.” Kuka ta sanya “Wallahi hajiya zuciyata kamar zata flto.” 
 Yi ta karanto hasbunallahu, ko ki karanta lahaula wala kuwwata illa billah, ko salatin annabi da sauransu kiyi ta yi,kiyi hakuri zan turo miki karima kinji.” To tace tana mai share hawaye. 
“Yanzu ki tashi kiyi duk duk abinda ya dace,banda barin jiki da kazanta, ki ci gaba da yi mai kwalliyar da kika saba, ko ya dawo karki yi wani hatsaniya, ki fawwalawa Allah, ki cigaba da duk yanda kike, an san da ciwo, to ki daure kinji auta, na sanki dajuriya da hak’uri, in zaki iyama, ki daure ki tayashi farin-cikib auren kinji auta.Wannan wani tarko ne mai kyau kinji.” Sharar hawaye kawai take tana saurararta.Kina jin me nace?.” Ina ji hajiya zan kwantata. 
“Yawwa Allah yayi miki albarka.” “Ameen” tace ta kashe wayar tana mai jin dan kwarin gwiwa. 
Hmm lallai kome zai faru

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Advertisements _____ Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *