[Advertisements⬇️]

HARSASHEN SO CHAPTER 9 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HARSASHEN SO
CHAPTER 9
Murmushi mai napep yayi sannan yaja suka fara tafiya, banda faduwa babu abinda gabanta yakeyi sai kuma tsoro daya fito kirikiri a jikinta dan har kyarma jikinta yakeyi, Cikin rawar murya tace ma mai napep don Allah zan samu aron gida da zan zauna a ta wurin nan kuwa? 
Saida yadan jinjina maganar sannan yace gaskiya babu aron gida saidai ki kama haya, menene haya? shalele ta tambayeshi! Malam baka san haya ba? Shalele ai ko na sani ina san karin bayani ne kasan matambayi baya bata ai ko? Murmushi mai napep yayi sannan yace ai ina tunanin koda ga kasar waje kazo kasan haya bare ma naganka bakayi kama da “yan binni, Ba Murmushi shalele tayi sannan tace gaskiya ne, amma don Allah kayi hakuri ka samanin ai ina da kudi sosai a jiki …….. Jin mai napep ya taka wani gigitaccen burki yasa “yan cikinta kadawa harda wani dan autan fitsari ya biyo daga baya, shine dalilin daya hanata karasa maganar da zatayi, Wani irin murdeden soja ne ya tare hanya kafarsa ya dora a ta gaban napep dib idanuwanshi kamar anyi musu watsin wuta, wani irin kallo yakeyi wa shalele wanda yasa shalele jikinta ya fara kyarma sosai “yan guntayen hawaye suka fara biyo idonta, ltama kallonsa takeyi amma ta kasa gano a ina ta sansa kodai ba komai ta taba ganinsa koda a cikin barci ne, tana wannan nazarin taga ya zagayo daidai inda take hannunsa ya mika ya fizgota tare dayi mata wata irin wurwura harsai data fadi ta goce hannu, 
Da sauri ta mike tsaye tare da gyara lullubin kanta, cikin dakiya tace bawan Allah me nayi maka haka ne? Daga munayin tafiyarmu ai kaga bamuyi maka magana ba, mai napep ne ya fito da sauri tare da durkusawa yace mai gida kayi hakuri ba nan zamu tsaya ba wucewa zamuyi, Kallon mai napep yayi sannan yace kai zaka iy komawa ciki, ita kuma tasan laiflnta, kallon shalele yayi sannan yace shekara biyar data wuce lokacin kina dan matashin namiji kina maza a lokacin kafin ki dawo mata kin tuna abinda kikai min a cikin dajin garinku daga nazo zan mayar dake gida? Wata irin mummunar faduwar gaba shalele taji tare da zaro kyawawan idanuwanta tana kallon sojan cikin kidimawa tace kayi hakuri yanzun na daina neman tashin hankali a hankali ta matsa kusa dashi tana rike da hannunta da yake mata ciwo ta rike kafarsa da hannun daya hannun har kyarma yakeyi saboda azabar da takeji a cikin jikinta har wuri biyu! Kayi hakuri don girman Allah ka yafemin dan san da kakeyiwa mahaifanka idan har ka sake samuna da wani laifi wanda bai maka ba ka cire min kaina dama na bawa mahaifina lumfashina ka kaini gabansa idan ya cire lumfashin kai kuma ka dauki kaina na baka gangar jikina kuma nayi alkawarinta, hannuwanta suna kyarma ta hadasu wuri daya cikin kuka tace don girman Allah kabarni badan halina ba! Kallon shalele yayi sosai sannan yace to miyasa kika fito a namiji daga farko lokacin da mai gidana yazo dake daga garinku? Cikin rawar murya tace yanzun mace kake kallona ko namiji? Kallonta sojan yayi sosai sannan yace shiga ce kikayi rabi ta mata rabi ta maza, 
Ajiyar zuciya shalele tayi a ranta tace zan raba maka hankali kuwa zan shige maka harsai na saba maka zan rika bace maka kamar fatalwa zan badda maka tunani harsai na mayar dakal’ kamar wani zararre, murmushi tayi sannan ta sake kallonsa tace “yar labai yanzun bana iya cewa komai amma kamin uzuri idan na samu dawowa daga hayyacina zanzo na warware maka komai, naji bugun maza harma na manta abinda ya kawoni birni,
Dariya yayi sosai jin an yabasa,jakarta ta bude ta dibo kudi ba tare data kirga ba ta mika masa tana mai cewa ka siyawa kannena sweet ai bansan zamu hadu ba dana taho maka da tsaraba kana da mutunci “yar labai, murmushin sojan yayi sannan ya anshi kudin yana mai cewa tou idan kin dawo kice a kira miki ‘MAI NASARA’ godiya shalele tayi shi kuma ya wuce dan shigewa cikin gidan Mubarak dama daga wani wuri yake yaga shalele ya tsaya dan bazai manta fuskarta ba har abadan duniya! Juya kallonta tayi wurin mai napep tace muje ko? Jinjina kansa yayi sannan ya shiga cikin napep din itama shiga tayi sannan ta sake kallon hannunta tace hannuna yana min ciwo, 
Bai mata magana ba yaja napep dinsa taflya mai nisa sukayi har sukaje wurin kofar wani gida sannan yayi parking, 
Fita yayi daga napep din ya shiga cikin gidan ya dade sosai sannan ya dawo, saida ya shiga napep din ya zauna sannan ya juya yana kallon shalele, magana ya farayi cewa, na sama miki ko ince ka gida, amma kafin nan ina san sanin waye kai mace ne ko namiji? Murmushi shalele tayi da gefen bakinta sannan tace ni mace ce! 
