HARSASHEN SO CHAPTER 15

HARSASHEN SO
CHAPTER 15
Ka fiddo min da zuciyarta nace, cikin sanyi Balaga yace Mai gida idan na farkata mutuwa zatayi ai, wani irin kallo Mai gida yayi masa tare da cewa ni zaka fadawa zata mutu? Shiru Balaga yayi, Mai gida yace to tunda har ‘HARSHASHEN SO” ya shiga cikin zuciyarta bai matar da ita ba, wallahi saika ciro min zuciyarta a gaban idon kowa zan goge soyayyar dan ‘MAKIYI NA’ sannan na dasa ‘KIYAYYAR SA’ a cikin zuciyar diyata, har abada karya da gaskiya basa taba haduwa, haka kuma so da kiyayya baza su taba zama wuri daya ba, ansar wukaryayi ya mike da sauri kafin mutane su ankara tuni mai gida ya sokawa Shalele wuka, cak haka kuwa yaji karar shigarwuka a cikin jikin Shalele, 
Wani irin ihu Shalele tayi saboda azabar da taji lokaci guda zufa tayo ambali ajikinta idanuwanta suka kada zuwa launin ja, a hankali ta sadda kanta kasa tare dakai dubanta inda mahaifinta ya caka mata wukar sannan ta dago kanta a hankali takai dubanta cikin idanuwan Mai gida. Innalillahi wa’inna ilaihir raji”un duk wanda ke cikin palon ya fada banda Mama data suma, Balaga kuwa da gudu ya isa wurin ya rike hannu Mai gida dan a lokacin ya zaro wukar da karfin tsiya yana kokarin kara dabawa Shalele ita. Wata irin hajijiya Mai gida yayi da Balaga ya wurwura sa gefe daya ganin haka yasa Alhaji Abas yasa Asma”u ta kamo Shalele da sauri suka dauketa suka fito. Mai gida kuwa cewa yakeyi Abas karka saka kanka abinda bai shafeka ba, Amma ko saurarensa Alhaji Abas baiyi ba, shiga motar yayi yaja cikin tashin hankali ita 
kuma Asma”u tana baya rungume da Shalele ajikinta sai kuka takeyi. Mai gida kuwa sai masifa yakeyi tare da tsinewa kansa albarka nadama kawai yakeyi na zuwansa duniya dan ya zabi mutuwa a rayuwarsa shi yasa yayi kokarin kashe Shalele dan yasan idan harta mutu shima kisa ne zai hau kansa ya yarda da hakan yabar duniya dashi da ita saiya fi masa farin ciki da kwanciyar hankali, Balaga kuwa shine yayi ta fifitawa Mama ko Allah zaisa ta farfado amma Shiru, wata zuciya tace masa kawai yaje ya badawa Bashir tashin hankalin da yasa mahaifiyarsa shiga damuwa ko za”a samu maslaha tsakanin gidajen nan biyu, goge hawaye Balaga yayi dan yasan har abadan duniya haka bazata taba faruwa ba. Dan haka hakura yayi yaci gaba da yi ma Mama fifita dan itace kadai mafita idan ta farko tasan abunyi tunda itace ta haifesu dukansu. 
