[Advertisements⬇️]

NAYI CUDUN GARA CHAPTER 9 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 9
Washegari ranar lahadi. Ramadan ya tafi gidansu laila. Da misalin k’arfe goma na safe, ya tsaya a daidai k’ofar gidan yana k’ok’arin kiran lailar a waya, sai gata ta fito cikin d’inkin doguwar riga ta atampa, k’ugun nan ya fito das! daga sama k’irjin nan ya matsae tsam! duk saman kirjinta awaje, fuskar nan, kamar za ta gidan biki, sai uban tashin k’amshi take. Wani taku take, wanda take dosar ramadan tana murmushi ta k’arasa daidai motarsa. D’an sunkuyawa ta yi, ta zira kanta zuwa rabin saman jikinta. Kafeshi tai da idunuwanta wadda take mai wani kalar kallon da shi ya san mai ya keji. “Ban san yanzu zaka zo ba.” Lumshe ido yayi tare da kafa idonsa kan k’irjinta, yaja miyau muk’ut! “Zuwan abba ne ai.” Dariya tai ta ce, “bari na shiga nai maka iso gurin abban. Nima gidan antyna zani.” “To.” Ya fad’a kamar ya susuce ganin yanda take tafiya.Wani wawan nishi ya sanya ya lumshe ido. 
Ba ta dad’e ba, ta fito tace mai yana zuwa, ta bud’e sitting room da k’ofarta ke gaban gidan. Nan ya Fito, ta kalleshi tun daga sama har k’asa,tabbas Ramadan shine irin mijin da kowacce mace za tai fatan ta samu, a jinsin maza kam za a kira shi handsome, wani irin murmusawa tai, tare daba shi hanya ya wuce.Ya shiga sitting room d’in. Bai dad’e ba, sai ga abban ya fito, yana ganinsa ya mik’e ya gaida shi. Abban ya amsa daga gefe “shin kaine mai son Laila ko?.” Ya amsa da “K’warai kuwa abba.” “Ina so, idan da gaskiya ka ke, to ka turo manyanka.” “To inaha Allahu abba.” Bayan gama sauraren maganar Ramadan d’in ya ce “na fita.” Ramadan ya sunkuya yana yi mai adawo lafiya. Bayan tafiyar abban laila, sai ga ta ta fito tana murmushi, da alama fitar zatai. “Muje na kaiki habibaty.” Su ka flta, ya Bud’e mata gaban motar ta shiga, ya yi kwana suka bar wajen. 
Saida ya biya da ita Oasis & bakery yayi sai mata kayan lashe-lashe, sannan ya kaita har k’ofar gidan antyn nata. Ya tafi yana mai jin dad’in kasancewa da ita, babu abinda yake da buri irin yajishi tare da ita yana nink’aya da manyan abubuwa da ya ke wa kwad’ayi a jikinta Saboda zumud‘in ance ya fito, ya sanya bai koma gida ba.Ya zarce gidansu. 
Gidan nasu babban gidane irin na masu kud’in da, wanda kana gani kasan da anyi tashen kud’i. Faka motarsa ya yi, ya shige gidan, direct shashin hajiyarsa ya tafi, da ya ke shashi biyu ne, na k’anin babansa, da na babansa. Wanda duk mallakin baban Ramadan ne gidan. 
Tana zaune tana bud’e wata leda, ga Tv na aIkI amma ba murya. “Hajiyata,” ya fad’a yana mai zama agefen kujerar da ke bakin k’ofar. Kallonsa ta yi tai murmushi “daga ina haka?.” “Wallahi hajiya daga wani wuri nake.” “Ya matar takaTana k’alau.” 
K’anwarsa Zainab ce ta fito ta gaida shi, ya kalleta wai “ke yaushe za ki koma gidanki ne?.” Zumb’ura ba ki tai gaba. “Wallahi yaya ni ba zan koma ba, na gama Auren ilyasu, ba shida mutunci, ga wulakanci, da fad’a.” 