Alhamdulillah, ni suna na Ahmad amma anfi sani na da bobo wannan gida da kika gani gidane na haya wanda ya tara yawan mutane sosai akwai maza akwai mata akwai kabilu da dama idan har kika iya allonki tou kin zauna lafiya, duk watan duniya abinda ake biya daki daya 15k ne shin hakan yayi miki ko kuwa? Yayi min, amma kafin nan ka sama min maganin ciwon hannunnan nawa, tou ba damuwa,jan napep in yayi suka taf’l, wurin wani dan tsoho yakaita aka mata kamu, sannan suka dawo gida, ta bashi 5k nashi da ta mishi alkawari sannan kuma ta bashi kudin hayar dakin data kama, Haka suka shiga ciki yana gaba tana baya har suka isa cikin gidan, a kofar dakin shalele ya tsaya sannan ya mika mata makullin dakinta fatan alkairi yayi mata sannan ya juya yayi tafiyarsa abunsa, Cikin natsuwa ta bude dakin ta shiga kullewa tayi bayan ta shiga, bin dakin tayi da kallo, dan madaidaicin palo ne wanda babu komai a cikinsa sai sumunti daya sha, a gefe daya 
kuma wani dan karamin kafet ne, wata kofa ta gani dan haka tabita, Bedroom ne sai toilet a ciki, palo ta dawo sai kuma taga wata kofa daban dan haka tabi kofar a tunaninta daki ne sai taga ashe madafar abinci ne! ’Daukar kafet in tayi ta mayar dashi a can cikin dakin bacci, kayama ta cire ta dora akan kafet din abinda tayi lullubi dashi ta daura ta shiga tayi wanka, bayan ta fito ta saka kayanta,zama tayi tare da tallabe kanta da dukan hannayenta! Bayan wani lokaci kuma ta jawo jakarta ta bude har yanzun akwai kudi masu yawa sosai wanda bata iya bazata iya kirgawa,ba ajiyar zuciya tayi tare da kwantawa ta fara lissafin da babu, 
Da gudu ta flto da wata irin shareriyarwuka har sheki wukar takeyi ga kam ga tsini na tashin hankali, da sauri Mubarak ya fito da towel daure a kugunsa yana kiran sunan khadija, Amma ko saurarensa batayi ba bare ma tasan yanayi, cikin fushi yace na rantse da girman Allah idan har kika kasheta wallahi da hannuna zan kashe ki babu wani abinda ya dameni dake mata ta ce, yana fadin haka ya juya da sauri ya koma ciki, Jin furincin Mubarak yasa ta hakura tare da dawowa ta zauna a saman kujera tana mai cewa kuma wallahi ko ba yau ba saina kashe ta! Mubarak yana komawa dakinsa kayansa ya saka masu matukar burgewa sannan ya fito, a palo ya samu khadija zaune ko inda take bai kalla ba ya fita, yana fita a kofar parlon yaga 
matar zaune rungume da wata “yar karamar yarinya wadda bazata wuce shekaru 4 ba, Duk wani soja dake wurin ya girmama shi , kallon matar Mubarak yayi yace baiwarAllah ya akayi ne? Cikin kuka ta kalli Mubarak tace ka tausayamin ka rufamin asiri yarinyata ke fama da cutar cancer ta budewa Mubarak lullubin da tayiwa yarinyar a idonta, innalillahi wa”inna ilaihir raji”un Mubarak ya fada tare da kauda idonsa cikin yanayin tausayi, 
Clkln kuka matar taci  gaba da cewa Ina da wata yarinya kuma a glda mota ta biget ta samu matsala sosai kuma mai motar ya gudu shima mijina ya gudu ya barni, banda kowa duniya sai Allah iyayena kuma suma sun rasu ka rufamin asiri don Allah, dakatar da ita Mubarak yayi sannan ya fara kiran sunan Mai nasara, Da sauri ya matso wurin tare da girmamawa, kallon matar Mubarak yayi sannan yace yanzun me kike so ne? Takarda ta mikawa mai nasara danshi ne yayi mata hanyar ganin 
Mubarak,din ansa yayi sannan yayi ma Mubarak bayani, Jinjina kai Mubarak yayi sannan yace ma mai nasara a bata miliyan goma, idanuwa mai nasara ya zaro tare da cewa ranka ya dade ai sai zuciyarta ta buga, kallonsa mubarak yayi sannan yace a bata miliyan ashirin yana fadin haka ya wuce, mai nasara yana ganin Mubarak ya wuce yacewa matar tou wallahi miliyan goma zan baki goma taki goma tawa 
tunda kinga duka ke miliyan 2 kika bukata, 
Matar tace taji ta yadda, mai nasara yace to anshi takardar kije gida saina dawo, godiya tayi sanna ta tafi zuciyarta cike da farin ciki, shi kuma ya nufl wurin da Mubarak yake shiga mota dan Hafsat zata zo ne! 