Suna isa cikin gari asibiti sukayi wa tsinke, tun kafin motar ta gama parking Asma”u ta fice da gudu tayi ciki, da gudu ta shiga cikin asibitin har tana tuntube jikinta jagejage da jini, Iikita …………. likita …… Likita a kawo dauki ku fito tiyatar gaggawa, ‘ Wani mutum ya riketa tare da cewa yarinya laf’lya? Cikin yanayi na wanda ya wahaltu tace kaine doctor? Ga doctor nan ya nuna mata gefen sa, yawwa likita kunayin tiyatar zuciya……? Sosai ma munayi haka likitan ya fada, rikesa Asma”u tayi tare da cewa ka taimaka min akwai mara lafiya da aka harba a zuciya kuma haryanzun tana numfashi tana iya magana tunda Allah yasa bata mutu ba don Allah ka nuna kwarewarka ta cikakken malamin lafiya ka ciro harsashen nan don ceton rayuwarta. cikin yanayin tausawa likitan ya bita da kansa suka fita, a lokacin Alhaji Abas ya fito ya shiga ciki sunsha banban da Asma”u shi ya shiga ita kuma sun dawo motar ita da doctor da wasu mutanen da zasu dauki Shalele. Haka suka jagalgali Shalele suka nufi ciki da ita, shidai doctor bai san abinda ya sami Shalele ba, kuma bai tsaya yayi bincike ba ya hado kan wasu likitoci da malam jinya dan ayi aikin zuciyar Shalele tare dasu. Har aka shiga dakin tiyata da Shalele Alhaji Abas baiga Asma”u ba kuma ya koma motar babu Shalele babu Asma”u wannan abu ya tashi hankalinsa sosai dan haka ya dawo cikin 
asibitin yaci gaba da watsa ido dan nemansu. A dakin tiyata kuwa ko wane likita yana kokarin gani ta inda harshashe ya shiga jikin Shalele amma Allah bai nuna musu ba, saidai cakar da Mai gida yayi mata suka gani kuma sunyi mata aiki a wurin, Fitowa likitan da suka hadu da Asma”u tun farko yayi sannan yace mata ke a ina aka harbi yarinyar can ne? cikin kuka Asma”u tace a zuciyarta ne da Babanta zaiyi mata tiyata aka samu akasi sai babanmu ya kawota asibiti. ‘ Likita yace ooo wai ta ina harsashen ya shiga ne? Asma”u tace saidai kuje ku tambayeta nikam dai ban sani ba tunda ba jikina bane, tsaki likitan yayu ba tare da yace komai ba ya koma ciki. Kara dubawa yayi yajuya Shalele sosai amma banda wannan ciwon najikinta babu wani alamar digon ciwo, kallon Shalele yayi wanda ta fita daga hayyacinta, cikin lallashi yace meye sunan ki ne? Saida Shalele ta goge hawayen idonta wanda tasha ihu a lokacin da ake mata dinki tace suna nan Ummu Suleim, murmushi likitan yayi sannan yace meya sameki ne? Ya karasa maganar yana mai kallon cikin kwayar idon Shalele. Saida tayi shashshekar kuka sannan tace jarabta ce ta rayuwa Allah ya doramin ta karasa maganar tare da kara goge hawayen idonta, kara matsawa likitan yayi kusa da ita tare da dan dafa daidai inda taji ciwon yadan latsa, wani irin ihu Shalele tayi saboda zafi cikin kuka tace don Allah ka daina min akwai zafi wallahi. Dukawa yayi saitin fuskarta sannan yace fadamin abinda ya sameki? Waye ya harbeki a zuciya ke kinajin zafin harsashen amma bakiga lokacin shigarsa ba waye? Waye shine Eye? 
Cikin kuka Shalele ta farayi masa bayani a hankali tana dan warware masa wasu abubuwan, kadan ta fada masa saita dora da cewa Mai gida na fada masa So yana daukar ka minti 1 kacal kaji kana ra’ayin mutum, zai kuma iya daukarka ka kwana daya kaji ka kamu da san mutum amma kuma zai dauke ka tsayin rayuwa ka manta da mutumin da ka damu da cutar san nasa, a koda yaushe bani da wani buri daya wuce inga na hadu da masoyin 
