[Advertisements⬇️]

GIMBIYA SA'ADIYA CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GIMBIYA SA’ADIYA 
CHAPTER 5
Cire takalmansu suka yi a daidai shigarsu bakin kangon dake kama da ginin da yayi shekaru hamsin ba tare da an shiga cikinsa ba. Don tsananin duhu, su kansu basa ganin junansu. Ko tafin hannunsu ba zasu iya gani ba. 
A hankali Kursiyya ta fara yiwa Zabbau magana ta yadda zata Iyajin ta, “Haryanzu na kasa sabawa da wurin nan. Duk sadda zan shiga cikinsa hankalina ba ya taba kwanciya har sai na ganni na gama abin da ya kaini cikinsa na lura. Ahh!” Ta saki ihu, sanadiyyar mummunan kayar data taka, wacce ta shiga Cikin kafarta sosai, tunda dama sun cire takalmansu tun a waje. “ 
Tsayawa tayi a wurin sanadiyyar kasa taka kafarta da tayi. Zabbau kuwa bama tasan cewa Kursiyyar ta tsaya ba, saboda tsananin duhun wurin. “Ranki shi dade, ni yau sai nake ganin tsawon tafiyar ma. ” Jin shiru babu amsa ya sata fadin, “Ranki shi dade. ” 
A nan ma shiru taji. Ita ma kanta Kursiyyar saiyanzu ta gane ashe bata tare da Zabbau. Kwala mata kira tayi, wanda sai da gaba daya wurin ya amsa. Jin kiran yasa Zabbau komawa baya. Cikin hikima tana dan Ialubar hanya har taci karo da Kursiyya. “Kafar ce tawa na kasa takawa Zabbau. Tamkarza ta cire haka nakeji. ” Zabbau tace, “Ki daure haka nan ki taka ranki shi dade. Kinga ai mun kusa karisawa.” Ta miko mata hannunta “Lalubo hannuna gashi nan ki kama, sai in taimaka miki.” a 
A haka cike da wahala suka bar wurin. Sannu a hankali suka fara iske haske, irin mai dishidishi din nan tamkar lokacin magrib yayi. 
Basu damu ba k0 kadan, basu tsorata ba, saboda dama sun saba. 
Tun daga nan suka fara jiyo wani irin sauti, mai tafiya da dukkanin ginin gidan. Ta ko’ina sautin
fitowa yakeyi. Hade da wata irin murya mara dadin saurara. K0 za a kashe su ba zasu iya fadin abin da ake cewa a sautin dake fitar ba. Daga nan kuma sai suka ringajin anajijjlka su, tamkar za a tayar dasu sama. Kankame junansu suka yi, idanuwansu runtse dajuna, sunajin yadda iskarguguwa ke rawa da kayan jikinsu. Da haka har suka isa wanidaki, wanda za a iya kiransa da zaure, saboda babu wani 
abun arzoki a cikinsa. Tsaye suka yi a bakin kofar, sunajiran a basu izinin shiga. Tun daga cikin dakin wata karamar kwarya ta tashi ta yisama, tana yawo bisa iska, a hankali har ta iso inda suke. Daidai fuskar Kursiyya ta tsaya, Kursiyya ta Iokaci jinin dake cikin kwaryar da hannunta ta shafa a saman goshinta. Ta sake lakata ta shafa a saman Iabbanta. Daga nan sai ta koma ga Zabbau. Ita din ma ta aikata sak abin da Kursiyya ta aikata Kwaryar na kama hanyar shiga dakin suka mara mata baya. Bayan ta dira kasa su ma suka 
dira kasa, hankalinsu kwance babu alamun tsaro ko firgici a tattare da su. A hankali ya bullo daga kasa. Da alama kamar ginin kasa (underground building) ne a cikin dakin. Fuskarsa babu annuri kamar koyaushe. Gashin gemunsa yayi tsananin tsawo, harya sauka bisa kirjinsa. Baya aske gashin kansa, da alama ya dauki tsawon shekaru rabon sa da aski. Idanuwansa farare ne tas, sai dai kwayar cikinsu cejajur tamkarjan gaushi. Bakinsa dan karami da gashin baki ya gama lullube shi. 
Kursiyya tayi gyaran murya. Ta sani sarai boka Fartsi baya sonjira. Da zararya bullo gare su to yafi so suyi abinda ya kawo su sukara gaba. Cikin wata irin murya, wacce sauraren ta kadai wani tashin hankalin ne, ya fara magana da 
madaukakin sauti, cike da izza da kasaita, yace, ”Aurenki dashi mutu-ka-raba ne. A yau-yau din nan zai mayar dake dakinki.” Akaifarsa ta yatsar haggu karamar yaballo da hannu. Da hannun haggun ya mika wa Kursiyya illa. Ta san sharuddansa, sam babu amfani da dama a wurinsa. Hakan yasa ta mika masa hannun haggu ta karbi akaifar tashi. 
