[Advertisements⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 18 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 18
‘Bayan wasu shekaru.‘ 
Gaba daya an kammala yin komai ansa rana da Fateemah ta kammala school za’ayi dan haka ginin su kawai suke yi. Gidane me kyawun gaske kowanne yake ginawa kowa kuma da yadda yake son abunsa. Gidan Abubakar yafi tsaruwa nesa ba kusa ba yafi na Sadeeq sosai kasan cewar shi yana son ya samu wani acan inda yake business dinsa idan sunje da matarsa babu wani fargaba dama yanada gidanshi dan haka biyu ya raba sabanin Abubakar dashi a abujan ma yana da katan gidaa quarters din asibitin da yake aiki. 
Fateema na shekarar karshe domin sauran ‘yan watanni ta kammala, yayin da a Gangaran INdo itama sai hamdala domin zata iya rubuta wasu kalmomin harma ta rubuta wasika da Hausa koda ajimi kuma ta fara iya yawancin surorin alkur’ani me girma an samu cigaba sosai. 
Kyawunta ya fito ta waye ta gage kai in baka cika ishasshe bama bata kulaka bare harkuyi hudda tare. Zaune malam Hamza da Inna suka suna tattaunawa akan yadda zasu yi da kayan dakin lNdo gashi INdo tace harda gararta zata tafi batason abin gori. “Toh malam ya zamu yi, iya abinda Allah ya bamu shi zamu yi mata ai suma sunsan damu dasu ba daya bane sun fimu ta ko’ina.” 
“Hakane Maryamu yanzu dai dole naje na siyar da gonata dake can saye guda daya, sannan na siyar da shanuna guda biyu sai ayi mata amfani da kudin nasan dai bazamu yi mata irin yadda take so ba saidai ai munyi kokari kuma ma wallahi dandai Dacta Habu zata aura hiyasa zanyi mata duk abinda nasan Zan iya sabida yaron nan dan kirki ne, duk sanda na kalli katangar nan naganta da suminti sai naji dadi.” “Hakane kam malam toh sai a siyar din Allah ya bada lada.”Malam Hamza yace “Amin.” 
Kwana hudu dayin zancen ya dauki abokinsa malam kallah suka tafi Saye bayan rabansa da zuwa kusan shekaru goma sha biyar kenan. Sun gaisa da kowa saidai tsakaninsa da yakumbo tsahare babu ko kallon banza, bayan an gayawa sarkin shanu aka yi cinikin shanun malam Hamza wanda shine ya baiwa yakumbo talatu su yace idan sun haihu ya barmata saidai duk lokacin da yake da bukata toh zai dawo ya karbi guda biyu. Dubu talatin-talatin aka siye duk daya nan aka bawa malam Hamza kudinsa dubu sittin, aka koma kan gona wani mutum ya siya dubu cassa’in malam Hamza ya karbo kudin suka dawo gida da dubu dari da Hamsin cas. 
Hadawa akayi da kudin nagani inaso dinta aka hada suka zama dari biyu cif malam Hamza yace aje ayi cinikin gado madubi da wardrobe, nan aka nuna musu kudadan ko wanne babu ma na kasa da dubu dari a cikin irin wanda INdo ta nuna tana so. 
Na dubu dari da hamsin suka zabar mata wata yayar Inna ce da take aure a dawakin tofa sukaje suka tayo. Sai kudin gudun mawar da aka dinga kawo musu dan su kauye basai ranar biki suke bada gudunmawa ba. Haka dame dari biyu dubu biyu gashinan dai aka dinga bawa inna da malam Hamza suka hade ya basu dubu hamsin da biyar da naira ashirin. Suka had’e da ragowar hamsin dinnan aka hada dari na kujeru gaskiya INdo taci Kudi wai…! 
Sai kuma masu kawo kayan amfani na kitchen me kofi , me tasa, me plate, gashi nan dai suma aka hada Inna tasa aka siyar da gonarta itama sai aka sissiya abubuwan da babu a kitchen din. 
Gidan su Fateema kuwa ko shirin basu farayi ba sabida su ba wani case karatunta kawai takeyi hankali kwance. Bangaren mazan kuwa, kayan lefe ake hadawa komai iri daya Mama tace azuba colors ne kawai suke ban-bantawa da kuma size domin lNdo tafi Fateemah jiki ita kuma Fateemah tafi INdo haske da tsawo. 
Akwatuna bakwai-bakwai akayi musu kowacce shakare da kaya domin mazajen ba karamin kokari suka yi ba sun kashe Kudi over. 
Ranar dasu Fateema sukayi graduation a ranar aka kai kaya murna biyu ta hadar mata. 
‘Bangaran lNdo ma ankai kayan tana gidan Rukayya kwance tana waya da Abubakar, cikin salon make muryar data koyo wajan su Zainab da Hadiza tace mai. “My key wai me kakeyi ne yanzu?!” 
“Ina office a zaune tare da frame dinki inata kallonki.” “Yeeee naji dadi nima ka tambaye ni..” “Habibty mekike yi yanzu..?” Ya fad‘a kamar yana cikin maye, dariya INdo tayi me sauti sannan tace. “Ni tunaninka nakeyi dan Allah yauhe zaka dawo.?l” Dariya yayi tare da cewa, “Sai ending din month dinnan, ya mekika tanadar min?!” Tace “kana nufin ending karhen Month watan nan k0?! 
“Eh haka nake nufi madam.” “Toh kenan kana num ankusa biki.” 
Yace “Eh amma ai Sadeeq yana nan ba kuma zai koma ba sai an gama biki kokina bukatar wani abun nasa ya aiko miki dashi ne?!” INdo ta kuma gyara kwanciya domin yarinyar ta iya karbar sakwan love tace. “Eh akwai abinda nakeso.” “Toh madam menene shi..?!” Tace cikin jan numfashi “Kai nake son gani.” 