da nake masa azababbiyar soyayyar dashi baima san inayi ba. Saida tayi shashshekar kuka sannan takai hannunta saman zuciyarta tace hakikajarabta iri iri ce a rayuwa, nidai tawa jarabawar fadawa soyayya da dan makiyin babana ne, kallon likitan tayi sannan taci gaba da cewa abu ya zamar min fitina yau har babana yana yankana da wuka da sunan zai fitar da zuciyata ya goge so ya dasa kiyayyah Wannan wane gaba ne da saboda ita zaka kashe dan daka aifa a cikinka  Eye?Murmushi likitan yayi tare da ci gaba da kallon Shalele amma baiyi magana ba, gage hawayen idonta tayi tare da dora hannunta saman goshinta ta lumshe idanuwanta, ganin bazata ci gaba da magana ba yasa shi cewa to kiyi hakuri kibi umarnin mahaifinki dan samun tsira da rayuwarki. ‘Dan gajeran murmushi Shalele tayi sannan tace a shirye nake da mutuwa dan a yanzun rayuwata bata da wani amfani dan a matsayin matacciya nake kallon kaina, ina ji amma bansan ta ina sautin magana yake fitowa ba, idanuwana a bude suke amma basa kallon hoton kowa haka ya tabbatar min da ni matacciya ce idan har aka gaji da zama da gawa a cikin masu lumfashi na tabbata lallai za”a gina min kabari a binneni zanci gaba da rayuwa a cikin ramin mutuwa harta Allah ta kasance a gareni, Mikewa tsaye likitan yayi tare da cewa kiyi hakuri ki danjira kafin mutuwarki komai a hankali ake binsa daga karshe ina miki gargadi da ki yafe ki manta dashi kwata kwata a ranki Allah zai baki wanda yafi sa, akwai matsala sosai kaso wanda baya sanka idan har kika auresa lallai wulakanci cin zarafi da cin fuska zai biyo baya, motsi kadan zakiyi yace shi baya sanki kece kike sansa gori da cin zarafi zakiyi ta fuskanta a rayuwarki dashi. Ya karasa maganaryana dariya, A hankali Shalele ta gyara kwanciyarta saida tayi wani azababben nishi na azaba sannan tayi dan gajeran murmushi kallon likitan tayi tare da cewa ai duk abinda kake so idan har da zuciya daya kake sansa duk abinda zai maka baka ganinsa a matsayin cin fuska ko cin zarafi na yadda yaci fuskartawa yaci zarafina ya wulakantani duk naji na yadda zan dauka ko bai aureni ba ya daukeni a matsayin mai masa share share da goge goge a gidansa kullum ya fito na gansa naji dadi koda kuwa idan ya fito duka zaimin da zagi wallahi ina sanka kuma har karshen numfashina ina sansa bazan daina sansa ba har ranar da zan fitar da lumfashina na karshe a duniya ……. Murmushi ya sakeyi da gefen bakinsa tare da jinjina kansa alamar gamsuwa, kidai jira 
kiga abinda gaba zatayi ko za’a samu maslaha sassauci da kuma jituwa tsakanin iyayenku, Murmushin takaici Shalele tayi tare da maida numfashin wahala, sannan ta fara magana cikin yanayin gajiya cewa,jinkiri ga yafiya a koda yaushe yana zama dana sani, idan tsautsayi ya kasance baya wuce ranar sa to me za’a kira kaddara da ko wanne dan adam yana da irin nasa? Idan tafiya tai nisa to waiwaye bai cika zama ado a cikinta ba. Itafa zuciya an halicce tane da soyayyar abinda take so, sannan babu abinda ta tsana irin mai bata damuwa, cutuka iri iri ne amma bana tunanin akwai mai zafi irin cutar so, ta karasa maganar tana mai digar da hawaye sosai daga cikin idonta, Majina taja tare da ci gaba da cewa hakika na riga na tafi tafiya mai nisa wanda idan nace zan tsaya lahira kawai zan zarce idan kuma na juyo hanyar ta riga ta cika da wuta kayoyi kuraye da kuma ajali ina dawowa baya idan har kura ta rikeni na samu na kwace dakel kaga nabi takan wuta na taka ta na kone sosai kayoyi sun caccakeni idan har na fita jinya zanyi sosai wanda ba lallai bane na rayu, idan kuwa ina juyowa nayi karo da ajali mutuwa ce, hakuri zanyi kawai inci gaba da tafiya har na cimma burina, ‘ Ajiyar zuciya doctor yayi tare da cewa ina miki fatan alkairi Allah kuma ya cika miki burinki idan har Alkairini, itama murmushi tayi tare da cewa amin ni k0 sharri ne ma Allah ya tabbatar min dashi. 