Shalele an samo gam an lika takardar da akayi mata zanen hoton Mubarak ta lillika a dakinta, Wanka tayi bayan ta gama ta saka wata “yarjallabiya irin ta maza hijabi ta saka katuwa har tana sharar kasa saboda Bobo yace ta gyara shigarta zuwa ta mata dan duk inda taje idan aka ganta a matsayin mace sai anfi jin tausayinta akan tazo a matsayin namiji, Bata dade da gama shirinta ba bobo yazo dan shine zai kaita wurin mai nasara tunda tayi masa alkawari idan ta samu sauki zata bashi labari, tou yanzun ta warke tas kuma karya takeyi babu wani labari da zata bashi tana san tasan shiga da fitar Mubarak ne saboda kudirinta na daban daya zama sirri tsakaninta da zuciyarta, Da sauri ta fito dan dukan kofar dakinta da Bobo yakeyi, tana fitowa ta rufe kofar dakin ta, suka tafi, tafiya sukeyi tare dayin “yar flra sama sama har suka isa kofar gidan Mubarak 
ajiyeta Bobo yayi sannan yayi tafIyarsa dan neman abincinsa, Kai tsaye ta tunkari kofar gidan da sauri sojojin suka taso bama tare da barinta ta iso ba, ita kuma sai kokari kauce masu takeyi amma su burinsu su tambayeta ina zataje ne? 
Ke ina zuwa ne? Ni ba wurinku zani ba, kawai zama zanyi ne, 0h ai munsha ciki zakije muji a ina aka samo masu shareriyar hijabi, murmushi tayi sannan tace iyakata nan kuma bama kofar gidanku zan zauna ba, basu sake magana ba suka wuce ita kuma ta samu gefe 
daya ta zauna dan fara nata shirin, A wani gesthouse dinsa ya sauka bai wani dade da zuwa ba Hafsat ta iso a cikin wata lutsetsiyar motar ta, ta wanku ta daurayu sosai saboda tasan farillan daukarwanka, 
Parking tayi a wurin da aka tanada dan ajiye motoci, bayan tayi parking ta fito da isarta take tafiya kamshin turarenta yana biye da ita sai kara zugata yakeyi harta isa parlon da Mubarak yake zaune, 
Shigarta yasa kowa ya fita bayan sunyi gaisuwa suka basu wuri su dan tattauna, Shiru ya ratsa palon na wani lokaci bakajin kukan komai sai kukan A C wanda ya sanyaya dakin da sanyi mai dadi, kamshi turarukan jikinsu ya hadu ya bada wani kamshi mai sanyaya zukatan masoya! 
Gyaran murya Hafsat tayi cikin maganarta mai dadi da daukar hankalin namiji tace kwana biyu kana ta guduna nayi ta kokarin mu hadu amma sai wani sulbewa kakeyi fadamin ko matarka ta sake rabamu ne? 
