[Advertisements⬇️]

GIMBIYA SA'ADIYA CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 1
Cikin takun kasaita take tafiya, yayin da dukkanin gabban jikinta suke motsawa, har zuwa lokacin da ta isa bakin kofar dakin mai martaba. Sanin kanta ne, dukkanin wanda zai shiga part din Sarki Sani wajibi ne gare shi ya cire takalmansa, haka kuma dole sai mutum ya janyo marufi ya rufe fuskarsa, tun daga kan mace har namiji. Wannan tsari ne, tun iyaye da kakanni. Girman sarautar ne yajawo haka, da kuma daukaka darajar sarakan nahiyar. A duk sadda Hafsa zata shiga bangaren Sarki jazamun ne sai tayi fada da masu kula da kofar sashen, saboda taurin kai da girman kanta. A yanzu ma abin daya faru kenan, tayi kokarin wucewa amma takubban da suka gitta su biyu ne suka zama garkuwa a gare ta, ta gagara shiga cikin dakin. Cike da masifa take kallon su, yayin da idanuwan ta suka kada suka yi jajur, tanajin kiyayyarsu na dada tsananta a cikin zuayarta. “Ranki shi dade ki mana gafara, amma ki daure ki cire takalmanki, ko da baki samu damar rufe fuskar taki ba. ” Kallon banza ta watsa wa wanda ya mata maganar, bata gama tunanin amsar da zata bashi ba tajiyo muryar dayan ya ce, 
”Ya kamata ace kin saba haka nan, ace kusan duk sadda zaki zo sai munyi rigima dake kan abu guda… .Tun bai rufe bakinsa ba yaji saukar matsiyacin mari a kuncinsa. Sannan ta hau murza yan yatsunta cikin bada umurni tana fadin, “Ni kake cewa wai ina rigima da kai? Ka yi kuskure! Ka tafka babban kuskuren da har duniya ta nade ba zaka taba daina dana sanin aikata shiba. Idan har a baya kun tausasa kalamanku yayin da kuke yimini magana na muku tsiwa, to banga abin da zaisa a lokacin da kuka fada mini munanan kalamai na kyale kuba. A yau din nan zaku bar aiki a nan, zaku koma cikin bayi, ku cigaba da bauta tamkar ba,a taba ‘yanta kuba. Kuma ku bani‘ wuri na wuce tun kafin na canza muku salon hukunci!” 
Jikinsu na karkarwa suka bata wuri ta wuce, zukatansu fal! da tsoron abin da zaije ya dawo. Sosai nadamar abin da suka aikata ya dirar musu, sai dai basu da yadda za suyi a yanzu kam, bakin alkalami ya riga daya bushe. 
Cikin isa take taku har ta karisa bangaren da mai martaba yake. Da sallama kunshe a bakinta ta isa gabanshi. Sai dai yanayinta kadai ya tabbatar masa da akwai damuwa a tattare da ita. “Hafsa ‘yan matan Umma da Abba. Hafsatutuna mai dadin suna. Ke dawa kuma?” Kara turbude fuska tayi tana sissinne kanta. Dafa kan nata yayi, ta yikokari tajanye har yanzu tana cuno bakinta. 
“Abba ban san me yasa ba, ni baka ce mini gimbiya. Koda yaushe sai dai ka rinka cewa 
Halimatu Gimbiya amma ni kake kira na da Hafsa Zlkau.” 
