[Advertisements⬇️]

BAKIN DARE CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Tue. May 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BKIN DARE 
CHAPTER 1
Hajiya Nafeesa a zaune take atsakiyar’yayanta Saiam Safna Suhaima Sahiba da Auta Samha Saiam itace first born sai mai
binta Safna sai Suhaima Sahiba da Auta Samha Hajiya Nafeesa yaranta duka mata ne Allah bai bata da namiji ba tana bala’in
San ‘yayanta sosai dan bata da burin daya wuce taga ta faranta musu rai zata iya yin
komai akansu Asalinsu ‘yan gombe ne ita da mijinta haifaffun can ne Aiki da Alhaji Nazifi keyi a Abuja ne yasa suke zaune a
Abuja acan duk ta haifi su Saiam sun taso cikin rufin asiri da sutura ta ubangiji Dan
babu laifi za’a iya saka su asahun masu kudi akwai soyayya mai tsafta atsakanin
iyalan da kaunar junansu most especially yaran Dan Kansu a hade yake sosai Dukkansu da Hajiya
Nafeesa suke kama dan Hajiya Nafeesa fara CE kyakyawa idan ka ganta bazaka yarda ita
ta haifesu ba dan karamin jiki ne da ita Samha ce kawai bata dauko hasken fatar taba kamanninta ya fita daban Dana ‘yayyenta
dan ita kalar Alhaji Nazifi ta d’auko ita ba baka ba ita ba fara ba abinda ake cewa madarar Kyau Samha Allah ya bata Dan tafi
su Saiam kyau sai dai su gaya mata hasken fata da gashi su Kansu wani zubin suna
admiring kyawunta ga diri dan ita yar duma duma ce bata fiye tsayi kamar su Saiam ba Hirar bikin Saiam da Safna da ya rage sati
uku sukeyi cikin nishadi inda suke ta tsara abubuwan da zasuyi a bikin Saiam da Safna
murmushi kawai suke yi suna kallon
Suhaima da Sahiba dake ta tsara yanda bikin zai kasance Hajiya Nafeesa kuwa nata
biye musu tana shafa kan Samha da tayi pillo da cinyar ta kananan kalaban dake kan Samha take ta shafawa Samha kuwa ta lumshe idonta dan tana jin dadin yanda
Hajiya Nafeesa ke wasa da kalaban kanta dan har wani bacci bacci taji yana Neman daukanta dukansu sanye suke da kayan bacci dan Sun kwanta Hajiya Nafeesa ce tazo duba su daga nan kuma ta zauna suna hira
Saiam kallon Hajiya Nafeesa tayi tace”Mummy kije ki kwanta idan kika biyewa su
Suhaima tsaf zasu rike ki da surutu dan ba gajiya zasuyi ba yanzu fa sha daya da minti
biyar”Hajiya Nafeesa daga kanta tayi ta kalli agogon dake jikin bangon dakin ta dawo da
kallonta kan Saiam tace
” Barni musha hira da ‘ya’yana sha biyu naje na kwanta”
Safna cewa tayi “Mummy yanzu Daddy kawai kika bari a bangarenku gaskiya nidai kije ki taya shi hira koni naje na taya shi”Dariya Hajiya Nafeesa tayi tace ” sai kiyi sauri kije ai Daddynku ya Dade da bacci”
Murmushi sukayi su Suhaima kuwa suka cigaba da hira
Hajiya Nafeesa haka kawai taji gabanta yayi wani irin mugun faduwa ahankali ta sunkuyar dakai tana karanta Innalillahi wa
inna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fil musibatiwa aklifnin khairin Minha
Sahiba da Suhaima shiru sukayi suna kallon Hajiya Nafeesa
Gabanta cigaba da Faduwa yayi tana ta sallati a zuciyarta ahankali taji gabanta ya rage fad’uwar dagowa tayi ta kalli su
Suhaima dan Saiam da Safna sun Dade da bacci Samha ma bacci ya d’auketa

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]