Bai sake magana ba yasa aka fitar da Shalele dan kaita dakin hutu, Alhaji Abas daya gano Asma”u dakel yaga an fito da Shalele ya isa wurin da sauri tare da fara jera mata sannu. A gidan Mai gida kuwa bayan Mama ta farfado kuka tayi sosai tare da fara tattara kayanta dan komawa gidan Bashir, idan hankalin Mai gida yayi dubu ya tashi kuka yakeyi kamar ransa zan fita, Mama ko saurarensa batayi ba taci gaba da hada kayanta. Kuka sosai Mai gida yakeyi tare da dafa kafafuwan Mama yace ta rufa masa asiri idan har tayi masa haka ya bani ya lalace zai shiga fushin ubangiji Mama ki rufa min asiri na rantse da Allah na bari kuma bazan kara ba, Mama tana san Mai gida fiye da tunanin mai tunani hakura tayi tace zata zauna amma bisa sharadi daya rak. 
Da sauri yace ya yadda ta fadi koma miye zaiyi wallahi, Mama tace duk abinda nace za”ayi a gidan nan shine za’abi akan sa idan har nace kar kayi to kada ayi idan kuwa ba haka ba zan bar maka gidanka in tafi inda akejin magana ta, cikin rawarjiki ya rike hannun Mama tare da cewa nayi miki alkawari mamana, jinjina kai Mama tayi ba tare da ta sake cewa komai ba. 
Alhaji Abas kuwa a Abuja ya kwana duk abinda ya dace za‘ayiwa Shalele shine ya biya kudi Asma”u ta kwana da ita shi kuma hotel ya kwana saida safe ya shigo asibiti ya duba jikin Shalele yaga da sauki, dan haka kudade ya kara musu sannan ya kama hanya dan komawa katsina, 
Asma”u ke kula da Shalele sai kuma likitan da bata san ko waye ba wanda ya shige musu kamar cutar cikawa, saida ya gama zamansa ya tafl, Shalele ta tashi gaba daya dakinsu yayi shiru dan kowa bacci yakeyi sai masu jinya da suma suka samu rumtsawa saboda wanda sukejinya sunyi bacci suma! Kallon Asma”u tayi da take ta shararar bacci, a hankali ta sauko da kafarta daga saman gado tare da dafe wurin da akayi mata dinki dan bata iya mikewa sosai a duke take tafiya. Da sando take taflya hana fita daga cikin dakin, ta tunkari hanya sosai taci gaba da tafiya, a duke take tafiya harta fice daga asibitin gaba daya …… , gidan Mubarak tayiwa tsinke gaba daya, Tana tafiya tana hutawa hawaye kuma suna aikinsu dan ita kadai tasan azabar da takeji kamar zata mutu jini ya fara tsirarowa daga wurin ciwonta saboda tafiya mai yawa da tayi kuma taki ta tsaya cikin dakiya da dauriya take tafiya harta isa kofar gidan. Wuri ta samu ta zauna ta kurawa get in gidan ido, tana zaune ita kanta bata san dalilin zamanta ba a wurin, babu agogo a hannunta amma ta kiyasta tayi zaman awa 2 da wasu mintoci murmushi tayi tare da tashi a hankali dan komawa daga inda ta fito. Mikewa tayi dakel harta fara tafiya wata zuciyar tace taje ta sunbaci get din gidan ko ba komai dai gidansa ne zataji dadi, A hankali ta juya ta nufi bakin get din tana isa ta dafa wurin tare da rumtse idonta takai fuskarta daidai get din a hankali ta dora bakinta kamardai yanda akeyin kiss tana kokarin ajiyewa taji wani irin gigitaccen horn hakan baisa ta fasa ba saida tayi abinda tayi niya sannan ta juyo. 
Shima kansa saida gabansa ya fadi ganinta a wannan lokacin da sauri yakai dubansa ga agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa dan duba lokaci shigowarsa garin kenan, 2:49am hankalinsa ya tashi sosai ganin Shalele. 