Murmushi ya saki sannan ya jawo ta ajikinsa tamkar karamar yarinya. A hankali ya rinka 
bubbuga bayanta. “Ai baza ki hada kanki da Gimbiya Sadiyya ba. Kin ga ita mahaifiyarta ta rasu tun tana jinjira. Sannan kuma ita ce karamarki. Ku biyu rak nake dasu mata, sauran duk maza ne. Yanzu wani abu ne don nace wa Sadiyya gimbiya ke bance miki ba? Duk daya kuke a wurina. ” 
Tabe bakinta tayi ba tare data bari ya ganiba. Ta taso daga kan cinyar tashi sannan ta Mika masa takardun hannunta. Tace”Abba gasu, Halimatu ce tace kace na kawo maka.” Karba yayi ya hau dubawa. “Ehh tabbas. Allah yasa dai kin gama dubawar.” Sosa kanta tayi cikinjin kunya tace”Na gama dubawa Abba. ” “To inajin ki. A cikinsu waya miki?” Ta dan dukar da kanta cike dajin kunya tace, “Yarima Abu Sufyan dan Sarkin Kubaisu.” Danjim, Sarkin yayi kafin ya ce, To, Allah yasa ya amince.don Yaron irin rikakkun yan boko ne. Yanzu haka ma yana kasar Italy a can yake karatunsa. Sai dai ban sani ba, watakila zai amince tunda har mahaifinsa ya aiko da sunansa cikin masu harin aurenki.” Lallausan murmushi ta saki, tanajin kaunar yeriman da bata taba ganinsa ido da ido ba 
har cikin zuciyarta. ‘ Sunjima suna fira da mai martaba kafin ta mike a kan kafafuwanta. Ta dan runtse idanuwanta, azuciyarta tana tunanin ta hanyar da za tabi wajen fada wa mahaifinta tana so a kori wayannan ma’aikatan na bakin kofa, su koma cikin bayi. ”Ya dai Hafsa?Akwai damuwa ne?” 
Kai ta daga masa alamar eh, sannan ta sadda kan nata kasa tana wasa da yatsun hannunta. “Dawo ki zauna to.” Tajiyo muryar mai martaba ya fada cike da kulawa. Babu musu kuwa ta koma ta zauna, haryanzu kanta na duke ta gagara hada ido da shi, hakan bai rasa nasaba da kwarjini na mai martaba, ba zata Iya hada ido da shi kuma tai masa karya ba, dole sai ta tona asirin kanta da kanta. “Uhm! Ke nake sauraro.” Ya fada cikin sanyin murya, yana son ta fito zahiri ta fada masa gaskiyar abin da yake damun ta. 
“Abba dama wa’yancan masu gadin ne, duk sadda zan shigo bangarenka sai su rinka ci min fuska suna yi mini rashin kunya a kan dole sai na cire takalmina. Wasu lokutan har tsawa suke daka min tamkar sa’arsu. Ko kadan babu Iadabi a tsakaninmu… Ba a nan taso ta dakata ba, sai dai daga yadda take maganar ta tabbatar cewa idanuwan mai martaba na kanta, duk da cewa ba kallon sa take ba. Duk sai ta samu kanta da tsarguwar kanta. Ta cigaba da sauraron abin da zai fito daga bakinsa. “Wannan ce matsalar kadai?” Kai ta daga masa tana tunanin tarkanta ya kama kurciya. Sai ta dan saki murmushi wanda bata san sadda ta sake shi ba. Tunanin kalarketar da zata wa bayin Allahn kawai take yi idan mai martaba ya bata dama. In don wannan ne, ki bari zanja musu kunne, kuma na tabbata zasu daina yi miki rashin kunya. Kema kuma sai ki kokarta ki daina shige musu. Ki rinka cire takalminki a can ba zai rage ki da komai ba. Wannan shi ne dokar shigowa bangaren sarki tun iyaye da kakanni. ” Tamkar an daba mata mashi a zuciyarta haka taji. Ta rasa wane irin hali mai martaba yake dashi. Tana mamakin shi din wane irin mutum ne da bai damu da tsananta mulkinsa ba. Cike da takaici ta mike tsaye, baki zunzure tamkar zata kai masa duka. ldanuwanta kuwa 
sun kada sunyi jajur kamar za tayi kuka.”Hafsa! ” Ya fada cike da mamakin yanayin data shiga cikin lokaci kalilan. “Hafsa wace irin magana ce zan miki da zata sa kiyi irin wannan mikewar da kika yi kamar zaki dake ni? Wai ke kam wace irin yarinya ce wacce sam bata san darajar Iyayenta ba? Kin kawo karar wasu a kan suna miki rashin kunya, ke kunyar kike da ita? Karamar yarinya Gimbiya Sadiyya ta fiki kunya. Ta fiki sanin darajata. Ta fiki sanin darajar mutane. Duk da cewa bata kasance yarinya mai farinjini ba, amma hakan baya hana ta kyautata wa kowa. Shekarunki nawa? Shekarun Gimbiya Sadiyya nawa? Ki nutsu Hafsa, ki san me kike yi. Shi yasa kikaga ina fifita ta a kanki. Saboda ta fiki kyawawan halaye.” ‘ 
Suna cikin haka saiga wata kyakkya war mace ta fito cikin takun kasaita. Sanye take da wani dakakken lace kalar hanta, ta yafa wani tafkeken mayafi mai kama da alkyabba. Hango matar da Hafsa ta yi yasa ta gaggauta isa gare ta, hade da fasa kuka maikarfi ta fada jikinta. ‘ Zara-zaran hannuwanta ta mika ta rinka tattaba matar, yayin da ita kuma matar ta hakikance har da gyara juyi tana barcinta. Sake zura hannunta tayi ta tattaba matar, sai a lokacin ta bude idanuwanta tana tunanin kalar rashin mutuncin da zata sauke ga koma waye yake tada ta daga daddadan barcin da take yi. 