Dak’uwa hajiyar tai mata. “Kinci gidanku, mijin na ki kike gayawa haka?kar dai ki manta har yanzu da aurensa akanki, Ga ta nan dai, yakamata ka yi mata fad’a, kullum mijin na hanyar ban hak’uri ta koma, amma tak’i, kuma abayanin da ya yi mini itace ba ta da gaskiya, ba tajin maganarsa ko kad’an, wai dan wulak‘anci mijinta muddin ya kai tara awaje saita rufe k’ofa, yazo ya yi ta bugu amma ba zata bud’e ba, sai dai ya yi shashin mahaifiyarsa. Sai ka ce gidanta, Ga almubazzaranci da abinci, shi ba wani k’arfi gareshi ba. Idan ya yi magana tace tunda ya aurota dole tai abinda ta ga dama, San nan ga shi, Kasan dai tare da uwar mijinta suke, gidan nasu ba d’aya ba katanga ta raba, ya ce tana kai mata abinci, gashi tana da ciwon sugar, haka zai siyo abinda ta keci ya ce tai mata, amma ba za tai ba, sai taga idonsa. Wataran kuma idan ta yi d’in, yarinyar nan 
sai ta k’i kai mata akan laokaci, sai yunwa ta sasuk’i baiwar Allah sannan za ta mik’a, mata Uwa ai ba wasa bane, inda kara mahaiflyarsa ai ta kice, yanzu ai ba za ta so ai mini haka ba, ranar da tayi yajin ranar ne ya kamata tanaima uwarsa rashin kunya. Shi kuwa ya mareta, shine ta d’ebo jiki ta dawo gida, na rasa ina zainab ta koyi d’abiar nan, ni dai ba haka taga ina yiwa nawa mijin ba, harya bar duniya yana yabona, ni ban musu tarbiyyar haka ba.” 
Harara ya makawa zainab da ke cika. “Ni ina ganin k’awaye ke zugata hajiya, in bacin haka, ni kaina na san ba haka zainab take ba.” Kuka ta sanya. “Wallah idan bai raba mana gida da ita ba, wallahi ba zan koma ba.“ “To ai shi ke nan, saiki yi ta zama, Ga mata nan irinki birjik a gari, kinyi wa kanki har ya hak’ura da ke. Ba shi da inda zai kai mahaifiyarsa sai nan, dan haka ki ci gaba. In kinfl san ki zama k‘aramar bazawara To. Yaro mai hak‘uri shi ya ke ma hak’uri da ke amma ke ce me wannan haukan.”Da ace mugun miji kika had’u da shi, wallahi da kin gane baki da wayo. Buga kafa tai ta koma ciki. “Allah ya kyauta.” Ramadan ya fad’a yana tuno Lad’ifarsa, shi kansa ya san Lad’ifa dabance.Kenan a zaman aurensu ita ce ke hak’uri da shi? Shafa gemu ya yi ya saki d’an murmushi. Kallan hajiya ya yi ya ce: “Zan nemi mijin nata, muzanta.” “Yawwa ya yi kyau.” Hajiya dama wata magana nake tafe da ita.” “Ina jinka.” “Aure nake san k’arawa, yanzu haka ma iyayen yarinyar sun nemi da na aika.” “Me matarka take maka?.” Ta fad’a da mamaki. “Babu komai.” 
“Ban aminta ba, yarinya me kirki me mutunci da sanin yakamata, ga hak’uri, ka ce za kai mata kishiya! Ni banga dalili ba, idan kuma dan ba ta haihu bane haryanzu. To ai wannan na Allah ne, kuma lokaci ne bai ba, tunda har b’ari ta yi, Dan haka ban amince ba, haba! k0 shekara ba kai ba, ka d‘ebo zan cen wani auren. ldan ma za kai to ba yanzu ba.” “Dan Allah hajiyata ki amince, dan Allah. wallahi ba dan ba ta haihu bane zanyi, kawai ra’ayi ne, dan Allah ki amince.” “Zancen kake so, duk da na san cewa Allah ne ya halatta muku,in banda abun namiji ma haryaushe ka yi auren.” 