Kije ki bude bakin wannan matar ki saka ta. Ki tabbatar kin aikata a yau, gudun samuwar matsala. Ku ajje dala dubu biyu ku tafi. Babu k0 gardama ta karbi’jakarta dake hannun Zabbau ta fiddo masa kamar yadda ya nema. Ka ‘idar aikinsa ke nan kamar yadda ta sani. Baya karbar naira sai dai dalar Amurka. a Bayan sun ajje suka mike domin tafiya. Ya dakatar dasu. “Lakuci jinin nan ki shafa a kafarki inda kikaji ciwo. Babu musu ta koma gaban kwaryar ta lakuto jini, ta zauna sannan ta shafa a kafar tata. A take taji babu ciwon kafar ko kadan, tamkar anyi ruwa an dauke. Da murmushi ta mike a bisa tafin kafar tata, sannan suka nufi barin wurin. 
An shafe kusan awanni biyar babu Khalili babu alamun shi. Hakan yasa mai martaba Sarki Sani yanke shawararya tura Waziri da mutum biyu daga cikin hadimansa. Sanin cewa akwaijikakka tsakanin Kursiyya da Mallam Khamis, ta iya yiwuwa cewa yayi ba zai zoba, shi kuma Khalili sai yaji nauyin zuwa ya sanar. 
A kofar gida suka dakata, har sai da suka sanar, aka musu iso zuwa cikin gidan Mallam Khamis. Sun same shi cikin kebabben dakinsa, wanda yake cike da tarin littattafan addini, da allo jere, da alama na dalibansa ne. Azaune yake bisa sallayarsa kalar tsanwa, wacce taji ado da gwaldin, tamkar dangin sarauta. Kanshi kuwa nade yake da rawani shima kalar tsanwa, dayake shi din maabocin kalar tsanwa ne. 
Da fara,arsa ya tarbe su, yace dasu su zauna a tabarmar dake kusa da inda yake. Babu musu waziri da sauran mutum biyun da suke tare suka zauna, sannan suka mika masa hannu suka yi musabaha. “Barka da kokari Allah gafarta mallam. Ya kwana biyu?” Waziri ya fada da kausasshen murmushi shimfufe a fuskarsa. “Da godiya ranka ya dade. Ashe abin da ya faru da Kursiyya ke nan.” 
Mamaki ya kama waziri. Kenan ma ya san abin dake tafe da su tunda har ya masa wannan tambayar. Saurin dakatar da tunaninsa yayi. Yace, ’ “Abin dake tafe damu kenan Allah gagarta Mallam. Ataimaka, Kursiyya na cikin mawuyancin hali ita da Zabbau. Muna bukatar ka da gaggawa, wala’allah ka taimaka mana daga cikin dabarun da Allah ya baka.“ 
Murmushi Mallam Khamis ya yi, sannan ya gyada kansa. 
“Ranka ya dade, ina mai neman afywa kan maganar da zata flto daga bakina. Na fade ta ga Khalili, sai dai tun a nan ya tabbatar min cewa ba zai iya fadar taba, don za a iya yanke masa wani hukuncin. Alhamdulillah! Tunda gaka, sai na fada maka. 
Idan har baka manta ba, kimanin shekaru biyu zuwa uku da suka gabata mun samu wata ‘yar matsala tsakanina da Kursiyya, wanda harta silar sa tasa aka yi mini dukan kawo wuta. Sannan aka daure ni har tsawon wata uku, tare da horo mai tsanani. Ba wai a kan wani dogon dalili ba. Kawai don na nemi gano wani boyayyen sirri dangane da ita. Ranka ya dade, dukwannan abun da Kursiyya ta min kuma yau sai a neme ni da nufin na tallafi rayuwarta? Ashe ina da amfani nima. Ashe dai mulki ko sarauta basu kai matsayi da darajar Iafiya ba, tun da gashi nan sun kasa siya mata lafiyar…” 
Yana neman ci gaba da magana waziri ya kokarta dakatar da shi, 
“Duk wannan na san da shi Allah gafarta mallam, babu bukatar maimaici. Sai dai wani abu, ana so idan mutum ya aikata maka sharri to ka saka masa da alkhairi. Kuskure dai Kursiyya ta yishi, duk mun sani daga ni har mai martaba. Don Allah a yi hakuri mallam, ka taimaka.” Shiru yayi jim! Kafin yace, “Na amince zan taimaka mata, amma da sharadi guda.” Dago kansa yayi waziri, yace, “Sharadi?” 
Mallam Khamis ya jinjina kansa. 
Hmm shin ko wanne irin sharadine wannan

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]