Mitsittsikar idanuwanta ta hau yi har suka gama budewa. Zabura ta yi a lokacin da taga mummunar halitta tsaye a gabanta. Gashi barbaje a kanta wanda ya sauka har bisa gadon bayanta. Idanuwanta sun hade wuri guda ba a ganin kwayar idon sai baki-kirin da suka yi. Labbanta a tsattsage tamkar an saka reza an yayyanka su. Baki daya fuskarta ramummuka ne wani wuri ya lotsa wani wurin kuma yayi tudu. Karkarwa jikin waccan matar ya hauyi, ta sunkuyar da kanta kasa, tana tunanin ko wace 
irin halitta ce a gabanta? 
“Kin cuce ni Kinci amanata Kursiyya!! Ba zan taba yafe miki ba har abada. Kamar yadda 
kika illata rayuwata, kema sai taki rayuwar ta illata. Sai kin yi dana sanin sani na a rayuwarki. Sai kin yi dana sanin zalunta ta da kika yi.” Cikin wata irin murya ta yi maganar, ita ba muryar maza ba, ba kuma ta mata ba. Ga 
maganar tana yi tana ciccije bakinta, har ta samu ta karisa kalaman da kyar. Har a lokacin Kursiyya bata dago kanta ba. Jikinta bai daina rawa ba saima tsananta da yayi. Bata san me zata fada ba, kamar yadda bata san ko wace ce a gabanta ba. Mutanen data zalunta din suna da yawa Atarihin rayuwarta, ba zata taba kidanye adadin mutanen da taci zalunsu ba. ‘ 
“Ke da farin ciki kun yi hannun riga Kursiyya. Ke da rayuwa mai dadi har abada. Dole ki dandani azaba kamar yadda kika azabtarda ni. Dole kiji yadda mutum keji a lokacin da aka mayar da shi mutum-mutumi. Zaki shiga rayuwar kunci, kamar yadda kika sa nima na yi rayuwar kunci na tsawon shekara goma sha biyar, ke kuma kika ci gaba da rayuwarki mai dadi. Ni bazan yi mai dadin ba, saboda kin riga kin gusar mini da shi tun ina cikin cikin mahaifiyata, har lokacin dana shekara goma sha bakwai a duniya, kika karisa lalata mini rayuwa. Na san bani da mamora a yanzu. Na san rayuwata ta riga data gurguntaka, ba kuma zata taba gyaruwa ba har abada. Sai dai hakan ba shi bane zai hana ni daukar fansar abin da kika mini ba Fitowa ta daga cikin kwalba daidai yake da gushewar rayuwarki. Kinyi kuskure! Kin tafka babban kuskure Kursiyya, na butulce wa boka Fartsi. Kinfi kowa sanin halinsa, saboda ba,a kaina ya fara yi miki aiki ba. Ina son ki sani, da goyon bayansa nake tsaye a gabanki yanzu haka. Da goyon bayansa zan dauki fansa daga gare ki.” Tana gama fadin haka ta kyalkyace ta wata irin mummunar dariya mai kara. Sai dai ko 
kadan fuskarta bata nuna alamar dariyar ba. Sai gangar jikinta dake motsawa da karfin gaske
Hmm Taflyar tamu ta kwan-gaba kwan-baya ce. Fatan za ku fahimci komai har zuwa sadda zai 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

daidaita ayi mikakkiyar tafiya.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]