A hankali ta matsa daga wurin har yanzun tana rike da wurin ciwonta a dukenta taci gaba da tafiya, dan bata tunanin Mubarak ne tunda tazo ance yabar garin kwata kwata, Mai nasara yana kokarin shiga gidan dan an bude kofa Mubarak ya dakatar dashi bin Shalele yayi da kallo harta bace daga inda yake iya ganinta, 
Shi harga Allah ya manta da Shalele amma yau kam ya tuno da ita dan duk yanda ta canja bai hana masa gane ita wace ce ba, fitowa yayi daga inda yake zaune yace ma Mai nasara ya fita, ranka ya dade ina zakaje ne? Tsaki Mubarak yayi ba tare da yace masa komai ba, hakan da Mubarak yayi yasa Mai nasara fita tare da girmamawa yaja baya, Da sauri ya shiga motar yaja sauran motocin da suke bayansa suka bishi da gudu, tsayawa yayi suma suka tsaya wanda ya fito dan tambayar lafiya Mubarak yace masa suje kada wanda ya biyoshi dan idan har suka ganshi da Shalele a cikin daren nan sai Babanshi yaji labari kuma ya rasa waye munafinki a cikinsu. Komawa sukayi shi kuma yabi bayan Shalele da gudu a lokacin har tayi tafiya mai nisa, horn yake mata amma ita a tunaninta ta tsaya a saman hanya ne dan haka ta rabe gefe daya taci gaba da tafiyarta, horn yaci gaba dayi amma Shalele bata saurara ba tafiyarta takeyi cikin rashin tsoro hankalinta kwance, Gabanta yasha da motar ya wani katse harsai da kura ta tashi, tsayawa Shalele tayi dan ta dauka masu satar mutane, sauke glass yayi tare da kiran sunanta, Ummu Suleim ………Ajiyar zuciya ta sauke tare da goge hawayen fuskarta da sauri tajuya dan duk duniya mutum daya yake da irin wannan murya kuma shine yake kiranta da wannan sunan dan ko a taron duniya taji murya zata gano mai ita. A hankali ta juya ta kalli wurin da takejin maganar Mubarak, da hannunsa ya kirata saida ta sake sauke ajiyar zuciya sannan ta nufi wurin da motarsa take, a gabansa ta tsaya amma 
batayi magana ba, shine yace shigo… 
Zagayawa tayi a lokacin harya bude mata murfin motar daga ciki, shine ya rufe bayan ta shiga ya jawo kamaryanda ya bude mata daga ciki, baiyi magana ba ya fara tafiya ita kuma taci gaba da hawayenta saboda ciwonta ciwo yakeyi, Hanyar gidansa ya koma amma kuma saiya wuce hanyar da zata sada ka da gidan nasa yayi gaba har yanzun baima Shalele magana ba itama bata ce masa komai ba dan jin abun takeyi kamar a mafarki saidai lokaci lokaci tana kallonsa murmushi yayi tare da kallonta da wutsiyar idonsa sannan yace daga ina kike ne? Ajiyar zuciya ta sauke irin na mai shashshekar kuka irin wannan ajiyar zuciyar da tasha kuka ta koshi wanda akeyinta ana janta din nan to irinta tayi, sauka yayi daga saman titi yayi 
parking a gefe amma bai kashe motar ba, 
Hannunsa yakai daidai agogon motarsa yace daga ina kike nace? Kallonsa tayi cikin kuka tace asibiti, me kikeyi a asibiti ne? Banda lafiya, meya sameki ne? Mai gida ne ta karasa fadar mai gidan da sakin kuka sosai ……….. To kiyi hakuri kinji ko? Ya bata hakurin cikin tausayawa, ki daina kuka kinajin yunwa ne? Ba tare data bashi amsar tambayar da yayi mata ba ta daga masa inda ciwonta yake, sorry haka kawai yace bai sake magana ba yaja mota yaci gaba da tafiya, cikin kuka Shalele tace don Allah zaka ‘AURE NI…….. Nema motartayi ta kwace masa yayi kokarin rikota sosai tare dakai kallonsa ga Shalele 

Hmm

About Ismail

Check Also

HARSASHEN SO CHAPTER 31

HARSASHEN SO  CHAPTER 31 Shiga yayi ya ajiye wayoyinsa, rage kayan jikinsa yayi ya shiga …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *