[Advertisements⬇️]

GIMBIYA SA'ADIYA CHAPTER 4 - Bankinhausanovels
Tue. May 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 4
Da faduwar gaba ta gama bude kofar, bayan ta saka  hannunta na dama ta dafe bakinta da yake a karkace yawu na dalala daga cikinsa. shafa’atu taja ta tsaya bayan ta dode hancinta. Da daya hannun take kore warin da ya daki hancinta, wanda a lokaci daya ya tayar mata da zuciya, kalacin da tayi yake barazanar fitowa waje. 
Sai a yanzu idanuwanta suka sauka ga Zabbau da har yanzu take nannade, kafafuwanta har suna tabo keyarta. Hannunta ta dora a ka, hade da fasa wata irin kara mai tsananin karfi 
Duk da Kursiyya taso ta dakatar da ita daga ihun da take yi amma babu hali. Har mantuwa 
tayi ta bude bakinta zatayi mata magana, sai ta sakejin azabar da ta wuce wacce take kanji a yanzu. Sosai ta kara kidima sadda taga yadda bakin Kursiyya ya koma. Da kuma abin dake fita daga cikin bakin nata. Ta bude bakinta za tayi magana kenan ta ga yadda mutane suka mamaye dakin. Sai dai kowa iyakarsa daga kofa. ‘Dakin Kursiyya ne. ‘Dakin Kursiyya kuwa yafi karfinsu. Iyakacinsu da shi kallo daga nesa. Sai dai abun mamaki shi ne, wane dalili ne 
zai sa Shafa’atu saka wannan ihun mai tsanani? Hannunta daya dafe da hancinta, da dayan take wa mutanen waje nuni da Kursiyya da 
kuma Zabbau. ldanuwanta na fitar da kwalla sosai. Mamaki bai gushe daga gare ta ba. Cike da tashin hankali mutane suke kallon wannan bakon al’amari. Sai dai tsananin tsoron Kursiyya da suke yi yasa babu wanda yayi kokarin shiga dakin, sai mutum daya, shi dinma ya shiga da nufin komai ta fanjama-fanjam ne Saboda dakin Kursiyya yafl karfinsu. 
Salati ya saki bayan ya shiga dakin. Dukka hannayensa tallabe da keyarsa. Idanuwa a bude yake fadin, “ 
“Babu lafiya. Maza-maza aje a sanar da mai martaba halin da ake ciki.” 
A daburce ya yi maganar, hakan yasa mutum uku suka arce da gudu, har suna bige wanda ke saman hanya. 
Isar su fada sun tarar mai martaba a tsaye, saboda har labari ya iso mishi, cewa akwai abin 
da yake faruwa a dakin Kursiyya. Cikin shessheka Haroun yace, “Ranka ya dade…yallabai, uhm…” yana yi yana sauke ajiyar zuciya. Cike da jarumta da kokarin kawar da tashin hankalinshi yace, “Inajin ka Haroun. Me yake faruwa a dakin Fulani Kursiyya?” Kasa magana Haroun yayi. Sai Muntari ne ya karbe da fadin, 
“Zabbau ta dunkule tamkar gammon kifi. Fulani kuma bakinta ya karkace, kazanta na 
Fitowa daga cikin bakinta yallabai. Kanta babu suma, ya koma tamkar na maza…” Tun bai rufe baki ba sarki ya dakatar da shi. Baya son yaji karashen zancen. Wannan mummunan zance ne, wanda ya shekara goma sha biyar rabon da yaji zance mafi muni 
kamarsa. Tome yake faruwa? Ya gyada kansa. 
Karya kuke yaran talakawa! Karyarku ta sha karya ku fada wa mai martaba zancen da zai saka shi a bakin ciki. Yau dole za a yanke muku hukuncin bulala hamsin da kwana biyar a cikin bursunA “Ya isa haka Khalili! Muje.” 
Kama hanyar sashen Kursiyya suka yi. Mutane sun yi dafifi a hanyar, ganin mai martaba ya 
sa duk suka ringa sunnewa suna darewa daga wurin. 