“Hajiya ki taimaka. Wallahi tallahi ba za ki sameni da wani abu ba, Albarkarki kawai na ke buk’ata.” “ldan kana son Albarkata, ka hak’ura ba yanzu ba, ban lamunta ba, ka tashi ka tafi.” Cikin sanyinjiki ya mik’e, ya ce mata ya tafi, ta bishi da kallo tanajinjina lamarin. Yasan halin hajiyarsa, in ta fad’i magana ta ga anata naci, ta kan sassauta, bata san damuwa. Zan jure inta binki hajiyata.” ya tafi gida duk jikinsa a sanyaye. Ga k’oshi ga kwanan yunwa. ‘ 
Washegan‘ Washegari ma haka ya koma yayi lallashin. Amma tai k’emagadau, ta ce atafau! ba yanzu zaiwa. Lad’ifa kishiya ba.Ta ce ba ta san yama k’ara zuwar mata da zancen. Hankalinsa ya yi dubun tashi,duk ya rasa sukuni,ji yake kamarya fasa ihu. 
Tana kitchen tsaye rik’e da cup, cike da had’in garin k’arin k’irji da ta dama tana sha. Wanda wannan shine shan k’arshe. Dan garin ya k’are. Ita dai sai ta ce ba ta ga wani canji ba, sai dai k’irjin nata da ya k’ara kyau, kuma shape d’insa ya dad’a Fitowa,sannan fatarta ta dad’a sulb’i, bayan haka babu wani girma da ya k’ara, kuma gashi ita girman take buk’ata, ga hips d’in ma bai k’aru ba jiya iyau tsaki tai. “Ba lalle ba dole. Haka Allah ke san ganina, sai na hak’ura.” Ta fad’a tare da ajje cup d’in, tana mai ci gaba da yanka kayan fruits, dan yin fruit salad. Muryar Ramadan taji yana kiranta. Ta yi mamakin jinsa, dan ba ta san yama dawo ba. Nan ta fita, tai mai sannu da zuwa.” Bai amsa mata ba, dan ko d’aga kai ma bai yi ya kalleta ba. Sai da yayi jim Sannan yace ya  gidan ta amsa. Lumshe ido ya yi, don ji yake zuciyarsa na tafasa, ji yakejikinsa har wani rawa -rawa yake, yana jin hukuncin hajiya yayi mai tsauri,dan ba zai iya hak’uri da laila ba. Ganin yanayinsa ya sanya ta juya kitchen, ta d’auko mai ruwan roba, da cup ta ajje agabansa, ta tsiyaya ta mik’a mai, bai musa ba ya karb’a. 
Ta koma kitchen dan k’arasa aikinta. Tana yi tana tunanin yanayinsa. Kamar akwai abinda ke damunsa. Sai da ta gama. Ta sanya a firij, Sannan ta Fita. Yana nan zaune inda ta barshi. Idonsa Arufe. Ya dafe kansa. Cikin sanyin jiki ta zauna agefensa. “Dear na menene?.” Ta fad’a da d’an fargaba kar ya gwaleta. “Ba komai ya ce mata. Ji yake kamar ya kurma ihu, yana jin wani irin tafasa aransa. 
“Ko za ka sha fruit salad yanzu na gama.” 
“Dan Allah Lad’ifa ki rabu dani bana son magana.” Ya fad’a tare da sakin tsaki. 
