[Advertisements⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 9 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 9
Still hannunsa na rik’e da nata ya rik’e sai kallon fuskarta yake dan ba k’aramin kyau kwalliyar tata tayi mai ba, INDO kuma sai k’ok’arin ture mai hannunsa take tana hawaye murya k’asa-k’asa kamar munafiki yake mata magana yace. “What’s your name make up artist..?!” INDO tayi shiru sai tasa ka hijjab d’inta ta sharo hawayen fuskarta duk bak’in kwallin da tayi kwalliya ya wanke hijjabin daga gaba Abubakar ya kalleta sosai shi har lokacin begane taba domin be taGa ganinta tsab-tsab kamar yau ba ya kuma cewa. “Baby ya sunanki ne.?!” Sai a lokacin lNDo ta fahimta ya kalleta ya kuma cewa, “kinga kin goge kwalliyan naki da kuka ki dena kinji k0? Ya sunanki??” Ta share majina da bayan hannunta wanda be rik’e ba ai yana gani yayi saurin sakar mata d’ayan hannun ita kuma ta matsa baya tare da cewa cikin kuka. “INDO malam Hamza.“ Abubakar ya d’an zaro ido waje kad’an kafin yace. Zonan gurin.” Ya nuna mata inda yake son ta tsaya da k’afarsa, a hankali taje gurin ta tsaya sai dai idanunta nakan tebur din da malam Sadeeq ya ajiye kayan kyautar da zai bada. Tsaye tayi mai k’ik‘am sam hankalinta baya kansa shi kuma ya kalleta yana murmushi yace. “Woww sunan Mama na gareki, toh amma ba zaki tsugunna ba kika min k’erere..?!” Da sauri ta tsuguna still fuskarta na wajan kayan, ganin bashi take kallo ba yasa shi maida kujerar sa saitin da idanta yake gurin tayi saurin kallansa ya tsuke fuska yace. “Menene baki yi ba aka fito dake?!” Ta cukwai-kuye hannunta tun kafin ta bashi ansa dan tasan mugune a hankali tana turo baki daya sha bakin kwalli a leban tace. 
“Wallahi nayi komai, kawai farce na manta ban cire ba shine malam Sadeeq yace na fito kuma wallahi malam…” Ya zabga mata harara tayi saurin toshe bakinta da hijjab kafin taga ya dena tace. “Kayi hakuri dakta Habubakar mantawa na keyi kace ba sunanka malam ba, amma wallahi nayi niyyar yankewa niko dan naciyo atamfa amma duk saina manta hef (shaf)..” “Ohh muga farcan naki..” Ta fito dashi yasha lalle a yatsun ta nuna mai, hannu yasa ya janyo nata yana kallah murya sanyaye INDO tace mai. “Dan Allah Dacta Habubakar kace ya bani ni yanzu ma zan iya cire farcen, dan iyayanka kace ya bani dan Allah kaji..?!” Sadeeq ne yazo gurin ya kalli d’an uwan nasa rik’e da hannun INDO hakan ya bashi matuk’ar mamaki da al‘ajabi cikin sauri Sadeeq ya zare hannun INdon daga na Abubakar cikin harshen turanci Sadeeq yake mai magana cewa. 
“Twinnie why na?am i dreaming or are you really the one holding a village girl hands,and if you have forgotten about it then I haven’t ,this villagers are cruel,l don’t want them to think something else in their mind ..This is so not you” Cikin ko’a jikinsa abubkhr ya daga kafada sannan yafara magana, “Habba twinnie sunan Momcy gareta fa shi yasa, gashi kuma tayi kwalliya irin wadda nake so that’s y kaga ina iya rik’e hand’s nata.” Mtwww “inajin baka ganeta bane shi yasa kake sakar mata fuska, toh bari na tuna maka kowa cece lNDo malam Hamza,ce wannan me satar amsar me cizon maza nasan yanzu ka harbo ta.” Oh”Really my twinnie? Abubakar ya fad’a yana sake maida kallonsa fuskar lndo, kwakwalwarsa kuma tana sake hasaso mai lakacin daya kamata ta duk’ufa tana kwafar note dan sam koda ta kwafo ma bagurin da aka tambaya bane, ya kuma kallon Sadeeq 
cikin mamaki yace “Gaskiya my twinnie kayi k’ok’ari indai haka ne. Ashe k’azan tace duk ta maidasu mahaukata Gaskia I’m sure nan gaba za’a sha mamaki indai suka d’ore da haka za’aji dad’i sosai.” 