Sadda ya isa duk mutanen sun watse sun bashi wuri. Saboda wata irin muguwar harara da Khalili keyi musu. Runtse idanuwansa yayi daidai sadda zai zura kafarsa ta dama a dakin. So yake ya iske sabanin abin dasu Haroun suka kai masa rahoto. So yake yaga akasin 
haka. So yake ace ba Kursiyyarsa bace ba ta nakasa. 
Ya bude idanuwansa a hankali yana ambatar sunan Allah. A bisa fuskar Kursiyya ya dire su. Hannunta matse yake da wuyanta, gudan kuwa shi ta saka a saitin bakinta wai don kar ya gani. Sai dai kuma a banza. Kallo guda za a ma fuskarta a tabbatar da ta nakasa. 
Da salati ya karisa gaban Kursiyya. Gyada kansa yake yi cike da al‘ajabin wannan al’amari. “Kursiyya meya same ki? Waye ne ya aikata muku wannan aika-aikar?” Sai a sannan ya miyar da kallon sa ga Zabbau, wacce ke dan motsawa a hankali, sai dai kuma yadda take dai haka take. Bai ji amsa daga bakin Kursiyya ba. Hakan ya saka shi sake maimaita tambayar, “Kiyi mini magana Fulani. Nayi alkawarin kwatar miki fansa. Koma wane ne ya aikata muku haka ba zai tsira ba. Sai na wulakantar masa da rayuwa.” Cije-cije ta ringa yi, tana daddatsar harshenta harjini na fita, hade da wannan mummunan 
yawun. Dode hancinsa yayi, duk yadda yaso ya daure, duk yadda yaso yaki nunar mata da warinta da yakeji kasawa yayi. Ji yake zuciyarsa na tashi tamkar zai yi amai. Tunda yake a rayuwarsa bai taba jin wari mai tsananin wannan ba. Ganin bata da niyyar magana yasa ya mike a bisa kafafuwansa. Fuskar nan tashi a tamke, da zarar ka kalle shi za ka tabbatar cewa baya a cikin walwalarsa. Ya juyo ya fuskanci hadimansa da dukkaninsu hancinsu a toshe yake da hannuwansu. Kallon su da yayi ya sa duk suka yi saurin cire hannuwan nasu suna sunne kai. Ya gyada kansa, yace, “Khalili, aje a nemo mini Mallam Khamis Ciro, a duk inda yake, a yanzu nake magana. A fada masa cewa ina son ganin sa. Karya bata lokaci Fulani babu lafia.” Kai yajinjina cike da girmamawa. Sosai yaji dadin aiken da aka masa. Ko ba komai zai daina shakar wannan mummunan warin da yakeji. a
Zirga-zirga take yi a cikin dakin nata. Tanajin yadda zuciyan‘ta ke mata radadi‘ da daci. Damuwa ta addabe ta, sai famar taunarebo takeyi tana kwafa. 
Tana cikin haka Zabbau ta iso gare ta. Rusunawa ta yi cike da girmamawa, tace
“Ranki shi dade an gama komai. Na gama tsara dukyadda za muyi mu fita a yau din nan. 
lzinin tafiyar kawai nakejira ” 
Murmushi’ Kursiyya ta saki, wanda takanjima ba tayi irinsa ba. In dai har aka ga tayi shi to 
tabbas ta aikata wata muguntar ne, ko kuma tana da niyyar aikata wa. “ “Babu wani abu daya rage wanda ya wuce in ganni a gaban boka Fartsi. ” Mikewa Zabbau tayi da murmushi shimfide a fuskarta. “Mu tafiyanzu?” Ta nemi’izinin Kursiyya. Kai tajinjina mata sannan ta duba madubi ta kalli kanta. Kyakkyawan kitson da aka matajiya ne barbaje harsaman goshinta, sannan kuma ga wani daya sauka bisa gadon bayanta. Wani karamin mayafi ta dora a bisa dakakkiyar mai kama da alkyabba. Sannan ta fesa turaruka masu kamshin gaske, tayi‘gaba Zabbau ta take mata baya. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]