Sunkuyar da kai tayi asanyaye. Sun dad’e a haka, ba em, ba in,in. daga bisan ya d’ago ya Kalleta, ganin yanda ta damu ya d’auke kai. Ita kuma saita kwantar da kanta kan saman kujerar. Can ya d’ago ya kalleta saita ba shi tausayi. Sosai acting d’inta na damuwa da shi ke burgeshi idan harta  ganshi cikin b’acin rai, to itama ba ta da sakewa. Lumshe ido yayi ya k’urawa lips d’inta idanu da ke k’yallin white lips, dan kullum  ba ta rabo da sanya shi, saboda kyan da lips d’inta ke yi.Hannu ya mik’a ya janyota jikinsa kallonsa tai tana san magana. Ya d’an dad’a matsarta jikinsa. Yana kallon fuskarta.Nan ya sanya hannunsa d’aya ya shiga goga leb’en nata, lumshe ido ta yi, saboda indai yanai mata hakan, wani irin dad’i ta keji, shi kuma hakan burgeshi ya ke. Magana ta ke san yi mai, sai ji tai ya sanya bakinsa kan nata ya shiga motsasu, sun dad’e cikin yanayin Sosai, daga baya suka saki juna.Ya kuma rungumarta yana maida numfashi. 
“Mai ke damunka zauji, dan na ga mood d’inka kamar ba irin na kullum ba, fad’a mini mijina kaji.” Gefen fuskarta ya shafa yana jin zafin zuciyarsa na raguwa. “Karki damu kinji.” “To zauji, kai ta karanta hasbunallahu wani‘emal wakeel.” Girgiza kai yayi tare da ci gaba da shafar fuskarta. Yana tunanin tabbas! Da za ta san akan me ya shiga wannan hali, da ta ji ba dad’i, lalle da ta san cewa dan an hana shi yi mata kishiya ne yake cikin b’acin rai, da sai ta jiKamar ta murk’urshe shi. Kodayake yasan Rauninta akansa.Dole abin yayi sauk’i. Tabbas dole yajajircewa hajiyarsa dan yana jin ba zai iya hak’uri da laila ba. Mik’ewa yayi ya d’an zameta daga jikinsa, ya doshi hanyar samansu yana rangaji. “Zauji.” “Yadai?.” “Ina son zuwa gidan mak’ociyata Maryam wacce suka tare kusan 2weeks. So wajen uku tana zuwa ni banje ba. Yanzu ina son zuwa.” “A dawo lafiya,” ya fad’a yana mai tab‘a step na benen. ‘Lallai abinda ke damunsa babba ne, tunda har be mata k’orafi ba, in ba ta manta ba, ta sha tambayarsa za ta shiga gidan, sai ya hau ce mata baisan shige-shige.’ Murmushi ta yi. Tabbas kowanne yanayi ba ya d’orewa.”Gogaggun hijabinta ta dauka da muk’ullin Gidan. Ta kulle k’ofar falon ta flta. Gidan mai bak’in get ta dosa ta tura a hankali take takawa, harta shiga tsakar gidan.Ta tsaya a k’ofar shiga tana sallama, d’an dariya tajiyo sai ta yi sallama ba aji ba,ta kuma kwad’awa ba aji ba. Dariyar mace da namiji ta keji, inda namijin ke cewa. “Tawan karki raina basirata mana wajjen sarrafa girki, a yayinda nake university a hostel, nike dafa 
abincina,haka duk abokaina suke saramin dan duk nafisu iyawa.” Dariya ta sanya, “abban Rauda banda cika baki,ayi dai mu gani a k’asa.dan yanda naga kana wasa wuk’a, dan kawai za ka yanka doya, na san ba za a wanye lafiya ba.” Sallama ta kumai. Sai lokacin matar ta ankare, da d’an sauri ta yi hanyar k’ofar shigowa. “Lahh! Lad’ifa ashe! Kece ke ta kwad’a sallama,banji ba ne.Ai da kin shigo.” Dariya tai “haba dai.” 
Tana shiga ta ga mijin na zaune sai datsa doya yake yana wak’a yana cewa “matata ‘yar bak’a kyakkyawa mai kyawun hali.” 