Abubakar saida tsigar jikinsa ya tashi yarrrr ya dora kafarsa kan table tare da jin gina da jikin kujerar dayake kai, hannu yasa a kirjinsa yana dan bubbugawa tsawon wani lokaci sannan yace mata. 
“Sorry Habibty da ace da yadda zanyi danayi na taho, saidai na riga na karbi aikin wani abokina inason idan na taho ya karbi nawa sabida idan munyi aure bazan dawo da wuri ba sai na gama shan amarci na.” INdo ta guntse bakijin abinda ya fada sannan taji yace. 
“Ko kina son da an daura aure na dawo ne.” Da sauri tace “A’a bana son ka koma.” “Toh ki tanadar min kanki a duk ranar da aka kawoki gidana.” Kit..yaji ta yanke wayar ya sauke yana kallon screen din yana murmushi bata san wannan zantuttukan baya manta ranar daya fara gaya mata irin maganganun tace mai ita ba ‘yar iska bace. Ranar yaci dariya kamar cikin sa zaiyi ciwo, bebi kiran ba yaci gaba da aikinsa yana ta murmushi INdo na bashi laugh yasan idan sukayi aure zai dinga shan dariya. INdo kuwa bata koma gida ba sai da tayi magariba sannan ta koma gida, wayyo Allah dataga irin akwatinan zamanin da Abubakar ya kawo mata bata san lokacin data fad’a jikin Inna ta rushe da kuka ba. Inna sai faman lallashi takeyi Sagiru da shehu suna kallon kayan kowa sai nuna abinda yake sukeyi da kyar tayi shiru aka cigaba da kallon kaya Inna ta nuna mata dubu hamsin tace, Gashi ‘yarnan sunce kudin dinki ne.” 
Karba INdo tayi tana godiya, tana gama kallon kayan suka rufe ta fita waje. Unguwar su kezy taje ta samesu zaune sai zukar sugari sukeyi ta toshe hanci tana musu magana. “Kai kezy aji tsoran Allah dai za’a mutu.” Tayi maganar tana sake toshe hanci, jazuli yace. 
“Kefa ‘yar rainin hankalice dan kinzama babbar yarinya shine zaki dinga yi mana kallon equal”Kai masifaffe ni gurinku nazo, kunsan ankawo kayan aurena, toh sonake kuzo gida kuyi gadi Allah ma yace tashi intemake ka, idan ma kune barayin nidai kuzo gobe he’in baku dubu goma.” “Kai hajiya INdo kin zama hajjaju fa Allah.” Kezy ya fada tace “Eh koma dai meye nidai kuyi min.” “Karki damu zamuci uwar hegen dazaiyi gigin zuwa.” “Toh nagode.” Tafad’a ta wuce ta shiga gidan su Sahura, ta dade kafin ta koma gida. Haka akayi suka yi gadin gidan Allah kuma ya temakesu babu wanda yaje. Washe gari ta basu 10k suka tafi, ta ciro atamfa daya ta bawa Nafeesa tayi ta murna sannan ta ciro tirmi biyar ta bawa Inna tace tasa da biki. Inna tace a’a itama INdo ta dage tace tabar mata. Cikin shaddojinta kuma ta zabo wata ash tace abawa babanta, gaskiya INdo batada kyashi wajan bawa iyaye abunta amma fur taki bawa Sagiru yayi mitar yayi magiyar tace bazata bayar ba yana da kudi. Aikuwa yaji haushi duk abinda tasashi bayayi mata shima.Kowanne bangare shiri akeyi ta kowanne side, Gangaran Fateema anje an fara jere haka itama lNdo an fara, saidai tsarin gidan yasa bazasu iya cewa sai sun saka mata komai ba 
domin basu da halin yin hakan. lya dakinta kawai suka sawa kaya sai parlon farko dnning area kuwa kokallansa basuyi ba gashi gidan yayi masifar yin kyau domin yafl na Sadeeq had’uwa. 
Ana sauran sati daya biki Abubakarya dawo kano, gidan su harya fara cika da bakin nesa sai tsiya suke mai da masu nuna cewarya auro ‘yar talakawa ga gida har gida amma babu kaya. Sharesu yayi yana yin wanka Sadeeq yazo suka fita. Gidan Sadeeq suka fara zuwa sai sambarka domin kayane nagani na fada aka zubawa Fateema, royal ne furniture din sannan babu inda ba,a bashi haqqinsa ba sannan suka wuce gidan Abubakar babu abinda yaji aransa na bacin rai suna shiga cikin bedroom din INdo ya fad’a kan gado katifar ta lotsa da alama sakance kuma ba vita form bace ya ware hannuwa yana cewa Sadeeq. twinnie remain 6days na kwana anan nida Humairah tah.” 
Sadeeq yayi murmushi tare da girgiza kai gaba daya INdo ta rikita mai dan uwa, shi har yau ya kasa manta INdon  domin duk sanda zai tuno ta a kazamarta yake haskilota har tausayin Abubakar yake idan yaga yana wani abun dominta.Cikin kwanaki uku Abubakar yasa aka sake zuba mai wasu kawatattun furniture’s a inda ba’a zuba ba aka sanya Iabulaye da site na dining area ba tare daya sanar da kowa ba sai Sadeeq domin cikin dare akaje akasa komai harda plasma TV. Koda dangin INdo suka dawo gidan ba karamin mamaki suka yiba. 
Ana gobe kamu/yini da daurin aure…. 
Hmm ga indo malam hamza ga dacta habubakar ta bakin mutuniyar

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]