Kafarsa yaji ana girgizawa hakan yasashi saurin kallon kafar indo ce takemai
alamar magiya tana nuna mai ya samo mata kyauta kota meye Sadeeq dake rike da kayan zai bawa wad’anda suka ci ya kalli Abubakar dake kallon lNdo kawai yaja tsaki sabida takaici. lNdo kam sai nunawa Abubakar malam Sadeeq takeyi alamar be zabo mataba zasu k’are yayi dariya cikin zuciyarsa ya kalli sauran masu kuskuran yace.”Kuzo nan muyi photo daku.” Suna jin haka suka ruga bayansa suka jeru amma sam lNdo batayi gigin zuwa ba hankalin ta yana wajan malam Saseeq dayake ta rabo zuciyar ta tamkar ta fito tsabar fargaban karsu k’are. “Humaira zo mana ayi dake.” Abubakar ya fad’a yana kallon Indo , ita kuwa bata masan da ita yake ba tanaji tana gani har malam Sadeeq ya kammala bada kyautukan taji wata muguwar tsanarsa tundaga k’asan zuciyarta ya game da ilahirin jinin jikinta tayi ta zagba mai harara bemasan tanayi ba yana can yana sake yiwa wad’anda sukaci kyautar nasiha da kuma muhimmancin tsabta da Ilimi. “Kuje kuma ku zauna kowa yaje gida yayi karatu ranar Monday zanyi muku test duk wanda ya fad’i ni nasan irin hukuncin dazan d’auka akansa kunajina ko?!” 
Malam Sadeeq ya fad’a bayan yaga yau twinnie d’in nasa da mutunci ya shigo, duk ‘yan ajin suka ce “OK uncle.” Dayake yana k’ara d’an wayar dasu, amma INdo data tashi sai da ta d’auki ledar littattafanta ta faki idonsu duk da cewar Abubakar nason yayi mata photo da kwalliyar ta yana can yana tambayar Sadeeq mezai iya bata koda ba babba bane ba sukaji tana cewa. 
“Baza’ayo karatun tess (test) d’in ba, kai idanma kun sake ganina a makarantar nan dan Allah ku soya ni. Wallahi malam Sadeeq yayi karya kuma ance babba me karya d’an wuta ne gobe k‘iyama yana kusa da fir’auna, Allah ya sakamin sabida na kashe kud’ina garin yin kunhi da gyara kambas d’ina sai Allah ya saka min. Yo dan baka bani atamfar ba seme, nima Inna ta zata sai min ai sallah ta kusa.”ji tayi an riketa ta baya tsananin tsoro da tashin hankali tayi k’ok’arin juyawa taga waye sai taga malama Murja ce ta cafketa tare da tura ta cikin ajin,  tana zuwa ne da yake period d’inta ya shiga sai taji irin rashin kunyar da takewa malamin hakan yasa tayi shiru sai data kai k’arshe zata gudu tayi saurin kamata. Tsananin mamakinta suka kama Abubakar, sai yanzu ya kuma tabbatar da cewa itace ya tashi a fusace yayi kanta jin yadda take gayawa twinnie d’in nasa magana. Sadeeq ne yayi saurin taresa yana kad’a mai kai alamar karya doketa, yana wani irin numfashi ya ture 
hannun Sadeeq d’in daga kafad’arsa yana cewa. “Ka rabu dani Sadeeq bakaji yadda take had’aka zama da fir’auna bane, barni naci uban shegiyar yarinyar nan da har ina tausaya mata ashe batada mutunci haryanzu.” “A’a twinnie barni da ita, kayi hakuri ka kwantar da ranka. Malama na gode da gudun mawarki, ke kuma zonan…” Sadeeq ya fad’a yana damk’o hannunta Abubakar kuwa jiyake tamkarya ya hadiye zuciya sabida bacin rai. Fita yayi da ita sai ihu take musu har suka k’arasa cikin staff room ya kalleta yace. “Kama kunnanki.” “Dan Allah malam kuyi hakuri.“ Babu wanda ya kulata sai dai duk malaman cikin staff room d’in saida suka bada shedar rashin kunyar INdo, ganin babu mebada hakuri ne yasa ta sunkuya ta zura hannunta tana nishi tana cewa “malam wallahi hannuna baya kaiwa abakacin sa kace nayi nibdom (kneel down) kaji.” 
Jiyosu ma tayi suna hira babu wanda ya kulata dan yau takaisu bango, tun tana magiya har tayi shiru. Ta dad’e tana kamun kunnen kawai suka ganta ta fad’i k’asa Abubakar dake kusa da gefenta besan lokacin daya kai hannu zai tarota ba amma saida tayi k’asan, ashe baccine ya kamata, kuma duk da fad’uwar da tayi hakan besa ta tashi ba saima zarcewa da tayi tafara sauke munshari. “Twinnie mu wuce tunda ka gama.” Beh jira cewar sa baya k’arasa inda INdo take kwance sai uban munshari takeyi tamkar wata babbar mata a hankali ya dinga k’iran sunanta amma inah k0 motsawa batayi ba,hakan yasa Sadeeq mik’ewa ya d’auki dorina yana zuwa ya tsula mata a baya. A razane ta mik’e ta rarumi Abubakar dake tsaye kusa da ita tana cewa. “Wayo Allah atamfata ce.” 
Sak’e tsula mata yayi tayi saurin sakin Abubakar tayi k’ark’ashin tebur d’in malam yahaya tana kuka tana sosa gurin cikin kuka take bashi hakuri yayin da shi kuma Abubakar ya flta daga cikin staff room d’in. Sai da wasu malamai suka bawa malam Sadeeq hakuri sannan aka ce taje ta tsugunna ta bashi hakuri tayi sannan ya hakuri yace kuma duk sanda ta kuma yin fashin zuwa makaranta sai yasa ankamota yayi mata duka tace toh. Fitowa yayi amma bega Abubakar d’inba har ya fita gate babu bare alamun motarsa, sosai Sadeeq yayi mamaki sai ya nufi gidan shima amma abin mamaki bako motarsa a gurin hakan yasa shi kiran wayarsa aka sanar mai cewar a rufe take, mamaki ya kuma sark’e Sadeeq. Yana tsaye a gurin har su INDO suka wuce suna gulmarsa be kulasu ba. Shi kuwa Abubakar yana fita motarsa ya hau yakama hanyar gida, haka kawai yau yaji baya son jin kukan INDO zuciyarsa harzafi take mai duk kuwa da cewar yasan itace batada kunya amma ya rasa dalili, tunda ya taho tunaninta yakeyi yayi-yayi ya halasto qibd’iya ya kasa sai dai INDO da kamanninta ya buga sitiyarin motarsa yafi sau ashirin harya k’arasa gida. Yana shiga yaji Maman su na cewa. 
“Kajishi can najiyo tsayuwar motarsa da alama ya dawo. Toh shikenan ‘biyu kyautar Allah kaima Allah yayi maka albarka.” Sai da ya bari ta kashe dan yasan da Sadeeq takeyin wayar sannan ya shiga cikin gidan nasu bakinsa d’auke da sallama…. Kuyi hakuri da wannan, kunsan bawa duk yadda yaso yayi abu idan Allah bebashi dama DA iko ba toh babu abinda zai iya yi a rayuwarsa. Nagode luv you all._ 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]