Dariya maryam tai tana cewa. “Ana fa gaida kai.” Sai lokacin ya ankare da Lad’ifa, sai ya basar. Don ya san taji, nan suka gaisa da lad’ifar, maryam ta jata suka shiga falon. Baki Bayan sun gaisa, ta hau yi mata tsiyar sai yau ta ga damar zuwa. Jin kiciniyar Abban rauda a kitchen ya sanya maryam ta mik’e. “Yi hak’uri Lad’ifa ina zuwa.” Nan ta fita ta shiga ta tsaya. Ta ganshi tsaye ya tsaya ga tukunya a hannu ya d’aga kai yana tunani Dariya ta sanya. “Nawan ya dai? naga ka tsaya kana tunani,faten za kai ko da miya?” ta fad’a tana k’unshe dariya. Had’e rai yayi “zan baki mamaki.” “In gani a k’asa, ta fita tana dariya. Dariyar shima ya yi. Nan ta koma falon. “Na barki lad’ifa. Ina fama da d’an rigimar mijina ne.” Nan suka hau hira. Lad’ifa na tambayarta ina yaranta. Ta ce mata suna gidan maman mijinta su biyu ne 
mace da namiji. Kuma kiranta yayi ta tashi. Ta je ta ganshi tsaye yana gyara takalmi. “Ya haka? Na ga kana saka takalmi? Kodai kwab‘a kai, zaka gudu.”Yau dai girkina ne. Kinsan dai haka muka tsara ko? to koma gurin bak’uwarki.Kuma bana son a lek’an girki, Zogale zan tsinko 
Murmushi tai. Allah ya barmun kai mijina.” 
Ta koma tace: “Yi hak‘uri ladifa kina tajin drama ta da Abban rauda ko, wallahi haka nan muke.” “Kuma kun burgeni. Daga gani a kwai fahimtar juna atsakaninku.” 
“Ai duk wanda zaizo gidanmu,sai yace mun bashi sha’awa, wallahi a kullum ina godewa Allah, duk wanda zaizo indai oga na gida sai ya kwashi dariya, nida mai gidana akwai fahimtar juna, haka za ki ga yana taimakamin da aiki,kuma ba raini, ke ni sai nace miki Abba Raudat ya fini hakuri. Dan sau da dama ni ce mai yin lefi, sai dai sanin yanda zaman namu ya ke, da k’afafuwana zan bishi na ba shi hak‘uri awuce wajen.Wataran kuma na rik’e wuta sai dai ya hau lallashi. Bayan kuma ni ke da laifl, shi,isa da dama ake cewa wai na mallake shi, bayan kuma ba haka bane, ba boka ba malam.” ‘Wannan da Ramadan ne, ai sai na mutu dan sai dai nina bishi na bashi hak’uri‘ ta ayyana aranta. 
Kallon maryam din tai. “Wallahi na ji miki dad’i, abinda ake so kenan. Allah ya k‘ara mana zaman lafiya.” ‘ “Shi dama zaman Aure. Indai kika ga ya d’ore, to an fahimci juna,ne ana kuma hak’uri, dole sai d’aya ya fi d’aya hak’uri, in akace dukka kowa nada zafi, ai abu ya b’aci, to irin hakane za ki ga, kullum babu zama lafiya. Wallahi akwai gidan da na sani sai suyi wata guda, suna gaba da junansu. Saboda tsabar kowa najin kansa asama.” Aini maman Rauda gani nake, mace itace a k’asa, idan hakan ta faru sai ta sakko ta fara neman shiri, in dai ta ga abin ya zarce munsherin, saboda durk’usawa wada ai ba gajiyawa ba ne.” “Yawwa inda tunanin hakan ba, Wasu ma’auratan yanzun ai girman kai ne dasu, ke mace in kika san kan mijinki, ai kinsan ta yadda za ku daidaita, ni kin ganni nan idan muka d’an samu sab’ani da abban rauda, to a teburin shawara mu ke zama, ya fad’i nasa na fad’a nawa, kowa ya nuna abinda d’an uwansa ya yi wanda bai ji dad’i ba, sai ki ga kan mu tashi mun daidaita ana kwasar dariya.Amma sai ma’auratan da suka fahimci junansu.” “Amma maman Rauda akwai mazan da zaku samu sab’ani da su,wallahi ko kin nuna nadamarki ba zai sauko ba, alokacin ma zai dad’a hawa, kuma alhalin shi ne baida gaskiya, sannnan kuma ba zai bada damar ma a wani zanta ba dan sulhu.Sai lokacin da ta huce. Ai irin wannan sai ka saka musu ido,sanda ya gaji sayya sakko da kansa,a matsayinsa na mijinka, karka fasa yi mai duk wani abinda ya zama hakkinsa ne. Akwai mazan da wallahi saboda bodadd’an hali, matan su ke kasa gane inda zasu bi dasu, saboda ba ka tab‘a gane gabansu, sai dai ki ga mace in mai hak’uri ce na ta kwasar bak’in-ciki, babu yanda za tai, in ta kai gida k’ara sai de a bata hak’uri, saboda ba za a tab’a yadda mijin zai mata wani abin ba, saboda tsabar canjawar da yake, kamar salihi, sai de mace taika k’unsar bak’in-ciki, har sai lokacin da Allah zai yaye mata. 
Amma kinga in ya had’u da irinsu ‘yar gagara. To sai kiga gida ya dawo kamar gidan ‘yan dambe. Irin wannan sai kiga auren ma ya mutu, ko dad’ewa ba ai ba, to macen da namijin duk ba hak’uri.Ba kuma fahimtar juna. Dariya Lad’ifa ta sanya. “Wacece kuma ‘yar gagara?.” Kiran mijin nata ne ya katse amsar da za ta bawa Lad’ifar. Ta mik’e tare da cewar tana zuwa. 
Har ka gama ne?.” “Aa wallahi, wani waje zanje yanzu, kije ki k’arasa, nina fita.” Ya fita yana dariya. Rik’e baki tai ta ce, Ramawa kenan ka yi.” Ta fada da murmushi ta shige kitchen d’in, dariya ta dinga kwasa, ganin yanda duk ya gwamutsa komai. Nan ta gyara. Ta koma wurin Lad’ifa. Ai ina gaya miki ‘yar gagara wata mak’ociyata ce a unguwar da muka ta so, wallahi in suka fara fad’a da masifa ita da mijin kowa na ji, akan kud’in cefane sai ki ji tashin muryoyinsu, ke cikin dare ma sai kiji hargowarsu, wataran mijin ya kileta,kiji taita ihu tana zaginsa Da yake katangarmu d’aya ce komai fa anaji. Wataran yana dukanta tana ramawa, ga bakinta baya shiru yana zaginta tana ramawa. Tun abin na bawa ‘yan unguwa mamaki ,har ya daina,kuma duk itace da bata da san zaman lafia, dan yan unguwa ma fad’a take, dasu ga yaransu har hud’u, ko tai yaji sai ya dawo da ita, dan sun riga sun saba da wannnan karnukancin, in har ba su yi ba, ba sajin dad’i,shi’isa 
aka sanyawa matar ‘yar gagara.” Cab! Lalle ta ci sunanta.Sai ka ce auren soja kai tsaye ni tsaye.” “Wannan ai sun wuce nan.“ “To Allah ya kyauta, ya bamu juriya da hak’uri. “Ameen.” “Ni bari na tafl.” “Ki bani lambarki ko whatsap mu nayi. Cewar maryam dake mik’ewa. “Eyya! maman Rauda,wayata ta lalace, amma inna sai sabuwa zan aiko miki.” Nan sukai sallama maryam nayi mata godiya. lta ko Lad’ifa, tana tafiya tana tuna yanayin rayuwar maryam da mijinta. Ji take dama ace haka suke ita da Ramadan, dan tana so ta ga tana wasa da dariya da mijinta, suna hira cikin nishad’i.Amma babu wannan. Dan mijin nata yana daga cikin maza masu wuyar sha’ani. Jinjina kai ta yi. Dama kowa da irinsa. Hakan ma ta godewa Allah.‘ 
Bayan kwana biyu. 
