HARSASHEN SO CHAPTER 8

HARSASHEN SO
CHAPTER 8
Cikin tashln hankali Shalele ya Isa gida saboda tsananin bacin rai da damuwa tun kafin dokin ya tsaya ya dire daga kai! 
Tun a wajen ya yarda rawanin kansa, da gudu ya nufi dakinsa yana mai kwalawa mama kira, Amsawa mama tayi amma kam ta fito daga dakinta tuni shalele ya isa dakinsa, cikin kuka ya fara warware damarar dake daure a kirjinsa wani dogon yadi ne yana da tsayi sosai shine yakecin damara dashi a kirjinsa, A sukwane ya isa gaban madubi yana mai kallon cikar halitar kirjinsa banda kuka babu abinda shalele yakeyi, sallama Mama tayi ta shigo cikin dakin tare da cewa shalele lafiya ne kake min irin wannan kiran haka har inajin faduwar gaba? Cikin tsananin bacin rai shalele ya juyo, da sauri mama tajuya tare da cewa mi zan gani haka shalele? 
Cikin sanyin murya shalele yace ke zan tambaya Mama, waye ni? Mene ne haka nake gani wannan wane irin tashin hankali ne nake fuskanta a rayuwata? Waye SHALELE? sannan kuma waye UMMU SULEIM? Mama na kasa ganewa kaina ya daure ki tausayawa rayuwata ki fadamin ko waye ni! Ba tare da Mama ta juyo ba tace kaine SHALELE sannan kuma kaine UMMU SULEIM A, a, mama shalele ya fada tare da dakatar da ita, sannan yaci gaba da cewa tunda na tashi ina karami suna daya nakejin ana kiranki dashi mai gida ma haka kowa na gidan nan sunansa daya ni miyasa aka bani suna biyu? Sannan me yasa aka boye daya ake amfani da daya? Mi yasa kukayi min sunan sirri sannan kuma kukayi min bayyanan nen suna? Mi yasa kuka canja min rayuwa zuwa rayuwarda ba tawa ba? Fadamin ni wanejinsi ne a cikin jinsin mutane, akwai mace akwai namiji ni waye a cikin biyun nan? A sanyaye Mama tace sanya kaya sannan nayi maka bayani, cikin kuka shalele ya dauki wannan dogon yadi ya ci gaba da nannadawa kamar dai yanda yakeyi a baya! Bayan ya gama yace na mayar Mama fadamin waye ni? Cikin tausasa murya mama tace hakika ba namiji kike ba mace kike, Zaro idanuwa shalele yayi sannan yace mi yasa kukaimin haka Mama? Ya karasa maganar yana mai goge hawayen idonsa, Jansa tayi suka zauna a gefen gado sannan tace bani nayi haka ba mahaufinka ne, cikin sarkewar murya shalele yace, wane laifi na aikata wanda ya mayar dani jinsin da bana ciki? Yasa na rika cudanya da maza na rika gogayya dasu? Bayan duk hakan babu kyau, wane laifl nayi masa wanda yasashi aikata min haka Mama? Ajiyar zuciya Mama tayi sannan tace kiyi hakuri mahaufinki baya da hali mai kyau, abinda yaga dama shi yakeyi baya shawara idan zai aikata abu yana da zuciya sannan kuma yana da riko yana rike gaba sosai sannan kuma yana kafa kiyayya, Baya yafiya kuma baya afuwa bai san tsautsayi ba haka kuma baisan kaddara ba, baida hakuri ko kadan tsananin ‘KIYAYYA’ dake tsakanin sa da dan uwansa yasa ya mayar dake namiji ta karfi da yaji, Bayan ya manta cewa mace a lugga: Mace wata halittace wadda ita bata kai matsayin namiji ba, amma kuma ta wuce namiji amfani ta wani fanni haka kuma a bayyane mace wani yankin jin dadi ne wadda Allah ya halitta dan adon rayuwa da jin dadin namiji da biyan bukatarsa ta ko wane nau”i, amma tare da bin shari’ar musulinci, 