Gyara zamansa yayi tare da harde kafafuwansa daya saman daya, kallon Hafsat yayi amma baice komai ba, murmushi tayi tare da tashi daga inda take ta koma kusa da Mubarak cikin gogewa ta kallesa da kallo mai narkar da zuciya sannan tace kayi hakuri bawai ina zargin matarka bane kawai dai banajin dadine ta shiga tsakiyarmu ne bayan kaine kamin alkawari cewa mace biyu kadai zaka aura a rayuwarka kuma ka tabbatarmin nine ta biyun miyasa haryanzun baka aureni ba? Munfa dauki tsawon shekaru da dama 
muna tare babu amfanin soyayyar da babu aure a cikinta! Shiru yayi baice komai ba, dan gajeran murmushi Hafsat tayi dan tasan dama ba wani abu zaice ba, haka ta kari surutunta ita daya amma Mubarak baice mata ci kanki ba, itace ta gaji dan haka tace masa zata tafi, jinjina kansa yayi, mikewa tayi tsaye tana mai kallonsa cikin so da kauna, itadai tana san Mubarak amma rainin hankalinsa yayi yawa, 
Juyawa tayi cikin fushi da gudu ta fita daga palon bin bayanta yayi da kallo tare da tabe bakinsa, a ransa yace dukanku haka kuke itama nan khadija kafin na aureta biyayya kuma bata san ganin bacin raina amma yanzun kullum tashin hankali banda kwanciyar hankali gidana, hmm aini babu ni babu kara aure har abadan duniya itama sawake mata zanyi in huta dan mata matsala ne hidimomina basu bari na nayi lokacin mace daya bare kuma hayaniyarta mata biyu ai na hada ma kaina tashin hankali itama dayar yana kare da ita! Dan gajeran tsaki yayi sannan ya mike ya fita dan komawa gida, 
Shalele tunda ta hasko kurar motoci ta sake lafewa sosai a inda take zaune saida motocin suka kusa kawowa wurin da take zaune, da sauri ta Ciro takarda da biron dake cikin hijabinta, rubutu tayi akai a daidai lokacin da motocin suka wuce ta gabanta, bin bayan motocin tayi 
da kallo bayan sun gama shigewa ta mike dan tafiya gida sai kuma gobe da safe! 
Haka dai shalele taci gaba da zuwa tana zama a wurin nan tana kallon shiga da fitar 
Mubarak, kuma a zamanta wurin yasa ta fara gane adadin kwanaki nawa yakeyi yana nan kwanaki nawa yakeyi baya nan, 
ldan ya canja lokacin Flta ta sani idan ya gyara kuma ta sani, amma har yanzun bata 
samu taganshi ko so daya ba wannan aikin kadai shine takeyi! Yaukam kasuwa ta tafl ita da Bobo waya ta siya sabuwa kal kirar nokia “yar karama ta siyi sabon layinta, a wurin ne ta tambayi mai siyar da layi cewa idan tana san ta kwashe numbobin waya daga kan wata waya zuwa saman layinta ya zatayi? Nuna mata yayi yanda akeyi, bayan ta gani tace to a kara mata layika guda goma, bayan ta siya akayi mata rejister godiya tayi sosai sannan suka tafi gida ita da Bobo! Bayan ya ajiyeta ne tace masa ya tsaya ta kawo masa abinci tunda sun dade a tare basuci komai ba kuma, yace mata ya gode bayajin yunwa, dan yanzun idan ta bashi kudi ya daina amsa, godiya tayi masa sannan ta shiga ciki, 
Baje layinka tayi duka a saman kafet dinta tana dubawa, kuma Bobo yace mata tunda tana da kudi ta siye gado ta rika kwanciya akai tace ita bata bukatar gado dan kwanciya a zaune ma take kwana saboda lokacin bacci baizo ba! Bayan wani lokaci kuma ta tashi ta nufi kicin, abinci ta zubo ta dauko dan ruwanta purewater ta dawo, tanacin abincin tana nazari harta gama, bayan ta gama ci ta dauke flet in ta mayar kicin, bayan ta dawo agogo ta kalla sannan ta maida dubanta ga jakarta, Tana zaune ba tare data motsa ba amma lokaci lokaci tana kallon agogo, babu abinda ta sakeyi har saida 9:30pm tayi tashi tayi da sauri ta dauki wata igiya ta fita a gidan …… , Kasa ta tafi daga gidan da take haya har zuwa gidan Mubarak kafin ta isa har 11:00pm, tsaye take acan gefe tana hango C C T V Camera dake kallon masu tahowa! Dan jujjuyawa tayi dan ganin ko da masu kallonta, bayan ta tabbatar babu sannan ta cire wani kyalle ta nannadeshi ta jefa wurin da take hango camera din kyalen kuwa ya sauka a saman C C TV camera din dan ta iya saiti, ajiyar zuciya tayi sannan ta koma ta boye dan ganin ko wani zaizo dubawa ………… 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]