$unday 11:30pm 
“Zauji, yau kimanin sati biyu fa da nai maka zencen kayan shafa na sun k’are, kullum kace zaka sayo amma har yanzu.” 
“Wai me yasanya har abada baki da d’aga k’afa ne? Ko mai ke kinfi sonsa cikin gaggawa. Ce miki akai ba zan sayo bane, abubuwane suke shamin kai.” Allah ya ba ka hak’uri,” ta fad’a jiki asanyaye. Tsaki ya sanya. “Ga 15k nan kije supermarket ko mall ki sayo. Kuma bana san ki shiga 
kasuwa.” “Hmm! kawai ta ce, a cikin zuciyarta, ‘dama ta san k’arshen abin kenan ya bata kud’i ta sayo da kanta, har abada shi dai baya maida komai nata da muhimmanci’ “Shi kenan na gode.” “Zanje jifatu na sayo anjima.” “To Allah ya kaimu, ya fad’a tare da dad’a saita karin hularsa ya fesa turare, ya yi mata sallama ya fice daga gidan. Dan direct gidan k’anwar mamansa ya tafl, dan yana so ta zo ta taushi hajiyar tasa, tanajin shawararta. Ko a samu ta yarda da aurensa da lailarsa. 
K’arfe hud’u, bayan ta yi sallah ta shirya cikin atampa kalar ruwan hoda da ratsin bak’i, ta sanya hijab ruwan hoda ta d’au jaka bak’a ta tafl. Adaidai k’ofar jifatu store d’an adaidaita sahun ya ajjeta, ta shiga direct wajen mayukan ta shiga dubawa, duk inda za ta duba bata samun set, sai d’ai d’ai, kuma ita tafi san set d’in man complete . Tunani kawai ta yi da ta fita kawai taje sahad, hakan kuwa akai, nan ta fita, ta kuma tarar adaidata sahun ya kaita sahad store. Anan ma dai ba duka saitin bane, amma sai dai sabulu ne kawai babu, nan ta d’auka ta sanya a kwando, sai ta yi tunanin sayan wani turare da ta gani wanda hajiyarta ke sansa. Zata kai mata. Haka ta tura ta tafi b’angaren.Turare 
Tana cikin dubawa, d’agowar da za tai idonta ya sauka akan Ramadan, rik’e da kwando, ga budurwa agefsa tana bashi yana sanya wa aciki, sai kallonta ya ke yana saita fuskarsa daidai wuyanta yana murmushi. Wani irin k‘ara cikinta taji ya yi, take taji kanta na sarawa idonta ya ciko da kwallah. Kishi ta ji kamarza tayi hauka. Bata tab’ajin b’acin rai irin na yau ba. Da ace ta iya fad’a da sai ta koyawa budurwar hankali. Amma ba za tai ba. Saboda darajar aurenta. Mamaki ya sanya ta sakin kwandonta, wanda hakan yasa Ramadan ya waigo suka hada ido, lokacin Laila ta yi gaba. take ya diririce. Ido cikin ido suke kallon juna. Wani irin kallo ta ke mai. Wanda ya sanya Ramadan duk ya dad’a dirircewa. Dan a iya zamansa da ita, bai tab’a ganin irin b’acin ran da ya hanga a idanuwanta ba, irin na yau. Tana ganin hakan, ta d’au kwandon ko gabanta bata gani ta yi wajen counting ta ajje, da ya ke ba wasu agabanta akai mata da wuri, ta bada kud’in ta fita da sauri tana kukan zuci. Shi ko Ramadan hankalinsa ne ya tashi, ya ce da laila yana zuwa, nan ya ajje da sauri yabi bayan Lad’ifa. Yana kiranta. Kafin ya k’arasa wajen har d‘an adaidaitan yaja. Sai kawai ya yi turus tare da shafa gefan hab’arsa.K’irjinsa na fat-fat. To fah! k’ak’a, k’ara k’ak’a koya zasu wanye? Ku dai cigaba da bibiyaryar wannan kayataccen book din 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]