 su mata gonakinkune ko kuma lambunanku ne “” to kunga karshen dadi shine mace. Haka a bokance: mace abu ce mai daraja wacce zata ibe maka kewar abubuwa da dama a rayuwa a cikin fleshy littafin ma emeka yace mace abuce wanda zaka dauko domin ka sadaukar da ahalinka gareta kuma mace ita wata hilltace mai rauni wacce ko wane namiji yana da kyau yaji tausayinta ta k0 wace siga, tou kinga kuwa ke kina daya daga cikin jinsi mai matsayi, Har abada babu yanda zakiyi ki zama namiji domin akwai abubuwa da dama wanda Allah ya banbanta tsakanin mace da kuma namiji, Wanda duk mai hankali da tunanin yasan ke ba namiji bace, idan akayi amfani da wasu abubuwan domin Allah yayi banbanci mai yawa kamar haka Al”aura tana da banbanci, 2. Haka zalika Allah yayiwa mata kirji sabanin namiji, Wannan shine banbanci da kika gani kika tabbatar ke bakya cikin jinsin maza, 3. Sannan kuma Allah yasa namiji ya zamo mai karfi da kazar kazar sabanin mace, Kinga kina da karfi amma karfinki baikai yanda na maza yake ba, daga tafiyarki za”a 
gane ke ba namiji bace saboda dame kikeyi irin ta mata! 4. Haka zalika mace tana da tattausar murya a halitta sabanin namiji, 5. Sannan ayoyi daga alkur”ani da hadissai ingantattu sun tabbatar da cewa akwai wani jini wanda mata suke fiddawa lokaci lokaci wanda ake kira da al‘ada, amma namiji kuma baya fitar da wannan jini, Kinga kwanaki kinyi kuka a kan wannan alurar wanda da kina zuwa islamiya domin neman ilimin addi”ni tun a lokacin zaki gane ke ba namiji bace amma a lokacin saina barki Bayani kadai nayi miki akan wannan lalura, Saboda haka hakuri zakiyi tayi har zuwa ranar da mahaifinki ya sauko, cikin tashin hankali shalele tace Allah ya sawake ai na tashi daga namiji har abadan duniya, Zamanki gidana ya kare har abadan duniya, na tsanaki bana kaunarki ki fitar min a gidana kafin bakin cikina ya kaiki lahira kamar yanda yakai mahaifiyarki, mai gida ne yake 
wannan maganar. Cikin tashin hankali gaba dayansu suka juyo suna kallon mai gida daga Mama har shalele, Cikin tashin hankali da murya mai firgitarwa yace ki fitar min a gidana tun kafin nasa a kashemin ke fita nace …………… Ya karasa maganar harsai dai gaba daya gidan ya 
ansa yana wani zazzaro idanuwa kamar mutuwa ta tunkaro shi Da sauri shalele ta durkusa saman guyawunta cikin muryar rarrashi tace kayi hakuri mai gida zan tsaya a yanda ka tsayar dani, kuma nayi maka alkawarin zan cika maka burinka zan kashe maka Bashir sannan zan kashe maka dansa nayi maka wannan alkawarin idan har ban kashe maka shi ba nan da lokacin daka ibar min na fansar da raina a gareka ka kasheni na yadda dan ban cancanci diya mai biyayya ga mahaiflnta ba, Kallon mama mai gida yayi yana mai cewa mama kina sheda ne? Shiru mama tayi dan tasan idan har shalele bata cika umarnin mai gida ba mutuwa itace kadai ta dace da rayuwarta a wurin sa, 
Murmushin karfin hali shalele tayi sannan tace Mama kina sheda, kallon shalele tayi sannan tace naji ina sheda shalele, godiya tayiwa mama sannan tace kaji mai gida Mama tana sheda ta karasa maganar tana murmushin karfin hali, ba tare da mai gida yayi magana ba yayi waje cikin bacin rai! 
Ajiyar zuciya sukayi dukansu sannan Mama tayi magana kasa kasa cewa zan baki labarin wannan bakar gaba da “yarana “biyu sukeyi, godiya shalele tayi sannan ta fita daga dakin ba tare data saje wa mama komai ba, Kai tsaye dakin mai gida ta nufa cike da ladabi da biyayya ta durkusa cewa mai gida yaushe zan tafl ne? ‘Dan sakin ransa yayi sannan yace tou shalele ai kawai da kin wuce yau 
ya karasa maganar yana mai dauko kwalbar data anso a wurin wannan bakin bokan, A gaban shalele ya tsaya sannan ya fara cewa, birni tana da hadari sannan kuma tana da rikitarwa tana sa dimuwa akwai banbance banbance sosai tsakanin kauye da birni ki kiyaye, ya fadi haka tare da mika mata kwalbar, Ansa tayi sannan kuma ya mika mata watajaka yace wannan kudi ne a ciki dasu zakiyi amfani na tabbatar zasu isheki har ki gama abinda kikeyi tunda nasan bazaki wani dauka lokaci mai tsayi ba zaki dawo, Cikin girmamawa ta ansa tare da mikewa tsaye saida ta dan girmama shi sannan ta fita, bata wani dauka komai ba sai zanen hotunan Mubarak, bankwana tayi da Mama, doki tahau sai kuma su Balaga suka bita a baya danyi mata rakiya har wajen gari, Tafiya sukeyi bata yara ba har suka isa bakin titi, saida shalele tahau motar sannan suka dawo da dokin data hau, Murmushi Shalele tayi ganinta cikin motar dan harta manta da abinda zai kaita gari, zanen hoton Mubarak ta fiddo ta fara tambayar “yan cikin motar ko sun sansa, 
Zane ne dai ba hoto ba, dan haka kowa dai idan ya kalla zaice kamar ‘ABAK‘ ita kuwa bata san wani Abak ba dan haka ta tashi daga mazauninta ta fara tafiya a cikin motar Har inda driver yake, mika masa takardar zanen tayi tana mai cewa don Allah ko kasan wannan ne? Tsaki yayi ba tare daya ce komai ba, Itama shalele tsaki tayi tare da cewa dakiki dakai wanda baida rabo ko a duniya, tana fadin haka ta mika hannunta sama ta rike wata makama ba tare data koma ta zauna ba, Haka dai sukaci gaba da tafiya har Allah yasa suka sauka lafiya, tuni shalele tama manta da wata banzar kwalbar da mai gida ya bata, dan haka tana fita daga motar taci gaba da nuna zanen hoton Mubarak amma babu wanda ya saurareta har dare yayi tana wannan aiki kamar tababbiya, 
Aiko ta daukarwa ranta idan har za’a busa kaho tana cikin neman Mubarak idan har bata ganshi ba saida ta mutu dan bata zama saita ganshi, shi kuwa Mubarak yama manta da zance wani shalelen sakarkari dan tsawon shekara biyar kenan basu hadu ba, shi tun a ranar ma ya rufe littafln banza, Har garin Allah ya waye shalele bata zauna ba haka tayi ta yawo kuma gari kowa yayi shiru tunda dai kowa yasan dare mahutar bawa,ne 
 daren jiya bai zamo hutu a gareta ba! 
Ganin ababen hawa sun fara suntiri yasa tayi shawarar samun abun hawa dan ya tayata neman inda ‘ABAK’ yake, bayan ta samu mai napep ta shiga tare da cewa mu tafi, Ina zamuje ne bawan Allah? Neman wannan ta nuna masa zanen kallon zanen yayi sosai sannan yace wai MubarakAbak? Shalele tace sunansa kenan? Yace sosai ma ai baya kasa, shalele tace tou ina yaje ne? Mai napep yace nikam ina zan sani tunda da zai tafi bai fadamin ba! Tou kaini gidansa mana, da sauri ya juyo tare da zaro idanuwa yana kallon shalele zuwa wani lokaci kuma ya kece da dariya tare da cewa amma kai ka cika mahaukaci, 
‘Dan bata rai shalele tayi sannan tace ban gane na zama mahaukaci ba, saida ya kara dan gajeran murmushi sannan yace yi hakuri abunne ya bani al’ajabi kaidai gaka kamar mutum amma tunanin tumaki kake da, banda haukarka kasan waye abak kuwa a garin nan? Idanma neman temako kakeyi ko wani abu to tun wuri rufawa kanka asiri kana kai kanka ne a mutuwa a tsautsayi ka nuna kasansa ma sojoji zasu rufa maka harsai sunkai ka, Ajiyarzuciya shalele tayi sannan tace nawa zaka kaini ne? Saida mai napep ya sakeyin murmushi sannan yace 1k, kallonsa shalele tayi sosai sannan tace zan baka 5k muje, 
Hmm

About Ismail

Check Also

HARSASHEN SO CHAPTER 31

HARSASHEN SO  CHAPTER 31 Shiga yayi ya ajiye wayoyinsa, rage kayan jikinsa yayi ya shiga …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *